Showing 24001 words to 27000 words out of 39853 words
Chapter 9 - MIJI GOMA Book Complete By Sadiya Abdul.pdf
ya yi aure, ta ce"Hamza idan za ka kore ni ba sai ka yi mini ƙarya
da gida ba naka ba ne, idan ka yi haƙuri dama ni ma wannan zaman da nake yi ba ni da niyyar
komawa, saboda haka ka sallame ni kafin ka tafi inda za ka je".
Ya ce"Wallahi ba gidana ba ne, ki tambaya ki ji, kuma sannan ni fa ba ni da manufar rabuwa da
ke, sai dai idan ke ce kika zaɓi hakan".
Ta ce"E ni ce na zaɓa ɗin, ka sake ni".
Ya ce"To gobe zan aiko miki saƙo".
Ya tashi ya fice, a tsakar gida ya samu Uwani zaune, ta ce"Ka fito?"
Ko kallonta bai yi ba ya yi dogon tsaki ya fice.
Ta shiga ɗakin dafe da ƙirji tana cewa"Na shiga uku ni Uwani, Maryam me zan gani? Mijinki ne
yau ya yi mini tsaki, a gobe kuma sai duka, wallahi saura zagi da duka, Maryam wa kika kwaso
mana ne haka?"
Jin shigowar saƙo wayarta ya sa ba ta kula Uwani ba, tana dubawa ta ga daga shi ne, ya
rubuto mata ya sake ta saki ɗaya, ta nunawa Uwani wayar ba ta ce komai ba, ta ce"To rubutu
nake gani, kuma kin san ni ba iya karatu na yi ba, na mene ne?"
Ta ce"Shi ne ya turo mini saƙo wai ya sake ni saki ɗaya".
Uwani ta sauke ajiyar zuciya ta ce"To Alhamdulillah! Tsaki da ya yi mini kuma ya je don kansa,
tun da dai ya sallame ki ni ya biya ni!"
Ta zauna tana cewa"Maryam ki kwantar da hankalinki, wannan ba komai ba ne, in sha Allah
nan gaba za ki samu miji na kere sa'a, wanda za mu yi alfahari da aurenki".
Maryam ta ce"Allah Ya sa".
Bayan kwana uku da sakin sai ga babar shi ta zo gidan, Uwani ta yi kicin-kicin ta tarbe ta a
tsiyace, saboda kar ma ta yi zancen kome, irin yadda take amsa mata gaisuwa a daƙile kamar
mai gyambo a maƙoshi har Maryam ɗin sai da ta ji babu daɗi, saboda ta zauna da matar lafiya
ba ta da wata matsala, babar Hamza ta ce"Ashe haka abu ya faru, ɗan yau dai ka haife shi ba
ka haifi halinsa ba, wallahi Hamza bai yi shawara da ni ba ya yanke hukunci, don Allah ku yi
haƙuri".
Uwani ta ce"Ai ba komai ba ne a wajenmu, duk wanda ya rasa Maryam shi ke da asara, don
haka shi za ki bawa haƙuri".
Ta ce"Ai kuwa ba a ce ba komai ba ne, aure irin wannan da albarkarsa har an fara samun
rabo..."
Uwani ta katse ta da faɗin"Cewa za ki yi har an samu rabo, idan kika ce an fara da saura kenan
za a ci gaba, kin ga mun gode amma don girman Allah ki ƙyale yaron nan sa hukunci shi, don
ba a yi wa yaran zamani dole".
Ta ce"Haka ne, to Allah Ya rufa asiri".
Uwani ta gyara zama ta ce"Dama ai jira nake a cika sati na ga ƙarshen abun, da ba ki zo ba
dama zan zo".
Babar Hamza ta ce"To lafiya dai ko?"
Uwani ta ce"Ƙalau, dama a kan wannan yaron ne, na ce ya za a yi da shi? Za ki karɓa ne ko
kuwa biya za ku dinga yi tana shayar muku da shi?"
Ta ce"A haba dai ga uwarsa a raye ai bai kamata a raba shi da nonon uwa ba, sai a dinga ba ta
wani abun".
Ta ce"To nawa za ku na badawa? Kin ga bayan shayarwa ma a kwai omo, sabulu, famfas kafin
kuma ya fara cin abinci".
Maryam da duk matar ta ba ta tausayi ta ce"To babarmu ai ba sai an wani tsadance ba, ko me
suka kawo Allah Ya saka masa albarka, ni ma fa ɗana ne".
Uwani ta galla mata harara, ita dai ta yi musu sallama ta tafi, ta ce gobe za ta dawo idan suka yi
magana da Hamza.
Tun daga nan duk sati biyu sai babar Hamza ta zo ta gansu, wataran kuma ta tiso shi a gaba
su zo tare, su ba su kuɗin shayarwa. Babu laifi Maryam ta samu kulawa sosai a wajen Uwani,
yanzu hankalinta a kwance yake tana ra rainon ɗanta da yake ta ƙara girma da wayo. Al'amin
yana da wata biyar ta ce za ta fara bussiness da kuɗin da ta siyar da kayan ɗakinta, Uwani ta
so daƙile ta, ta nuna mata wannan fa duk cake ne ba samun ciniki ake ba, har gara ma siyar da
abincin, ita kuma Maryam ta ga ya za a yi ta sana'ar abinci da ƙaramin ɗa, to da yake Uwanin ta
san idan Maryam ɗin ta coge ba a iya ture ta sai ta rabu da ita, ita take zuwa kasuwa da kanta
tana yo sarin abubuwa iri-iri, ta tallata a maƙota da kuma status kuma Alhamdulillah Allah sai Ya
sakawa abun albarka, Uwani tana kallo take ƙirga ribarta tana adanawa.
Da ta yaye Al'amin sai ta daina zuwa kasuwar da shi, ta fara ɗaukar wanka don shirin fara
zawarci, ai kuwa zawarawan suka fara layi, tana ta cafke musu ƴan canji,domin ta koyi roƙo
sosai, idan ma kai faƙiri ne ko marowaci soyayyarku da Maryam ba ta taɓa yin ƙarko, bani-bani
ne zai kore ka, idan gari ya waye dare ya yi ba su ci kaza ko balangu ba ita da Uwani to sai dai
idan ita ce ba ta so ba, ma'ana idan ba ta bawa kowa damar zuwa ba, amma muddin ka ce ga
ka nan tafe to za ta lissafo maka abin da za ka taho da shi, ai kuwa har wata ƙiba ta fara yi, ta yi
kyau abunta.
Ba ta tsayar da mijin ba, tana ta tantancewa dai, yayin da ƴan'uwanta ƴaƴan Uwani suke yawan
yi mata nasiha kan auren shi ne rufin asirinta, idan a gaban Uwani ne kuwa nan za ta
hayayyaƙo tana cewa su ba su san ƙaddara ba? Ai ita Maryam ƙaddararta kenan, shi ma Baba
ya fara matsa mata, don haka ta tsayar da wani Nasuru, a kasuwa suka haɗu, ya faɗa mata ya
taɓa yin aure ƴaƴansa biyu suka rabu da matar, Nasuru ba shi da rowa, sosai yake sakar mata
kuɗi, kuma ba shi da wata makusa a halitta, ta ji tana son shi za ta iya auren shi, don haka ta ba
shi dama ya turo bayan ta gama shirinta.
A wannan karon wata biyu aka saka, aka ɗaura aure, aka mayar da Al'amin wajen babar
Hamza ta ci gaba da kula da shi, a wannan karon Uwani ta san babu buƙatar yiwa ƴar tata wata
huɗuba domin ta riga ta haddace karatunta, musamman ma a wannan zawarcin da ta yi ta ƙara
samun gogewa ta rayuwa, don haka hankalinta kwance yake, ta san yadda ta tafi haka za ta
dawo.
An kai amarya lafiya, zamansu da Nasuru lafiya ƙalau babu wata matsala daga farko, haka
kuma shi yana son haihuwa ba kamar Hamza ba, don da ta samu ciki ya nuna mata kulawa
sosai, bai taɓa nuna ƙosawa da yanayin laulayinta ba. Yaran shi suna zuwa gidan, wani lokacin
ma har su kwana biyu idan sun zo ranar Juma'a sai ya mayar da su ranar Asabar, a yadda ta
lura da alamunsa yana son yaran su zauna a wajenta, ita ma kuma ba ta ɗauki hakan a komai
ba, tun da ba ƙananu ba ne sosai ballantana ta ce za ta ci kashinsu da fitsari, babban
shekararaa tara, sai ƙanwarsa shekararta baƙwai, to da yake komai na gidan aurenta a tafin
hannun Uwani yake ita ce ta nuna mata sam kar ta sake ta riƙe masa ƴaƴa, ɗan kishiya ruƙon
mai haƙuri ne, ta zuga ta a kan idan ta haihu tana kallo zai yi ta fifita yaran a kan wanda za ta
haifa, saboda an fi marmarin ɗan fari, haka dai ta harhaɗa mata raunana hujjoji marasa tushe
bare makama, sai ta hau kai ta zauna ta fara baya-baya da yaran.
Nasuru ɗan kasuwa ne, dole ba zai rabu da mata a waya ba, musamman yanzu da kasuwancin
ya koma na online, sannan da daddare ne yake samun damar zama ya nutsu ya duba
saƙƙonnin da bai duba ba, sannan ya yi ta saka hotunan kaya a groups ɗin shi, ita kuma
Maryam wannan karkata da yake yi a kan waya yana mugun ba ta haushi, ko kuma ta ga wata
ta kira shi suna magana, duk da ga shi a zahiri tana ji zancen kaya ake yi, amma sai ta yi ta yi
masa tijara tana cewa ƙarya yake yi alaye yake yi mata, kurman baƙi ne kawai suke yi saboda a
gabanta ne, kuma da fari ba haka take yi ba, ta yarda da shi sosai, nan ma Uwani ce ta zuga ta
ta ɗora ta a keken ɓera ta ce duk ƙarya ce, dama ƴan kasuwa ba a isa a raba su da mata ba, ga
su da watsewa da masu abinci, har da cewa Allah Ya sa ma bai ɗebo mata alaƙaƙai ba.
Tun daga ranar da Maryam ta ji haka shikenan ta kasa zaune ta kasa tsaye a gidan aure, ta
matsewa Nasuru lamba take tuhumarsa babu dare babu rana, dayake yana sonta haka yake ba
ta hujjojin kare kansa, daga ƙarshe ma ta ce munafurci ne yasa yake saka password a waya
dole sai ya cire, kuma ta cire ɗin saboda a zauna lafiya, don haka ta samu damar bincikar
wayarsa kullum, tsakar dare za ta tashi ta ɗauki wayar ta fice falo ta yi ta bincikenta, yana
kallonta amma bai damu ba tun da ya san babu komai ba rashin gaskiya da za ta gani.
Ana haka ne ya sayi wata waya sakan a wajen abokinsa, ya ɗora wani daga cikin layinsa a kai,
da yamma ya karɓi wayar bai ma duba ya ga mene ne a ciki ba, ashe da fina-finan batsa
kala-kala, ta ɗauki wayar ta duba ta gani, shi ne ta tashe shi tsakar dare suka yi tijara har ya
sake ta, tana ganin ba komai ba ne don aurenta ya mutu, sai kuma ta dawo a ranar ta san
matsayinta da gadar kwalin da Uwani ta sakawa rayuwarta ta hau kai ta kwanta a rashin sani.
Wannan shi ne abin da ya faru a baya, yanzu za a ci gaba da labari.
08028966015
[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_
*SADIYA ABDULRAZAƘ*
*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne
hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman
aure?*
Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu
*FIRST CLASS WRITERS*
https://chat.whatsapp.com/G08KLEmlF3gJ3X4npkfIee
PAGE 11
Wunin ranar Maryam ba ta bar zuciyarta ta huta ba, tunani kawai take yi na irin zuciyar wasu
mutanen, ta ɗauki Uwani tamkar mahaifiyarta, tana yi mata kallon gatanta, kusan ma za ta iya
cewa ta fi sonta fiye da mahaifinta, saboda yadda take riƙe ta da amana, tun tana yarinya take
kula da ita bayan rasuwar mahaifiyarta, ba ta taɓa ganin wani abu na nuna bambanci a
tsakaninta da ƴaƴan da ta haifa ba, kuma da yake ita ma Maryam tana da sakin jiki da mutane
da surutu sai ya zamana ba ta rakuɓewa kamar na ƴaƴan da babu uwarsu a gida, sabgarta
kawai take kamar Uwani ce ta haife ta.
Ita Hansatu mahaifiyar Maryam ƙawar Uwani ce tun ta ƙuruciya, kowa ya san amincinsu komai
tare suke yi, ƙawance irin na da mai cike da tsafta da yarda da juna, musamman da suka
kasance maƙota, ga gida ga gida, Uwani ta samu miji da wuri ta yi aure, saɓanin Hansatu da ta
samu jinkirin aure, har ana cewa aljani ne ya aure ta sai da ta girma Uwani ta yi haihuwa uku
sannan ta samu miji, shi ma abokin mijin Uwanin ne, wanda bai yi auren wuri ba shi ma abun ya
damu iyayensa, kawai sai mijin Uwani ya yi wani tunani, ya ce tun da ƙaddararsu ta zo ɗaya da
Hansatu kawai a haɗa su a gani ko za a dace, kamar wasa aka haɗa su suka fara soyayya,
kuma sai abun ya ɗore har aka yi aure, wata biyu da auren Hansatu da Malam Habu Allah Ya yi
masa rasuwa, sanadin hatsarin mota, da yake direba ne shi, yana kai kaya Legas.
Nan fa marasa ilimi suka ƙara gasgata lallai aljani ne ya auri Hansatu, bayan ta fita daga
takaba babu zato babu tsammani mijin Uwani ya ce zai aure ta, Uwani irin matan nan ne ma su
tsananin kishi don haka ta girgiza matuƙa da jin zancen, ta tada hankali ta ce ba ta san zance
ba, a cewarta Hansatu fa aljani ne ya aure ta, idan ya aure ta shi ma mutuwa zai yi, shi kenan
ya bar ta da marayun ƴaƴa, ta ci kuka ta yi magiya, shi kuwa namiji idan ya so ƙara aure babu
mai hana shi sai Allah, don haka ya ɗaura ɗamara, musamman da ya kasance ita Hansatu tana
son shi ta karɓe shi hannu biyu-biyu, duk kuwa da caccakar da ake ta yi masu a gari ita da
iyayenta na cewar za su yi auren cin amana, a haka dai aka yi auren nan tun da Allah Ya
ƙaddara, kuma ana yi aka samu rabon cikin Maryam.
Sam ba a ga miciji a zaman nasu, duk yadda Hansatu ta so su sasanta Uwani ta ƙi ba ta dama,
masifar yau da ban ta gobe da ban, a haka har aka haifi Maryam, sai kuma Allah Ya jarabci
Uwani da son Maryam, idan ta rarrafo ta fito waje haka za ta ɗauke ta, sai ta ga fitowar Hansatu
sannan ta ajiye ta ta shige ɗaki, to da Maryam ta girma take shiga ɗakin Uwani sai suka ja ta a
jiki sosai, yaran suka haɗe kansu kamar ba ƴaƴan kishiyoyi ba, shekarar Maryam bakwai a
duniya mahaifiyarta ta rasu, wajen haihuwa ta biyu, dama tun farkon cikin ya zo da matsala,
kuma Allah Ya yi cikin ma abokin tafiya ne, ba ta haihu ba ta rasu, kuma dama tun da ta fara
naƙuda aka tabbatar ɗan ya mutu a cikinta.
Kowa ya ji tausayin ƴar marainiyar nan Maryam, mutane sun yi mamakin yadda Uwani ta saka
ta a jikinta ta rungume tsam, ta hana dangin babarta tafiya da ita, dama shi ma Baba ya hana,
saboda ya san kishin Uwani da uwar kawai take yi tana son ƴar, haka aka bar mata Maryam,
ana ta yabonta a gari, ita kuwa ta haɗe ta da ƴaƴanta aka ci gaba da yaruwa.
Sai dai me? Mayam ita ce ƙarama a kan ƴaƴan Uwani Mardiyya da Murja, amma samari ita
suke hari tun tana ƙwailarta, ita a tunaninta Maryam za ta yo ƙashin baƙin jini irin na babarta, sai
ga shi ta ga saɓanin hakan, nan hassada ta fara shiga zuciyarta sannu-sannu, ta fara jin
haushin Maryam ɗin, su kuwa su Mardiyya ba su damu ba, don sun ɗauki Maryam ƙanwarsu
kamar uwa ɗaya suke, sai Uwani ta dinga nuna musu suna cikin matsala sanadin haka, a
cewarta babarta ce kafin ta rasu take yi mata maganin farinjini, su dai ba su saka a ka ba.
Da farko sai ta samu Baba kamar abun arziƙi take nuna masa illar wannan farin jinin na
Maryam, ta ce tana da ƙuruciya mazan za su iya amfani da wannan damar su hillace ta, saboda
haka a samu wani Malamin wanda zai iya dakatar da maza daga kanta zuwa sanda za ta yi
hankali ta isa aure, Baba ya nuna sam bai yarda ba, duk da shi ma abun yana ba shi tsoro,
musamman da ya kasance ita ta fi ta zakka da sauran yaran gidan, ita ba ta jin magana sosau,
ga yawon bin gidajen ƙawaye, wani feleƙe da rawar kai da son girma ga kwalliya kamar babbar
budurwa, Baba ya ce ko maza dubu ne za su zo babu wani dakatarwar Malami da ake buƙata,
tun da dai ba zance ta fara yi a ɓoye ba, to a barwa Allah komai, kuma ba yanzu zai yi mata
aure ba ai, sai ta gama sakandari, haka Uwani ta haƙura ta bar zancen.
Amma ta kasa haƙura, sai da ƙawarta ta zuga ta ta karɓo rubutun farinjini take bawa ƴaƴanta ba
tare da sanin Maryam ba, a haka dai har suka samu mijin, a rana ɗaya aka haɗa na Mardiyya
da Murja, dama daga su sai Maryam sannan ƙaramar ƴarta Fatima, wanda tsirarsu kaɗan ne da
Maryam, don bai kai shekara ba.
To ita ma Maryam ɗin da yake ba ta jin magana, sam babu auren a gabanta, duk wanda zancen
aure ne ya kawo shi ba ta fiya sauraron shi ba, tun ba a farga ba har aka gane, Uwani ta fara
farinciki tana tunanin ƙila ita ma ƙaddararsu ɗaya da mahaifiyarta.
A hankali shaiɗan ya tunzurata, take tuna auren da ta kira da na cin amanarta da aka yi
tsakanin ƙawarta da mijinta, ta ji a ranta lokaci ya zo da ya kamata ta ɗauki fansa a kan
Maryam, ta yi ta tunanin abin da za ta yi mata, kafin ta yanke shawarar hana ta zaman aure, ba
ta yin shirya kuma ba ta so ta yi a kan Maryam, sannan idan ta yi mata cutarwa ta ƙiri-ƙiri
mutane za su gane da wuri, a yi mata terere,