Showing 39001 words to 42000 words out of 47874 words

Chapter 14 - Mijin Marainiya Book Complete Hausa Novels by Fadila Lamido .pdf

16 Mar 2025

4103


safna?
dadi sosai jalal yaji yace lafiyar ta lau tare muke tana falo.
alhaji fada ya farawa jalal yazaka bar ta afalo saikace wata bakuwa jeka shigo da ita.

jalal zuwa yayi ya riko hannun safna suka shiga falon alhaji bayan ta gaida alhaji ta juya ta
gaida ummi ta amsa ba yabo ba fallasa.
ummi kara kallon safna tayi sosai gani tayi takara cika tayi kyau sosai cikinta harya fara fitowa,
juyawa tayi gurin jalal ta fara janshi da hira harya fara sakin jikin shi.
sai yamma su safna suka bar gidan su ummi jalal sai washe hakora yake .

kwanci tashi ba wuya gashi har cikin safna ya isa haihuwa suna jiran haihuwa ko yau ko gobe ,
komai sun tanada anty nusaiba na kula da safna sosai dan akai akai take zuwa dubata da tace
ina son kaza anty nusaiba saita nemo

itako ummi ta rage nuna tsanar safna afili jalal kuwa jitake kamar ta hadiye shi, babu abinda
yake damun ummi ayanzo ila rashin samun yar da saudatu ta bari .

safna ce ta fito daga daki tana fiya daker, har ta isa gurin jalal tana zama ta kalli jalal dake
kwance ya rufe ido, taba shi tayi tace yaya ka tashi nasan idonka biyu.
tashi yayi ya zauna yace safna nasan maganar muguwar matar nan zakiyi min, ni kuma bana
sojin ko sunanta.
[7:06PM, 12/20/2016] Fadeela lamido: í ½í²˜í ½í²í ½í²MIJIN MARAINIYAí ½í²í ½í²í ½í²˜



Story
&
Written
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📊

106-108


safna kasa tayi da murya tace yaya dan Allah kayi hakuri ka kaini inason naga nima ina da 'y an
uwa kamar kowa kaga ko badan goggo ba kodan yaya iro da salame ai naji .
kara daure fuska yayi yace yan zon kina nufin harkin manta da wula kancin da mahaifiyar su
tamiki toh bazaki ba indai nine mijinki bazaki wajen wannan muguwar matar ba idan ma kina
tunanin ni zan kaiki toh kima cazan tunani dan wlh bazan jeba, waima me kike nema awajen su,
me kika nema kika rasa da zaki nace sai kinje wajen su? kuka safna ta fara tace yaya yan uwa nane fa, bani da kowa fa sai su

kara kulewa jalal yayi ya fara magana cikin fada baki da kowa saisu ko, haka kice ko, ni ma ba
komai bane awajen ki ko, duk abin da ake miki baki gani, kin raina ko?
a,a yaya ba haka nake nufi ba nidai kawai inason naje naga yan uwa na dan Allah kayi hakuri
ka barni naje.

Jalal kara daukan zafi yayi yace wlh safna idan kika kara cemin 'yan,uwan ki saina mareki
susan tarajar kine suka wurgar dake a titi.

safna ta kara fashewa da kuka tace yaya gori kuma kake min?
eh ammiki gorin kiyi abinda zakiyi wawiya kawai mara wayau.
safna daki ta nufa cikin matsanan cin bacin rai taita kuka.
shikuwa jalal bayan ya gama fadan gidan ya bari sai dare ya dawo, ya samu dakin safna rufe
dakinshi ya wuce dan yasan fushi take.
Washe gari bayan ya gama shir yawa ya fito yaga falon na nan yadda yake yagane safna fata

fitoba ji yayi babu dadi a zuciyar shi ya isa bakin kofar yayi ta bugawa taki budewa hankalin shi
ya kara tashi waryar shi ya ciro ya dannan number daddy yana dauka ya fara fada mai safna ta
rufe daki tun jiya taki budewa.
alhaji yace wani abu ya farune ko kunyi fada ne?
shiro jalal yayi bece komai ba dan ya tuna kargadin daddy akan safna.
Alhaji yace jalal baka da gaskiya kenan, bari nakira safna.
safna dake zaune adaki taci kuka ido duk sun kunbura taji ankira wayar ta tana dubawa taga
daddy ne tasa wayar akunnen ta tana kuka ahankali alhaji yace safna me ya faro ne, jalal ne ko,
gayamin me yayi miki?
kasa magana tayi ta kara fashewa da kuka.
alhji yasake ciwa jinan safna daina kuka bakisan wannan kukan zai iya miki ila ba, tashi maza
ki shirya ya kawaki koma me yayi miki zanyi maganin sa, kinji ko.

jalal na zaune amota safna ta fito ya kalli fuskarta yaga tayi jawur saboda kuka dogowar
rigace jikinta da hajjab madaidaici .
suna isa ta bude motar ta fita , ta samu alhaji shida ummi afalon ummi ta mata wani irin kallo,
zamatayi akasa ta gaida su, suna cikin amsawa jalal ya shigo alhaji yace kai jalal baka da
hankali ko, waya gaya maka ana tayar ma me ciki da hankali?
shiro yayi yanemi guri ya zauna.
Alhaji ya kara cewa ina murna zan samu takwara ko mata zaka mana sa... be karasa maganar
saba ummi tace Allah ya kiyaye karku sake kusa sunana dan ni ba sa,ar wasan ku bace asa
mata sunan uwar ta amman bani ba.
safna ta daga jajayan idanun ta, ta kalli ummi ta fashe da kuka, tare dajin matsanan ciyar
tsanan ummi azuciyar ta .
alhaji yace zaliha tashi ki bamu guri tunda ke ba,a magar hakali dake.
tana tashi alhaji yace safna gayamin me jalal yayi miki?
Cikin dashashiyar murya ta gawa alhaji abinda ya faru.
alhaji yace ah ah jalal yayi laifi sosai toh kai jalal banda abinka haka akeyi ba yafiya, tunda
tace tanason ganin su aisai kayi hakuri ko baka so kabarta taje, itama ta hakura ta yafe bare
kai.
sai alokacin jalal yayi magana daddy ai itama dan bata da hankali ne shiyasa ta yafe.
murmushi alhaji yayi yace jalal ai wannan abinda tayi shine hankalin abun da kawai ban yadda
tashi ba tafiya da ciki dole kiyi hakuri har ki haihu nida kaina zan sa akai ki, kai kuma ka kiyaye
bakin ka inrai ya baci hankali baya gushewa, haka alhaji yayi ta musu nasiha sannan yace
kutashi kuje gida. tana mikewa jalal yace zomuje muyiwa ummi sallama haka safna tabi bayan shi badan ranta
yaso ba.
sun sami ummi zaune abakin gado tayi ta gumi jalal yace ummi zamu tafi tace ku gaida gida
safna ta juya zata fita ta daga kai taci karo da tangamemen hotun iyayen ta tana rike ahannu
su, daga hannun ta tayi sama tana nunawa jalal , yaya kallah bata karasa ba jalal yaga tana
kokarin faduwa [6:51PM, 12/21/2016] Fadeela lamido: í ½í²˜í ½í²í ½í²MIJIN MARAINIYAí ½í²í ½í²í ½í²˜

Story
&
Written by
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📊

​ *dedicate*​
​​dis page to
hajiya amina lamido Kilishin yammaí ½í±í ¼í¿»


*gaisuwa agereki*
*Aysha mazoji* *marubuciyar*
*Zaheedah*
*Jaleelah*
_The boss wife_

​
109-1012


Da sauri jalal ya tare safna ta fada jikin shi, ganin inda safna keta nuna hoton yasa ummi ta zaro
ido ta mike tazo kan safan tana fadin kar dai ace safna yar saudatu ce, jalal be saurari me ummi
take fada ba kiran sunan safna kawai yake amman shiru babu amsa ummi ce ta lura jini na
zuba ta kasan safna da gudo ta fita tana fadi alhaji dauko mota safna babu lfy .

da ummi da jalal ne suka kinkimi safna suka sakata amota, jalal ya fita haiyacin shi ummi ko
kamar mahaukaciya sai fifita takewa safna da gyalen ta,
bayan sun isa asibitin aka shiga da safna ciki jalal yaso ya shiga suka dakatar dashi.
Komawa gefe yayi amman ya kasa tsayuwa guri daya sai naushin hannun shi na hagu yake
da hannun shi na dama.
ummi kuwa tunani ne ya dame ta dan haka ta matsa kusa da alhaji tana share zufa tace alhaji
kasan abin da safna ta gani ta shiga wannan halin, hoton saudatu ta gani.
da sauri alhaji ya mike ya cire hular sa ya fara fifita da ita ya na zaware kamar yadda jalal
keyi, ummi ta mike tabi bayan shi tana kokarin magana alhaji ya dakatar da ita karki ce komai
kibari muga lfyr yarinya tukuna.
komawa tayi ta zauna zuwa cen ta sake mikewa.
daga cen su kaga an turo kofar Dr sulaiman ne ya fito dasauri alhaji yabi bayan shi, jalal ma
mikewa yayi amman alhaji ya waigo yace koma jalal.
bayan ya shiga Dr sulaiman yace alhaji haihuwa ce sai dai muna tunanin yariyar bazata iya

haihuwa dakan ta ba sakamakon jinin ta ya hau sosai saida kuyi ta mata andu,a .
haka alhaji ya fito jiki babu kwari jalal ya mike yace daddy mutuwa tayi.
a,a jalal tana nan daran ta haihuwa ce amman jalal kayi ta mata andu,a Allah ya rabasu lfy .
jalal be yadda da abinda daddy ya fada ba dan haka ya fara share hawaye.
alhaji yakira anty nusaiba yagaya mata halin ta suke ciki nan da nan saiga su ita da matar
baba salisu suna rike da kayan baby ganin ummi agurin abin ya basu mamaki.
2:46pm sukaji safna tayi kara mikewa jalal yayi zai shiga anty ta rike shi ta bude baki zatayi
magana suka sake jin wani ihun, wannan karon sai da alhaji yasa hannu suka iya tare shi, yana
fadi daddy kuka fah takeyi haka sukai ta bashi baki juyawa yayi ya fita yasamu wani dan dutse
ya zauna yata share hawaye. yana zaune agurin anty ta fito da gudu tana dariya jalal albishirin ka.
mikewa yayi yana kokarin share hawayen shi yace anty ta haihu ne?
Jalal mu godewa Allah safna ta sauka lfy mun samu yan biyu.
jalal ya zaro ido yace anty da gaske cikin sauri ya nufi ciki ya same su alhaji sai dariya suke
alhaji ya dafa jalal yace jalal kuka ya kare ko?
kunya ce ta kama jalal yayi kasa dakai yana murmushi yace daddy wai da gaske yan biyu
ne?
alhaji yace 'yan buyu ne jalal mace da namiji kana mamaki ko, ikon Allah kenan.
bayan angama gyara jarirai aka basu damar shiga ummi ce kan gaba tana shiga ta sauke
idanun ta akan safna da sauri ta rintse ido gurin ta ta nufa takira sunan ta taji shiru, alhaji yace
zaliha kirabu da ita kila bacci takeyi daidai lokacin nusaiba ta dauki macen takalle ta sannan
tamikawa alhaji tace yaya ga matar ka ta juya zata dauki dayan ta ganshi hannun matar baba
salisu haka suka taro suna kallon yaran gwanin ban Sha,awa.
Shiko jalal gurin gurin matar sa yake son zuwa amman ummi tana jikin gadon dan haka ya
kasa zuwa wajen.
alhaji ne yace jalal yanaga ka koma gefe kazo kaga yaran mana.
sosa kai yayi ya kalli safna yace daddy ina zuwa.
alhaji ya fahimce shi yace kazo ka gansu mana safna ai bacci take.
da saurin sa yace daddy ba bacci take ba idon ta biyu.
sai da alhaji ya kalli safna sannan yace zaliha fito daga nan gurin.
cikin sauri ummi ta fito daga gurin duk arude take so take kawai safna ta tashi .
Jalal yana isa gurin ya duka yanawa safna magana cikin kunne zuwa can ta fara magana
ahankali cikin kuka, jin safna na kuka yasa duk suka maida hakali gurin su, amman basajin me
suke fadi, jalal ya dago hankalin shi atashe ya kalli ummi ya hada rai.
ummi ta tsargu tace jalal me safna tace maka.
yi yayi kamar beji ba ya mikawa alhaji hannu ya bashi yaran ya kure su da ido.
lokacin da aka sallame su ,alhaji yace awuce da ita gidan hajiya motan jalal ta shiga su anty
nusai ba ma haka.
hajiya ta tare su da murna nusaiba ta mika mata yaran ta kalle su tace ikon Allah ga jalal ga
safna , hajiya fatima ta shigo rike da safna ta zaunar da ita akan kujera jalal ma ya shigo dauke
da kaya ya ajiye agefe hajiya ta kalli jalal tace yaya haka kuma jalal menene haka kaida ka
samu karuwa kuma menene naka na hada rai, ta kalli safna tace au kema kuka kikeyi toh abin
naku bana lfy bane

anty tace jalal nima nakula akwai abun da yake faru har anty zaliha ma akwai abun da yake
damun ta ko kallon yaran batayi ba
hajiya tace tunda sunki mgn ku kiramin alhajin har zalihar ,wannan ai iskanci ne Allah yayi
muku kyauta kuzo kuna tur bune mana fuska.
suna cikin haka alhaji ya shigo ummi na bishi abaya hannu ta rike da wanan huton.
bayan sun zauna hajiya tace nifa kun sani aduhu wai me yake faruwa ne?
alhaji yace hajiya wani babban al,mari ne yake shirin faruwa ya karbi huton ahannu zaliha ya
mikawa hajiya yace wannan haton safna ta gani kawai sai gani sukayi ta fadi shine muke
tunanin ko ta sansu ne .
hajiya kallon huton tayi tace wannan ai musa ne.
alhaji yace hajiya wani musa kuma ?
tace musan iya mana ko kana nufin baka gane shi bane.
alhaji kallon huton yayi sosai yace innalillahi wa,inna ilaihir raju,un

Safna na daga gefe kuka kawai take murya hajiya taji tana fadin safna kinsan musa ne?
cikin dashewar murya tace babana ne.
hajiya ta zaro ido a,a safna ko dai kama suka miki wannan fa dan yayata ce uwar mu daya
uban mu daya, yanzun nan kina nufin ke jikar iya ce.
cin kuka tace eh.
kowa afalon gumi ne yake karyo mishi itako ummi hankalin ta yafi na barawo tashi.
hajiya ta share zufan da ya karyo mata tace ke zaliha Ina kika samu wannan huton ?
jalal najin anyi ma ummi wannan tambayan ya fita afalon dan yanajin kunyar abin da ummi
tayi.
cikin kuka tace hajiya wannan matar itace kanwa ta da nake baki labari, zaro ido safna tayi ta
mike tace ummi kina nufin kece yar mahaifiyata, ina wlh wlh bazai wuyo ba gara naga mutuwa
ta da naga wannan ranar����
[8:57PM, 12/22/2016] Fadeela lamido: í ½í²˜í ½í²í ½í²MIJIN MARAINIYAí ½í²í ½í²í ½í²˜


Story
&
Written by
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📊

1013-1016

Anty nusaiba ta kama safna ta zaunar da ita tana fadin safna ki natsu mana baki san jikin ki
babu kwari ba ne.
safna tace anty ni ki sakeni tafiya zanyi wlh bazan zauna ba.
kowa afalon share hawaye yake sautin kukan ummi kawai kake ji.
alhaji yayi gyaran murya yace safna zo ki zauna, batayi musu ba kusa da hajiya ta zauna ,

hajiya ta kalli safna tace tabbas biri yayi kama da mutun lokacin da hanne tazo gidan nan zaliha
ta tambeye ta amman sai tace ba, ita ba ce, kuma nima na tambaye ta ina yar da kishiyar ta
tabari sai tace min tana gurin dangin mamar ta , hajiya ta nisa takara cewa toh me hanne take
nufi da haka. alhaji ne ya dago yace hajiya ga dalilin ta nan bata san inda yarinyar take ba kame kame take
tunda su tace musu tana gun dangin baban ta ke kuma ga abinda tace miki.
hawaye ne yake zuba afuskar hajiya tace amma ko indai haka ne ni kaina naci amana, dan tun
lokaci da aka ma iya aure da baban musa dangin mu duk suka guje ta saboda mijin da ta aura
bame karfi bane babu me zuwa inda take sai ni dama mu biyu ne mata sai yayyen mu maza
guda uku haka in naje iya zatai ta min korafin ita ba me zuwa gurin ta, nice me lallashin ta har
sai naga hankalin ta ya kwanta, ana cikin haka nima aka aurer dani, tun daga lokacin ban sake
zuwa garin ba sai da iya ta haifi musa mijinta dakan shi yazo ya fada balefi dagi sunje tun daga
sunan musa ban sake zuwa ba sai dai ita tana zuwa gida na akai akai dan haka ban cika
damuwa ba ,dan bata rufe wata bata zoba haka muka ci gaba da tafiya sai dai rashin lafiya ko
wani babban abu muke zuwa gurin ta duk da cewa ita ko da yaushe tafe take, kuma duk wani
Sha,ani sai dai in bataji ba, ko koma bata da lfy bana mantawa zuwan ta na karshe gidan nan
nasiha tai tamin akan zumunci ko sati daya ba,ayi ba mukaji lbrn rasuwan ta kuka ne yaci karfin
hajiya ta jawo safna tana fadin naci amanar iya.
safna lafewa tayi jikin hajiya tana kuka hajiya ta dafa kan safna hawayen ta na diga jikin safna
tace safna ki yafe min nina saka ki a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login