Showing 27001 words to 30000 words out of 39853 words
Chapter 10 - MIJI GOMA Book Complete By Sadiya Abdul.pdf
ta ruguje yardar da aka yi mata akan Maryam,
shiyasa ta ga gara ta yi mata kisan mummuƙe, ta so a ce ta ƙi aure kamar babarta, yadda za ta
fake da dama gado ta yi, sai ga shi ta tsayar da Nazifi, don bayan auren ƙanwarta Fatima sai
Baba ya matsa da zancen auren nata.
Tabbas Maryam ta shiga ƙunci, ta ji baƙinciki da takaici, ta yi kuka tsakar dare ta share, wanda
ta saka a ranta ba za ta sake hawaye saboda butulcin babarsu a gare ta ba, sannan ta saka a
ranta ko da wasa ba za ta taɓa nuna mata ta san mummunan ƙudirinta a kanta ba, Uwani ta
nuna mata so, ko da a ce ba so ba ne duka taku ne to fa tabbas ta yi ƙoƙari, don wasu ba sa iya
sarrafa kansu har su danne ƙiyayyar mutum, sannan ta kasa yarda ma da cewar Uwani ba ta
sonta, kawai ta fi yarda da shaiɗan ne da zugar ƙawayen banza ya sa take aikata mata haka, ko
kuma ta ce ta aikata haka a baya, saboda komai da Uwani ta yi mata na hana ta zaman aure ya
wuce a zuciyar Maryam, ta saka a ranta yanzu sabuwar rayuwa za ta fara yi, sai yanzu ta gane
tabbas ta yi kuskure, ta kuma yi nadama.
Baya ta wuce, yanzu ta gaba ake yi, gaba ake iya gyarawa ba baya ba, don haka dole za ta yi
gyara a rayuwarta, yanzu ita dai ba za ta fito ƙarara ta nunawa Uwani ta ajiye zancenta na miji
goma ba uba goma ba ne, saboda shi maƙiyi ba ka ba shi ƙafar sanin abin da yake ranka,
saboda kar ya canza taku ya shigo maka ta bayan gida.
A wannan daren Maryam ta ɗaukarwa kanta wani alwashi, ta ƙudure a ranta tabbas sai ta ba
wa Uwani kunya, sai ta rusa mata burikanta, kuma ta hanya ɗaya hakan zai tabbata shi ne ta
ɗaura ɗamarar jure zaman aure, ta saka a ranta za ta yi aure na mutu-ka-raba, idan ta gama
idda ta yi aure ko wa ta aura, kuma ko wace matsala ta tarar a gidan auren, za ta yi haƙuri da
ita, za ta zauna ta jure duk wani ƙalubale, kawai saboda mafarkin Uwani ya zama ƙarya.
Duk da tana kallon abun da kamar wuya gurguwa da auren nesa, saboda ta riga ta ginu a kan
kalaman Uwani na ƙanzon kurege, ta san ba abu ba ne mai sauƙi a ce a lokaci a ɗaya ta sauka
daga kan wannan hanyar da ta yi nisan tafiya a kanta, wannan ƙudurin da ta ɗauka daidai yake
da mayar da kanta ƙasƙantacciya, a yanayin halittarta dama can ba ta da haƙuri, to ta ya za ta
koyi wannan haƙurin ta dinga jure halin mijin da za ta aura ko yaya yake? Wannan shi ne
babban ƙalubalen da take ganin za ta fuskanta, amma ta saka a ranta za ta jure ta kuma haɗa
da addu'ar Allah Ya tallafe ta Ya zama gatanta.
Duk wata jarumta da dauriya Maryam ta yi, wajen nunawa Uwani ba ta gano komai na shirinta
a kanta ba, ita kuwa Uwani da ba ta san wainar da Maryam take toyawa a zuciyarta ba sai ta ci
gaba da biya mata karatunta, wanda sai yanzu ne Maryam ta ƙara gasgata lallai ita doluwa ce a
baya ta yi wasa da damarta.
Ba ta ma gama tsinkewa da lamarin ba sai ranar da Murja ta yo yaji, saboda mijinta zai ƙara
aure, ta ce ita wallahi sai dai ya sake ta, tun kafin Uwani ta ce wani abu a kai Maryam ta yi farat
ta ce"Lallai wannan miji naki akwai ɗan banza! Duk zamanku nai ƙara aure ba sai yanzu?
Wallahi kar ki yarda, da ki zauna da kishiya gara ki yi zaman gida, ai miji goma ba uba goma ba
ne".
Uwani ta yi wuƙi-wuƙi ta ce"Amma Murja wa za ki barwa ƴaƴanki?"
Maryam ta ce"Ƴaƴa kuma ai dama tarbiyyarsu a hannun Allah take, ta bar masa su can su
ƙarata ya riƙe su, ta nemi wanda ya fishi ta aura, ai wallahi wanda ya rasa Anti Murja shi ya yi
asara, kalle ta fa sankaɗaziyya da ita, ƙila ma ta samu wani saurayin ya yi wuf da ita".
Murja ta yi dariya ta ce"Kai Maryam, ni kuwa wani saurayi ne zai kwashe ni? Kina kallon yadda
wahala ta fara mokaɗar da ni?"
Maryam ta gyara zama har da kamo hannun Murja ta ce"Wallahi Anti Murja ni nan na yi miki
alƙawarin sai na samo miki miji na gagari ko ba saurayi ba, ke dai ki yi ƙoƙari ya sake ki kawai,
ina haihuwa na tsige yaron ko yarinyar mu fara falla zawarci, yasin sai na wayar da ke, idan kika
fantama a gari sai an taro ki, wai wa ya ga Anti Murja a gaban motar wani Alhajin!".
Ta kwashe da dariya tana kallon yadda fuskar Uwani ta nuna rashin jin daɗi, hakan kuwa ya
ƙara raunana zuciyarta tabbas wata kishiyar uwar ba uwa ba ce, kuma ba za ta zama uwar wani
ba har abada.
Maryam ta dage ta dinga zayyanowa Murja jawabai, tana kwaɗaita mata yadda rayuwar zawarci
take, Uwani ƙarshe tashi ta yi ta fice daga ɗakin, ta fara kiciniyar ɗora girki gabanta yana
faɗuwa da fargabar kar fa Maryam ta yiwa Murja huɗuba, ta zo ta kashe aurenta ta rasa miji,
tun da dama can sai da ta basu rubutun farinjini suka samu mijin, tana buduruwa ma kenan, ina
ga yanzu da ta yi haihuwa huɗu? Lallai dole ta yi wa tufkar hanci, amma ta yadda Maryam ba
za ta gano komai ba.
Ta ƙwallawa Murjar kira, ta fito, Uwani ta rufe ta da faɗa"Kin shige ɗaki kin bar ni da aiki, ni zan
yi muku girkin kenan ko? Sai surutan banza kuke yi kamar yau kuka taɓa sanin juna?"
Maryam ma ta fito, Uwani ta ƙaƙalo murmushi ta ce"La Maryam ba da ke nake ba, ke ai kin yi
nauyi, ina ke ina aiki? Ki koma ki yi kwanciyarki".
Maryam ta koma tana tunanin shin ta zuga Murja ta kaso aurenta saboda Uwani ta ɗanɗani
baƙinciki, ko kuwa Murjar za ta kalla da matsayin ƴan'uwantaka da ke tsakaninsu ta ƙyale ta?
*Mun kusa gama free page fa, za ku iya biyan kuɗin karatunku 500 kacal ta nan*
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay
Ko ta nan
1869739740
Sadiya Abdulrazak access bank
08028966015
[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_
*SADIYA ABDULRAZAƘ*
*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne
hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman
aure?*
Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu
*FIRST CLASS WRITERS*
https://chat.whatsapp.com/G08KLEmlF3gJ3X4npkfIee
PAGE 12
Jin shiru babu motsinsu a tsakar gidan sai ta leƙo ta kuwa ga wayam, alamun suna cikin
ɗaki, ta fito ta nufi ɗakin ta laɓe jikin labule tana sauraron su, daidai sanda Uwani take cewa"Shi
ne za ki biyewa shirmenta? Ita ba ki ga kalarta ba? Kin manta da farinjininta? Ko kin manta sai
da na karɓo muku taimako kafin ki samu mijin? Kina buduruwa ma kenan, ina ga kin zama
bazawara? Maza ki tattara ki koma ɗakinki, kishiya ba kanki farau ba, ni ma na zauna da ita
ballantana ke!".
Murja ta ce"Amma babarmu..."
Ta daka mata tsawa ta ce"Rufe mini baki! Wallahi sai kin koma, uzuri ɗaya kawai zan yi miki za
ki zauna har sai ya zo biko, amma yana zuwa to wallahi ƙafarki ƙafar shi, ni za ki ja wa abun
magana a gari?"
Daga nan Maryam ta ja ƙafa ta koma ɗaki jiki a sanyaye, sannan ta yi kokowa da zuciyarta da
take ta faɗa mata ta zuga Murja, ta raya a ranta ƴar'uwarta ce, idan ta cuce ta kanta ta cuta,
haka kuma idan an kasa gulmarta a tire ba za ta ji daɗi ba, don haka ta share su, kwananta biyu
a gidan mijin ya zo, ai kuwa ko Baba ma bai shiga zancen ba, ita ce ta sasanta su, ta bi shi
suka tafi, suka ci gaba da zamansu shiru abunsu.
Nasiru ya zo ya kawowa Maryam kayan abinci, sannan ya ba ta kuɗi don a yi siyayyar jariri,
a haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har Allah Ya sauke ta lafiya, ta haifi ɗanta namiji, aka yi suna
yaro ya ci sunan mahaifin Nasiru Yusufa, suna ce masa Abba, duk wata sai ya zo ya ba ta dubu
ashirin, amma sam bai yi zancen kome ba, wanda a lokacin a yadda Maryam take ƙishin yin
aure da burin ta yi zaman aure babu abin da zai hana ta yarda ta koma gidan nasa, sau tari
takan tuna da Nazifi ta ce dama ya dawo ya ce ta koma da za ta zauna da Gwaggo lafiya, to
amma damarta ta wuce sai dai ta gaba, sai ta ci gaba da kula da ɗanta, ta kuma koma
kasuwancinta, tana ra adana ribarta.
Taimako ɗaya da Allah Ya yi mata ma shi ne tana da farinjinin masoyan, wannan karon ma tun
kafin ta yaye Abba maza suka fara sallama da ita, sai dai ta ce musu sai ta yaye ɗanta. Akwai
wani Alhaji Haruna da suka haɗu da shi a kasuwa, ya fi kowa naci cikin masu sonta, don har
cewa ya yi zai aure ta a hakan, amma ta ce a'a sai ta yaye, ita bai ma wani kwanta mata sosai
ba, saboda yana da matarsa da ƴaƴa huɗu, ita kuma tana da kishi, sam ba ta son zama da
kishiya, amma ta sani tun da ita ma yanzu ba buduruwa ba ce dole ta jingine burinta a gefe,
aurenta uku da ƴaƴa biyi ba zai yiwu ta ce sai saurayi ba, don haka take ɗan kula shi.
Sanda ta yaye Abba ta fara zancen aure sai Nasiru ya ce to zai ɗauki ɗansa, don har ma ya yi
wani auren, nan Uwani ta fara subaɗaɗi tana cewa a bar mata shi, a cewarta yaron ya shiga
ranta, ba za ta iya rabuwa da shi ba, ita kuma Maryam ta fi zargin wannan dubu ashirin ɗin da
yake kawowa duk wata ce ta ruɗe ta, don haka ta ce a'a gara ya ɗauke shi ɗin, ba ta so a ɗora
mata wahala, haka dai Nasiru ya ɗauki ɗansa, gidan iyayensa ya kai shi, tun da ba a daɗe da
yin auren na shi ba, kar ya hana su cin amarci, duk sati ake kawo mata yaran nata su wuni
wataran ma su kwana ɗaya sai a mayar da su, tana jin babu daɗi a ranta, saboda fargabar
yadda tarbiyyar yaran za ta kasance, idan ba ƙaddara ba me zai saka uwa tana raye a raba ta
da ɗanta? Haka dai take danne damuwarta tana bin su da addu'a, kwanciyar hankalinta ɗaya ce
duk mariƙan yaran suna son su, ba ta ga alamar wahala a tare da su ba.
Wata ɗaya da mayar da Abba, Alhaji Haruna ya zo da zancen aure faka-faka, ya ce sati biyu
za a saka, Maryam da yake har lokacin ba sosai take son shi ba sai ta fara yi masa
kwana-kwana, a wannan karon aure take son yi na har abada, saboda haka yana da kyau ta
samu wanda zuciyarta ta amince da shi ɗari bisa ɗari, shi auren wanda kake yi wa so sahihi fa
yana da alfanu, saboda idan zama ya yi zama saɓani ya fara shiga tsakaninku wannan son da
kake yiwa mutum yana taka muhimmiyar rawa wajen haƙurtar da zuciyarka ka ci gaba da zama
da shi, kana jure wasu abubuwa, saɓanin wacce ta yi auren manufa babu son miji a zuciyarta,
daga wannan abin da ta aure shi don shi ya gushe, shikenan sai ta tsane shi, tun da dama babu
so tun farko, idan kuwa ka tsani mutum ba za ka taɓa yi masa uzuri ba, komai ya yi na laifi sai
ka yi masa hukunci.
Ƙiri-ƙiri Uwani ta nuna ba ta son wannan auren, saboda ganin yadda Alhaji Haruna yake son
Maryam kamar bai taɓa aure ba, sai bushasha yake yi mata da kuɗi kamar ba ya so, da alama
duk ya fi mazajen ƴaƴanta rufin asiri, dama mijin Mardiyya shi ne abun tutiyarta da nunawa a
gari ƴarta ta yi goshi tana auren mai kuɗi, sai ga shi Maryam za ta dusashe tauraruwar
Mardiyyar, don haka ta ɗauki hassadar duniya ta saka a ranta, ta yi ta zuga Maryam a kan kar
ta aure shi, ta ce"Ke yanzu Maryam da ajinki da kyaunki da komai za ki auri babban mutum mai
mata da ƴaƴa huɗu? Ni sai nake ganin kamar kin faɗo"
Maryam ta yi murmushi ta ce"Ba faɗuwa ba ne babarmu, kin ga zaman gidan ba shi da wani
amfani, kuma idan kika duba kika gani ni ma fa kullum ƙara girma nake, ban yi ƙanƙantar da za
a ce Alhaji ya yi mini girma ba, saboda haka wannan ba komai ba ne, Allah dai ya ba mu zaman
lafiya".
Uwani ta ce"Amma Maryam za ki iya zaman kishi kuwa? Ba mu san halin matarsa ba".
Ta ce"Babu ruwana da ita, ba zamanta nake yi ba, idan kin ji kanmu to ita ce ta so hakan".
Duk inda ta yi sai Maryam ta tare, haka dai ta rabu da ita ta zubawa sarautar Allah ido, tana jira
a yi auren ta ji ta ina matsala za ta fara, ita dai ta san a yadda ta tafi haka za ta dawo, ko ta
dawo da ciki ta ƙara haihuwa a gida, haka za ta yi ta rabon yara gida-gida.
Sai da Alhaji Haruna ya je wajen Baba da ƙoƙon bara kan a yi wa Maryam magana ta amince
da auren da wuri, saboda babu amfanin jinkirtawar, Baba ya zaunar da Maryam ya yi mata
nasiha sosai, saboda ya yaba da hankalin mutumin, kuma shi ma a yanzu ya fi so ta auri babba,
kamar zai fi haƙuri da halinta, saɓanin yara da ƙuruciya kawai ake zabgawa a zaman auren, ya
faɗawa Maryam shi Alhajin ya ce zai yi mata komai na kayan ɗaki, don haka ba ta da wani uzuri
na cewa ba ta shirya ba, ta ce shikenan ta amince, Baba sai ya bi ta da kallon tausayi, ba ya jin
daɗin wannan mace-macen auren nata, ga shi kwana biyun nan ya ganta duk a sanyaye kamar
tana da wata damuwa, duka ta rage tsiwa har ma yawon bin ƙawaye.
Yayin da Maryam ta amince da auren Alhaji Haruna, shi kuma yana can ana gumurzu a gidan
shi, matar shi Rabi masifaffiyar mace ce, tun da ya yi zancen ƙara auren shikenan ta kasa
zaune ta kasa tsaye, sai tijara take yi, amma shi ya ce mata aure babu gudu ba ja da baya, sai
ya yi, wannan ne karo na uku da yake niyyar yin aure, amma sai ta je gidan su yarinyar ta tada
tarzoma har a fasa, don haka wannan karon sai ya zaɓi sanarwa Maryam halinta.
Ranar ya zo zance yake cewa"Maryam a gaskiya ba zan ɓoye miki ba, matata ba tana da kishi
sosai, tun tuni nake son ƙara aure ta hana ni, dama kuma dai lokaci bai yi ba, amma a yanzu
ina ji a jikina ke ɗin ce ta aure in sha Allah! Saboda na shirya fito na fito da ita a wannan karon".
Maryam ta ce"A'a don Allah ka lallaɓata, kar ka rabu da matarka saboda ni".
Ya ce"Ba zan rabu da ita, amma aure dai babu fashi, ke kuma sai ki shirya zama da ita, kar ki
ce za ki rabu da ita ta ci tuwo a kanki, ku zauna lafiya dai kawai saboda ni ma hankalina ya
kwanta, tun da kin ga gida ɗaya za ku zauna".
Maryam ta ce"Ni idan da hali ka raba mana gida mana".
Ya ce"Wallahi haka na tsara tun farko, ginina na mata biyu ne ita ma ta sani kuma tun da na
gama ginawa na sanar mata zan ƙara aure".
Ta ce"To shi kenan, Allah Ya sassauta zuciyarta".
Ya amsa da amin, sannan ya nuna mata vedion gidan a waya, gida ne babba mai kyau, daga
farfajiyar tsakar gida babba sai a shiga babban falo, mai ɗauke da manyan kujeru, kayan kallo
da firji komai dai an saka falo ya haɗu, akwai dining a ciki, sai kitchen da banɗaki, sannan a
shiga cikin gidan, ɗakin da zai saka Maryam ɗin ne a farko, ciki da falo da banɗaki a ciki, ita ma
na uwar gidan haka yake, sai ɗakin shi da kuma ɗakunan yara guda biyu, sannan wani
banɗakin a tsakar gida, ga bantileson mai ɗauke da shuke-shuke da famfuna, gidan ya burge
ta, ta miƙa masa wayar tana cewa"Ma sha Allah ya yi kyau".
Ya ce"Zuwa gobe jibi za a gama kayan ɗakinki, sai a saka, zan ba ki kuɗi sai ki sayi kayan
kitchen ko? Gobe muka yi da ƴan gidan namu za su kawo kayan lefe".
Ta ce"Allah Ya kaimu".
Ya ɗan yi jim kafin ya ce"Don Allah ku yi haƙuri da abin da ƙila ƴan'uwana za su iya yi a yayin
kawo lefen, kin san da yake Sauda ƴar'uwata ce, auren gida aka yi mana, kuma ita Innar tawa
ita ta riƙe ta tun tana ƙarama, da ta isa aure ta aura min, to yanzu haka tana nan tana