Showing 36001 words to 39000 words out of 39853 words
Chapter 13 - MIJI GOMA Book Complete By Sadiya Abdul.pdf
har farar
shinkafar da akwai, da yake gas ɗin mai huɗu ne tana wanke waken sai ta ɗora miyar, sannan
ta zauna ta ci taliyar.
Tana tafiya kitchen Momy ta tashi ta shige ɗakinsu, ta ɗauki waya ta shiga banɗaki ta kira
Ummansu, tana ɗagawa ta zayyane mata komai, Sauda ta ce"Amma dai Allah Ya yi miki
albarka Momy, yanzu kin san yadda za a yi?"
Ta ce"A'a".
Ta ce"Idan ta gama tuwon ku yi loma ɗaya ku ce babu daɗi ku ba kwa ci kun ji ko? Ko kun ji
daɗi fa kar ku ci".
Momy ta ce"To Umma yunwa muke ji fa".
Ta ce"Idan kun ƙi ci sai ku shiga kitchen ku ɗauki golden morn ku haɗa ku sha, idan ya dawo ku
ce masa ba ku ci komai ba yunwa kuke ji, ku ce ba ta ba ku tuwon ba".
Momy ta ce"To". Amma a sanyaye, saboda yunwa take ji.
Sauda ta ce"Ki yi haƙuri kin ji ƙawata, ni na san me zan siya muku".
Ta ce"To".
Ta ajiye wayar, sai da Maryam ta koma kitchen sannan ta sake tsarawa yaran, ta ce inji Umma,
ta ce sai sun ƙi ci za ta dawo, ai kuwa suka yarda.
Sai da ta sauke tuwon ta dada indomin saboda ta manta, ta zubo ta kawo musu,lokacin har
ƙarfe uku ta gota, ta ajiye ta ɗakkowa Nana indomi, ita kam ana ajiyewa ta fara ci ta manta da
gargaɗin yayarsu saboda yunwa take ji, kuma dama duka-duka shekararta huɗu, su kuwa
manyan ba su saɓa ba, loma ɗaya kowa ya yi a layi, idan wannan ya ci, sai wannan ya ci, sai
suka tsaya suna kallon tv, Maryam ta ce"Ya dai? Ku ci mana".
Momy ta ce"Ni dai ba na ci, na ji babu daɗi, ko Kausar?"
Su ma suka haɗa baki wajen faɗin"E babu daɗi".
Ran Maryam ya ɓaci, lallai sun yi sa'a a wannan karon zama ta zo na mutu-ka-raba, da babu
abin da zai hana ta fesawa babbarsu mari, ba ta ce komai ba, ta kwashe ta kai kitchen, babbar
ta shige ɗaki, duk suka bi ta, babu jimawa kuma ta fito ta shiga kitchen ɗin Maryam ta bi
bayanta, ta tarar tana haɗa golden morn, ta haɗa shi kofi uku ta ƙwala musu kira, suka fito suka
ɗauka suka koma ɗaki, ita kuwa Nana sai ta zauna a nan falon tana kallo.
Maryam ta cika da mamakin yaran sosai, ta kuma saka a ranta ta san zaman da za ta yi da su.
Da yamma da ta yi baƙi sai ta ba su taliyar, tuwon kuma ta rufe musu shi, tana jira babansu ya
dawo ta sanar masa ta ga matakin da zai ɗauka.
LITTAFIN NAN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 500
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay
08028966015
*MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_
*SADIYA ABDULRAZAƘ*
*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne
hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman
aure?*
Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu
*FIRST CLASS WRITERS*
https://chat.whatsapp.com/BuEB69AOiqBKg0PMiBzdG3
PAGE 14
Suna ƙule a ɗakinsu baban nasu ya dawo, Maryam ta tare shi ranta fess, ta haɗa masa
ruwan wanka ta kai banɗaki, abin da ba ta taɓa yi wa sauran mazan da ta aura ba, ko ruwa a
buta ba ta taɓa zuba musu ba, amma shi wannan da yake zaman gaskiya ta zo ta ɗaura
ɗamarar yi masa hidima iyakar iyawarta, tsaf ta taya shi shiryawa bayan ya fito, sannan ta ja
hannunsa kamar wani ɗanta zuwa falo, ta kawo masa tuwon, tana ba shi a baki suna ta firarsu
cike da nishaɗi, har ya yi mamakinta saboda shi kansa ya san kafin auren ba wani son shi take
sosai ba, kiran sallar magriba ne ya tashe shi, ya yi alwala ya tafi masallaci yana jin shi fess da
shi, ya manta rabon da ya samu kulawa da soyayya irin wannan, sautari sai bayan magriba
yake yin wanka saboda sai ya ce Sauda ta dafa ruwan take dafawa, wataran ma a haka yake
kwanciya ko ya yi da na sanyi, sannan Momy ce mai kai masa abinci dining, idan ma ya shiga
ɗakinsa yana wani aikin ko kuma ya shigo da wata damuwar, babu ruwan Sauda da zuwa ta ji
dalilin ƙin fitowarsa, sai dai ta aiko masa da abincin ɗakin nasa, sannan babu ruwanta da
tambayar shi fita unguwa, indai ka ga ta tambaye shi sai dai idan nesa sosai za ta je, gidan Inna
kuwa idan za ta je tun rana idan ta tafi sai dare idan ya je yi mata sai da safe su taho tare, babu
ruwanta da me zai ci ranar, babu dai wata kulawa akwai matsaloli birjik, wanda shi ne dalilinsa
na son ƙara auren, kuma tun yau ya fara tunanin za a samu canji in sha Allah!
Ya dawo daga masallaci Maryam ta ga bai yi maganar yaran ba, ta dai leƙa bayan fitarsa ta ce
duk su yi alwala su yi sallah.
Ta ce"Alhaji dama ina so mu yi magan a kan yaran nan".
Ya ce"To, wasu yara?"
Ta ce"Yaranka".
Ya ce"Me ya faru? Ba za ki samu matsala da su ba in sha Allah! Kin ga ma yara ne, uwar ma
don Allah ki kau da kai ga matsalolinta".
Ta ce"Ba wata matsala ba ce, ka ga yau taliya na dafa da safe, na ba su suka ce wai ba sa cin
taliya, sai kowaccensu ta shiga zaɓar abin da take so, ni kuma na ga ba zao yiwu na yi girki har
kala huɗu ba, ko hakan bai zama almubazzaranci ba ai ka ga ni ma ina buƙatar hutu, tun da ba
bautarsu na zo yi ba, sannan ba ma tarbiyya ba ce yara su dinga zaɓin abin da za su ci, na ce
su tsayar da guda ɗaya, suka ce tuwo, shi ne na yi, loma ɗaiɗai suka yi suka ce mini ba daɗi,
ƙarshe sai suka sha golden morn suka ƙule a ɗaki".
Alhaji ya ce"Ikon Allah! Wai kina nufin su yaran suna gidan nan? Waye ya kawo su?"
Maryam ta ce"Wai dama ba ka sani ba? Daga makaranta mai adaidaita sahu ya kawo su".
Ya ce"Yanzu suna ina?"
Ta ce"Suna ɗaki".
Ya shiga ƙwala musu kira ransa a ɓace, suka fito, Kausar da Momy suka haɗa baki wajen
faɗin"Abba yunwa muke ji, ba mu ci komai ba".
Ya daka musu tsawa da faɗin"Ku nemi wajen zama!".
Suka zauna duk suka sha jinin jikinsu, saboda Abban nasu ba mai yawan faɗa ba ne.
Ya ce"A cikinku waye ba ya cin taliya? Yaushe kuka daina cin taliya?"
Duk suka yi shiru suna raba ido.
Ya ce"Wato ku har kun yi girman da za ku yiwa babba rashin kunya? Ku sa ta yi tuwo ku ce
babu daɗi?"
Ya kalli Maryam ya ce"Idan akwai ki sako musu".
Ta tashi ta je ta ɗakko shi a yadda suka bar shi, ta ajiye, ya saka su a gaba sai ga shi sun cinye
tass, har da ƙari, ya yi mamakin dalilin da ya sa suka yi mata haka, ya zaunar da su ya yi musu
nasiha sosai, ya nuna musu ita ma Maryam babarsu ce, duk abin da suka san ba za su yiwa
babarsu ba to kar su yi mata, suka ce to, sannan ya saki jiki da su suka yi fira, Maryam ta ce su
je ta yi musu wanka, ba su yi musu ba suka wuce, sai a lokacin ma ta sa suka yi home work,
ƙarfe takwas Abba ya ce su je su kwanta, ita kuma Maryam ta kwashi unifom ɗinsu ta tafi
wankewa, sai ga shi sun yi wankin a tare da Alhaji suna yi suna fira.
Ita kuwa Momy suna shiga ɗaki ta ɗauki wayar ta sanarwa Sauda duk yadda aka yi, Sauda
ranta ya ɓaci matuƙa ta ji kamar ta taso ta taho gidan yanzu, ta fara tunanin wato daga zuwanta
za ta sa ya tsani ƴaƴansa har yana yi musu faɗa? Nan gaba ai sai duka, kenan ya goyi bayanta
nan gaba ko ita ce da laifi tana kallo za a tauyewa ƴaƴanta haƙƙi, ai kuwa ba zai yiwu ba, ta fara
tunanin hanyar da za ta bi don ta hana su cin amarci, sai dai yaran sun yi ƙanƙantar da za ta
saka su yi wata kissar, don haka kawai ta yanke gara ta dawo su fara gabza yaƙin, ta ce wa
yarinyar ta yi haƙuri su kwanta, amma kar su sake bari ta yi musu wanka, ita ta yi da kanta
sannan ta yiwa ƙannenta.
Washegari haka Maryam ta yi sammakon tashi saboda yaran, don tun a daren ya faɗa mata
girki biyu ake yi da wanda za su ci, da wanda za su tafi da shi, ta dafa shayi ta soya doya da
ƙwai ta saka musu a lunch box ɗin, sannan ta tafi ɗakinsu, ta tarar Momy ta yi wanka za ta fara
yiwa sauran, Kausar tana cewa ita ba za ta yi mata, ta ce"Ya za a yi ki yi musu? Ke ma ai ba
wuce wankan kika yi ba, ku wuce na yi muku".
Momy ta ce"Mu fa Ummanmu ce kawai take yi mana wanka".
Maryam ta ce"Tun da yanzu ba ta nan ai dole ku bari na yi muku".
Ta ce"Mu dai a'a".
Maryam ta juya ta fita, ta sanarwa da mahaifinsu, da mamaki ya ce"Ha'a, wai me yasa yaran
nan suke haka ne?"
Ya fito ya zo ɗakin, ya ce"Ke Momy! A kan me ba za ta yi muku wanka ba?"
Ta ce"Ummanmu ta ce kar mu yarda da ita".
Maryam ranta ya ɓaci ta ce"Ai shikenan". Ta juya ta bar ɗakin.
Ya ce"Ummanku? Au haka ta tsara muku? Abin da ta turo ku ku yi kenan? To zan haɗu da ita!
Ku saka kayan naku a haka ku tafi, idan ta damu sai ta dawo ta dinga yi muku wankan".
"Maza ku saka ku fito, mintu uku na baku". Ya ƙarasa a tsawace yana jin dole ya takawa Sauda
burki don ba za ta lalata masa tarbiyyar yaransa ba.
Yana fita Momy ta shiga banɗaki ta kira Sauda ta sake faɗa mata, ai kuwa ta hasala tana ta
zage-zage.
Suka fito kowaccensu babu sakewa, sai a lokacin suka gaishe shi, ya amsa kafin ya ce"Kun
gaishe da Antinku?"
Duk suka yi shiru, sannan suka gaishe ta ɗaya bayan ɗaya, suka karya mai adaidaitansu ya zo
suka tafi makaranta.
Sun gama karyawa ya ce da Maryam"Don Allah ki yi haƙuri, yara ne kin san duk yadda aka
tsara musu ba za su yi nazari ba, amma zan same ta na yi mata magana, idan ba za ta barki ki
yi yadda ya dace da su ba, to ta zo ta zauna da su".
Maryam ta ce"Allah Ya kyauta".
Kafin ya tafi kasuwa ya tsaya a gidan nasu, ya gaida Inna, ya samu Sauda tana karyawa, ko
kallon shi ba ta yi ba, ya ce"Yawwa Sauda na ga kin aiko mini yarana, ina son ki sani Maryam
za ta iya riƙe su fiye da yadda kike kula da su, sai dai ki sani indai kin bar mata su to fa sai dai ki
koma gefe ki yi kallo, ba zai yiwu tana tufka kina warwarewa ba, saboda shirme kin zauna kina
tsarawa yara shirmen banza, to matata uwa ce a gare su, ya zama dole su yi mata biyayya tun
da ni na haife su!".
A hasale Sauda ta ce"Ita ta haifar mini su? Wallahi babu shegiyar da ta isa ta tsarawa ƴaƴana
yadda za su yi, yarinyar da ba ta samu tarbiyya ba tun daga tushe, har kana kallona kana faɗa
mini kalmar matarka?"
Sai kuma ta saki wata dariya mai kama da ta tsantsar baƙinciki ta ce"Heee masu mata manya!
To a yi mu gani idan tusa za ta hura wuta, yarinyar da ba ta zaman aure har wata abar alfahari
ce? To sai ka jira ka ga zaman ya yiwu kafin ka fara wulaƙanta ni ka watsar da ƴaƴanka!".
Ya ce"Ni dai na faɗa miki, idan kuma kin ƙi ji ba kya ƙi gani ba!". Ya fice ya barta tana ta
bambami.
Inna duk a gabanta a ka yi komai, ba ta ce wani abu ba, dama idan da sabo ta saba da faɗan
nasu, sai da ya fita ta ce"Sauda a nan fa ba ki da hujjar da za ki saka yara su raina matarsa,
idan har ba kya son ta shiga sabgar yaranki to ya zama dole ki koma kansu ki ci gaba da kula
da su, kin ga dai yadda ya gigice a kan yarinyar nan yake rawar kai, kina nan a zaune za ta
gama mallake shi da kissarsu ta zawarawa, irin wannan gogaggun yaran da suke yin aure-aure
wallahi ki kiyaye su,sai kin tashi a tsaye kin ɗaura ɗamara, saboda haka ni yanzu umarni nake
ba ki ba shawara ba, ki kama hanya ki koma ɗakinki a yau, ki kula da ƴaƴanki, sannan ki yi iya
yinki na ganin ba ta mayar da ke bora ba, kar ki yarda ta ƙwace miki mijinki da gidanki".
Sauda ta ce"Shi kenan Inna an jima zan koma".
Inna ta ce"Ko ke fa, wannan ai kina nuna mata ta fi ƙarfinki ne ba za ki iya da ita ba, saboda
haka ki koma ki nuna mata gida naki ne, kuma miji da ƴan'uwan shi ma naki ne!".
Sauda ta jinjina kai cike da gamsuwa, ta tashi ta shige ɗaki.
Zama ta yi ta kira ƙawarta a waya ta sanar da ita za ta koma, ta ɗora da faɗin"Don Allah ya za a
yi ki haɗa ni da wannan mai maganin? Na san shegiyar tana nan ta gigita shi, bazawara ana
marari za a samu miji".
Aliya ta sheƙe da dariya ta ce"Alhamdulillah! Allah na gode maka da ka nuna mini ranar da
Sauda za ta nemi maganin gyara zama".
Sauda ta ce"Au shaƙiyanci za ki yi mini kenan".
Ta ce"To ai ke ce kullum cikin kuri kike kina da ni'imarki ba sai kin sha komai ba, yanzu kika
dawo hanya Hajiyata, zan turo miki lambarta".
Sauda ta ce"Malama yanzu fa nake so, zai yiwu ta aiko mini kayan a yau?"
Aliya ta ce"In sha Allah!".
Tana turo mata, ta kira ta a waya, suka yi ciniki gabaɗaya irin wanda ake cewa ban da me
kishiya su ta siya na dubu ɗari, kuɗin gudunmawa ne dangi suka haɗa mata don ta yi gyaran
dama, da yamma aka aiko mata da kayan, ta gama shirinta tsaf jira kawai take yi ya zo yi wa
Inna sai da safe ta bi shi su tafi.
Yau ɗin Maryam shinkafa da miya ta yi, da alama yaran ba ma su taurin kai ba ne, don kuwa
yau babu wanda ya yi magana a kan abinci, kowa ya ci, sannan sun tsaya ta yi musu wanka,
ban da babbar da ta ce ita ce take yi da kanta dama, sai ta rabu da ita, amma dai sam sun ƙi yin
fira da ita, don haka ita ma ta ke ta harkar gabanta.
Da yamma da ya dawo sai da ya tambaye ta yaran, ta ce babu wata matsala, ya yi wanka ya ci
abinci, ya fita sallah ya dawo, dama idan zai fita sallar isha'i da mota yake fita saboda daga can
yake wucewa gidan Inna ya yi mata sai da safe, don haka yau ma ya wuce, ya ɗan zauna
bayan sun gaisa, hat yanzu ta ƙi dawo masa kamar baya, babu wata fira haka dai babu yabo
babu fallasa, ya tashi zai tafi ta ce"Ka zauna".
Ya zauna yana sauraronta.
Ta ce"Sauda za ta bi ka ta koma kan ƴaƴanta, saboda haka kar na ji kar na gani, ka zama mai
adalci a tsakaninsu, kar sabo ya sa a watsar da tsoho, ta farkon dai ita ce dahir ɗinka, ba zan
ɗauki wulaƙanta mini ƴa ba wallahi, don haka ka ja kunnen yarinyar nan, ta kula ta kiyaye, tun
da zuwa ta yi ta tarar da ita da ƴaƴanta, ba ta san faɗi-tashin da aka yi kafin ka kai matakin da
kake a yanzu ba".
Ya ce"To Inna za a kiyaye in sha Allah!".
Ya tashi ya fita yana yi mata sai da safe, ya ɗan jima a motar kafin Saudar ta fito da akwatinta,
ta buɗe motar ta shiga ya ja suka tafi, babu wanda ya ce wa wani ƙala har suka ƙarasa gidan,
lokacin yaran suna ɗaki, Maryam kuwa tana hakimce a babban falo cikin wata fitinanniyar rigar
bacci, suka shigo da sallama, niyyarta idan ya shigo ta je yin oyoyo amma sai ta yi turus ganin
shi tare da wata wacce ba sai an faɗa ba ta san matarsa ce, sai da gabanta ya faɗi, ta daure ta
ce"Sannunku da zuwa".
Alhaji kuwa ya bi ta da kallon burgewa, wankan ya burge shi, don Sauda babu ruwanta da wani
wankan dare ballantana kuma kayan bacci, dogayen riguna ne marasa nauyi kayan baccinta
tun da ta fara haihuwa, ya haɗiyi wani yawu muƙut wanda har Sauda ta ji sautin, zuciyarta ta
ƙara kumbura, ta kasa shigewa kawai tana tsaye tana ƙarewa Maryam kallo, sai Alhaji ne ya
katse shirun nasu da cewar"Na barki ke kaɗai a gida".
Sauda ta yi masa mugun kallo ta ce"E tabbas ita kaɗai,