Showing 3001 words to 6000 words out of 47874 words

Chapter 2 - Mijin Marainiya Book Complete Hausa Novels by Fadila Lamido .pdf

16 Mar 2025

4092

karamin hijjabin dake jikin ta safna ko kuka take
tana kokarin guduwa amman Ina sun riga sun rike ta dukkan su ukun har sun yaga mata riga
dama bawani kwari ke gare suba suna kokawan kwance mata zani .

wan,nan motar ta dazun ce ta sake dawo ,mutun daya ne acikin ta sabani dazun da suke
su biyu jin uhun yariyar yasa shi tsayawa ya haska su da fitalan motar yaga abinda ke faruwa
da sauri ya fito yafara takawa zuwa wajen yana musu tsawa cikin fada ya daga murya sosai .

daya daga cikin su yace kai kuzo mu gudu yaya abduljalal ne da gudu suka kwasa
abduljalal ya matso kusa da ita ya tsoguna ya dauko hajjabin ta ya mika mata ta karba ta saka
kuka kawai take abduljalal yace yanzun ina zaki?

tace goggo nace tabar agun wata bishiya tace na jirata kuma naga ta dade bata dawo ba,
sheni na biyo hanya ko zan ganta.
cikin mama jalal yace kina nufin mahaifiyar ki kece abarki a titi.

a,a kishiyar mama tace.
yace to ke ina mamar ki?
cikin kuka tace suyi hatsari har baba na sun rasu.
Jalal ya tausaya mata sai dai har yanzun be gama yar da, da yarinyar ba yana ganin kamar
dai ta fito yawo ne, ya juya yace Ina yan uwan ku suke,
tace nibasan kowa daga cikin dangin muba kakata kawai na sani itama ta rasu jiya akayi
bakwai, shine akace ma goggona takaini gun dangin kakata, shine ta barni tace najira ta
tadawo.

hankalin jalal ya tashi ya rasa yan zun ya zai yi da yariyar nan gashi dare na dadayi ,

zuwa yayi yabude motar sa ya shiga da gudu safna ta biyo shi tana fadin dan Allah karkabar ni
anan.
ai bazan barki a nan ba ya bude dayan gefen yace shiga mutafi , bayan tashiga ta zauna
jalal yace ya sunan ki?
tace sunana safna.

Jalal ya sake maimaita sunan safna da sauri yafara neman fitilan motar haske ya baiyana
yace safna bake bace shekarun baya na saya rake wajen ki, dama ke ma rainiyace.
cikin kuka tace eh.
Yace to kibar kuka safna insha Allahu zakiji dadin rayuwan ki , jan mutan yayi ya fara tafiya
yana tunani yadda zasu kwashe da ummin sa.

lokacin da ya isa gida me gadi yabude mai ya shiga yarasa yadda zaiyi da safna dan yasan
yanzun ummi batayi bacci ba saitaga dawowan shi , kilama yanzun tana kallon shi, dan haka
dibara tafado mai yace safna inazuwa bari naje nadawo.
cikin sauri safna ta rokoshi tace dan Allah karka gudu ka barni kaima.

cikin kwatar da murya yace bazan guduba safna yanzun zan dawo ai nan gidan mune da
guduwa zanyi ai bazan shigo dake cikin gidan muba, ban so ne ummi na ta ganki daddaren nan
saboda kartayi wani tunani daban kuma nasan tananan tana jiran shigowa ta, sabo da haka
kijirani yanzun nan zan dawo. Gyada mishi kai kawai tayi amman bata son ya bar ta anan.

yana shiga ya samu ummi sai zagaye falon take da sauri shi yaje ya rungume ta, hannu ta
tasa ta tukude shi.
abinda kuma zaka fara kenan yawon dare Ina ka tsaya har 1:30 shiyasa babanka yake
cewa ninake sangarta ka.
tsugunawa yayi ya kama kafar ta yace immi kiyi hakuri kabir ne be fito da motar saba sai
da nakaishi gida kuma ummi kisan gidan su da nisa amman ummi dan Allah kiyi hakuri bazan
kara ba.
hannun ta tasa ta dago shi ta rungume tace jalal dole hankali na ya tashi kaikadai nake
kallo naji farin ciki ya lulubeni nazaci kai kadai ne kwaina a duniya sai daga baya Allah ya kawo
mana Kairat alokacin dana cire tsanmani kuma har yanzun baji sonka ya ragu azuciya taba,
jalal nakosa naga matarka zataga gatan da babu wacce ta taba samu a gurin sirikar ta, balle
kuma naga yaran ka.

dukar dakai yayi yana murmushi , ummi tasake cewa jalal baka fara tunanin aure bane har
yanzun.
da da durkusar dakanshi kasa yayi yana sosa keya.
ummi tace yau kuma kunya ta kakeji , hmmm jalal mayan kasan, abin da nake so dakai in
katashi nemu mata kasamo mana yar manyan mutane kar ka sake kawo mana yar matsiya ta.

07014197556
[9:30PM, 11/24/2016] Fadeela lamido: í ½í²˜í ½í²í ½í²MIJIN MARAINIYAí ½í²í ½í²í ½í²˜


Story
&
Written
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed

10-12

jalal ya dago ya kalli ummi yace ba komai ummi karki damu, ummi bari naje na kwanta tace to
ba damuwa Allah ya tashi mu lfy,mikewa yayi yanufi hanyar dakin shi ummi ta bishi da kallo
tana murmushi har ya Kule.

shiko jalal ko dakin shi be shiga ba yabi ta kofar baya ya fita, ya bude murfin mutan yaga
safna tayi zuru zuru roko mata hannu yayi suka shiga ciki ya bude dakin shi suka shi , yace
kinaji yunwa ne?
tace a,a .
to ga bayi nan kishiga kiyi wanka inki fito kisaka wannan rigar yanuna mata wata karamar rigar
shi.
in kin gama ki hau gado ki kwanta da safe zan shigo karki sake ki fito.

futowa yayi falo ya kwanta
washe gari jalal najin kiran sallah subahi ya mike ya shiga dakin ya tashi safna dake bacci
akan makeken gadon shi, sannan ya wuce masallaci.

bayan safna ta idar da sallah tana zaune kan darduma, taji anturo kofar da karfi , wata yar
yarinya ta gani ba zata wuce shekara biyar ba , tana fadi yaya jalal jiya inata jiranka har nayi
bacci baka dawo ba ,waige waige ta fara da safna su kai ido hudu dan haka ta saka kuka ta
juya aguje tafita adakin, tana fita sukaci Karo da jalal , yarike ta yana fadin me ya sa meki ?
dakin ka naji neman ka ban gan kaba sai wata aljana nagani .
Jalal dariya yayi sosai sannan yace ba aljana bace anty ki ce na kawo miki amman karki
gayawa ummi.
da sauri tace sabo da me baka son ummi ta sani.
saboda bana son ummi ta koreta koke kina son ta kore ta.
a,a to yaya matar kace.
a,a kairat itama kanwa tace kamar yadda kike kanwata , janta yayi suka shiga cikin dakin.
lokacin safna na zaune abakin gado tayi tagumi.

ya dade tsaye akanta bata masan ya shigo ba.

sai da safna ta kwana uku ummi bata san da zuwan ta ba.

ummi ko na lura da jalal baya kwana dakin shi kuma yanzu baya cin abinci sai dai yakai
dakin shi , sabanin da yana ci yana sha gwaba, dan haka tace azuciyar ta koma me yake baye
mata yau zata gain.

yauma kamar kullum jalal ya dauke abincin shi ya nufi dakin sa ummi na kallon shi, tana
nan zaune har ya fito, binshi da kallo kawai take, ya dade zaune ya mike yace ummi sai da
safe, to kawai tace dashi.

Yashiga kenan ya zauna yaji anturo kofar , razana yayi ya mike yana fadi ummi lafiya, ummi
bata bi ta kansa ba zuwa tayi ta dago safna dake kwance akan gadon jalal tayi wurgi da ita.

jalal ya mike da sauri ya daga ta yasa ta ajikin shi yana rarashin ta dan har ta fita hai yacin
ta.

ummi ce ta kara matsowa cike da mamaki tace yaro Ina kasamo yarinya har ka ajeta
adakin ka ban sani ba.
kallon shi tayi taga yasa ta a kirjin sa , sai faman rarrashin ta yake, cikin daga murya tace
jalal kaine ka kawo min karuwa har cikin gida kasata a kirjin ka agabana dan ka nunamin kai
tantirin dan iska ne ko?

cikin sauri ya sake safna yace ba haka bane ummi wlh ummi ban taba zinaba kuma wlh
safna ba karuwa bace marainiya ce bata da uwa bata da uba kuma abin da yasa na kasa
gayamiki nasan bazaki fahimce ni ba ne.

ummi tace shi yasa ka muna fun ce ni , to maza maza ka tarkata ta ka fitar min da ita agidan
nan, dan kaga na kwalfa rai akanka shine zaka neme ka watsa min kasa a ido , kasani sarai
bana hada guri da talaka.

abduljalal yace to naji zata fita ummi amman nima bazan xauna ba zan je na nemar mata
gurin da zata zauna tunda mu arzikin mu talaka bazai amfana da shiba.

cikin taga murya tace ni kake mayarwa da magana akan wata banzan yarinya, to katafi
din in baka tafi ba karai na Allah kuka tasa harda kururuwa yau ga dan ta na cikin ta yana
mayar mata da magana, tace indai ko kabi yarinyar nan Allah ya isa nono na ?da kasha.

Jalal ya zaro ido yace ummi abin har yakai haka, to shi kenan ummi na hakura ke safna
tashi ki tafi , safna tana kuka ta mike ta fita daga dakin.

Jalal ma tsugunawa yayi ya soma kuka yana fadin ummi,ba ta san kowa ba fa , kuma
bata da inda zata ummi marainiya ce fa , ummi ko gezau bayi ba.

suna cikin haka suka ga alhaji mustafa rike ta safna ya shigo har dakin abduljalal, ummi
da sauri tace alhaji shine bayi waya kana hanya yau ba sai dai kawai muganka.

jalal mikewa yayi yakoma jikin dady ya kwanta alhaji yace wanan wacece na ganta
Waje tana kuka .
cikin sauri ummi tace bamu santa ba.

alhaji yace karya kike yi zaliha duk naji abin da ya faru wai kece kike kin talaka dau la
yasa kin manta asalin ki, to tun da kin manta bari na tuna miki
[9:07PM, 11/25/2016] Fadeela lamido: í ½í²˜í ½í²í ½í²MIJIN MARAINIYAí ½í²í ½í²í ½í²˜


Story
&
Written
Fadeela Lamido
Mmn yazeed


13-15

ummi kuka ta fara ta fita adakin da sauri ta shige nata dakin.

alhj ya kalli abduljalal yace akan wannan har kake zubar da hawayan ka, meyasa tunda kaji
kana son ka tai maketa baka kirani awaya ka gaya min ba, kar ka kara zubar da hawayen ka,
bama wannan yariyar ba duk wanda kake son ka tai maka ma kamin magana kabar biyewa
ummin ka kaje ko.
jalal kwanciya ya da da yi ajikin daddy yana murmushi.
alhj ya sake cewa jalal zamu zauna tare da yarinyar nan zan sata makaranta zan riketa kamar
yarda na hai fa idai har zakai farin ciki da hakan, amma da sharadi guda daya, sai nayi binkece
na tabbatar maganar da yarinyar nan ta fada gaskiya ne.

Jalal tsuguna wa yayi yana ma alhj godiya tare da amicewa da maganar alhj.

har alhj ya fita ya dawo ,yace jalal raka yarinyar nan dakin kairat, kar na sake ganinta a
barayin ka.
cikin sauri jalal ya amsa , haka yakai safna har dakin kairat ,kairat batayi bacci ba dan haka
taji dadin ganin anty safna a dakinta.

bayan alhj ya shiga dakin ummi ya same ta tana zaune bakin gado tana share hawaye,
kusa da ita yaje ya zauna ya dafata yace zaliha meye kuma abin kuka.
dole nayi kuka alhj naga kana neman ka tona min asiri agaban dana har da wata bare,

wadda bamusan asalinta ba, kuma ni din da kake neman wulakantani ai a gaban iyaye na gaje
ka aure ni, kuma duk gorin da zaka min nasan be wuce kace ka ganni ne lokacin da nake kora
shanon mahaifina ruga ba har kaji kana sona , ai baza a hada da wannan banzan yarinyar ba,
kuma ni abinda yafi damu na kar fa jalal yace son yarinyar nan yake dan nikam ko zanyi yawo
tsirara bazan bari yaro ya aure taba.

alhj ya gama sauraran ummi cike da mamaki yace zaliha kina bani mamaki to meye a ciki
dan yace yana son ta, ni dai na dauki alkawarin zan riketa kamar sauran yarana, kuma kema
inason kireta kamar yar da kika haifa.

ummi tace naji zan riketa amman sai dai in jalal yayi min alkawarin ba aure tsakanin shi
da ita.
Hmmm zaliha kinan dai akan bakan ki kenan yanzun kuma amiki magana kice ammiki gori,
to shi jalal din da kikace sai yayi miki alkawari bazai ce zai aure ta ba, yasan gaibu ne, be
saurari me zata sake cewa ba ya fita adakin afusace.

ummi kasa bacci tayi dan haka washe gari da safe ta nufi dakin jalal ta same shi kwance
akan gado ya najin shigowan ta ya miki, kusa dashi taje ta zauna yace ummi dama yanzun
nake shirin nazo na ganki nasan kina fushi dani ummi safna abin tausayi ne , tausayin ta ya
kamani. cikin dibara ummi tace na fahimceka jalal komai ya wuce safna zata zauna tare damu
amman da sharadin nan gaba baza kace zaka aure taba

dariya sosai jalal keyi cikin dariyar yake fadin haba ummi dama akan haka kike tada
hakalin ki , idai wannan ne ki kwantar da hakalin ki , ummi me zanyi da safna ga haddadu babys
a gari haba ummi ni wlh ummi kin ma bani mamaki yama za ai haka ta faru.

ummi ji tayi zuciyar ta fes tundaga ranar ta fara jan safna ajikin ta, hakalin safna ya kwan
ta ta koma makaranta ita da Kairat suke ta fiya .

akwana atashi gashi yau safna kusan shekaran ta daya da wani abu agidan jikin ta yayi
kyau ya murje tayi fes in kasan safna ada kagan ta yanzun zaiyi wuya ka iya shai da ta, fari tayi
sosai har nema take ta wuce ummi a fari ga gashin har gadon baya ga cikar halitta ummi
ayanzun inta kalli safna har mamaki abin yake bata saika rantse yar wani hamshakin mai kudi
ce.

shiko jalal rabon shi da ganin safna yama manta dan tunda ya lura ummi bata son ya
rabeta ya rege shiga barayin su gaba daya saidai jefi jefi yakan shiga amman allah besa sunci
karo da safna ba, sai dai yana samun sakon gai suwata agun kairat dan kulum sai taje dakin sa
kuma tana shiga zata ce yaya anty safna na gai da kai hakan na mishi dadi.
itako ummi tunda ta lura safna kyakyawa ce murna ta kamata lallai ta samu jari dan haka
tafara hada ta har ka da yayan manyan mutane dan acewan ummi safna matar manya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login