Showing 15001 words to 18000 words out of 39853 words
Chapter 6 - MIJI GOMA Book Complete By Sadiya Abdul.pdf
ya na ta zaune yana jiran shigowarta ya ji shiru, sai da ya ji ta fara daka sannan ya fito ya
shiga kitchen ɗin ya tsaya yana kallonta, ta gama dakan ta ɗauku ruwan da ta wanke kayan
miyan ta watsa masa da gayya, ya matsa gefe yana cewa"Subhaballah! Mene ne haka?
Maryam ƙalau kike kuwa?"
Ta ce"Gobe ma Gwaggon zan watsawa shi".
Nan ransa ta ɓaci ya ce"Ke Maryam kar fa ki ga ina lallaɓa ki, ki yi zaton za ki taka mahaifiyata
na rabu da ke..."
Ta katse shi da faɗin"Ai ban ga alamar ka san darajarta ba, kuma wallahi ko ita ce ta zo ta yi
mini tsaye a kai sai na watsa mata".
Ya ce"Me kike so da ni?"
Ta ce"Ka sake ni!".
Ya ce"Ba zan sake ki ba, ki ma daina wannan tunanin, don ba sadaƙa aka ba ni aurenki ba".
Ta ci gaba da aikin gabanta, ya ce"Wallahi ban yi zaton haka daga gare ki ba, na faɗa miki indai
Gwaggo ce ta ce kowa ya yi sabgarsa, ba ki ga ta kwashe kayanta ba ma ta bar miki kitchen ɗi
ba?"
Ta yi banza da shi.
Ya ce"Jiya kika kulle ƙofa, idan Gwaggo ta gane hakan kin ga ba za ta ji daɗi ba, sai ta ga
kamar har yanzu ba ma zaman lafiya, ko me za mu yi don Allah kar ki sake yi mini haka, mu yi
abun mu a ɗakinmu mu biyu".
Nan ma dai ba ta kalle shi ba.
Ya ce"Kenan kayan miya kika siyo? Ki yi haƙuri ai ga shi ma na siyo miki, bai kamata ki fara fita
tun yanzu ba, har gara ki aiki Yasmin".
Ya ce"Mun shirya ko? Me kike dafa mana?"
Ganin dai da gaske ba za ta kula shi ba sai ya fice daga kitchen ɗin, ya shiga ɗakin Gwaggo
yana cewa"Bari na koma, cefane na kawo mata".
Cike da tausayin shi ta ce"Allah Ya tsare".
Da ta gama girkin ta juye a kula ta kai ɗaki, dama iya cikinta ta dafa wanda zai ishe ta har dare,
ta ci ta ƙoshi, ta kira babarsu a waya suna ta fira, tana ba ta labarin abin da ya faru tsakanin jiya
zuwa yau, ta ƙara zugata sosai ta ce ita ma Gwaggon ta fara taɓa ta don sai ya fi fusata.
Da magriba da ya dawo ya shigo ɗakin, ya ƙaraci surutunsa ba ta ce masa ƙala ba, sannan ya
tambayi abinci ba ta ba shi ba, har aka kira isha'i yana zaune, yana tafiya masallaci, ta fito ta yi
alwala ta sakawa ɗakinta sakata, da ya dawo ya ga ta rufe ƙofar sai da gabansa ya faɗi, ga shi
ba ya son ya cikata da bugun ƙofa har Gwaggon ta gane, sai ya shiga ɗakin nata, ya zauna
shiru, ta ce"Nazifi ka ci abinci kuwa?"
Ba don yunwar yake ji ba da zai yi ƙaryar ya ci, sai ya girgiza kai alamar a'a, ta miƙo masa kula
tama cewa"Shiyasa na dafa muku shinkafa kai da Yasmin".
Ya ɗauka ya ci, ya gama ya zauna shiru, yau ya kasa taya ta firar ma, saboda hankalinsa ba ya
kanta, yana can wajen tunanin mafita a wannan auren nasu, har tara ta yi, ta ce"Ka je ka
kwanta mana Nazifi, na ga kamar ba ka jin daɗi ko?"
Ya ce"To sai da safe".
Ya tashi ya fita, ya je a hankali yana buga ƙofar ɗakin, wanda Gwaggo tana ji, dama ta na son
tabbatar da jiya a falo ya kwana, don haka ta leƙo kaɗan, ta kuwa gan shi tsaye, can kuma sai
ya juya ya shiga falon ya rufe ƙofa, ita ma ta rufe ƙofarta tana jin tausayin shi, sai ta ji nadamar
zuwa gidan tun farko, da ta sani ta yi zamanta a gidanta ƙila da haka ba ta faru ba.
Washegari ma haka ce ta faru, da safe a ɗakin Gwaggo ya karya ya fita, ƙarfe tara Maryam ta
fito ta gama karyawa ta shiga kitchen tana wanke-wanke, ta gama ta fito da ruwan, ta samu
Gwaggo duƙe tana sharar tsakar gidan, ta ɗaga ruwan ta sheƙo shi duka a kanta, Gwaggo da ta
samu saukar ruwan babu zato firgita ta yi, ta ɗago da mamaki take kallon Maryam, Yasmin
kuwa salati ta rafka har da ɗora hannu a ka, ta ce"Kai Gwaggon kika watsawa ruwa?"
Ita kuwa Maryam kamar wata makauniya kuma kurma haka ta koma kitchen ɗin ta fara
sharewa, ta gama ta zo ta wuce ɗaki, har lokacin Gwaggo tana tsaye mamaki ya daskarar da
ita, ta jinjina ki ta shiga ɗaki ta zauna jaɓar, saboda ba za ta iya ƙarasa sharar ba, a ranta tana
ta tunanin wace irin mara kirki Nazifi ya kawo cikin rayuwarsa?
Yasmin ta ce"Ruwa fa ta watsa miki Gwaggo".
Gwaggo da zuciyarta take a kumbure ta ce"Babu komai Yasmin".
Ta shiga haɗa kayansu, ta ɗauki waya ta kira lambar babban ɗanta Shazali, suka gaisa ta
ce"Don Allah zan iya samun ɗaki a gidanka ko na sati ɗaya ne?"
Ya ce"Gwaggo kamar ya? Mai zai hana? Ai ke kika ƙi tun farko".
Ta ce"To ga ni nan zuwa".
Ta ajiye wayar, tun da Shazali ya gina gidansa ya ware ɗaki ɗaya har banɗaki ya yi a ciki ya ce
nata ne, amma ta ƙi zama saboda tunanin Nazifi bai yi aure ba ba za ta koma wani gidan ta bar
shi ba, kuma ba za ta so ya koma gidan yayan nashi da zama ba, daɗin daɗawa ita ba ta son
nisa da Nazifin ta fi son zama a gidansa, saboda shi ya fi kwanta mata a zuciya duk cikin ƴaƴan
nata, ashe hatsabibiyar matarsa ba za ta bari burinta ya cika ba. Ƙatuwar akwatin kawai ta
ɗauka, ta rufe ɗakin suka tafi, Maryam tana leƙe ta gefen labule ta ga sanda ta ja akwatin suka
fice, ta yi wata shegiyar harara tana cewa"Da kika ce za ki jure!".
Bayan sallar magriba Nazifi ya dawo daga kasuwa, da mamaki ta fara cin karo, na ganin ƙofar
ɗakin Gwaggo a rufe, ya san ko ba ya nan idan za ta je unguwa tana faɗa masa, ya kalli ƙofar
ɗakin Maryam ya gan shi a buɗe, sai ya ƙarasa ya ɗaga labulen, tana zaune tana chart, ya
ce"Maryam unguwa Gwaggo ta tafi?"
Ta ce"Dama ajiyarta ka ba ni? Ko ita ƙaramar yarinya ce da zan saka mata ido a kan shige da
ficenta?"
Ya ce"Ke dakata! Maryam kin fa fara fusata ni a kan mahaifiyata, wallahi kar ki yarda ki kai ni
bango!" Ya yi ƙwafa ya saki labulen.
A tsakar gidan ya tsaya ya kira lambarta, ta ɗaga ya gaishe ta kafin ya ce"Gwaggo unguwa kika
je ne?"
Ta ce"E Nazifi ina gidan shazali".
Ya ce" Ba ki taho ba? Ba na son kina kaiwa dare a waje".
Ta ce"Ai a can zan kwana, gobe idan Allah Ya kaimu sai ka haɗo sauran kayana ka kawo mini
nan ɗin, don hakan zai fi".
Gabansa ya faɗi ya ce"Gwaggo me hakan yake nufi? Me ya faru?"
Ta ce"Idan ka zo goben ka ji".
Ta kashe wayar, ya kasa zama, ya fice daga gidan yana fatan Allah Ya sa ba Maryam ce ta yi
mata wani laifin ba.
Ya shiga gidan, suka gaisa da matar yayan nasa, a tsakar gida ya tarar da yara suna cin abinci,
Yasmin ta yi farat ta ce"Yaya Nazifi ka dawo? Mun dawo nan da zama, matarka ce ta watsawa
Gwaggo ruwan wanke-wanke, ta hiƙewa jagab!"
Wani tashin hankali ya rufto masa, ya ce"Ruwan wanke-wanke!?" Yana zazzare ido kamar
yarinyar ce ta yi masa laifin.
Ya shiga ɗakin da aka ce masa Gwaggon tana ciki, tun kafin ya zauna ya ce"Gwaggo da gaske
ruwa ta watsa miki?"
Ta ce"Zauna Nazifi".
Ya ce"Ina zuwa".
Ya fice daga gidan cikin sauri, a hanya sai ya kasa haƙuri, kawai ya ciro wayarsa ya rubutawa
Maryam gajeren saƙo "Na sake ki saki ɗaya".
Tana cikin chart ta ga shigowar saƙon, gabanta ya ba da rass, kafin kuma farin ciki ya biyo
baya, ta tashi ta zauna ta ƙara tashi, ta ma rasa me za ta fara yi, ta ina za ta fara haɗa kayan?
Sai ta kira lambar babarta a waya, tana ɗagawa ta ce"Albishirinki!" Ba ta jira amsarta ba ta
ce"Ya gaji ya sake ni!".
Uwani ta miƙe tsaye cike da farinciki ta ce"Alhamdulillah! Ƴata ta rabu da ƙaya ta samu
ƴancinta, maza tashi ki haɗa wata akwatin, dama ga wata a nan, gobe tun safe za a siyar da
kayan ɗakin nan".
Maryam ta ce"Ina sha Allah! Wallahi sai na ji kamar an cire mini wata ƙaya".
Uwani ta ce"To ai irin wannan auren sartse ne, idan kika rabu da shi dole ki ji haka".
Ta ajiye wayar ta shiga haɗa kaya.
08028966015
[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_
*SADIYA ABDULRAZAƘ*
*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne
hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman
aure?*
Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu
*FIRST CLASS WRITERS*
PAGE 7
A zuciye sosai Nazifi ya ƙarasa gidan, ko sallama bai yi ba ya banka ɗakin Maryam, ba ta
ɗago ta kalle shi ba ta ci gaba da aikinta ranta fess, ya ce"Ke Maryam akan wane dalilin kika
watsawa babata ruwan ƙazanta?"
Ta ɗago tana hararar shi cike da tsiwa ta ce"Ƙila tare mini hanya ta yi".
Tass! Ya ɗauke ta da wani zazzafan mari, ta tsaya tana mamaki ya ƙara sauke mata wani, yana
nunata da yatsa a fusace kamar zai tsokane mata ido ya ce"Wallahi uwata ta fi kowa a wajena,
ke ba ki kai wacce za ta wulaƙanta uwata ba, duk duniya ma babu indai ina raye ina kuma da
ikon rama mata..."
Ta katse shi da faɗin"To ai ba ka rama mata ba, wanke-wanke za ka yi ka watsa mini ruwan na
yi tsumu-tsumu kamar an tsoma kaza a ruwa shi ne zan san ka rama mata".
Tana rufe baki ya naushi bakin nata, ya ce"Wallahi ni dai na yi asarar kuɗi da lokacina wajen
aurenki, maza ki tattara gayyar tsiyarki ki bar mini gidana".
Har ya juya zai tafi, sai kuma zuciya ta ciyo shi, ya tuna yadda ya dinga sintiri a ƙofar gidansu
yana yi mata wahala, yana yi mata ladabi kamar uwarsa, ya tuna kuɗin da ya kashe a kayan
lefe, da shagalin bikin, da ya san wacce zai aura ai da a kasuwa ya saka kuɗin ya ƙara jari ya
ciji leɓe, sannan ya dawo kamar an jeho shi, tana duƙe tana haɗa kaya, ya yi mata wani dundu
a bayanta, sannan ya rufe ta da duka ta ƙo'ina yana cewa"Wallahi sai na daki kuɗina, ƴar
wahala wacce ba ta san halacci ba!".
Maryam ma ta taso tana kai masa duka daidai iya ƙarfinta, sai dai ƙarfin ba ɗaya ba ne, idan ta
dake shi ma ita ce take jiggata hannunta saboda ƙaƙƙarfan ƙashi kawai take duka, don haka
cikin ƙanƙanin lokaci Nazifi ya yi mata lilis ya tara mata gajiya, fuskarta kuwa har ta kumbura,
dama naushin da ya yi mata bakinta ya fashe, bai bi ta kan ashar ɗin da take ƙundumawa
Gwaggo ba, ya fice daga gidan, saboda idan ya biyewa zuciya sai ya kashe ta, tun da ta lura
bakinta ba zai yi shiru ba.
Kuka sosai Maryam ta ci kafin ta saka hijjabi ta tafi gida, don fasa haɗa kayan ma ta yi, yana
daga runfar maƙotansu a zaune, dama jira yake yi ta fice ya zo ya rufe gidan, sai da ta yi nisa
sannan ya shiga, sai ya ga kayan duka a baje ba ta haɗa ba, nan ya yi tozali da tarin kayan
lefen da ya haɗa mata, zuciya ta faɗa masa ya ragewa kansa zafi a kansu, ai kuwa ya ɗauki
atamfofi guda biyar, leshi guda biyu, ya kwasarwa Yasmin kayan kwalliya, sannan ya rufe ɗakin
ya tafi gidan Gwaggo, a hanya ya tsaya ya samu leda ya zuba kayan, ya zauna a gaban
Gwaggo cike da kunyar abin da matarsa ta yi mata ya ce"Gwaggo don Allah ki yi haƙuri, na ja
miki tozarci, wallahi inda na san haka za ta faru da tun farko ma ban yi auren nan ba".
Gwaggo ta ce"Ba komai Nazifi, kowa da irin halinsa, ba ga shi na bar mata gidan ba? Yanzu sai
ku zauna lafiya".
Ya ce"Haba Gwaggo, ai ko ita ta gwal ce wallahi ba za ta yi miki wannan abun na iya ƙara
kwana ɗaya da ita ba, na sake ta".
A ranta ta ji daɗin yadda ɗanta ya nuna tana da muhimmanci a wajensa, ta ce"Na gode Nazifi,
Allah Ya shi albarka, amma da ba ka rabu da matarka ba, tun da na tafi ƙila ku ci gaba da
zaman lafiya, dama fa ba lallai ne sai matarka ta so danginka ba, wata nagartar tata za ka duba
sai ka yi haƙuri da wani halin nata".
Ya ce"Haba Gwaggo ina nagarta ga wacce za ta iya wulaƙanta mahaifiyarka? Ba fa zama za ki
yi a gidan nan ba, kin ga idan sun gama kwashe kayanta sai ki koma, ba na son su zo wani ya
ganki ya zage ne, amma da a yau ɗin za ki koma, gara na haƙura da auren matuƙar za ki zauna
lafiya".
Ta yi murmushi ta ce"Ai ba duka aka taru aka zama ɗaya ba,nan gaba sai ka ga ka samu wacce
za ta bi ra'ayinka".
Ya ce"To Allah Ya sa, ga wannan kayan Gwaggo kya ɗinka".
Ta karɓi ledar da ya miƙo mata, tana cewa"To daga ina kuma? Na ga sallah da saura".
Ya ce"Na lefen yarinyar nan ne, na kwaso saboda na rage asara".
Gwaggo ta yi ƴar dariya ganin yadda ya yi maganar bil haƙƙi, ta ce"Nazifi kenan, idan ka yi wani
abun sai ka ce yaro ƙarami, yanzu dai ka san wannan wata fitinar ka siyo ko? Lefenta ai
haƙƙinta ne ka je ka mayar mata, ni ba yafe".
Zai yi magana ta ɗaga masa hannu ta ce"Ka je ka mayar".
Ya ce"To".
Daga nan suka shiga fira, ta ba shi abinci ya ci, sai tara da rabi ya koma gida, washegari da
safe ya haɗa kayan shi ya saka a ɗakin Gwaggo ya kulle, ya ɗauki kayan da ta ƙi karɓa ya tafi
da su kasuwa, sai ya bawa wani mai kanti dake kusa da su mukullin gidan, ya ce idan wasu sun
zo ya ba su.
Ita kuwa Maryam da kuka sosai ta shiga gidan nasu, lokacin Baba yana tsakar gida yana cin
abinci, Uwani da take ta jiran dawowar tata ta miƙe tana rafka salati kamar ba ta san komai ba
ta ce"Ba dai yaron nan sakinki ya yi ba?"
Baba ya yi mata wani kallo bai ce komai ba, tun da ya san dama sakin suke so.
Maryam ta shige ɗaki tana ƙara sautin kukanta, Uwani ta mara mata baya, tana cewa"To ai ya
isa haka, na ji daɗi da kika shigo da kukan kissar nan wallahi, kin ga babanki zai ce ba da son
ranki komai ya faru ba".
Ganin Maryam ta ƙi daina kukan kuma ta ƙi ɗagowa sai ta sha jinin jikinta, ta ce"Maryam to ko
dai kina son mijinki?"
Sai a lokacin ta ɗago, Uwani ta yi arba da kumburarriyar fuskarta, ta ce"Innalillah wa inna ilaihi
raji'un! Faɗuwa kuka yi a adaidaita sahun?"
Tana kuka ta ce"Dukana ya yi".
Uwani ta ji daɗi a ranta, ta ce'Allah Ya ƙara, kaɗan ma kika gani'.
A fili kuwa ta ce"Duka!? Duka dai wanda na sani?Me kike yi da ba ki ɗauki turmi kin rotse shi
ba?"
Sai ta yi waje tana"Malam! Mun shiga uku...".
Baba ya katse ta da faɗin"Kun shiga uku dai".
Ta ce"Shigo ka ga fuskar yarinyar nan, bayan sakin da ya yi mata, har da yi mata dukan kawo
wuƙa, fuska ta kumbura kamar an saka mata yis".
Baba ya ci gaba da cin abincinsa bai ce komai ba.
Ta ce"Ga duka ga tsinka jaka? Wallahi ba zata saɓu ba bindiga a ruwa, sai na bi mata kadinta!".
Ta shiga ɗakin, ta tashi Maryam zaune tana cewa"Bar kukan haka, wallahi sai na ƙarti daidai da
shi sun yi masa duka, ke dai tun da kin rabu da ƙaya Alhamdulillah!".
Ta fita ta kunna wuta, ta ɗora ruwan zafi, daidai nan Sunusi ya shigo, Baba kuma ya fita, ko
sallamar da ya yi ba ta amsa ba, ta tare shi da faɗin"Sunusi ka ga abin da wannan
tambaɗaɗɗen yaron ya yi wa ƴar'uwarka? Ya yi mata dukan mutuwa sumanta uku, kuma ya
sake ta, da ƙyar ta kawo kanta gidan nan tana jiri tana faɗuwa".
Ya ce"Subhanallah! Ya sake ta kuma? Ko fa sati ba a yi da auren ba, gobe Lahadi shi ne zai
cika sati ɗaya cif".
Uwani ta ce"Ubanka kai da satin, ina maka zancen duka wato kai mutuwar auren ce ma ta
dame ka!".
Ya ce"To babarmu kin san wane tudu da gangare suka hau har ya dake ta? Kin san fa Maryam
ba ta da kunya, ƙila zagin shi ta yi".
Ta ce"Kai dalla gafara, kar na gwabje ka, ashe dai bayan raina ba za ka