Showing 39001 words to 39853 words out of 39853 words

Chapter 14 - MIJI GOMA Book Complete By Sadiya Abdul.pdf

25 May 2025

7747

tun da a yanzu ita kaɗai kake kallo a
mutum, su ƴaƴan naka ba mutane ba ne, komai ma ya same su ta matarka kake yi! Hmm!" Ta
wuce fuuu ta yi cikin gidan.

Ya yi murmushin yaƙe ya ce wa Maryam"Kin ga Sauda ta dawo ko? Don Allah ku zauna lafiya,
kin ga ma tun da ta dawo kan yaranta za ki fi kula da ni sosai ko?"

Ta yi farr da ido ta ce"Ƙwarai kuwa, zo ma mu je ka gani".

Ta yi ɗakinta, shi kuwa ya bi bayanta kamar raƙumi da akala, a gaban Sauda suka shige ɗakin
nata, wacce ta fito daha ɗakin yaranta za ta shiga nata, ta manta rabon da ya shiga ɗakinta, sai
dai ita ta bi shi nashi ɗakin idan ya kira ta, amma shi ne ya zo ya shige ɗakin amarya ko kunya
ba ya ji, ta yi ƙwafa tana cewa"Lallai akwai aiki a gabana, tsohuwar kilaki ya kwaso".
Ta gagara zama a ɗaki, ko wanka ta kasa yi, sai leƙe take yi tana jiran fitowarsa amma shiru har
ƙarfe sha ɗaya ta yi, ga shi ko sallar isha'i ba ta yi ba, kuma ta kasa yi, saboda tana son
tabbatarwa da gaske a nan zai kwana? Shi kuwa Alhaji yana can Maryam ta saka shi a kwana
ta kalallame shi, ta kanainaye shi har ya manta ma a ɗakinta yake.
Ƙashe dai sai sha biyu Sauda ta haƙura da leƙen ta yi sallah, ta kwanta, sai ta gagara yin bacci
gabaɗaya ya ƙaurace mata, ta fara tunanin yanzu fa yana can tare da ita, lallai namiji ba shi da
kunya, can dai ta fara tunanin ya za ta yi ta hana su sukuni, ta tashi ta fito a hankali ta shiga
ɗakin yaranta, ta haska su, sai baccinsu suke yi hankali kwance, ta shiga tashinsu bisa
shawarar zuciyarta, ta dinga jijjiga su duk suka tashi suna murza ido, ta sakawa fuskarta
alamun firgici ta ce"Ku tashi don ubanku, aljanu ne suka shigo gidan! Suna ɗakin nan a
ƙarƙashin katifarku!".

Ai kuwa a tare suka fara ihu, ta ce"Ku kwanta ba za su yi muku komai ba".

Suka fara kuka suna rirriƙe ta suna cewa a ɗakinta za su kwana.

Ta fizge tana cewa"Suna can a ɗakina sun cika ɗakin kowa ya yi ta kansa".

Ta fice a guje suka mara mata baya, amma kafin su shiga ta banke ƙofarta ta saka sakata,
gabaɗaya suka ruɗe suka dinga ihu a mugun firgice kamar za su shiɗe.

A tare Maryam da Alhaji suka fito a ruɗe, suka tarar yaran suna ta buga ƙofar ɗakin babarsu,
fitowarsu ya sa suka yi wajensu suna shigewa jikinsu cikin matsanancin kuka, Alhaji ya ruɗe ya
fara tambayarsu me ya faru?

Suka ce"Aljanu, Abba aljanu a ɗakinmu".

Gabansa ya faɗi ya ce"Aljanu kuma? Me kuka gani?"

Inaa sun ruɗe, sai a lokacin Sauda ta fito tana cewa"Mene ne?"

Suka yi kanta suna kuka.

Alhaji ya ce"Kin ji wai aljanu".

Ta ce"Aljanu kuma?"

Ya wuce ɗakin a tsorace yana addu'a, ya haska bai ga komai ba, ya dawo a sanyaye ya
ce"Abun ya bani mamaki wallahi".

Sauda ta ce"To kar dai fa ture aka fara yi musu".

Ya ce"Wane irin ture? Waye zai yiwa yaran nan ture?"

Ta ce"Wanda suka tsonewa ido mana, an ga yara sun cika gida tubarkalla ana son haukata su
don kar ƴaƴana su moru".

Alhaji ya ce"Subhanallah! Kar na sake jin magana irin haka!".

Ya janyo yaran yana cewa"Tsorata kawai kuka yi babu komai a ɗakinku kun ji? Ku je ku kwanta
zan yi muku addu'a".

Sauda ta ce"Au da gaske sai ka kora su, saboda kar kwanan ɗakin amarya ya wuce ka? Hmm
dama uwa ce ba ta gudun ƴaƴanta duk runtsi, ku shigo nan!".

Ya ce"Ba za su shiga ba! A ɗakin nasu nake so su kwana ina son fahimtar wani abu ba ne kafin
Allah Ya kaimu gobe na kira malamai a yi addu'a".

Maryam ta ce"Allah Ya rufa asiri". Ta koma ɗakinta, ita ma duk sai tsoron gidan ya kama ta.

Ya saka su a gaba suna turjewa suka shiga, ya zauna ya kunna karatun qur'ani a wayarsa,
yana addu'a yana tofa musu, amma da bacci ya fara ɗaukarsu sai su zabura su farka suna
maƙale shi, a haka suka kwana, ita kuwa Sauda ta yi baccinta ranta fess, tun da dai ta haramta
musu wannan daren to ita fa buri ya cika, kuma ta saka a ranta yanzu aka fara wasan, ta ɗau
alƙawarin sai ta fitini gidan gabaɗaya, sai kwana a ɗakin shi ya gagari Maryam, kafin ta tankaɗa
ƙeyarta waje.



LAST FREE PAGES! A NAN ZAN TSAYA DA FREE PAGE, DAGA WANNAN SHAFIN DUK
WANDA KUKA GANI A PAID PAGE NE, ƳAN'UWA KU BIYA KU KARANTA CIKIN AMINCI,
YANZU ZA A FARA WASAN NAN, TAFIYA TA KISHI MAI CIKE DA ƘULLA-ƘULLA TURA ƊARI
BIYAR ƊINKI TA NAN KI SHA KARATU CIKIN AMINCI.
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay


08028966015

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login