Showing 24001 words to 27000 words out of 47874 words
Chapter 9 - Mijin Marainiya Book Complete Hausa Novels by Fadila Lamido .pdf
tayi cikin kirjin shi tana dariya.
Shima kara matseta yayi yana dariya suna cikin haka saiga kairat ta shigo.
da sauri jalal ya ajiye safna yace ke bacewa nayi kije gurin ummi ba.
a tsora ce tace ummi ce tace na dawo na zauna.
sai alokacin jalal ya tuna ummi na jiran shi, sau kowa yayi yaje kunne safna ya rada mata
wasu magana ya fita yana dariya ita kuma tasa hannu ta rufe ido.
yana fitowa yace ummi muje
kallon jalal tayi ta daure fuska ahaka zaka tafi kayan ka a yamutse.
[7:56PM, 12/8/2016] Fadeela lamido: í ½í²˜í ½í²í ½í²MIJIN MARAINIYAí ½í²í ½í²í ½í²˜
Story
&
written by
Fadeela lamido
Mmn yazeedí ½í³
67-69
Sai alukacin jalal ya kalli kayan sa sun yamutse amman saiya dake ya kalli jikin shi yace muje
kawai ummi.
Wlh bazaka fita a haka ba ,kai kadai ne me mata, ko akan ka aka fara, haka kaga sauran
maza suna fita?
shiru yayi mata bece komai ba.
suna cikin haka alhaji ya fito yace me yayi ne naji kamar kina mai fada?
cinki daure fuska tace jifah kayan shi wai haka zai fita.
alhaji yace me kayan nasa sukayi?
jifa inda kayan shi suka ya mutse sai kace akan shi aka fara aure.
alhaji hada rai yayi yace jalal jaka abin ka.
da sauri jalal ya juya ya shiga dakin sa. alhaji ya kalli ummin yace wai zaliha ko hauka za kiyi
ne, ina ruwan ki da kayan sa, irin wannan ai sai ya raina ki, yaya mutun da matar sa zaki saka
masa ido.
alhaji bazance sa ido bane maganar gaskiya ne, ai wannan rashin kunya ce.
toh shikenan nasan maganin abin ai in da suna gidan sune baza ki saka musu ido ba, haba na
menene zakibi kita kurawa yara wucewa yayi ya fita ya ta fada.
bayan jalal ya canza kaya ya fito suka dau hanya ahanya ne ummi ta kalli jalal taga fuskar shi
murtuk tace jalal fushi ka keyi dan na gaya maka gaskiya .
a,a ummi ni ba fushi nake ba.
ta sake cewa jalal ni bawai ina kinka da safna bane, abinda yake damuna shine sultan ya taba
neman safna kuma kasan sultan ba irin yan iskan da be nema ba, ina jin tsora kar ace ya shafa
mata ciwon zamani shiya sa nake tsoron karka kusan ce ta, ta shafa maka.
jalal yace ummi dan Allah karki kara irin wannan maganar ba komai atsakanin su kuma lfyr ta
kalau.
kar kace zaka shede ta dan ni na taba ganin su da ido na .
jalal yace dan Allah ummi kibar maganan nan ni bana so.
ai ina gaya maka ne dan ka kiyaye.
toh zan kiyaye eh ummi naji zan kiyaye.
ganin da tayi kamar ya shiga damuwa yasa ta murna tafara nasara.
shikuwa jalal yasan cewa shi ya fara bude matar sa a leda, amman zuciyar shi ta fara raya
mishi anya kuwa sultan be lalube safna ba kuwa , dan haka ya kosa ya koma gida ya tuhu
meta.
da haka suka isa kofar gidan yaya rabi , ummi ce kadai ta shiga, jalal ya tsaya a mota.
ummi ta shiga tare da sallama yaya rabi ta fito daga cikin dakin ta sukayi ido biyu da ummi.
ta fara fadin zaliha kodai gizo idona kemin.
ummi tace ba gizo bane yaya rabi nice.
aguje yaya rabi ta fada jikin ummi tana kuka, ummi ma kuka ta saka , haka sukai tayi babu
mai lallashin su .
bayan sun natsu suka shiga tattauna wa akan halin da suke ciki, ummi ta kwashi duk yadda
sukayi da baffa ta gayawa yaya rabi.
yaya rabi tace banga lefin baffa ba zaliha .
ummi tace nima banga lefin saba amman matakin da ya dauka yayi tsauri yanzun a ina zan
nemo saudatu, kawai ina ganin bazai yafe min bane shiyasa yace saina nemo ta.
toh nidai abinda nake gani zaliha ki jaraba ki gani ko Allah zaisa adace.
toh ni yanzun ta ina zan fara, alhaji yace min wai agidin wata bishiya aka bar ta ko?
dan Allah ina son ki tambaye min su baffa wacce bishiya ce kuma awace unguwa ne.
murmushin takaici tayi sannan tace zaliha kenan ko kisan saida nayi shekara biyar ina zuwa
gidin bishiyar ina zama ko Allah zai sa na ganta amman ko me kama da ita ban gani ba.
ummi nisawa tayi sannan tace kuma kin tamya agurin?
tambaya kuma ai sai da na zama kamar mahaukaciya duk wanda nagani saina tambaya.
ummi shiru tayi sannan tace yaya rabi banida saura wata dama ila kawai ki gayamin gurin
inje in jaraba ingani
yaya rabi tace kusa da unguwar ku ana cewa unguwar 'yan mangorori, akwai wata katuwar
bishiya agurin ada amman ayanzun babu bishiyar amman akwai wata tsohowa tana kasa
kayan miya.
tuni ummi ta gane kwatance domin tasan unguwar sosai sai dai unguwar talakawa ne.
jalal ne ya fara kiran ummi awaya tace au na manta nabar jalal awaje yaya rabi tace shine ya
tsaya awaje sai kace bako.
mikiwa sukayi suka fito tare, jalal na zaune idon nan jawar ya kosa ya koma gida ya tambaye
safna ko sultan ya taba taba mata jiki.
bayan sun gaisa da jalal suka dau hanya jalal yaso su wuce gida amman ummi tace sai sun
biya yan mangorori.
suna isa ummi ta sauka ta isa gurin tsohuwa me kayan miya bayan ta gaida ta , tace dan
Allah mama tambaya nake?
yar tsoha cikin murna tace Allah yasa na sani hajiya.
dan Allah mama shekaran ki nawa agarin nan?
ai ni hajiya agarin nan aka haife ni ban taba zuwa ko ina ba.
nan ummi tashiga karanto mata tambayar ta.
tsohuwa tsayawa tayi tayi shiru zuwa cen tace, nidai kamar nasan lbrn nan amman na manta
tasake yin shiru
ummi kuka tashiga yi tana fadi mama ki nutsu ki tuna ahankali, ko kudi kike so zan biya ko
nawa ne kowa.
tsohowa tace yarinya ki kwatar da hankalin ki insha allahu zan bincika miki kinga yanzun zan
tattara kaya na gobe ki dawa kin ga gidana cen koda baki ganni anan ba sai ki shiga ciki.
haka ummi ta aje ma tsohuwa kudi masu yawa ta wuce.
Suna komawa gida jalal ya fita amotar da sauri yariga ummi shiga gida , ummi binshi tayi da
kallo tazata maganar da tagaya mishi ne yake damun shi , shikuwa jalal cewan da tayi ta taba
ganni su da idon ta shine abinda yake tayar mai da hankali.
yana shiga falo yaga safna kwance tana bacci besan lokacin da ya finciko taba yafara janta
yana kokarin shiga dakisa da ita.
safna cikin firgita ta fara ihu dai dai lokacin ummi ta shigo , hango jalal tayi yana jan safna
idon shi arufe.
ummi tarogo da gudo tana fadin jalal metayi maka.
ai jalal babu magana jan safna kawai ya keyi
[4:35PM, 12/9/2016] Fadeela lamido: í ½í²˜í ½í²í ½í²MIJIN MARAINIYAí ½í²í ½í²í ½í²˜
Story
&
written
Fadeela Lamido
Mmn yazeedí ½í³
70-72
Daker ummi ta kwaci safna ahannun jalal ta kaita dakin su .
da sauri ta juya ta nufi dakin jalal dan tana tsoron kar yagayawa alhaji dan idan yaji maganar
nan kashinta ya bushi.
tana shiga ta same shi sai faman share zufa yake tace jalal kardai maganar da mukayi dazun
ce tasa ka shiga cikin wannan halin ?
jalal yace ummi kefa kikace kin taba ganin su da idon ki
a,a jalal bahaka na ke nufi ba, karufa min asiri kar alhaji yaji wannan maganar, nidai nace
kayi hakuri kabari ayi mata test , kuma ko safnan ban ce kagayawa waba bare baban ka.
toh ummi ai bai kamata ayi shiro ba ya kamata kowa yasani.
nidai nace karka gayawa kowa, kai wlh duk kabi karice akan safna.
jalal kallon ummi yayi cike da ta kaici wato haryan zun tana nan akan bakan ta saita raba mu
, wai ita ummi bazata gyara halin taba ne, tana cikin wannan halin baza ji da abin da yake
damun taba.
yace shike nan ya wuce, ummi mikewa tayi ta fita, dasauri jalal ya dauki wayar shi yakira
safna bata dauka ba saida yakira sau biyar yaji shiru ya tabbatar safna fushi tayi mikewa yayi
yaje kofar dakin su yaji ta kulle, yasan ko ya buga ba budewa zata yi ba haka ya koma dakin sa.
washegari 8:00 jalal ya fito cikin shiri shi na tafiya office bayan yayi wa ummi sallama ya leka
dakin safna har yan zun kofar akule take, ya juya ya fita.
ummi ma guri 12:00 ta bar gida ta nufi yan mangorori, sai safna kawai ta rage agidan, dan
kairat ma tana makaranta.
safna na zaune ita daya agidan dan me aikin gidan ma tayi tafiya ga yunwa ta dame ta
rabonta da abinci tun jiya da rana gashi kuma yau hakanan ta tashi da son cin zogale .
mikewa tayi ta shiga kitchen ta duba bataga wani abu da ya bata Sha,aw ba bude wata roba
tayi nan taci karo da garin daddawa murna ce ta kamata tun daga nan tafara lasa tana lumshe
ido, da sauri ta daura miyar daddawa tana gamawa tayi tuwo ta dai dai cikin ta tafito falo ta fara
ci ,saiga kairat ta dawo makaranta, zuwa tayi ta zauna zata saka hannu dan sun saba cin abinci
tare.
kairat tace anty wannan miyar meye na ganshi baki.
safna tace kedai in zakici kici miyar daddawa ce.
da sauri tajanye hannun ta tana toshe hanci anty dama anayi miyar daddawa ne.
safna tace ke nidai kawai yunwa nakeji ,bayan ta gama cin towan ta dauki miyar ta fara sha
kenan saiga jalal ya shigo.
safna naganin jalal ta mike da miyarta ahannun ta zata bar wajen.
da sauri jalal yasha gaban ta ya tsareta da ido sai kallonta yake, itako kasa tayi da kai.
jalal yace miye wannan kike sha?
banza tayi dashi tana kokarin aje miyar dan ta samo daman guduwa tana aje miyar kuwa ta
mamaye shi ta sheka aguje ta shige daki.
jalal binta yayi da kallo yasan safna nashiga rufewa zatayi dan haka bebi taba.
tsugunawa yayi ya dauki miyar ya koma ya zauna yalli kairat dake kwance akujera yace
kairat faten meye wannan?
kairata ta kwashe da dariya tace yaya ba fate bane , miyar daddawa ce.
miyar daddawa kuma a ina ta samo shi?
ita tayi da kan ta tace yinwa takeji
yunwa babu kayan abinci ne a kitchen din sai daddawa, mikewa yayi yace kairat tashi kije ki
zubar da shi.
ummi bata dawo ba sai yamma jalal na zaune aharabar gidan yana shan iska , ummi ta
nufoshi tun daga nesa jalal ya fahin ci babu nasara.
bayan ta zauna jalal yace ummi akwai nasara kuwa?
ummi tace ba wata nasara jalal , yau nasha bakar wahala jalal , rabon da na wahala haka na
manta, munyi yawo nida tsohowar nan har mun gaji amman bamu dace ba, duk gidan wani
tsoho da yake garin muje amman babu lbrn ta, ummi ta fara share hawaye jalal ina cikin wani
hali banda me tausaya min duk duniyar nan sai kai, sai kuma yaya rabi dubi duk abin da na
mata bata juya min baya ba, amman dubi alhaji yana shirin ya juya min baya, babu ruwan shi
da damuwa ta kamar ma dadi yakeji.
ummi ki daina fadin haka kuma ki kwatar da hankalin ki insha allahu indai tana raye
za,aganta
ummi fashewa tayi da kuka to yanzo jalal inta mutu ne yaya zanyi kenan su baffa bazasu yafe
min ba.
jalal yace ummi insha allahu zasu yafe mike amman ummi kunje har gidan me unguwa?
ummi tace a,a
Jalal yace ummi ni gobe zanje na bin cika.
washe gari da wuri jalal ya fito yasamu ummi afalo kamar jira take ya fito , mikewa tayi tace
jalal mutafi.
jalal yace a,a ummi ki zauna agida ki huta.
ummi tace nidai kawai mutafi haka suka tafi badan ran jalal yaso.
suna zuwa gidan me unguwa suka tambaya aka nuna musu bayan sun isa sun tarar da wajen
cike da mutane dukkan su suka sakko suka isa gurin tare da sallama, ummi ce tayi bayanin
abin dake tafe da su.
me unguwa ya nisa yace da kamar wuya ku me yasa tuntuni baku nemeta ba sai yanzun,
aiko tana raye kila bata garin nan, har sun mike zasu tafi me unguwa yace amman bari akai ku
gurin babana kuyi mishi bayani ko zakuci sa,a ya fahimci me kuke fada, dan ya dade kwance
babu lfy.
bayan an kaisu gurin shi tsoho ne sosai ummi ta mai baya ni.
tsoho yayi shiru zuwa cen ya kira dan sa me unguwa yana magana ahankali me unguwa
yasa kunne me kake cewa baba.
baba tsoho yace karaka su gidan iya me kosai.
me unguwa yace baba ai iya ta dade da rasuwa.
sai gani hawaye sukayi yana bin kuncen baba tsoho ya sake cewa kukai su gurin danta
malam musa.
Me unguwa ya sake cewa baba malam musa yariga iya rasuwa sai dai matar sa
[9:31PM, 12/9/2016] Fadeela lamido: í ½í²˜í ½í²í ½í²MIJIN MARAINIYAí ½í²í ½í²í ½í²˜
Story
&
written
Fadeela Lamido
Mmn yazeedí ½í³
73-75
Da sauri ummi tace toh ku tai maka ku kaini gurin matar tasa.
suna fitowa ummi ta nufi mota mutumin da me unguwa ya hada su dashi yace hajiya ai mota
bata shiga unguwar.
nan suka bar motar suka yanka a kafa tafiya suke tafiya taki karewa ummi ta gaji jalal yace
ummi ko zaki zauna ki huta ne?
a,a jalal mu tafi kawai kafin su isa ummi taci bakar wuya takalmin ta har ya bare zufa ke
yanko mata ta ko ina kafar nan futo futo kamar ba itaba, suna zuwa ya nuna musu gidan.
ummi ce ta shiga jalal yana waje
sallama tayi acikin gidan ,goggo ta taho da sauri tana fadin hajiya batan kai kikayi ne
ummi tace a,a baki ne mu , munzo gurin mijinki sai muka same lbrn rasuwar sa.
goggo tace ayya malam ai ya dade da rasuwa, shigo ki zauna dauko tabarma tayi ta shin fida.
ummi ta zauna tana fadi ba zama ma zamuyi ba muna sauri ne.
goggo tace ai ban shai da kiba hajiya kin dai yimin kama da wata wadda na sani.
cikin murna ummi ta gayawa goggo abinda yake tafe da ita.
goggo tace ikon Allah ni ko na san saudatu kishiya ta ce tunda malam ya tsunto ta shekarar
ta uku babu wanda yazo neman ta dan haka malam ya aure ta amman Allah yayi mata rasuwa
tare da malam sukayi hatsarin mota su rasu.
da karfi ummi tasa ka kuka , jalal dake waje yaji kukan ummi ya shigo aguje.
yana shigowa ummi ta fara cewa