Showing 45001 words to 47874 words out of 47874 words

Chapter 16 - Mijin Marainiya Book Complete Hausa Novels by Fadila Lamido .pdf

Advertisement

16 Mar 2025

4115

duba unguwar bata ba lbrin ta gashi dare
yayi ganin haka muka nufi gida akafa ko Allah zaisa gida ta nufa, sai tsakar dare muka isa gida
tunda lokacin ban sake samun lfy ba har yau sai dai sauki kowa agurin kuka yakeyi daidai
lokacin jalal ya shigo ya same su cikin wannan hali.
ummi mikewa tayi taje gaban baffa ta tsuguna tana neman gafarar shi.
bece mata komaiba yana rike da hannun safna, dan haka hajiya taje har gabasa itama
tsunawa tayi tace baffa kaduba girman Allah yafewa yarinyar nan, ganin hajiya da yayi akasa
cikin sauri yace Allah ya yafe mana baki daya.
[7:32AM, 12/27/2016] Fadeela lamido: í ½í²˜í ½í²í ½í²MIJIN MARAINIYAí ½í²í ½í²í ½í²˜



Story
&
Written by
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📊

123-125

Godiya tayiwa baffa sosai sannan tasa hannu ta daga ummi ta kaita gaban mahaifiyar ta.
mama rahane kin amsawa tayi ta juyar da kanta gefe sai da hajiya tasa baki.
baffa yana rike da safna mama rahane tazo tarike safna tana fadi ya sunanki ne?
safna shiro tayi tana zunbura baki, hajiya tayi murmushi tace sunan ta safna ai fushi take daku
tace dama cen baku son saudatu tunda har kuka manta da ita.
baffa yace ayya yarinya barashin so bane akwai yanayi na rashin wayewa ada bakamar
yanzon ba, amman munji mun dauka kiyafe mana kaddara ce .
kowa agurin murmushi yayi banda jalal dake tsaye, alhaji yace kai kuma yaya zaka zo katsaya
mana akai.
yace daddy inason naje gida ne , bana jin dadi. alhaji yace ka bari muma yanzon zamu tafi,
baffa yace alhaji kafin kutafi bari akira mamar ta rabi ta ganta, ya fara kira rahane dauko mayafi
kije gidan rabi ki gayo mata, cikin sauri ummi ta mike tace bari naje, kiran jalal tayi suka fita tare.
bayan sun dau hanya ummi tace jalal me ya hadaka da safna?
mamaki ne ya kama jalal dan haka yace ummi wani ne yace miki munyi fada.
hararar shi ummi tayi tace ina tambayar ka kana tambaya na, dan baka da kunya.
bahaka bane ummi ai naga baki cikin gidan ne lokacin.
toh ina sauraron ka me ya hadaka.
ummi rashin kunya take min kwata kwata ta raina ni.
dakatar dashi ummi tayi jalal inason kayi hakuri da duk wani abu da safna zata maka bana son
in sake jin ance kunyi rigima kajiko, kuma yan zon kaje ka bata hakuri.
da sauri jalal ya kalli ummi yace inbata hakuri fa kika ce ai ita ce tamin laifi ita ya kamata tabani
hakuri.
eh na sani ka dai bata hakuri bana son ganin yariyar cikin bacin rai.
ummi ni gaskiya bazan bata hakuri ba, kin ga inda take gaya min magana ne.
ummi shiru tayi bata sake cewa jalal komai ba har suka isa gidan, yana tsayawa ta bude ta fita
bata jima ba sai gata sun fito da yaya rabi har da yarta aliya sai murna suke.
baya suka shiga ummu na gaba suka kama hanya ahanya ne jalal ya kalli aliya yace ummi na
dade banga aliya ba tun tana karama , sai kuma naga kamar tana kama da safna.
ummi banza tayi dashi sai yaya rabi ce tace ikon Allah itama zaliha haka tace, nina zaku ma
naganta wlh.
jalal ya juya gurin ummi yace ummi lfy kuwa?
banza ta sakeyi dashi, yaya rabi tace zaliha abduljalal na magana kinyi banza dashi. rabu
dashi yaya, jalal bashi da kunya ninace mai yayi abu yacemin shi gaskiya bazaiyi ba, kiri kiri.
nan da nan yaya rabi tashiga yiwa jalal fada , har suka isa gidan fada takemai.
suna shiga ta gane safna ta juya barayin ummi tace amman zaliha kin ban mamaki da har kikai
zama mai tsayi da safna baki gane taba, hannu tasa ta daga safna, safna ma gani tayi kamar
mamarta sunyi kama da mamarta sosai dan haka ta rungume ta tana kuka take taji son yaya
rabi ya kama ta jinta take kamar mahaifiyar ta, duk da cewa da kaga yaya rabi kasan tana cikin
yanayi na talauci.
aliya tazo ta baya ta tsaya tace anty safna. Cikin sauri ta waigo sukayi arba da juna safna
sakin yaya rabi tayi ta rike aliya haka sukaita murnan ganin juna sai gurin la,asar suka fito,
safna na rike da aliya wai ita adole sai dai sutafi da ita.

mama rabi tace safna kibari ran suna in munzo sai tazauna tamiki kwana biyu kinga yazon
kayan ta duk suyi dauda.
safna tace mama toh basai ta saka nawa ba. ummi tace yaya ai hakuri zakiyi kawai mutafi da
ita.
mama rabi tace toh Allah ya tsare sai munzo suna.
bayan sun dauki hanya hajiya tace toh kodai zamuyi gaba daya ne daga nan mu wuce gidan
goggo safna cikin murna tace eh Hajiya.
alhaji ne yace toh bari akira jalal agaya mishi dan motar sa daban kar ya wuce gida.
bayan alhaji yagama waya da jalal yace yaran dai zamani basu da kunya kunga wai jalal
tunanin yaran shi yake wai cewa yayi za,a kwasar musu iskar mota, dariya sukayi ummi ta kara
rufe jariran ta rungume su ajikin ta, suna isa gidan malam musa alhaji da hajiya ne kadai suka
sauka amotar suka shiga gidan da sallama, goggo ta fitoh daga daki tana fadin wai wai hajiya
kece da kanki sannun ku da zuwa tabarma ta shin fida bayan sun gaisa goggo tace bari naje na
sowo muku shinkafa da wake.
hajiya tace a,a ni ba zama nazoba nazone naga jikokina.
cikin fadowan gaba tace aiko basa nan iro yana gun yansan da an kamashi itako salame
yanzon ta dauki tallan gyada.
cikin mamaki hajiya tace a,a batayi aure ba?
hawaye ta fara sharewa tace ai ya fasa tunda yagano ciki gare ta.
hajiya ta girgiza kai tace toh kizo ki raka mu gidan da dayar yariyar take naganta.
goggo tace ayya ai sun bar garin nan kwata kwata yanzon bansan inda suke ba.
alhaji yace tohfah mukuma gashi ganinta mukazo ya sunan tane ?
baki na rawa tace safna , suna cikin haka saiga ummi sun shigo da jalal goggo ta zabura
tamike tami tana fadin yau na shiga uku karya ta takare dan Allah ku rufamin asiri wlh bansan
inda safna take ba, nan da nan tashiga basu lbr tana kuka .
bayan ta gama ne hajiya tace to yanzon meye ribarki?
babu wlh kawai bakin kishi ne ya debeni har na aikata haka gashinan alhakin ta na bibiya ta
yara na duk babu nagari kuka goggo taci sosai babu me lallashin ta hajiya fadi take kigama
kukan kije ki ne momin jikata dan ba yadda zanyi ba.
Idon goggo duk sun fito waje kuka harda majina.
alhajine yama jalal umarnin ya shigo da matar shi, dan haka ya juya ya shigo da safna safna
na shigowa goggo ta kara tsorata , tace dama kunsan safna ne, a Ina kuka same ta, zuwa tayi
ta fara duba jikin safna tace ikon Allah safna ce haka kamar yar wani hamshaki , ni inan cikin
bakin ciki da tashin hankali muta ne na nunani wasu suce min uwar karuwa wasu sucemin uwar
barawo, cikin kuka take maganar ki yafemin safna na tuba bazan kara ba.
hajiya tace kima Kara mana, ina zaki ganta bare ki kara ita da take dakin mijin ta cikin fada
tace ku kuma kutashi mutafi, duk mikewa sukayi suka fita safna ko tsayawa tayi tana kokarin
daga goggo hajiya tazo ta jata
[10:21AM, 12/28/2016] Fadeela lamido: í ½í²˜í ½í²í ½í²MIJIN MARAINIYAí ½í²í ½í²í ½í²˜



Story

&
Written by
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📊

126-130


Lokacin da suka koma gidan hajiya mangariba tayi dan haka alhaji yana sauke su hajiya da su
safna suka wuce gida harda jalal, jalal dai fushi yake da safna sosai dan har suka rabo basuyi
magana ba.
suma suna sauke ummi masallaci suka wuce saida sukayi sallar ishsha suka dawo gida.
bayan sunja girki ne jalal ya mike yace daddy bari naje gida.
alhaji yace me zaka je kayi agida bayan matarka batanan kayi zamanka mana anan, koba
haka ba zaliha?
ummi tabe baki tayi tace alhaji ni yanzo jalal yafi karfi na. Alhaji yace me kuma ya faru kai jalal
dawo nan ka zauna, jalal na zama alhaji yace me yake faruwa, me ka mata?
sunkuyar dakai yayi yace daddy akan maganar safna ne, yanzun kwata kwata ta rainani rashin
kunya take min, kuma wai ummi tace wai dole ni zan bata hakuri, daddy ai ni ya kamata taba
hakuri, amman yaya za,ayi kuma ace ni zan bata hakuri ai sai taji dadi nan gaba ta kara yimin.
alhaji yace zaliha yaya haka, haka ake hukunci?
alhaji nifa bana son ganin safna cikin bacin rai, dan haka ni dai kawai kaje ya bata hakuri, shi
wanene da bazata mai rashin kunya ba, ai nima gashi nan kanamin rashin kunyar, wlh inhar
bakaje ka rarrashi yariyar nanba zakaga abin da zan maka.
kallon ummi yayi yace toh shike nan ummi naji, a han zar ce ya bar wajen dakin sa ya nufa.
alhaji yabi jalal da kallo yace zaliha bafa haka akeyi ba kina nufin yanzon kinfi son ganin nashi
bacin ran akan na safna?
Alhaji aishi babba ne kuma cewa nayi yayi hakuri yabata hakuri.. Katseta alhaji yayi yace aiko
indai haka zaki ringayi bakice su zauna lafiya ba dan zaki samai tsanar ta, ai shi amatsayin shi
na namiji baxai so matar sa ta raina shiba, kuma nina tabbata ta bata mai rai ne shiya sa yayi
fushi da ita amman yana son matar sa bakuma wai dan jalal yana dana bane na yabe shi,
dukkan su yaya nane kuma daidai gwargwado nasan halin su. haka alhaji yayita ma ummi
nasiha me ratsa jiki.
zuwa cen ummi ta fara kuka bakin ta yana rawa tace alhaji akwai abin da yake damuna ina
tunanin idan kaji mgnr zaka tsora ta dani amman yazama dole na fada dan innemi gafarar ka
amman dan Allah ina neman wani alfarma karka gayawa kowa wannan maganar dan idan
maganar nan ta fito toh lallai naji kunya kukanta karuwa yayi saida ta waiga ko akwai wani dake
tahowa sannan tace alhaji gidan jalal daya kone... Alhaji be Bari ummi ta karashi maganar taba
yace nasan komai xaliha bake da madina kuka shirya komai ba ai tuni nasa aka kama madina
da kanin ta duna sai da madina ta kwashe sati buyu gurin yan sanda, shiko duna har yanzun
yana hannu .
kuka ummi take sosai tana rokon alhaji gafara tana fadin sharrin zuciya ne.

alhaji ya fara share mata hawaye yace bar kuka zaliha ni tuni na yafe miki komai yawuce sai
dai muce Allah ya kiyaye gaba.
nagode alhaji har ina tunanin inkaji wannan maganar zaka sakeni ashe kai kallona kawai kake.
alhaji yake yayi yace aitun lokacin tarewar jalal nasan komai dan lokacin na tsane ki shi
yasama dazan tafi ban miki sallama ba dan gani nake zaki iya kisa.

washe gari karfe 7:30 jalal ya fito cikin shirin shi na zuwa office sallama yayi ma ummi ta amsa
bakamar yadda jalal ya zata ba, sannan ya mike yace nafi.
waigowa tayi tace zaka biya gurin yan biyu ne sannan ka wuce ko?
Jalal yace a,a saina tashi office saina tsaya acen.
a,a jalal be kamata ba kadai biya ko atsaye ne ka gansu sai ka tafi, ga kairat cen katafi da ita
daman ta dame ni wai bataga yan buyu ba.
suna isa gidan kairat ta fita aguje ta shi gidan lokacin da jalal ya shiga ya same tana rike da
yaran sai faman jagwalgwala su take wai ita tana musu wasa .
saida ya gaida hajiya ya tabaye ta anty nusaiba bataxo ba, hajiya tace na nan tafe.
safna nazaune kusa da hajiya tace ina kwana.
kasa kasa ya amsa yamike yaje gaban kairat ya tsuguna ya sunbaci yan biyu ya mike yace
hajiya na tafi.
safna ta mike tabi bayan shi, yana fita daga falon ta rike shi, juyowa yayi yace safna sakeni
karki ya mutsamin kaya anjima zan dawo .
kara shagwar gwabewa tayi tana buga kafa kamar yanda kananan yara keyi tare da kuka
ahankali .
murmushi jalal yayi yasa hannu ya riko safna yace toh ya isa haka safna, me kike so.
cikin kuka tace bakai bane kaketa fushi ko kallona baka yi. Jalal yace safna kenan bake kikace
na daina miki magana ba, har kina min rashin kunya.
toh kayi hakuri banzan kara ba.
dadi jalal yaji yace shikenan safna ya wuce shiga ciki idan na dawo zan zo .

haka safna tacigaba da zama gidan Hajiya cinkin kwanciyar hakali kowa kokari yake ya faranta
mata rai Ana gobe suna su yaya rabi suka iso gidan hajiya ita da mama rahane washe gari
akayi suna nagani na fada alhaji da ummi sun kashe kudi sosai, jalal kuwa ya tara abokan shi
sosai itako safna dama bawasu kawaye gare taba dan haka bawasu mutane ta tara ba daga
safiya sai halima su kadai ne adakin sai kuma kanwar ta aliya haka taro ya tashi lfy yaran
sukaci sunan ummi da daddy wato yusuf da zaliha.
Washe gari suna saiga goggo da salame sunayin sallama hajiya tace su fita mata daga gida
kuka goggo ta saka tana fadin hajiya dan Allah kiyi hakuri ki bari na neme gafarar safna.
safna tana daki ita aliya suka fara jiwo kukan goggo fitowa tayi da sauri , goggo nagani safna
tace safna naxo neman gafarar ki ne karna mutu da wannan nauyin dan Allah ki yafemin
itama safna share hawaye tayi sannan tace goggo kitashi ni dama na yafe miki komai ya
wuce, kallon salame tayi taga cikin ta har ya fara fitowa sai yama suka tafi safna ta roko su har
bakin gate ta basu kudi masu yawa tare dace ma goggo idan suna bukatar wani abu su mata
magana.

bayan shekara uku jalal da safna ne tafe a mota daddy da ummi suna baya sai faman surutu
suke , safna tace yaya wai ina zamu ne?
yace yau gidan ummi zamu tun da ke baki cewa zaki, ke sai dai gidan mama rabi ko kunyar
ummi bakiji sai dai ita idan taji ganin ku tazo.
kunya ce ta kama safna tace ba haka bane yaya abin da yasa nafison gidan mama rabi muna
hira da aliya. hararan ta jalal yayi bawani ai ummi ma tana jinki da hira saiki ta wani zilzillewa.
daddy ne ya leko da kanshi saitin jalal yace abba ni gidan baffa nake so bana son gidan ummi.
tsawa jalal yayi mishi tare da fadi daddy In na sake jin kace baka son gidan ummi saina zane
ka.
cikin murna ummi tace yauwa abba kamai balala ni ban da ni inason gidan ummi. Jalal yace
yauwa ummina ashe dai kin gane. Jalal ya juya barayin safna yace kinga kin koya ma daddy kin
gidan ummi ko.
safna shiru tamai domin miyau ne ciki da bakin ta daha suka isa gidan Kairat ta fito da gudu ta
rike hannun ummi da daddy suka shiga ciki, sun same ummi da alhaji afalo gudu ummi karama
tasake hannun kairat ta fada jikin ummi daddy ma da gudun shi ya nufi alhaji cikin dariya alhaji
yace au wato kun raba kenan safna ce ta shigo jalal nabinta abaya sai fada yakeyi. alhaji yace na kula jalal so yake yazama mafadaci daga shigowa sai fada.
daddy wai yariyar nan idan bata son tamin magana sai ta tara miyau abikin ta.
ummi tace a,a jalal bada gangan take ba saidai idan ciki gare ta. cikin sauri jalal yace ummi ai
idan tana da ciki bahaka take yi ba daddawa take ci
dariya sukayi gaba dayan su sannan ummi tace jalal ai ko wani ciki da kalar sa.

*ALHAMDULILLAH*
_anan na kawo karshen wannan lbrn_
Fadeela Lamido
Mmn yazeed
07014197556
*Ni makauniya ce ido na baya ganin comment din kowa saina masoya na😜*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login