Showing 33001 words to 36000 words out of 47874 words
Chapter 12 - Mijin Marainiya Book Complete Hausa Novels by Fadila Lamido .pdf
&
Written
Fadeela Lamido
Mmn Yazeedí ½í³
89-91
Alhaji ne ya kalli safna yace sabo da me zakice bayan zon ba?
daddy abari sai naji sauki bani da lfy fah
daddy d'aga hannun shi yayi ya mata dakuwa kinci gidan ku, yau din nan zaki wuce dakin ki
kin fi son ki zauna anan kina hana hajiya bacci ko?
daddy nifa bance kada tayi bacci ba ita da kanta tashi ta zauna, dariya hajiya tayi tace toh
safna ba dole na tashi ba ni ina bacci nafara jin gunjin kukan ki.
to aini kaina ne yake min ciwo lokacin. alhaji yace ai ko bakin kine yake ciwo yau zaku tafi,
nima hankali na ya kwanta tunda aka daura auran nan hakali na ba,a kwan ce yake ba, buri na
kulum be wuce nagan ku acikin gidan Ku ba.
Safna shiru tayi ita gaskiya fushi take da jalal, muryar daddy taji yana cewa safna kuyi hakuri
da junan ku ban da fada , kai jalal kaine babba banda saurin fushi , babba da hakuri aka sanshi,
ke kuma safna ki sani jalal mijin ki ne dan haka kimai biyya, tuni safna ta fara kuka ji tayi auren
ya dawo mata sabo. alhaji juyawa yayi gurin jalal yace jalal ya maganar karatun safna, ina fatan dai kana da burin
taci gaba karatu?
eh daddy insha Allah .
alhaji yace to yayi kyau Allah yayi muku albarka ya baku 'ya'ya masu albarka.
gaba dayan su kasa amsawa sukayi sai hajiya ce ta amsa.
safna kuwa ta kifa kai sai faman kuka take. alhaji yace jalal zan tafi ko anan zan barka?
a,a daddy tare zamu tafi ai ban fito da mota ba
sun mike zasu tafi safna ta dago jajayan idonta ta harari jalal, yace Allah ya huci zuciyar ki.
daddare kamar yadda alhaji ya tsara nusaiba tazo ita da matar baba salisu suka raka safna
gidan ta, har bakin gado suka zaunar da ita sai faman kuka take.
wurin takwas suka ceto mufa zamu wuce dare nayi. safna tace anty dan Allah karku tafi tsoro
nakeji.
nusaiba tace wani irin tsoro to bari na kira jalal.
shikowa jalal lokacin da anty nusaiba ta kira shi yana kokari zuba akwatunan su amota ta kofar
dake baya yake fitar da akwatin daddy na sakawa amotar har suka gama, jalal yaso yayiwa
ummin shi sallam ko bazata amsa ba amman daddy yace ya rabu da ita, dakan shi ya raka jalal
har cikin falon su , su anty nusaiba kuwa suna jin zuwan su suka tafi bayan daddy yasa musu albarka ya wuce gida , da niyar shima da safe zai wuce gurin aikin
sa
alhaji na fita jalal ya mike ya leka dakin safna daga bankin kofar ya tsaya ya kalli fuskar ta da
sauri ta dukar da kai kasa, murmushi yayi yace ina zuwa, waje ya fita yafara ciro akwatunan su
daga cikin mota, saida ya fara shigar mada safna nata sannan yashiga da nashi daki, yana
ajewa ya shiga wanka bayan ya fito yasa ka kaya marasu dauyi ya nufi dakin safna. yana shiga ya same ta daidai ta fito wanka tana goge jikin ta tana ganin shi ta jawo hijjabi ta
dake gefen gado tana kokarin sakawa.
dariya taba jalal sosai ya matso kusa da ita ya zauna, yace to meye kuma na saka hajjabi me
zaki boye min.
gani yayi ta kara rudewa dan haka ya matsa ya riketa yace safna meya sameki?
cikin muryar kuka tace bacci nakeji.
murmushi kawai jalal yayi dan yasa ba gaskiya ta fada ba.
yace to waye ya hanaki bacci. shiro tayi.
Matsawa jalal yayi yace zoki kwan ta.
zuwa tayi ta kwata ta kudun dune cikin hijjabin ta
jalal ya fahimci safna bata sone ya nemi wani abu awajen ta, kollon ta yayi ko mai bata shafa
ba, yace safna.
amsawa tayi batare da ta waigo ba, yace haka zaki kwanta baki shafa mai ba bare kuma
turare.
yaya ai ni yanzun bana shafa mai.
saboda me?
tace wari yake min
jalal yace wari man nakine yake wari, kitashi kawai ki shafa ke da kin ga baki son abo saikice
yana wari, haka ranan kikace ina wari.
Wlh yaya ban son warin man ne , sabolon ce ma na bayi na kasa wanka dashi ahaka niyi
babu sabulu.
jalal yace kina nufin ba sabulu kikayi wanka, kice ba wanka kikayi ba kin jiko datti, ai irin
wanna saiki fada irin wadda kike so asiyo miki.
batace komai ba ta juya tayi shiru
ganin ta kwanta shima ya hau gadon ya kwanta zuwa cen ya fara kai hannun shi jikin safna ,
yi tayi kamar tayi bacci ahankali tafara jin hannun shi acikin hijjabin ta har zuwa marrar ta taso
ta rike hannun amman sai tai tunanin in yaga tayi barci zai barta dan haka tayi kamar tana bacci
saiji kawai tayi yana kwance towel din da yake daure jikin ta dasauri ta rike hannun shi, tace
yaya jikina fa akwai datti , bakace na tayar da datti ba.
cikin rauna nan niyir murya jalal yace ni banji wani datti ba yace gaba da abinda yake tun
safna na ture jalal har sakon ya fara kaiwa gare ta, ta fara mayar mai da martani, nidai daga sun
rikece, nayi waje agujeí ¼í¿ƒí ¼í¿¼í ¼í¿ƒí ¼í¿¼í ¼í¿ƒí ¼í¿¼na jawo musu kofar.
washe gari da safe 9:10 akafara buga kofar falon su da karfi, safna dake kwance jikin jalal ta
zabura shima mikewa yayi da sauri ya saka jallabiya ya fita har yanzun buga kofar ake
[7:25PM, 12/16/2016] Fadeela lamido: í ½í²˜í ½í²í ½í²MIJIN MARAINIYAí ½í²í ½í²í ½í²˜
Story
&
Written by
Fadeela Lamido
Mmn Yazeedí ½í³
92-95
Abduljalal a tsora ce ya isa kofar dan gani yake kamar ummi ce , yasa hannu ya bude kofar
yariyar dake aiki gidan anty nusaiba yagani tsaye da kayan abinci a hannun ta wani haushi ya
turnekeshi besan sanda ya daga hannun shiba ya wanke ta da mari.
a tsora ce yariyar ta dafa kuncin ta, ta ajiye abin cin ta arta aguje, abduljalal ya tsuguna ya
dauki basket din yakoma afalo ya jiye yakoma dakin safna ya same ta sai faman raba ido take,
yace ki kwatar da hankalin ki wannan yariyar ta gidan anty nusaiba ce, mikewa tayi cikin sauri
tace bari naje nasan anty ce ta aiko ta kama hannuta yayi yace ai ta tafi abinci ne ta kawo,
koma wa tayi ta zauna tayi shiru tafara tunani, lallai ummi bata son auren nan gashi yanzun tun
daga gidan anty nusaiba aka kawo mana abinci kuma ai munfi kusa da ummi.
muryar abduljalal taji yana fadi safna tunanin me kike?
yaya tunanin kairat nakeyi mun barta ita kadai. yace karki damu idan muka gama cin amarcin
mu zan dauko ta tadawo nan da zama gaba daya.
safna tace yaya ummi ko zata bari?
da sauri yace safna bar wannan maganar kisan tunanin me nakeyi .
gargiza kai tayi yasake cewa ina tunanin gashi kin haifi yaro me kama dani.
Safna tace nidai yariya nakeso.
nima inaso safna amman nafiso ki fara da namiji dan nasa mishi sunan daddy.
safna tace toh yaya in mace ce wani suna za,a sama ta. bude baki yayi ahankali yace na baki
zafi.
safna ta sake cewa baza,a samata sunan ummi ba?
mikewa yayi yace taso muje muci abinci. safna ta lura yaya ko sunan ummi beson yaji ta Kira
suna cikin cin abin cin ne wayar abduljalal tayi kara ya dauka yasa akunne sa, yana fadin ina
kwana anty.
anty bata amsa gai suwan shiba ta shiga yimai fada jalal me bilkusu tayi maka ka mareta har
fuskarta ta kunbura haka?
anty zuwa tayi muna barci taita buga kofar, safna duk tabi ta firge
da sauri anty tace lallai jalal safnar yariyar goye ce da zakace wani an firgita ta, har yanzun
dai kanan da bakar zuciyar ka , ita kuma safna tana kallo kamari yariyar muta ne ko, toh shike
nan idan ka kuma ganin bilkisu agidan ka kasa bulala ka zaneta ba mari ba yana kukarin yin
magana ta kashe wayar. ture abincin yayi gefe ya sake kiran ta bata dauka ba mikewa yayi ya shige dakin sa.
safna binshi tayi da kallo domin bata fahimci abin da suke fada ba, ta fara kwashe kayan da
suka bata takai kitchen saida ta wanke su sannan ta fito har lokacin jalal be fito ba, wuce wa
tayi dakin ta tayi wanka kwalliya ta tsaya tayi sosai sannan ta nufi dakin jalal tana tura kofar
tajita bude sallama tayi . jalal dake ciki ya amsa , tana saka kai ta ganshi tsaye ga dukkan
alamu wanka yayi dan daga shi sai gajeran wando ga dogon wando a hannun sa yan kokarin
sakawa.
safna naganin haka ta juya baya , murmushi jalal yayi ya aje wandon hannun shi ya iso
gare ta jin shi kawai tayi ya rogumeta, ta baya yana kaimata kiss ta ko ina kamar zai hadiye ta,
zuwa cen yadan dakata ya leko da kansa zuwa daidai fuskar ta dan jalal dogo ne sosai, yace
har kinyi wanka, Allah yasa dai yauma ba haka kikayi wankan ba sabulu ba. safna na rugume jikin jalal tace ai na samu wani sabulu acikin akwati na bashi da wari sosai.
jalal yace jinan safna in kinji abu namiki wari ki daina cewa yana wari cewa zakiyi bana son
kamshin shi, dan kinsan Allah idan kika kara cewa ina wari saina fasa miki baki.
kallon shi tayi da mamaki tace yaya yanzo nan kai sai ka dake ni.
me zai hana na dake ki ,kiyi abin dokan kigani.
haba nina san bazaka dakeni ba in kuma zaka iya bismillah. jalal yace ai baki min komai ba
yanzun.
dan tureshi tayi kadan ta rike hancin ta tace yaya jalal wari yake.
murmushi kawai yayi yace Ina binki bashin duka idan kika haihu zan miki.
a,a ni ban yadda ba yanzun nake so.
matso wa yayi ya riketa yace daidai ina zan daka.
safna cikin ta, tanuna tace ka daki nan
dariya jalal yayi yace lallai safna ke muguwa ce ,toh naki.
haka zaman su yaci gaba da kasan cewa
cikin farin ciki da kwanciyar hankali jalal yana nuna mata so daidai gwargwado har wani cika
su kayi suka kara haske sukan leka gidan hajiya da daddare gidan ummi kuwa tunda suka tare
ko jalal be leka ba bare safna, amman bata san cewa jalal baya zuwa ba gashi har sun kwashe
sati uku da tarewa
alhaji kuwa tun washe garin ranar da ya raka jalal gidanshi yabar garin ko sallama bema
ummi ba.
itako ummi ranar ta wayi gari daga ita sai kairat acikin gidan tayi tunanin wato jalal fushi yake
da ita ko ganin shi baya bari tayi, alhaji kowa abakin kairat taji lbrin ta fiyar sa.
tun tana ganin abi kamar wasa ne har ta fara tsora ta.
kiran alhaji tayi har ta gaji be dauka ba, ta fara tunanin kiran jalal, amman kuma da kunya
takira shi bayan tace mai bata son ganin shi, fadi tayi a fili me yake shirin faruwa dani ne,
iyayena sunki karbata saboda halina dagin mijina basa sona saboda halina mijina dake takama
dashi ya juyamin baya saboda yana kuka da halina, dana dake matukar so shima ya hakura ni
,afili take fadi kamar mahaukaciya zuwacen ta sake kuka haka taita yi babu me rarrashin ta
yau ummi ta tashi da matukar so taga jalal tuni ta lura jalal kwata kwata baya shigowa gidan a
lissafin ta sati hudu kena da barin su gida wata zuciya tace kodai tare sukayi tafiyar da alhaji be.
mikewa tayi ta nufi dakin jalal tana tura kofar taji ta bude shiga ciki tayi me zata gani duk wani
abu na amfanin jalal babu shi adakin, juyawa tayi gurin da aka aje a kwatunan safna nanma
wayam babu komai.
rawar jiki ta fara tana haki take fadin na shiga uku, dakin ta tafada ta dauki gyale drive takira
tace zoka kai ni gidan hajiya, rabota da gidan hajiya ta dade.
hajiya na zaune taga ummi tashigo kamar ankwato ta daga bakin kura
07014197556âœ
[6:31PM, 12/17/2016] Fadeela lamido: í ½í²˜í ½í²í ½í²MIJIN MARAINIYAí ½í²í ½í²í ½í²˜
Story
&
Written by
Fadeela Lamido
Mmn Yazeedí ½í³
96-99
Hajiya tsoro ne ya kama ta cikin kidima tace zaliha daga ina haka?
cikin kuka take fadi hajiya nazo neman gafararki dan Allah kiyafemin a yanzun nagane kure
na , kuka take sosai.
hajiya tace alhamdulillahi dama haka ake so naji dadi da kika fahimce haka ni daman ban
kullace kiba tunda ismail yakawo ki amatsayin matar sa dole nasoki balle kuma ga yara har biyu
atsakani.
ummi tace nagode hajiya tana share hawaye.
hajiya tace amman zaliha bayan wannan akwai wani abun da yake damunki ko?
hajiya aini duniyar gaba daya ta cakude min iyayena suki karbata amatsayi yar su saboda
lefin da na aikata , nan ta shiga bawa hajiya lbr hajiya tace ikon Allah abin mamaki baya karewa
, toh zaliha banda abinki ina kika taba jin mutun yaki iyayen sa, toh ai dole kirasa kwanciyar
hankali kadan ma kika gani, ai iyaye ba abin wasa bane, karki kara ai kata nakaman cin
wannan, kinji ko? In Allah ya yarda bazan kara ba nagode hajiya.
hajiya tace tashi kije kitchen ki debi abinci. hajiya bana jin yinwa naci abinci agida.
shiru sukayi nadan wani lokaci sannan hajiya ta kalli zaliha tace megidan fa yaushe zai dawo?
tofah hajiya ta sosa ma ummi inda yake mata kaikayi wani sabon hawaye ne yake fita a idonta
tace hajiya aini rabon da naga alhaji sati hudu kenan sanda zaitafi ma ko sallama bemin ba
kuma ko kiransa nayi baya dauka jalal ma basan inda yake ba, hawaye take sosai.
hajiya ta tausaya mata tace ya isa haka share hawayen ki, kikace rabon ki dashi sati hudu?
eh
hajiya tace toh ai yadawo yayi kwana biyu ya koma, yau kwana biyar da tafiyar sa, kina nufin
ba,a gida ya kwana ba kenan,toh ko kin masa wani abune?
shiro tayi tana ta share hawaye.
hajiya tace toh kidaina kuka ai tunda kukayi aure shekara kusan talatin ban taba jin kan kuba,
mijiki nasonki yayi hakuri da ke duk da cewa yasan baki son yan uwan sa, ina ganin dai akwai
abinda kika masa.
hajiya wayar ta dauka ta shiga daki number alhaji takira bayan ya dauka tace me matar ka
ta maka katafi kabar ta babu ko sallama?
alhaji yace lallai zaliha bata da kunya gidan ki tazo shakaran ta nawa batazo gidan ki ba.
hajiya tace nidai ba wannan na tambaye kaba babu ruwanka , koma me tayi maka kayi
hakuri bakaga inda ta fita haiyacin taba ta rame tayi baki kai ko kunya bakaji abokan ka su
ganta ahaka, ai sai ace wahala take Sha.
hajaya kirabu da zaliha makirar mata ce, inda kisan halin ta bazaki yarda da tubanta ba, kice
mata kawai ta wuce gida saina dawo.
nidai nace ka kira ta, ka kwatar mata da hankali abin ya mata yawa jalal ma kai ka hana shi
zuwa gidan kenan, toh yanzun yaya kake son tayi.
alhaji yace shike nan hajiya zankirata.
ummi bata tafi gida ba har dare gashi kuma har yanzun alhaji be Kira taba sai gurin 7:30 taga
kiran shi jiki na rawa ta dauka tafara gaida shi be amsa ba yace kina ina ?
cikin sauri tace ina gidan hajiya.
yace toh maza kitattra kayan ki kije gidan iyayen ki sai