Showing 15001 words to 18000 words out of 47874 words

Chapter 6 - Mijin Marainiya Book Complete Hausa Novels by Fadila Lamido .pdf

16 Mar 2025

4064

tashige cen longu ta zauna
ta fara shafa mai, acikin hijjab take shafawa jalal Nata kallon ta, cen yace bazaki gaishe ni
bane, kafin ya rufe baki tace ina wuni, shiru yayi sai cen yace bazan amsa ba, saida naroka,
safna tace ina fa shirin gaisheka kayi magana.

toh nidai bazan amsa gaisuwa daga nesa ba, saikin matso kusa dani.
safna tana kokarin ajiye man shafawa tace inazuwa bari nasa kaya.
a,a kizo ahaka.

anty tana gefe ta jin su tace ke dauki kayanki kishiga bayi ki saka, wai dama jalal ashe baka
da kunya haka, agaba na .

jalal yace to menayi kuma daga nace ta matso kusa dani.
safna bata saurari me suke cewaba tashiga bayi tasaka kaya dogowar riga tasaka na atamfa
tayi kyau duk da bawani kwalliya tayi sosai ba, ta dora karami hijjab akai sannan ta fito, gurin
jalal ta nufa tace ina wuni, mamayan ta yayi ya rike hunnuwan ta, yace tsorona kikeji kuma.
tsugunawa tayi tana boye fuskar ta cikin cinyoyinta shiko jalal yana rike da hannuwan ta
yana kokarin daka kanta, ciki ciki suke sosai safna da jalal waishi dole sai yaga fuskarta
itakuma taki bari ,
safna taga jalal yafi karfinta dan haka ta fara kiran anty kin ganshi ko?


anty dake gefe tana kallon ikon Allah tace wlh jalal zan bata maka rai, ko kunyata bakaji
nazama babba banza kenan .

dasauri ya sake ta yana fadin na bari Anty na mance ne, ya mike yace bari naje anty , yaza
ayi maganar kunshin ?

karka damu yanzun zankai ta amman inaga acen zan barta ta kwana dan naga bawani
gyara da aka mata.

jalal yaja ya tsaya anty kuma harda kwana toh abar kunshin mana ai badole bane


kallon jalal tayi tace ai yan zon baka da ikon hanata fita saika bari sai an daura auran.


**********

haka anty nusaiba tadauki safna ta kaita gidan kawar ta hajiya asata me ygara amare, hajiya
asata tana ta yiwa anty ko rafin me yasa ba,akawo ta da wuriba sai ana jibi biki.

bayan anty ta dawo gida tasamu alhaji awaje ranshi abace saboda ummi ta kitsa mashi
magan ganu iri iri.
tun daga nesa alhaji ya farawa anty nusaiba fada, nusaiba ina kukaje har dare yayi haka?
wlh yaya nakai safna kunshi ne.
shine kuka kai dare haka, to yanzun ina safna.

yaya tana cen sai gobe zan koma nadauko ta.
alhaji ya fara fada ta inda yake shiga battanan yake fita ba.
lokacin da nusaiba ta shiga ciki ta samo ummi da kawayen ta sai shewa suke suna ganin
nusaiba suka fara yadda habaici.
Madina ta kalli dayar dake kusa da ita to amara kirjin biki komai shishige wanki dai, dan nan
namu ne, kuma duk inda akaje dole adawo
[8:23PM, 12/3/2016] Fadeela lamido: í ½í²˜í ½í²í ½í²MIJIN MARAINIYAí ½í²í ½í²í ½í²˜

Story
&
Written
Fadeela Lamido
Mmnyazeed🐽

46-50

Nusaiba bata ci gaba da sauraren suba ta wuce dakin safna, anan ta samu su hajiya fatima,
tace ya naga kun dawo nan kuma. hajiya fatima tace to me gidan tace mushiga daga ciki zatayi
baki, shiyasa muka yo nan.

anty nusaiba nisawa tayi tace anya kuwa zamu zauna agidan nan har agama biki, kodai
zamu koma gidan hajiya ne muyi namu acen, dan nifa gaskiya bazan dauki wula kanciba .
Hajiya fatima tace nima nayi tunanin haka amman saina tuna hajiya fah da zamu taho tana
ta gargadin kar muce zamuyi fushi muyi hakuri da duk abin da muka tarar dan haka gara mu
hakura mu zauna ko dan kan ran hajiya ya baci.
nusaiba tace bari na kira hajiya muyi shawara, ta daga waya ta kira hajiya ta gaya mata halin
da ake ciki har fadan da alhaji yayi mata, ran hajiya ya baci tace kark taho ku zauna nima gobe
zan taho da Jama,a ta,

washe gari kuwa saiga hajiya ta dira agidan dan nata, da misalin 10:12 am rabonta da gidan
tunda tazo barkan abduljalal.
jalal na zaune shida wasu abokan sa, ya hango hajiya na fitowa daga muta da sauri ya
karaso yana cewa hajiya lfy kuwa?
hajiya na murmushi tace nazo bikin mijina ne.
Jalal yace hajiya kodan kishin nan bakiyi ne kama hannuta yayi, ya waiga gurin da abokan sa
suke yace faisal kuzo ga amaryar ta iso, dariya sukayi suka matsu suka gaida hajiya sannan
sufara diban kayan da sukazo dasu suna shiga dashi cikin gida.

ummi na zaune ta fara ganin ana shigo da wasu kaya tace wannan kayan fa daga ina?
daidai lokacin jalal yashigo yana rike da hannun Hajiya, ummi ta mike tana fadin sannu da
zuwa, hajiya ta amsa Mata ba yabo ba fallasa, sannan tace ina su nusaiba ban gansu afalon
ba, ko basukai su zauna anan bane.
ummi tace a,a ba haka bane naga dai sun fita tun safe, ina sukaje?
basu gayamin inda za suje ba.
hajiya ta sake cewa me gidan fa baya nanne, ummi tace yana ciki bari na kira shi
da saurin shi ya fito yana fadin hajiya da kanki, Allah yasa dai lfy, lfy nazo ne ayi komai akan
idona dan ni bana son tashin hankali, nidai na gargadi iya laina kaima inason ka gargadi matar
ka bama son tashin hakali.

alhaji yace hajiya ki kwantar da hankalin ki babu wani abunda zai baru.
tace toh nima ai nafi son haka.
wayar alhaji ce tayi kara ya dauka bayan ya sauke wayar yace ina nusaiba cikin sauri ummi
tace bata nan ta fita.
alhji yace kash gashi kuma kamafani da zasu kawa kayan safna sun isa gidan.
Hajiya tace ka Kira ta awaya mana.
kafin hajiya ta rufe baki, ummi tace alhji key na wajan tane.
a,a gashi agurina nusaiba tace ya kamata mace ta tsaya agurin.
ummi tace hakane alhji toni ai da nasan gidan da naje, alhji dadi yaji sosai yace ai jalal
nannan awaje sai ya kaiki.
hajiya taso ta hana sai kuma taga karta cika takura masu dan haka tayi shiru.
itako ummi dadi taji dan dama jira take afadi gidan da jalal zaizauna su cika kudurin su ita da
kawar ta madina.

bayan sun dauki hanya dukkan su gaba suka zauna ummi ta daga waya zuwa cen tace dona
madina tama bayani ko ? , jalal beji amsan me aka bataba, ta kashe wayar tana murmushi Kara
kiran wayar tayi tace madina har yanzun baku zoba, nagaji da jira gani ma zantafi gidan danki
za a zuba kaya agidan , bayan ummi ta gama waya jalal yace ummi naga kina shashshare bikin
nan ne.
tace ba haka bane jalal aini babu wadda yakaini farin ciki ayanzun na fahimci kana son safna
da yawa dan haka nima na fara jin Ina sonta , saidai abu daya yake damu na , ban so ka aure
yariyar da sultan yayi soyayya da ita ba, saboda sultan fa dan duniya ne.
Jalal be gane inda ummi ta dosaba yace ummi ki daina tuna wannan yariga ya wuce kuma
sultan ai babu abinda ya isa yayi min, nidai burina kawai adaura auren.

ummi ma ta gane jalal be fahimce taba, da wannan tunani suka isa gidan, kan kace meye
har angama gyara gidan, ummi tsayawa tayi tana kallon dukiyar da aka zuba agidan, alhaji ya
kashe kudi saikace kairat zai aurar, badan madina tace tabi komai ahankali ba toh da yau
saisun kwashi rigima da alhaji, haka suka kamo hanya ita da jalal amota jalal sai santin gidan
yake.
gani inda yake ta murna ummi tace gaskiya jalal guri yayi kyau.
cikin murmushi ya waigo yace ummi ai bakiga kyauba sai safna ta shiga gidan, zakiga yadda
zai kara haske.
kulewa tayi sosai amman bata bari ya gane ba tayi mai murmushi kawai.
Jalal kuwa dadi yaji ummi ta fara son safna tuni ya nemi haushin ta da yakeji da ya rasa, dan
haka yashiga zuba mata shagwaba, ummi kinsan menene?
tace a,a yaro sai ka fada.
yace safna fah sai kin dan mata fada bata sakin jikinta dani, kamar ma tsorona takeji kuma
dacen ba haka take minba, cikin shagwaba ya fadi maganar.

ummi daurewa tayi tayi murmushi tace jalal manya, kabari mana adaura aure duk zata Bari
da haka suka isa gida lakacin yamma tayi sosai, tana shiga falon sukayi ido hudu da safna
tana kusa da hajiya a zaune ganin tayi ta kara kyau da sheki gawani zanen filawa wadan tunda

take zuwa bikin yaran kawayen ta bata taba ganin wada yakwai haduwar wannan ba, sai satar
kallota take , tare da kara jin haushin anty nusaiba tasan tayi ne dan jalal ya rikice, bayan ta
gaida hajiya ta shige dakin ta.
hajiya ta kalli safna tace me yasa baki gaishe da ummin ku ba, maza ki bita daki ki gaida ta.
safna tashi ga da sallama ummi ta dago ta kalle ta, tace yaushe kuka dowa?
tace bamu dade da shigowa ba.
tasake cewa jalal yasan kundawo? nima basan ko yasani ba, tabe baki tayi tace fita kibani waje.

da daddare gidan ya kaceme gidan biki sosai sai haya niya ake aharabar gidan kuwa su jalal
ne da abokan sa sai hayaniya sukeyi.
zuwa cen kawayen ummi suka fara shigowa wannan karon basu tsaya a falo ba barayin ummi
suka shiga, zuwa cen suka saki sauti.


bayan ansaka safna alalle tana ta kuka yau itace za,ama aure ba dangin ta ko guda daya ita da
zata samo ko goggo ce tagani agurin bikin nan da zatayi farin ciki da haka da ace babu kowa
nata kasa bacci tayi sai juye take babu wadda tafi fado mata arai kamar iya taso Allah ya bar
mata iya, haka taita share hawaye dan bata son anty nusaiba ta juwota, daga cen ta fara jiyo
muryar alhji yana fadin innalillahi wa,ina ilaihir raju,un sai maimaitawa yakeyi mikewa tayi ta
zauna ,tana kallon su hajiya suka fita akabarta ita kaidai adakin, dan haka tabiyo bayan su, gani
tayi duk sun tsaya sunyi cirko cirko, alhaji ko sai share zuba ya keyi jalal na gefe daga shi sai
gajeren wando, ummi kuwa sai rusa kuka take, cikin rudu safna tace me yafaru?
anty nusaiba tace karku gaya mata saida safe.
ummi tace ai gara agaya mata tunda kowa yasani, safna gidan da zaku zauna ya kone babu
abinda aka dauka acikin sa.
safna neman kujera tayi ta zauna ta rufe ido bata sam ma me zata ceba.
jalal kuwa kansa akasa yake, yaki dagowa.
alhji yace bakomai kowa ya koma ya kwata saida safe Allah yasa haka shine mafi alheri.
ummi tace ai alhji bamuga ta barciba munfah gaiyata muta ne gashi gobe ne daurin aure,
yaka mata asan abinyi, ni ina ganin kawai adaga bikin kawai hankali kwance.
bata gama rufe baki ba jalal yace ni gaskiya ban yaddaba ummi, ni dai kawai ayi.
cikin fada alhaji yace kai jalal baka da kunya ko ya manya suna magana zaka saka baki, ai
biki yazama dole adaga shi, wuce kaba mutane waje.
da sauri yabar wajen ya shige dakin shi ya bogo kofar.
hajiya tace toh yanzun kayanke hukunci ne kabamu umarni mu watse koko shawara kake
nema.
sai lokacin ya tuna mahaifiyar shifa tana wajen dan haka yace hajiya kiyi hakuri nayi kuskure,
shawara nake nema yanzun yaya kamata ayi.
hajiya tace toh nidai ban yadda adaga ba kowa yaci gaba da abinda yake biki nanan babu fashi


07014197556.....âœ
[8:48PM, 12/4/2016] Fadeela lamido: í ½í²˜í ½í²í ½í²MIJIN MARAINIYAí ½í²í ½í²í ½í²˜

Story
&
written by
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📊

51-53


Alhaji yace shikenan hajiya duk inda kikace haka za,ayi,haka kowa ya koma ya kwanta kowa
zuciya babu dadi, jalal kuwa bayan ya koma daki kuka ya saka gidan da aka dade ana ginawa
saida aka gama kashe kudi, zargi kala kala ya ziyarci zuciyar shi gaskiya yana zargi sultan da
mahaifiyar shi ,kafin safe idon jalal yayi jazur sun dan tasa .
karfe bakwai jalal ya fito sanye da jallabiya fara sol , da bakin glass a idon sa, saboda baya
son afahimci halin da yake ciki , saida ya fara gaida su hajiya sannan ya wace dakin alhaji, yana
shiga yacire glass din ya rike ahannun shi, alhaji ya kalli jalal yace wai kai ba kasan kaddara
bane ji inda fuskar ka ta koma saikace ba musulmi ba. Jalal yace daddy ba haka bane abin da yake bata min rai nasan gidan nan kona shi akayi
kuma wlh nasan bazai wuce sultan bane dan nasan shi kadai ne zai min haka.
dakatar dashi alhaji yayi cikin fada karna kara jin kafadi wannan maganar mubarwa Allah
kawai shiyafi, kuma daurin aure nanan insha Allah ajima za,a daura .
dadi sosai jalal yaji yace daddy nagode yana fitowa dakin ummi ya shiga suna saune ita da
wata kawar ta data kwana agida.
ummi tace kardai kacemin kuka ka kwana kanayi jalal kana sone kayi kanka illa akan yariyar
da badamuwa tayi dakai ba.
dokar dakai yayi yace ummi me yasa kikace haka, ni nasan safna nasona kawai domuwa ne
ya mata yawa shiyasa ma nafi son adaura auran ko hakalin ta zai kwanta, nima kaina hakali na
ba,a kwance yake ba bare kuma safna.

hajiya adama kawar ummi dake zaune agefe tace rabo da ita jalal kaji , ance maganar bikin
nanan ko?
eh yana nan in Allah ya yarda
hajiya adama tasa ke cewa toh yanzun a ina zaka zauna kenan?
yace nima ban sani ba.
jalal ya gaji da tambayoyin su dan haka yace ummi bari naje

bayan ya fito yayi tunani yaje yaga halin da safna take ciki dan haka ya doshi daki, dakin cike
yake da mutane, su anty nusaiba ne sauran dai duk besan suba, bayan yagaida su, ya hango
safna daga cen bayan anty nusaiba, yace anty dan turomin yariyar cen, yajuya zaita fi anty ta

tsaida shi tace zoka zauna kuyi maganar adaki dan abin ya fara bani tsoro, mikewa sukayi suka
fita jalal yashigo cikin dakin ya zauna abakin gado yace safna tashi mana, ke wacce irin amarya
ce har yanzun kina kwance.

mikewa tayi ta gaida shi, jalal yace safna kinji abinda ya same mu ko, dan Allah karki ce
zakisa wannan abun a zuciyar ki ya dame ki,
tace bakomai yaya Allah yasa haka shi yafi alheri
ameen safna .
ta sake cewa yaya me yasame ka a ido naga yayi ja?
jalal yayi mamakin ya akayi ta gani bayan ba kallon shi take ba kanta akasa, dariya yayi yace
ta yaya akayi kikaga idona bayan ba kallona kikeba?
juyar da kai tayi tace nifa gani nayi kamar yayi ja
Eh ai naji shine nake tambaya ko kina da ido ne atakiyar kai dan ni kanki kawai nake gani.
safna bata ce komai ba tayi shiro tana wasa da yatsun hannun ta.
daidai lokacin aka kirashi awaya yadauka yana fadin amir kun iso ne, ok to ganinan zuwa.
juyawa yayi yakalli safna yace, yarinya zama ki bari ne, dan yau a gado daya zamu kwana.
dasauri ta kalli jalal ta sake yin kasa dakai.
jalal yace a,a ki kalleni da kyau.


karfe 2:30 Jama,a da dama suka shaida daurin auren abduljalal da safna acikin wa,inda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login