Showing 3001 words to 6000 words out of 39853 words
Chapter 2 - MIJI GOMA Book Complete By Sadiya Abdul.pdf
yi wata dariya ya ce"To ballantana ma ban da ra'ayin ƙara aure, ai ba irinki ake yi wa kishiya
ba my Love".
Maryam ta taɓe baki ta ce"Ni dai ba ka ba ni amsar tambayata ba, me yasa ka kulle? Ko
turakarka ce ai dai ka buɗe ko labule na saka maka".
Ya ce"'A'a ma wallahi ba turaka ba ce, ki yi haƙuri ban faɗa miki ba, dama Gwaggo ce za ta
dawo nan da zama, don ma ba a gama ginin da wuri ba, da sai ta riga mu tarewa, yanzu kuma
da ta ga abun ya zo dab sai ta ce idan an gama bikin kin tare sai ta dawo".
Wani abu ya daki zuciyar Maryam, wai ita yake nufi ta zauna gida ɗaya da uwar miji, tun tana
amarya? Ta ce"Wai kana nufin da Gwaggo za mu zauna? To inda take a da me ya same shi?"
Ya ce"Ai kin san dama gidan haya ne, ina da burin gina mata gida, to da na ci rabin ginin nan na
ce mata nata ne, sai ta ce sam ita dai na yi aurena na tare idan ya so sai na ba ta ɗaki ɗaya ta
zauna, gobe za ta dawo in sha Allah".
Kamar wacce aka fizgi zancen daga bakinta ta ce"Kuma tun gobe?"
Ya ji tambayar ba ta yi masa daɗi ba, da alama dai Maryam ba ta maraba da mahaifiyarsa, ya
ce"To ai dayake ita kaɗai ce dama a gidan, sai wata jikarta ƴar yayana ita kuma yarinya ce, kin
ga tare muke kwana a gidan, yanzu kuma ba na nan, akwai dai ƙanwata wacce take
makarantar kwana, kin ga yanzu sai ita kaɗai, ba na son barinta ita kaɗai a gidan, shiyasa na ce
gobe sai ta taho".
Maryam ta jinjina kai ta ce"To Allah Ya kaimu".
Ya amsa da"Amin my Love, ki yi alwala, ni ma bari na yi".
Ta ce"A'a ni na yi sallar isha'i yanzun nan".
Ya ce"To ai ta godiya ga Allah za mu yi".
Ta ce"Ka bari dai gobe ma yi".
Ya ce"Da dai kin daure mun yi yau ɗin, don ina cike da ɗokin kasancewa da amaryata, kin ga ya
kamata mu fara gabatar da sallar tun da sunna ce".
Maryam ta kyaɓe fuska kamar mai ƙyamar wani abu ta ce"Wallahi kar ma ka saka rai, don yau a
gajiye nake, sai dai mu bar wa gobe".
Ransa bai so ba, amma ba ya son takura mata, don haka ya ce"Yau da gobe ai duk ɗaya, ni
bari na yi nafila".
Ya ɗauki buta ya shiga banɗaki, ita kuma ta koma ɗaki da sauri, ta ɗauki wayarta ta kira
babarsu, ta ɗaga tana cewa"Maryam lafiya kuwa da daren nan?"
Maryam ta ce"Babarmu kin ji wata sabuwa? Wai ashe wannan ɗaki da ya kulle na babar shi ne
a nan gidan za ta dawo ta zauna".
Uwani ta dafe ƙirji ta ce"Na shiga uku! Me kika ce Maryam? Hauka ake yi? To wallahi ba ki
samu gidan zama ba, kada ma ki miƙe ƙafa!".
Ƴarta Mardiyya da take kwance tana shirin yin bacci ta ce"Haba babarmu! Yanzu Maryam ɗin
da aka kai yau kowa yana murnar ta yi aure kike cewa ba ta samu gidan zama ba? Me ta ce
miki?"
Uwani ta ce"Maryam ki kwanta kin ji, gobe za mu yi waya, akwai ƴan sa ido a ɗakin" Ta kashe
wayar tana tsuke fuska.
Mardiyya ta tashi zaune tana cewa"Wai me ta kira ta ce miki?"
Uwani ta ce"Mardiyya ba na son shiga shara ba shanu, ina ruwanki ne?"
Mardiyya ta ce"Gaskiya da ruwana! Ya za a yi a ce awanni da kai ta ɗaki har ta fara kiranki tana
kawo miki ƙorafi? Ke kuma ai bai kamata tun yanzu ki ce mata ba ta samu gidan zama ba, ki
duba ki ga fa duk mun yi aure sai ita kaɗai a gidan nan, ana ta murna ita ma ta yi kuma sai ki ƙi
ƙarfafarta ta zauna? Me yafu ma wai?"
Uwani ta ce"Mardiyya me kike nufi ne? Na fa fi ku damuwar ganin Maryam ta yi aure ta zauna,
gani na yi kamar ba ta yi dace na, wai ashe wannan ɗakin da kuka ce ya ce ban da shi a jere
babar shi ce za ta dawo ta zauna".
Mardiyya ta ce"To sai me? Ita Naziyya da take zaune da uwar mijinta a gida ɗaya mene ne ya
same ta?"
Ta ce"Babu komai, amma ita ai kin ga kowa da ɓangaren shi, ita kuwa Maryam ga ɗaki ga ɗaki
fa suke, suna shaƙar numfashin juna, a kan idonta fa za su shiga wanka su fito, ko leda ya
shigo da ita idonta a kai, to kuwa ina za su more amarci?"
Mardiyya ta yi ƴar dariya ta ce"Ta ina za su shaƙi numfashin juna kamar a ɗaki ɗaya za su
kwana?"
Uwani ta ce"Ke dalla can rufe min baki, ku da ba ku san komai ba".
Mardiyya ta koma ta kwanta tana cewa"Allah Ya kyauta".
A ɓangaren Maryam amarya haka suka kwana tana tunanin irin zaman da za su yi da
mahaifiyarsa, da yake babu nisa tsakanin gidansu da gidan su Nazifi ta san mahaifiyar tashi, sai
dai taƙaimaimai ba za ta ce ga halinta ba, tun da su kaɗai ne a gidansu ballantana wani ya ga
wani halin nata mara kyau, ita dai ta saka a ranta babu ruwanta da babar shi tun da ba a kanta
za ta zauna ba, kowa ya yi ta kansa, sai dai fa ba za ta ɗauki raini ba, duk abin da ta ga an yi
mata ba daidai ba ba za ta yi shiru ba, don gidan aurenta ne tana da cikakken ƴancinta,
Gwaggo ta ja girmanta ita ma ta ja ƙanƙantarta. Haka shi ma Nazifi ya kwana da tunanin Allah
Ya ba su zaman lafiya da mafimtar juna a zaman su da Gwaggo, yana son Gawaggo yana son
Maryam don haka dole zai yi wa kowa adalci don ganin sun zauna lafiya.
Washegari da safe suna cikin karyawa sai ga kiran Gwaggo, ya ɗaga suka gaisa ta ce"Nazifi ka
manta da mu ka tafi aiki ne?"
Ya ce"A'a ina gida yanzu dai zan fito".
Ta ce"Ikon Allah! Yanzu ƙarfe tara kana gida Nazifi? Daga yin auren jiya za ka watsar da aikinka
kenan? To ni dai na shirya ina jiranka".
Ya ce"To ga ni nan zuwa".
Maryam tana jiyo sautin muryar gwaggo da tattaunawarsu, ta jinjina kai kawai tana ayyana lallai
wannan tsohuwar a tsaye take, to ai kuwa muddin tare za su zauna dole sai ta zaunar da ita,
zaman dirshan ma kuwa.
Bayan ya fita ta wanke kofunan da suka ɓata, ta share gidan ta koma ɗaki ta kwanta, sai ga
sallamar Nazifi tare da Gwaggo tana cewa"Gafaranku dai!".
Maryam ta tashi zaune tana taɓe baki, tana ji suna ta shiga da kaya ɗakin nata, ba ta fito ba sai
da ta ji an buɗe mata kitchen, ta fito tana ɗaura ɗankwali da rarraba ido, Gwaggon ce ta buɗe
har ma ta shige, kamar ta bi ta sai dai ta daure ta koma falo ta zauna, Nazifi ya shigo yana
cewa"Maryam ki fito ku gaisa mana".
Ta ce"Ai za mu gaisa ita da ba yau za ta tafi ba, ba gobe ba, gaggawar ta mene ne?"
Ya ce"Hakane".
Ta ce"Na ga an buɗe min kitchen? Me ake nema?"
Ya ce"Tukwanenta da kwanuka ta ajiye".
Ta ce"Ok".
Ya daɗe da fita sannan ta fito ta shiga ɗakin Gwaggon, ta yi sallama Gwaggo ta amsa tana yi
mata kallon tsaf, Gwaggon irin uwayen nan ce masu kishin ɗansu haka siddan, kuma haka
kawai ta ji Maryam ba ta yi mata ba, saboda rawar jikin da Nazifi yake yi a kanta, Maryam ta
gaisheta, ta amsa babu yabo babu fallasa, ga jikar tata a kusa da ita, wacce take ta kallon
Maryam ɗin ba tare da ta gaishe ta ba, yarinyar za ta kai shekata tara, a ganinta ai ta san gaida
manya, ta tashi za ta bar ɗakin Gawaggo ta ce"To mu fa ba mu karya ba muka taho".
Maryam a zuciyarta ta ce'To zumuɗin uban me kuke yi?' A fili kuma ta ce"To" A daƙile ta tashi ta
fita tana tura baki gaba, saboda ita fa gani take takura ne zaman uwar shi a gidanta, shayi ta
dafa dama biredi biyu ya shigo da shi jiya, ta kai mata ta ajiye ta fice, ta same shi yana shirin
fita, ya ce"Zan fita, zan aiko da cefane, sai ki dafa da ɗan dama tun da ga Gwaggo kuma na san
za a yi baƙi ma ko?"
Ba ta ce komai ba, har ya gama shirinsa ta ce"A dawo lafiya".
Yana fita ta ɗauki waya ta kira babarsu, sun gisa ta ce"Ya kuka kwana?"
Maryam ta ce"Lafiya ƙalau, amma fa kin ga tsohuwar nan har ta dawo, ta jera kayanta, wai
abun takaici har kitchen ma haɗawa za mu yi, haka ta kwaso jiki don sauri ko karyawa ba ta
tsaya ta yi ba".
Uwani ta rafka salati da sallallami kamar wacce ta ji mutuwa ko tashin hankali ta ce"Har ta dawo
gidan, kenan amarcin ma a gabanta za ku ci!? Maryam wannan wane irin gidan aure kika faɗa,
anya ba za ki yi bore ba kuwa?"
Maryam ta ce"Bari dai na ga yadda zaman zai kasance, idan na ga ba zan iya ba wallahi sai dai
na bar mata gidan, yanzu ma har yana cewa ba yi girki da yawa, ga baiwa an kawo musu".
Uwani ta ce"To ai shikenan, idan dai kin ga da matsala kar ki yi shuru ki cuci kanki, aure irin
wannan da aka fara shi da matsala babu inda yake zuwa, idan kuwa kin ga ya yi nisan zango to
tabbas durƙushe matar aka yi, irin matan da suke ɗaukar miji kamar rayuwarsu, ke kuwa daraja
da ƙimarki ta fi gaban nan wallahi, ƴata wanke hannu ka taɓa ce ta wuce zaman haƙuri a gidan
miji wallahi".
Maryam ta ji daɗin maganganun babarta mai sonta, tana murmushi ta ce"Zan dai ga
take-takensu tukunna".
Uwani ta ce"Yawwa, kuma kin san su iyayen miji idan kika nuna musu ke mai haƙuri ce da
biyayya to fa tamkar kin ce musu ke bola ce a zuba miki kowace ƙazanta, wallahi ke ce ƴar iska
a idonsu, don haka idan ta yi miki kallon yamma ki yi mata na arewa, wannan cewata ce".
Maryam ta naɗe huɗuba tass a kanta, suka yi sallama, ta ɗakko kazarta ta jiya da ba ta ci ba ta
fara ci. Wajen sha ɗaya babarsu ta aiko mata da sauran kayanta, da kuma kula fal da jar miya
wacce ta ji nama, shi ma Nazifi ya aiko cefane, sai ta soya naman da ya kawo ta ajiye ta dafa
taliya ta ɗauki wata kula cikin tarkacen kayan Gwaggon da ta ajiye a kitchen ɗin ta zuba mata,
ta yi sallama ta kai mata, tana ajiyewa Gwaggo ta buɗe ta ce"Kuma kya zuba miyar a kai?"
Maryam ba ta ce komai ba ta fice daga ɗakin, har zuciyarta take jin haushin matar kuma daidai
take da zamaninta, dayake tana ta yin baƙi taliya leda uku da ta dafa ta ƙare, dab da magriba ta
dafa macaroni leda ɗaya, ta raba gida biyu ta zuba mata rabi ta bar wa Nazifi rabi, don ita ba ta
jin yunwar ma, da ta kaiwa Gwaggo ta buɗe ta gani, sai ta tura kular gefe.
Ana idar da sallar isha'i Nazifi ya dawo gidan, da ledojinsa biyu, ya siyo musu balangu da biredi
ne, ya fara shiga ɗakin mahaifiyarsa da sallama, ta amsa tana yi masa sannu, ya ce"Yawwa
sannu Gwaggo, ga wannan".
Ya miƙa mata biredin da balangu, ta buɗe ta ce"Allah Ya amfana, dama ban ci komai ba".
Da mamaki ya ce"Ba ki ci abinci ba Gwaggo?"
Ta taɓe baki ta ce"To ka san ni ba cin kayan basir ɗin nan nake yi ba, da rana ta dafa taliya, da
daddare ta dafa macaroni, ni gaskiya ba zan iya wannan rayuwar ba, gara ma tun wuri ka auno
garin tuwo, idan ba za ta ci ba ni ta dinga dafa mini, na fi gane na ci tuwona idan zan kwanta, da
safe na ci ɗumame".
Jikinsa ya ɗan yi sanyi, ya ce"To babu damuwa in sha Allah gobe zan siyo, amma dai yau ɗin ki
daure ki ci macaronin".
Ta ce"To bari na gani".
Ya fita ya shiga ɗakin Maryam, tana kwance tana kallon hotunan biki a wayarta, ya sakar mata
murmushi ya zauna a kusa da ita cike da shauƙin sonta, yau dai ta karɓe shi sun sha
amarcinsu, sanda suka fito suna alwala ma sai da Gawaggo ta leƙo ta ce masa"Alwalar me
kuke yi? Me kake yi a waje ba ka yi sallar isha'i ba?"
Cike da kunya ya ce"Na yi sallah Gwaggo kawai dai zan kwanta da alwala ne".
Ta taɓe baki ta koma ɗaki, haka da komai ya wakana ya ji kunyar fita yin wanka, sai ya bari sai
tsakar dare sosai sannan ya fita ya yi, kuma ya yi taka-tsan-tsan sosai wajen zubar da ruwa ta
yadda ba sosai za a jiyo ƙara ba, bai saka a ransa Gwaggo za ta saka musu ido ba, kawai dai
shi ne yake jin kunya.
Ita kuwa Maryam da asuba ta yi nata wankan, lokacin ya tafi masallaci, Gwaggo da ta makara
yau ta fito don shiga banɗaki ta ji ƙarar ruwa ana yin wanka, ta ce"Waye a ciki? Waye yake
wanka da asubar fari?"
Wani ƙululun baƙinciki ya tsayawa Maryam a wuya, sai da ma ta ɓata lokaci sosai sannan ta fito
tana haɗe rai. Gwaggo ta ce"Ashe ke ce".
Ba ta kula ta ba, ta shige ɗaki.
Da sassafe ta ji motsin an buɗe kitchen, don tun asubar ba ta koma bacci ba, tana dai kwance
tana jira gari ya waye ta fita, ta fara tunanin me tsohuwar nan za ta yi a kitchen? Jin shiru ba a
rufe ƙofar ba ya tabbatar mata har yanzu ana cikin kitchen ɗin, ta tashi ta fito ranta yana ɓaci,
daidai sanda Gwaggo ma ta fito daga ɗakinta, tana cewa"Haka kawai kun ƙule a ɗaki kun bar
mutane da yunwa? Yasmin!" Ta doshi kitchen ɗin tana ƙwalawa jikarta kira.
Ko kallon arziƙi ba ta yi wa Maryam ɗin ba, ita ma kuwa ta bi su kitchen ɗin, zaune ta samu
Yasmin ɗin a kan turmi ta saka kwanon naman da Maryam ta soya jiya da rana a gaba tana ta ci
har ta kusa cinyewa, ranta ya ɓaci don dama ita ba ta cikin jerin mutane masu haƙuri, ta
ce"Kutt! Ke uban wane ya ce ki shigo mini kitchen har ma ki ɗauki abu ki ci?"
Gwaggo ta ce"Ke dakata! Kar ki zagar mini ita, don ta ci naman da ba da kuɗinki aka siya ba?"
Nazifi da y ƙaraso kitchen ɗin yanzu ya ce"Me yake faruwa ne?"
Takaici ya hana Maryam cewa komai, saboda ba ta son nunawa babar shi halinta tun yanzu, sai
kawai ta jinjina kai ta fice daga kitchen ɗin.
08028966015
[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_
*SADIYA ABDULRAZAƘ*
*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne
hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman
aure?*
Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu
*FIRST CLASS WRITERS*
PAGE 3
Ɗakinta ta shiga ta riƙe ƙugu tana huci kamar mai jiran dambe. Nazifi jiki a mace ya
ce"Gwaggo ya kamata ki nunawa Yasmin kuskurenta fa, wannan ai ba ɗabi'a ba ce mai kyau ta
dinga ɗaukar abin da ba a bata ba".
Gwaggo ta ce"Au! Nazifi kenan dai ka goyi bayan matarka ko? Yanzu ƙarfe nawa? Ƙarfe bakwai
da rabi kun ƙule a ɗaki kuna ta bacci ba ta fito ta sallame mu ba? Saboda na dawo gidanka da
zama sai karatun yarinya ya ɓalɓalce? Ai shikenan". Ta faɗa tana rausayar da kai kamar abar
tausayi.
Sannan ta ja hannun Yasmin tana cewa"Mu je ki shirya sai na ba ki kuɗi ki sayi koko a hanya".
Nazifi ya shiga ɗaki ya samu Maryam kamar za ta fashe, ya ce"Maryam yarinyar nan ba ta yi
daidai ba, amma ke ma bai kamata ki yi magana ba, da sai ki faɗa min na tsawatar mata, kin
san tana zuwa makaranta to don kar ta yi latti ne ya sa ta nemi abin da za ta ci".
Ta ce"Ka ga dakata Nazifi! Ta ya zan san tana zuwa makaranta alhalin a sharuɗan auren ba ka
sanar da ni har da kula da wasu ba?"
Ya ce"Gwaggon ce wasu?"
Ta ce"Duk yadda ka ɗauka!".
Ya jinjina kai ya ce"To ki yi haƙuri ki je ko shayi ne ki dafa musu tun da akwai biredi, amma daga
yau sai ki dinga tashi da wuri, tun da ita Gwaggo ta fi son karyawa da abinci ko kunu da ƙosai,
shi ma sai idan babu ɗumamen tuwo, na manta na faɗa miki anjima zan auno gari, ita ta fi son
tuwo".
Maryam ta ƙanƙance ido ta ce"Ni Nazifi na tambaye ka mana".
Ya ce"Ina ji".
Ta ce"Ku nawa aka aurawa ni? Kuma sannan zaman wa nake yi?"
Ya ce"Maryam! Kina nufin mahaifiyata ba ta da matsayin da za