Showing 9001 words to 12000 words out of 39853 words

Chapter 4 - MIJI GOMA Book Complete By Sadiya Abdul.pdf

25 May 2025

7745

mamaki, sai kuma jikinta ya yi sanyi, ita dai ba ta ga abin da aka yi da zai saka ta yi
yaji ba, "Daga kunna gas? Allah Ya kyauta" Ta faɗa tana shigewa ɗakinta.

A ɓangaren Maryam ranta fess ta ƙarasa gida, duk da tana ɗan fargabar abin da Baba zai ce,
faɗa ne ta saba da shi musamman ta wajen shi, kuma shi Baba yana da wani hali wanda yake
burge ta, idan ya yi maka faɗa da nasiha a kan abu, ka ƙi yarda ko ka ƙi dainawa, shikenan sai
ya ce ka fi ƙarfinsa ya zare hannu a tafiyarka, sam ba zai takura maka ka yi dole ba, shiyasa
take ganin ba zai takura sai ta koma gidan Nazifi ba.

Ai kuwa da Baban ta fara cin karo, a ƙofar gida ta same shi, suna tattaunawa da wani
maƙocinsu, dama gaida manyan unguwa ba ɗabi'arta ba ce, don haka kanta tsaye ta wuce su
ta shiga gidan, Baba da ya gane ta sai da gabansa ya faɗi, ya bita da kallo.

Tana shiga da sallama Uwani ta tare ta ta rungume tana cewa"Sannu da zuwa, maza shige
ɗaki, ai ba neman kai muke yi da ke ba" Ta yi maganar tana jan akwatin zuwa ɗaki.

Maryam ta shiga ta ajiye hijjabinta, ta kwanta a gado, Uwani ta shigo tana cewa"Kuma Nazifin
yana kallo kika taho?"

Ta ce"A'a ba ya nan, sai dai ya dawo ya ga wayam".

Uwani za ta yi magana suka ji sallamar Baba, ya ɗaga labulen ɗakin yana cewa"Wace ta shigo
yanzu kamar Maryam?"

Uwani ta ce"Ita ce, zama ya ƙi daɗi, tun a daren da aka kaita suke ƙunsa mata baƙinciki ba ta
huta ba".

Baba ya ce"Ban gane zama ya ƙi daɗi ba, amma dai kin manta kwana biyu da kaita gidan miji
ko? Da har za ta kwaso ƙafa ta dawo ta shimfiɗa miki ƙarairayi ki yarda. Ke ta shi ki fice ki koma
gidanki".

Uwani ta rafka salati har da tafa hannu kafin ta ce"Wallahi Malam irinku ne masu siyar da ƴarsu
a gidan auren, ta yi ta bauta da sunan zaman aure, ai aƙalla ka tsaya ka ji me ya dawo da ita
tukunna kafin ka kore ta".

Ya ce"Wane irin rashin haƙuri ne zai sa ta dawo gida kwana biyu da aure?"

Ta shiga tsara masa ƙarya da kashi-kashi, har da cewa yau ɗin Gwaggon har marinta ta yi a
gaban shi bai ce komai ba, ga shi kullum sai ta yi mata tuwo, ga jikarta tana zaginta. Baba ya yi
shiru yana nazari kafin ya ce"Uwani duk da hakan wannan bai kai ta taho gida, ko waya ce sai
ta yi wani ya je a sasanta yanzu idan aka fahimci har ta zo gida me duniya za ta ce?"
Uwani ta ce"Ita fa rayuwa indai za ka biyewa duniya za ka ƙare a wahala ne, ina ruwanka da
duniya ko mutanen cikinta, yadda za su yi suka don ta dawo haka za su yi idan miji da uwarsa
sun kassara ta".

Tsaki Baba kawai ya yi, don ba ya iya doguwar ja in ja, ya fice daga gidan.

Uwani ta ce"Maryam dole fa ki buɗe baki ki ƙwatarwa kanki ƴancinki, idan ba haka ba wallahi
kwasarki zai yi ya maida ki, ƙarama da ke da ƙuruciya ki ƙare a wahala da uwar miji? Duk yadda
za a yi ki ce ba za ki koma ba, kar ki sake ki sare, don auren kwana biyu mene ne marabarki da
buduruwa? Yanzu wani saurayin zai aure ki wanda ya fi shi komai, Allah Ya sa dai bai ɗora miki
idda ba".

Ta tsare ta da ido tana jiran amsarta, Maryam ta ce"Sai dai kar a kuma".

Uwani ta ce"Ya cuce ki! Allah Ya saka miki".

Nazifi yana komawa gida ya tarar an karo ƙofar ɗakin Maryam, ga shi dai ba lokacin sanyi ba
ballantana ya ce shiyasa ta rufe, sai ya raya a ransa ko bacci ta yi da wuri, duk da sai yanzu
ake kiraye-kirayen sallar isha'i, ya fara shiga ɗakin Gwaggo da sallama, ta amsa ya shiga ya
zauna yana yi mata sannu, ta ce"Ni kam Nazifi matarka wace iri ce? Daga magana a kan kunna
gas shikenan ta haɗa kaya ta bar gidan?"

Gabansa ya faɗi ya ce"Ta bar gidan kuma?"

Gwaggo ta ce"Ka ga Nazifi ni kam zan bar gidan nan, na tabbata Auduwa bai saka ƴan haya a
gidanmu ba, ka taimaka ka yi masa magana na koma, idan na mutu ni kaɗai shikenan, ko na
kumbura babu wanda ya sani duk tsiya dai kafin na fashe na ishi duniya da wari wani zai shigo
ya gan ni".
Nazifi ya ce"Haba Gwaggo wannan wace irin magana ce kike yi?"

Ta ce"Ka ga ka je ka dawo da matarka, gobe zan bar gidan nan, yanzun ma don dare ya yi ne,

ka faɗa mata ta yi haƙuri ni ba baƙuwar zafi ba ce".

Nazifi ya tashi ya fita jiki a mace, a ƙofar gida ya tsaya ya kira lambar Maryam, ta ɗaga ya
ce"Maryam kina ina?"

Ta ce"Gidanmu".

Ya ce"Don Allah me yasa za ki yi mini haka? Me ya yi zafi?"

Tsaki kawai ta yi ta kashe wayar, ya bi wayar da kallon mamaki, bai taɓa zaton da gaske za ta
iya yin yaji a kwana biyu da aurensu ba, ya mayar da wayar aljihu ya kama hanyar gidansu.

Yana ƙarasawa yayanta Sunusi ya zo shiga gidan, suka gaisa yana ce masa"Ya Maryam ɗin?
Ko wani abun za ka karɓar mata?"

Nazifi ya yi yaƙe ya ce"Ai tana ciki ma, zuwa na yi mu tafi".

Sunusi ya zaro ido ya ce"Kamar ya tana ciki? Uban me ta zo yi?"

Nazifi ya fara kame-kame kafin ya ce"Ba wata matsala ba ce, za mu sasanta".

Sunusi ya shiga gidan ransa a ɓace, ya fara ƙwalawa Maryam kira, ta tashi zaune tana
harare-harare, Uwani da ta fito daga banɗaki ta ajiye buta a fusace ta ce"To Allah Ya dawo da
kai! Lafiya kake yi mata kiran mafarauta? Uwar me ta kashe maka?"

Ya ce"Yanzu na ga mijinta a ƙofar gida, wai babarmu uban me ya dawo da ita tun yau?"

Ta yi masa daƙuwa ta ce"Ubanka ne! Kuma wa ya sako ka a wannan rigimar?"

Da mamaki ya ce"Rigima fa kika ce? Lallai, kenan nufinki waje za ki ba ta ta zauna? Ke
Maryam!"

Ya ƙarasa yana shiga ɗakin, kamar zai dake ta ya ce"Uban me ya haɗa ku da shi, da har kika
kwaso jiki kika dawo?"

Ta yi banza da shi, tana turo baki, ya ce"Ai dama na san zai yi wuya ki zauna wallahi, idan na ce
da motsi a kanki sai a ce ba haka ba, to ga shi dai an fara gani, sai ki wuce ga shi can yana
jiranki a ƙofar gida".

Uwani ta ce"Kai Sunusi ka kiyaye ni fa! Ka fita daga idona na rufe, ina ruwanka da zancen nan
wai?"

Ya ce"Allah Ya kyauta". Ya shiga ɗakinsa.

Uwani ta saka hijjabi ta fita, ta samu Nazifi tsaye yana jira, ya tsuguna ya gaishe ta, sannan ta
ce"Ka shigo daga ciki, magana ai ta wuce ƙofar gida".

Ya bi bayanta yana sunne kai ƙasa irin na surukai.

A tsakar gida ta shimfiɗa tabarma, ya zauna sannan ta shiga ɗaki ta ce da Maryam"Ki fito,
kuma saura ya yi miki kallon soyayya ki haƙura, shi fa aure irin wannan da ya fara da matsala
wallahi matsalar nan ba ta taɓa ƙarewa, sai dai ta yi ta girmama, ki tsufa a haka kina shaƙar
baƙinciki, idan kuma kin ji kin gani to sai ki bi shi ki koma".
Maryam ta tashi ta fito, suka zauna aka ƙara gaisawa, Uwani ta fara magana"Nazifi ka ba ni
mamaki, ka yi mana bazata! Ashe kai uwarka ka aurowa ƴata ba ka yi bayani ba? Ta ya za ku
rufar mata da bauta ba ta da hutu ta ko'ina? Ka ga a gidan nan ma da na saka Maryam aiki gara
na yi, saboda ba na so ta wahala, a gaskiya wannan zama naku ba mai yiwuwa ba ne, tun da
abun har ya kai ta fara dukanta to kawai ka sake ta kowa ya huta tun ba ku fara tara zuri'a ba".

Gabansa ya faɗi ya ce"Duka kuma? Maryam Gwaggon ce ta dake ki?"

Ta ɓata rai ta kau da kai gefe.

Uwani ta ce"To ƙarya za ta yi mata kenan?"

Ya ce"A'a kawai dai na yi mamaki ne, saboda ita Gwaggon ba ta ce mini an yi haka ba".

Ta taɓe baki ta ce"Dama mutum zai yi ya ce ya yi ne? Nazifi don Allah salun-alun ka furta mata
kalmar saki, ba sai ka wahalar da shari'a ba".

Ya ce"Haba Umma wannan ai ƙaramar matsala ce wacce za a magance ta, abun bai kai na
rabuwa ba".

Ta ce"Ban ga alama ba! Uwarka ce fa, ba za ka taɓa canzata ba, don haka ita ya kamata ka
zaɓa ba matarka ba, yanzu idan ta kwashe maka albarka kana ganin zan bar ƴata ta ci gaba da
zama da kai da rashin albarkar uwa? A'a ba zai yiwu ba, ka rabu da ita kawai shi ne maslaha".

Nazifi ya ce"A yi haƙuri don Allah, indai babata ce ta ce ma gobe za ta bar gidan, shikenan babu
wani abu da zai sake tasowa kuma in sha Allah".

Uwani ta ce"To ai gata nan, idan za ta koma shikenan!" Ta tashi ta shiga ɗaki.

Ya kalli Maryam ya ce"Haba Maryam, yanzu wannan har ya kai ki taho gida? Wannan ƴar
matsalar da za mu daidaita a tsakaninmu?"

Ta ce"Kai kake mata kallon ƙaramar matsala, ni kam babba ce a wajena".

Ya ce"Wannan ma ai abun kunya ne a ce har kin yi yaji, ki rufa mini asiri ki zo mu koma".

Ta ce"Abun kunya ya wuce na zuwan uwa ta zaune a gidan yara?"

Maganar ta dake shi sosai, ya ji haushi amma ya dake ya ce"To ki tashi dai mu tafi".

Ta ce"Nazifi wai da wane yaren ake yi maka bayani? Aka ce maka wannan auren ba mai
yiwuwa ba ne ba fa! Don haka ka sallame ni kawai".

Ya ce"Ba dai Gwaggo ba ce? Za ta tafi ai na faɗa miki".

Ta ce"Ni ko ta tafi na fasa auren, ka sallame ni idan kana son zaman lafiya".

Nazifi ya ce"Shikenan bari na tafi, zuwa gobe idan kika huce na dawo mu yi magana".

Ta ce"Nu babu wata hucewa da zan yi, za dai ka ɓatawa kanka lokaci".

Ya fice daga gidan yana jin ransa babu daɗi.



08028966015
[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_



*SADIYA ABDULRAZAƘ*


*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne
hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman
aure?*

Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu

*FIRST CLASS WRITERS*

PAGE 5


A hanya ya tsaya ya siyawa Gwaggo tuwo ya tafi da shi gidan, ya miƙa mata ya zauna ya yi
shiru, ta ce"Nazifi, ko daga gidan nasu kake?"

Ya ce"Daga can nake".

Ta ce"Ya kuka yi?"

Ya ce"Wallahi ita da babar tata sun ƙi fahimtata, wai zancen ma na sake ta suke yi".

Gwaggo ta ce"La ila ha illallahu! Saki kuma? Duk saboda ni? Ka ga taya ni haɗa kayan nan na
bar maka gidanka yau, ba ka ba ta haƙuri ba ka faɗa mata ni ba baƙuwar zafi ba ce?"

Nazifi ya ce"Na faɗa mata za ki tafi tun da haka ta zaɓa, amma duk da haka zancen rabuwa
take yi".

Ta ce"To Allah Ya kyauta".

Ganin ta janyo tsohuwar akwatinta ta fara haɗa kaya jikinsa ya yi sanyi kamar an zare masa
laka, zuciyarsa kuma ta fara kumbura, sai a yanzu ne ma yake ganin Maryam da uwarta fa sun
ci mutuncinsa, ya tuna ƙima sa daraja irin ta uwa, ya tuna goyon ciki, haihuwa har zuwa
shayarwa da raino, ga kula da tarbiyya da karatunsa Gwaggo ba ta gajiya ba, anya kuwa idan
ya zaɓi ra'ayin wata mace wacce suka haɗu rana tsaka ya wofantar da mahaifiyarsa zai gama
da duniya lafiya? Sai ya ji tausayinta ya kama shi, har ya ji gara ya zaɓi rayuwa babu aure a kan
ya zama silar ɓacin ranta, ya matsa kusa da ita, ya mayar da kayan ya zuge akwatin ya matsar
gefe, sai ya sunkuyar da kai, Gwaggo ta kafe shi da kallo, ya ce"Gwaggo babu inda za ki je fa,
ke uwata ce ba a canza uwa, amma ana canza mata, babu macen da za ta raba ni da ke dare
ɗaya, zan iya rayuwa babu auren ma gabaɗaya matuƙar ina tare da albarkarki".

Ita ma sai jikinta ya yi sanyi, ta ce"Nazifi ba zai yiwu ka ƙi aure saboda ni ba, wallahi so ne yasa
na zaɓi zama a kusa da kai, ka sani duk cikinku na fi sonka, ba zan so abin da zai takura
rayuwarka ba, saboda haka gara na tafi ɗin kawai tun da haka ta zaɓa".

Ya ce"Gwaggo wallahi ba za ki tafi ba, indai ba za ta zauna da ke ba a gidan nan, to tabbas zan
haƙura na sake ta kamar yadda ta ce".

Gwaggo ta ce"A'a kar ma ka fara, ba zai faru ba ma, tun da ka ce sai na zauna to zan kwashe
kayana daga kitchen ɗinta, sannan zan dinga girkina a murhuna, idan ta ga dama ma ko gaishe

ni kar ta yi, tun da ba zamana take yi ba, indai hakan ya yi mata shikenan".

Ya ce"Wallahi da na san haka Maryam take da ba zan fara aurenta ba"

Gwaggo ta ce"Ka daina yiwa kanka baki, ai idan ka lura har da ƙuruciya da rawar kai irin ra
yaran zamani, Allah dai Ya kyauta".

Ya ce"Amin, bari na siyo miki tuwon".

Ta ce"To kai me ka ci?"

Ya ce"Tun kunu da na sha a kasuwa".

Da sigar tsokana ta ce"Kai dai sunanka angogu ba ango ba, to ko ƴar taliya za ka dafa mana?
Ka ga Yasmin tuwon rana da ka siyo ma ba ta ci ba, ka ganta ta yi lakur ko motsin kirki ba ta
iyawa saboda yunwa, ba mu iya kunna gas ɗin ba, kuma matarka ta ce za mu babbake, na ce
to mu bar shi tun da ba mu san kalar kaifin bakinta ba".
Ransa a ɓace ya ce"Kamar ya za ku babbake?"

Ta kwashe labarin yadda aka yi da Yasmin ta zo kunna gas ɗin ta faɗa masa, ya ce"Tabb ai
kuwa da kun babbake ɗin, gaskiya kar yarinyar nan ta sake gwada irin wannan tsautsayin,
nawa take da za ta ce za ta yi girki?"

Ya tashi ya shiga kitchen ɗin, sai bai ga kayan abincin ba, ya koma ɗaki nan ma bai gani ba,
saboda Maryam a cikin sif ta loda su ta kuma rufe ta zare mukullin ta tafi da shi, abun ya ba shi
mamaki, kamar ya kira ta ya tambaye ta, sai kuma ya ga ai ba shi ya siyo ba dama gararta ce,
don haka ya fita ya siyo taliyar ya dafa musu, suna ci suna fira cike da nishaɗi kamar suna
gidansu na da.

Ƙarfe tara ya yi mata sallama ya tafi ya kwanta, sai dai ya kasa baccin, ya shiga tunanin yadda
rayuwar aurensa ta fara da ƙalubale, yana son Maryam sosai, har zuciyarsa yake son ƙare
rayuwarsa da ita, sai dai ya fara tunanin ita ba son shi take yi ba, tun da har wannan ƴar
matsalar za ta saka ta ce ya sake ta, wajen goma da rabi ya kira ta a waya, har sau uku ba ta
ɗaga ba, ya kunna data ya ganta a online, kamar ya yi mata magana sai ya fasa, ta ajiye wayar
yana jira gobe ta yi, ya je ya ji yadda za su kaya da ita, don shi dai bai shirya rabuwa da ita ba.

A ɓangaren Maryam kuwa bayan tafiyar Nazifi, Uwani ta saka ta a gaba da zuga, tana nuna
mata ya zama dole ta haƙura da auren nan indai tana son kanta da arziƙi, ta na ta nuna mata
mutuwar aure ba komai ba ce, ballantana ita da ba ta haihu ba ma, nan da nan wani da ya fi shi
zai fito ya aure ta, ta nuna mata da ka yi rayuwar aure cikin ƙunci da rashin ƴanci gara a ce ka ƙi
zaman auren ma, ai dai ka san kana da cikakken ƴancinka.

Shi kuwa Baba bai sake bi ta kanta ba, ya zuba ido ta ga gudun ruwansu.

Tsaf ta kwashe karatun da aka biya mata, don haka har ta fara jin tsanar Nazifi shi da auren
nasa duka, ta kuma saka a ranta ba za ta koma ba, dole ya sake ta, shiyasa tana kallon kiransa
ma ta ƙi ɗagawa, lafiya ƙalau ta shari baccinta sai ta ji kamar dama ba aure ta yi ba, unguwa
kawai ta je ta kwana biyu ta dawo gidan babarta mai ƙaunarta.
Washegari Nazifi tun safe ya kira ta a waya ba ta ɗauka ba, haka dai ya tafi kasuwa, sai la'asar
ya tashi ya dawo gida ya yi wanka ya canza kaya ya tafi gidan nasu, da ita ya fara cin karo
bayan ya shawo kwanar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login