Showing 18001 words to 21000 words out of 39853 words

Chapter 7 - MIJI GOMA Book Complete By Sadiya Abdul.pdf

25 May 2025

7742

iya ƙwatarwa ƙannenka
ƴanci ba, Allah wadaran naka ya lalace".

Sunusi ya buɗe ɗakinsa ya shige, ita so ta yi ya fusata ya kwashi abokansa a daren su je su
yiwa Nazifi duka, ashe ba zai iya komai ba.

Sai da ruwan ya yi zafi sosai sannan ta juye a baho ta kai banɗaki, ta shiga ɗakin ta taso
Maryam ta ce"Maza ki je ki yi wanka, ki gaggasa jikinki sosai da zani, idan ba haka ba ba za ki
iya bacci ba, Allah Ya saka miki".

Maryam ta yi wanka, ta zuba mata abinci ta ci, ta kwanta nan take kuwa sai bacci ya ɗauke ta.

Washegari Uwani ta kira ƙawayenta da maƙota suka je suka kwashe kaya tass, a ranar kuwa ta
siyar da su aka ajiye kuɗin. Sai bayan kwana biyu da Maryam ta nutsu sannan ta gane an
kwashi wasu daga cikin kayan lefen, amma dai ta yi shiru ba ta ce komai ba, don ta fi tunanin a
cikin masu kwaso kayan ne wata ta ɗiba.
Nan fa ta gyara zaman idda, ta manta da ta taɓa rayuwa da Nazifi, kullum Uwani ƙara koyar da
itw darussa take yi, ita kuma tana kwashewa tana adana su a kanta, a haka har ta gama
iddarta, ta ɗiɗɗinka kayan lefenta, tana shiga tana fita, sai Uwani ta ba ta shawarar ta fara
sana'a don zawarci sai da sana'a, da fari Baba ya hana ya ce ba za ta yi ba, to akwai ƙawarta
da take siyar da abinci a tashar kusa da layin nasu, Maryam sai ta tsiri cin kwalliya ta je ta
zauna kawai a wajen, suna kwashewa da maza, Baba ya yi faɗan har ya watsar, ƙarshe
abokinsa ne ya ba shi shawarar gara ma ya barta ta fara sana'ar don a san zaman tashar nata
mai dalili ne, don haka ya barta, ta fara dafa shinkafa da taliya tana kaiwa tashar, uwar kwalliyar
da take ci da tsaftarta, uwa-uba kuma yadda take ƙawata abincin, da yadda take sakin baki su
yi ta fira da maza shi yake ƙara janyo mata hankulan maza, da ta fito za ta siyar ta koma gida,
ta ƙirga ribarta cass ta adana, nan da nan kuwa zawarawa suka fara tururuwar zuwa wajenta,
amma sai Uwani ta nuna mata kar ta sake ta ce za ta yi aure yanzu, ta bari sai ta tara wani abu
tukunna, don haka duk wanda ya zo da zancen aure sai ta saita masa hanya, wanda kuma
dama su ƴan a bi yarima a sha kiɗa ne, ƴan rage dare sai ta yi ta cin kuɗinsu, amma hakan ba
ya saka ta bawa wani jikinta, sai dai ta yi ta maka wayo, har ka gaji ka kama gabanka.

Ta kusa shekara a gida, ta haɗu da wani Hamza, lokaci ɗaya ta ji tana ƙaunar shi, kuma za ta
iya auren shi, don haka duk yadda Uwani ta so nuna mata ba yanzu ba, ba ta yarda ba, ƙarshe
dai ta rabu da ita, suka sasanta tsakaninsu, babu jimawa Hamza ya turo manyansa, bayan
gabatar da bincike an ga ba shi da matsala aka saka ranar aurensu wata biyar, suka ci gaba da

soyayyarsu suna kuma shirin aure.


08028966015
[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_



*SADIYA ABDULRAZAƘ*


*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne
hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman
aure?*

Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu

*FIRST CLASS WRITERS*

PAGE 8


A wannan karon Uwani ta dage sosai wajen yiwa Maryam karatunta, ta riga ta gama hawa
gada ɗoɗar, ta yarda zawarci ba komai ba ne, don haka ba za ta ɗauki raini ko tauye haƙƙi daga
wajen miji da danginsa ba, tun da miji goma ba uba goma ba ne. Kusan rabin kayan ɗakin da
kuɗinta ta yi shi, Hamza bai yi lefe ba, kuɗi ya bayar ta sayo kaya ta ɗinɗinka, aka ɗaura aure
aka kai amarya ɗakinta, gida ne madaidaici, mai ɗauke da babban falo da ɗakuna uku a cikinsa,
sai kitchen da banɗaki, gidan ya yi kyau babu laifi komai fess.

Maryam tana son shi, don Hamza ɗan soyayya ne, sosai take tarairayarta hakan ya ƙara mata
ƙaunar shi a zuciyarta, kuma ƴan'uwan shi ma suna sonta suna ba ta kulawa da janta a jiki, don
sai da ta yi sati ɗaya ta fara girki, tun washegarin ranar da aka kaita ake aiko musu abinci daga
gidansu, fal kula su ci su zubawa baƙi, na safe kawai take yi, ga gararta da ta zo da ita, cefane
kawai yake yi a yi lafiyayyen girki.

Uwani tana ta baza kunne da ido ta ji ta inda matsala za ta ɓullo ta ji shiru, ta sha ƙara

jaddadawa Maryam idan da matsala fa kar ta ɓoye ta cuci kanta, amma sai ta ce mata lafiya
ƙalau suke zaune, takaicin duniya ya ishe ta kuwa, kullum da lamarin take kwana.

Watan Maryam ɗaya a gidan ta samu ciki, mai masifar laulayi kuwa, ga kwaɗayi sosai, sai ta ce
a siyo mata abu idan aka kawo kaɗan za ta ci ta fara kwara amai, ga muguwar kasala ta sa
kwalliyar ma ta daina yi, kuma ta tsani Hamza ya matso kusa da ita, sai ta ji ba ta son warin
jikinsa ko da kuwa yanzu ta fito daga wanka, indai za su kasance to fa sai ta yi ta kwara amai,
ƙarshe sai take komawa wani ɗakin ta kwana, tun Hamza yana daurewa har abun ya fara ba shi
haushi, duk wata ƴar soyayya da kulawa ta daina ba shi.

Watarana ya sameta kwance a ɗaki, yana haɗe rai ya zauna ya ce"Tashi za mu yi magana".

Ta tashi tana kallon shi, ya ce"Maryam na ga wannan cikin yana wahalar da ke, kalli yadda duk
kika rame kika zama wata iri, duk kin kojale..."

Ganin yana maganar yana taɓe baki kamar mai ƙyamarta ta katse shi da faɗin"Hamza! Ni kake
cewa na kojale? Kar fa ka manta ko me ya same ni sanadin cikinka ne, dama na lura wani
kallon rainin hankali kake yi mini kwana biyun nan!". Ta ƙarasa maganar a hasale.

Ya ce"Kin ga ni ban ce ki ɗaga mini murya ba, masalaha ce na zo da ita".

Ta yi shiru tana sauraron shi . Ya ce"Maryam kin ga fa har yanzu ba a yi wata biyu da aurenmu
ba, ɗan amarcin nan ba mu ci ba, ni da na so a ce matata sai ta yi shekara ɗaya ko wata shida
haka kafin ta samu ciki, kin ga lokacin an ci amarci an fara marmarin samun ɗa ko ƴa, amma
yanzu kalle ki fa don Allah, ni yanzu a shawarata kawai a cire cikin nan, tun da ba ƙwari ya yi
ba, sai na siyo miki ƙwaya ki dinga amfani da ita, idan aka kwana biyu kika huta kamar nan da
wata shida haka sai ki ɗauki wani cikin, don ni gaskiya yanzu duk na takura gidan ma ba daɗi
yake yi mini ba".

Haushi ya kamata ta ce"Ka gama?"

Ya ce"Na gama".

Ta ce"Hamza ashe haka kake ba ka da kirki ba ka san ya kamata ba? Yanzu idan da tausayi ina
ta wahala da cikinka za ka kalle ni ka ce na cire shi? To bari ka ji na faɗa maka, ko cikin shege
na yi ba zan cire shi ba sai na haife shi, ballantana na halak, idan ka ga ba za ka iya zama da ni
a haka ba ka sallame ni, ba a kanka na fara rabuwa da miji ba, miji goma ba uba goma ba ne!".
Tun da ta furta masa ba shi da kirki ya kafe ta da ido cike da mamaki, duk da ya san Maryam ko
a wajen siyar da abinci ba kanwar lasa ba ce amma bai yi zaton za ta iya kallon mijinta ta ce
masa ba shi da kirki ba, ya ce"Kina cikin hayyacinki kuwa? Ni ne ba ni da kirki?"

Tana yi masa wani mugun kallo ta ce"Akwai ƙarshen rashin kirkin da ya fi wannan? Ina fama da

cikinka a maimakon ka tausaya mini sai ka ce a cire?"

Ya ce"Kin ga, ni fa ba tausayinki ne ba na yi ba, kawai dai dama can na tsara idan na yi aure
matata ba za ta haihu da wuri ba".

Ta ce"To da ka san haka me ya hana ka zuge tazugen wandonka? Ai ka ga da ba zan ma samu
cikin ba ballantana ka ce a zubar na ƙi".

Ya yi shiru ya rasa abun cewa, ta ce"Hamza! Na aureka ne saboda ina sonka, wallahi son da
nake yi maka ba zai saka na ɗauki wulaƙanci daga gareka ba, idan ka san ba za ka iya ba tun
wuri ka sallame ni, na je na raini cikina a gaban iyayena".

Tsaki kawai ya yi ya tashi ya fita.

Yana fita kuwa ta ɗakko waya, ta kira babarta ta juye mata komai, Uwani a zaune take amma
sai da ta miƙe tsaye, a ranta tana faɗin 'lokaci ya yi'

Ta ce"Innalillahi! Ke dai Maryam ba kya dacen mazan aure, shi kuma ba ya son haihuwa? To ai
har gara ma Nazifin shi matsalar babar shi ne, shi fa miji da ba ya son haihuwa ya fi uban kowa
matsala a rayuwar aure, kin ga wannan maganar ma ai ba ta waya ba ce, gobe zan zo mu baje
ta a faifai, ina! Ai ba ki ga wajen zama ba".
Maryam ta ce"To Allah Ya kaimu".

Haka kuwa aka yi, washegari da yamma ta je gidan nata, tana ganinta ta fara salati tana tafe
hannu ta ce"Maryam kin ga yadda kika zama kuwa? Kamar wata horuwa! Mun shiga uku, nan
duk cikin ne babu yunwa?"

Ba ta ce komai ba, ta gaishe ta ta kawo mata ruwa da abinci, ta ce"Ai Maryam ba zan iya cin
komai ba, wai me ma kika ce mini? Har ya ce a cire cikin?"

Ta ce"Haka ya ce, ni kuwa babu mai saka ni na cire cikin nan wallahi!".

Uwani gabanta ya faɗi jin ba za ta yarda a cire cikin ba, ta san halin Maryam sarai idan ba ta
son abu babu wanda zai mata dole, sai dai da siyasa da dabara.

Ta ce"Maryam kin san matsalar wanda ba ya son haihuwa kuwa? Kin ga na farko dai idan kika
samu ciki a wulaƙance zai dinga kallonki, ga wahalar laulayi ga wulaƙanci da rashin kulawa, irin
su gani suke ma asara ce su kashewa cikin kuɗi, sai ki ga mace idan ba sana'a take yi ba zuwa
awo ma ya gagare ta, wani kuma hanawa zai yi ko da kuɗin nata, ke akwai wacce tana naƙuda
mijin ya kulleta a ɗaki tana ihu tana magiya har sai da ta haifo ɗan ya mutu sannan ya buɗe..."

Dariyar da Maryam ta yi ce ta katse ta daga shararo ƙaryarta, ta ce"Maryam! Dariya ma kike

yi?"

Maryam ta ce"To ai abun dariya ma ya bani, ya rufe ta a ɗaki fa?"

Ta ƙara sautin dariyar ta ce"Lallai wannan ba shi da kirki, ai kuwa da ni ce idan na fito kai ma sai
na shaƙe ka ka mutu".

Uwani ta ce"Kina wasa da iskancin maza, to ai ni ba ma wannan gaɓar ce ta fi damuna ba, kin
san kuwa idan aka haifi ɗan shi da babu duk ɗaya a wajensa? Wallahi ko sutura ba yi masa zai
yi ba, wani ma sai ki ga yana tsangwamar yaron kamar ba jininsa ba, wani agolan ma ya fi shi
gata, sannan kina nan zaune sake da baki zai auro yarinya ta yi planing su yi ta soyayyarsu
suna ƙunsa miki takaici".

Maryam ta ce"Kamar dole? Wallahi babu namijin da zai yi mini haka".

Uwani ta ce"To kuwa maganin kar a yi kar a fara, muddin ba za ki iya ɗaukar wannan ba gara
ma ki cire cikin nan, kuma ki nemi saki, don haihuwa da irin wannan mijin ba ƙaramar matsala
ba ce".

Maryam ta ce"Ni fa ba zan cire cikin nan ba, haka kawai nake jin ina son abin da zan haifa, idan
na haihu komai sai ya biyo baya".

Uwani ta ce"Kina nufin za ki jure cin mutuncin shi kafin haihuwar?"

Ta ce"Ba zai ma fara ba".

Duk ta inda Uwani ya ɓullo sai Maryam ta kauce, saboda ita ba za ta zubar da ciki ba, don
haka Uwani ta tattara ta tafi, lokacin dab da sallar magriba.

A ƙofar gida suka yi kiciɓus da Hamza zai shiga, ya rage tsayi ya gaishe ta, ta amsa tana
cewa"Ya mai jikin?"

Ya ce"Da sauƙi".

Ta ce"Ai yau dai na ce bari na zo na duba ta, ashe haka ta zama ta yi yarab kamar haihuwa ta
goma? Na ci to Hamza dai sai haƙuri ba a samu damar angwancewa ba, to wannan yaushe
mutum ta tada komaɗarsa? Ana ta jigilar amai da yawu".

Hamza ya ce"Wallahi kuwa, sai haƙuri".

Ta ce"Haƙuri ya zama dole ai, tun da abun nata na gado ne, uwarta ma fa haka ta yi, idan ta
samu ciki duk haƙurin Malam sai ya ƙosa, ƙarshe daina rabon kwana yake da ita, kuma ba ma
wannan ba, haka take haifo ɗan a yaƙune da cutar tamowa, duk mutuwa suka yi sai Maryam

ɗin ce ta rayu, amma fa ta ci wuya, an kashe kuɗi maƙudai, idan aka kwantar da ita kamar
gawa, a yaƙune, uwar ta sha mantawa ta fizgota ta yi zaton zani ne babu mutum a ciki".

Hamza ya cika da mamakin surutun matar nan, gefen zuciyarsa kuwa cike yake da tsoron kar a
haifo masa ɗa irin wannan.

Ta ƙara da faɗin"Kai dai ka fara banki kawai, don da alama ita ma gado ta yo, sai anjima Allah
Ya sawaƙe".

Ya ce"Bari na raka ki titi".

Suna tafe tana ƙara zuga shi da ƙarairayi kala-kala, shi kuwa ya hau kai ya zauna daram, ya
sake jin haushin Maryam da ƙin zubar da cikin da ta yi, ya samar mata adaidaita sahu ya biya
kuɗin sannan ya koma gida.

Ya tarar da ita tana sallah, ya yi alwala shi ma ya fita masallaci, da ya dawo ya zauna ta kawo
masa abinci, ya ci kaɗan, saboda yanzu abincin nata ma ƙyanƙyamin shi yake ji saboda amai
da tofe-tofen yawun da take yi, shi a yadda yake jin labarin haihuwa wannan jinin biƙin da
sauransu bai ma san yadda zai zauna da ita inuwa ɗaya ba idan ta haihu, dole dai ta tafi gida
dab da za ta haihu, idan ɗan ya yi wata uku sai ta dawo, saboda shi ko wata mata ce a
unguwarsu take siyar da wani abu, daga ranar da aka ce ta haihu to fa ya daina siyan abu a
wajenta, ƙyanƙyami yake ji, har sai ya manta ɗan ta ɓa girma sannan ya ci gaba da siya,
ballantana kuma a ce matarsa wacce dole ya ci abincinta.

Ya yi nisa a duniyar tunani ya ji muryar Maryam ta ce"Wai me yasa yanzu ka rage cin abinci?"

Ya ce"Babu komai".

Sannan ya tashi ya fice daga gidan.

Tun daga ranar ya yi mugun jan baya da ita, duka ya canza mata, a da yana biyo ta ɗakin da ta
koma da kwana su kwana tare ko ba ta so, daga baya ya daina, tsakaninta da shi da safe idan
ya fito zau tafi aiki ya zauna ya karya, da yana dawowa ya ci na rana daga baya ya daina, sai
na dare shi ma ba kullum yake ci ba, sannan ba ya dawowa gidan da wuri, sai ya kai sha biyu a
waje, kuma tun da gara ta ƙare ta lura shi mutum ne mai maƙo da bin diddigin abinci, idan ya
auno shinkafa kwana ɗaya sai ya yi ta mitar ta ƙare da wuri, ya ce duk cikin nan ne yake saka ta
cin abinci, idan ta yi faɗawa Uwani ba ta ba ta shawarar komai sai ta cire ciki, wanda ita kuma
ba ta so, don haka ma ta daina faɗa mata komai, jira take kawai ta haihu ya sake ta ta ƙara
gaba.

Cikin yana wata biyar wataran ya shigo mata da balangu da lemo, ta manta rabon da ya siyo
mata nama, ko ƴar kankana da lemon nan ba ya siyo mata, cike da marmari kuwa ta cinye tass,
ta shanye lemon dama jarka ɗaya ne, babu jimawa kuwa ta fara jin ciwon mara, abu kamar

wasa ciwon yana ra ƙaruwa, fitsari ya matseta, tana shiga banɗaki ta ga jini, ga shi ita kaɗai a
gidan, ta nemo wayarta don ta sanar masa ta rasa ta, don ya ɗauka ya fita da ita, a tunaninta ba
za ta nemi wata mafitar ba sai ta zauna har cikin ya zube.

Da ta ga abun ba na wasa ba ne, sai ta saka hijjabinta ta tafi gidan iyayen shi, da yake ba su da
nisa, a jigace ta shiga gidan, tana shiga ta durƙushe a gaban Umman shi dake zaune a tabarma
tare da ƙannen shi, da yake da hasken wutar nefa ta gane ta, ta ɗago ta tana faɗin"Maryam
lafiya?"
Ta ce"Marara ciwo take kuma na ga jini".

Umma ta hau salati ta ce"Tashi mu tafi asibiti wannan ai ba ƙaramar matsala ba ce".

Suna zuwa aka ba ta maganin da aka yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login