Showing 33001 words to 36000 words out of 39853 words

Chapter 12 - MIJI GOMA Book Complete By Sadiya Abdul.pdf

25 May 2025

7748

wacce ba sai an faɗa ba ta san matarsa ce, sai da gabanta ya faɗi, ta daure ta
ce"Sannunku da zuwa".

Alhaji kuwa ya bi ta da kallon burgewa, wankan ya burge shi, don Sauda babu ruwanta da wani
wankan dare ballantana kuma kayan bacci, dogayen riguna ne marasa nauyi kayan baccinta
tun da ta fara haihuwa, ya haɗiyi wani yawu muƙut wanda har Sauda ta ji sautin, zuciyarta ta
ƙara kumbura, ta kasa shigewa kawai tana tsaye tana ƙarewa Maryam kallo, sai Alhaji ne ya
katse shirun nasu da cewar"Na barki ke kaɗai a gida".

Sauda ta yi masa mugun kallo ta ce"E tabbas ita kaɗai, tun da a yanzu ita kaɗai kake kallo a
mutum, su ƴaƴan naka ba mutane ba ne, komai ma ya same su ta matarka kake yi! Hmm!" Ta
wuce fuuu ta yi cikin gidan.

Ya yi murmushin yaƙe ya ce wa Maryam"Kin ga Sauda ta dawo ko? Don Allah ku zauna lafiya,
kin ga ma tun da ta dawo kan yaranta za ki fi kula da ni sosai ko?"

Ta yi farr da ido ta ce"Ƙwarai kuwa, zo ma mu je ka gani".

Ta yi ɗakinta, shi kuwa ya bi bayanta kamar raƙumi da akala, a gaban Sauda suka shige ɗakin
nata, wacce ta fito daha ɗakin yaranta za ta shiga nata, ta manta rabon da ya shiga ɗakinta, sai
dai ita ta bi shi nashi ɗakin idan ya kira ta, amma shi ne ya zo ya shige ɗakin amarya ko kunya
ba ya ji, ta yi ƙwafa tana cewa"Lallai akwai aiki a gabana, tsohuwar kilaki ya kwaso".
Ta gagara zama a ɗaki, ko wanka ta kasa yi, sai leƙe take yi tana jiran fitowarsa amma shiru har
ƙarfe sha ɗaya ta yi, ga shi ko sallar isha'i ba ta yi ba, kuma ta kasa yi, saboda tana son
tabbatarwa da gaske a nan zai kwana? Shi kuwa Alhaji yana can Maryam ta saka shi a kwana

ta kalallame shi, ta kanainaye shi har ya manta ma a ɗakinta yake.

Ƙashe dai sai sha biyu Sauda ta haƙura da leƙen ta yi sallah, ta kwanta, sai ta gagara yin bacci
gabaɗaya ya ƙaurace mata, ta fara tunanin yanzu fa yana can tare da ita, lallai namiji ba shi da
kunya, can dai ta fara tunanin ya za ta yi ta hana su sukuni, ta tashi ta fito a hankali ta shiga
ɗakin yaranta, ta haska su, sai baccinsu suke yi hankali kwance, ta shiga tashinsu bisa
shawarar zuciyarta, ta dinga jijjiga su duk suka tashi suna murza ido, ta sakawa fuskarta
alamun firgici ta ce"Ku tashi don ubanku, aljanu ne suka shigo gidan! Suna ɗakin nan a
ƙarƙashin katifarku!".

Ai kuwa a tare suka fara ihu, ta ce"Ku kwanta ba za su yi muku komai ba".

Suka fara kuka suna rirriƙe ta suna cewa a ɗakinta za su kwana.

Ta fizge tana cewa"Suna can a ɗakina sun cika ɗakin kowa ya yi ta kansa".

Ta fice a guje suka mara mata baya, amma kafin su shiga ta banke ƙofarta ta saka sakata,
gabaɗaya suka ruɗe suka dinga ihu a mugun firgice kamar za su shiɗe.

A tare Maryam da Alhaji suka fito a ruɗe, suka tarar yaran suna ta buga ƙofar ɗakin babarsu,
fitowarsu ya sa suka yi wajensu suna shigewa jikinsu cikin matsanancin kuka, Alhaji ya ruɗe ya
fara tambayarsu me ya faru?

Suka ce"Aljanu, Abba aljanu a ɗakinmu".

Gabansa ya faɗi ya ce"Aljanu kuma? Me kuka gani?"

Inaa sun ruɗe, sai a lokacin Sauda ta fito tana cewa"Mene ne?"

Suka yi kanta suna kuka.

Alhaji ya ce"Kin ji wai aljanu".

Ta ce"Aljanu kuma?"

Ya wuce ɗakin a tsorace yana addu'a, ya haska bai ga komai ba, ya dawo a sanyaye ya
ce"Abun ya bani mamaki wallahi".

Sauda ta ce"To kar dai fa ture aka fara yi musu".

Ya ce"Wane irin ture? Waye zai yiwa yaran nan ture?"

Ta ce"Wanda suka tsonewa ido mana, an ga yara sun cika gida tubarkalla ana son haukata su

don kar ƴaƴana su moru".

Alhaji ya ce"Subhanallah! Kar na sake jin magana irin haka!".

Ya janyo yaran yana cewa"Tsorata kawai kuka yi babu komai a ɗakinku kun ji? Ku je ku kwanta
zan yi muku addu'a".

Sauda ta ce"Au da gaske sai ka kora su, saboda kar kwanan ɗakin amarya ya wuce ka? Hmm
dama uwa ce ba ta gudun ƴaƴanta duk runtsi, ku shigo nan!".

Ya ce"Ba za su shiga ba! A ɗakin nasu nake so su kwana ina son fahimtar wani abu ba ne kafin
Allah Ya kaimu gobe na kira malamai a yi addu'a".

Maryam ta ce"Allah Ya rufa asiri". Ta koma ɗakinta, ita ma duk sai tsoron gidan ya kama ta.

Ya saka su a gaba suna turjewa suka shiga, ya zauna ya kunna karatun qur'ani a wayarsa,
yana addu'a yana tofa musu, amma da bacci ya fara ɗaukarsu sai su zabura su farka suna
maƙale shi, a haka suka kwana, ita kuwa Sauda ta yi baccinta ranta fess, tun da dai ta haramta
musu wannan daren to ita fa buri ya cika, kuma ta saka a ranta yanzu aka fara wasan, ta ɗau
alƙawarin sai ta fitini gidan gabaɗaya, sai kwana a ɗakin shi ya gagari Maryam, kafin ta tankaɗa
ƙeyarta waje.



LAST FREE PAGES! A NAN ZAN TSAYA DA FREE PAGE, DAGA WANNAN SHAFIN DUK
WANDA KUKA GANI A PAID PAGE NE, ƳAN'UWA KU BIYA KU KARANTA CIKIN AMINCI,
YANZU ZA A FARA WASAN NAN, TAFIYA TA KISHI MAI CIKE DA ƘULLA-ƘULLA TURA ƊARI
BIYAR ƊINKI TA NAN KI SHA KARATU CIKIN AMINCI.
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay


08028966015
[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_



*SADIYA ABDULRAZAƘ*


*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne

hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman
aure?*

Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu

*FIRST CLASS WRITERS*

https://chat.whatsapp.com/G08KLEmlF3gJ3X4npkfIee

PAGE 13


Alhaji Haruna har zuciyarsa ya yi niyyar kamanta adalci, saboda haka duk da Sauda tana
gidansu da ya tashi siyan kazar amarci haka ya siya da nata kashin, dama a baya kashi biyi
yake siya da nata da na Innarsa, yau kuwa sai ya sayi kashi uku, ya tafi gidan don ya yiwa Inna
sallama kamar yadda ya saba a kowane dare, lokacin tara saura kwata, ya same su a falo, ya
ƙarasa a sanyaye ya zauna yana gaishe da Inna, ta amsa fuska babu walwala, ga yaran can
rakuɓe a gefe, sun nuna kamar ba su san shi ba, saɓanin da, da idan ya shigo gida a guje suke
rige-rigen zuwa gare shi, yaran su huɗu ne, Momy ita ce babba shekararta goma sha ɗaya, sai
mai bi mata Kausar, shekararta takwas, sai Ummi shekararta shida, sannan Nana mai shekara
huɗu, daga kan Nana ya ce mata ya kamata ta ɗan yi planing don mahaifarta ta huta, ta biye
masa ta saka inplan na shekara uku da ya yi expire ta cire ta sake saka wani, don haka yanzu
take ganin dama shi burinsa ta tsaya da haihuwar saboda amaryarsa ta zo ta zazzago masa
ƴaƴa, kallo ɗaya ta yi masa ta kau da kai gefe, saboda mugun haushin shi da take ji, ya ce da
babbar ƴar"Momy ko gaisuwa babu?"

Sai ta waiwaya ta kalli mahaifiyarsu, saboda tun da suka yi yajin nan kullum sai ta zaunar da su
ta faɗa musu babansu yanzu ya daina son su dukansu, shiyasa zai ƙara aure, kuma shi ya kore
su dukansu, sannan amaryar da zai aura muguwa ce, kashe ta za ta yi ta zama ita ce uwarsu,
kuma dukansu za ta dinga yi, tana hana su abinci, shi kuma baban nasu ba zai yi komai ba,
saboda ya daina son su, haka dai ta tsara musu abubuwa kala-kala daidai da tunaninsu, su
kuwa hakan ya sanya musu damuwa da jin tsoron baban nasu.

Sai da ya yi magana sannan suka fara gaishe shi ɗaya bayan ɗaya, ya amsa yana ce musu"Ya
makaranta?"

Sauda ta yi wani huci kamar zakanya ta tashi buguzun-buguzun ta bar falon, kasancewarta

mace mai ƙiba kuma doguwa, ya bi ta da kallo, sai ya ajiyewa Inna ledarta ya bi bayan Sauda
ɗin, zaune ya tarar da ita ta naɗe hannu a ƙirji, ya yi sallama tana kallon shi yana kallonta ta ƙi
amsawa, ya zo ya zauna a gefen katifar da take, sai ta miƙe za ta fita, ya ce"Kin ga Sauda
zauna mu yi magana".
Ba ta zauna ba, amma ta fasa fitar,shi ma sai ya tashi tsayen ya ce"Ni fa ban ƙara aure saboda
kin gaza mini ba, sai don ina da ra'ayin yin hakan, kuma dama can mata biyu ne a ƙaddarar
aurena, idan mai afkuwa ta afkuwa ya kamata ki ajiye komai a gefe, ki koma ɗakinki, ni sai nake
ganin ba girmanki ba ne a ce yarinyar nan ta zo ta tarar kin yi yaji, kamar hakan zai janyo miki
raini".

Ta yi shiru dai ba ta ce komai ba.

Ya ci gaba da faɗin"Maryam ƙanwarki ce, kuma tana da sauƙin kai, za ku zauna lafiya in sha
Allah, ni dai yanzu ki wuce mu tafi gida kawai, wannan abin da kika yi sai ki jawo mini zagi a
gari, nan kuwa ba ni na kore ki ba".

Ta ce"Babu inda zan je, ka je ka zauna da wacce ka zaɓa, kuma sannan zan aiko maka da
yaranka, tun da ita ka zaɓa kake ganin za ta iya sai ta riƙe maka!".

Ya ce"To shikenan, ni dai ba zan yi miki dole ba, musamman ma da Inna ta goya miki baya,
saboda haka ki yi duk yadda kika tsara, amma ki sani ni dai ba zan sake ki ba".

Ta ja dogon tsaki.

Ya ce"Akwai abin da kuke buƙata?"

Sai a nan ta ce"Ba na buƙatar komai daga gareka, kai kanka bana buƙatarka ballantana abun
hannunka, ita da kake baƙo a wajenta ka je can ka yi mata komai!".

Ya yi ɗan murmushi ya ce"Sauda kina da kishi, amma ban taɓa zaton za ki bar gidanki saboda
kishiya ba, wai har kina barazanar za ki ba ni ƴaƴana, to ki ba ni, zan riƙe su".

Ya ajiye mata ledar hannunsa, ya ciro kuɗi a aljihunsa ya ajiye mata ya fice, bai tarar da kowa a
falon ba, sai ledar da ya ajiyewa Inna, cike da dumuwa ya bar gidan. Amma ko da ya je gida ya
tarar da amaryarsa sai ransa ya yi fess, yana son Maryam sosai, suka sha amarcinsu hankali
kwance har ta mantar da shi yana cikin damuwa.
Washegari ya tafi kasuwarsa, ita kuma ta gyara gidan, tana ta baƙi jefi-jefi da maƙota da
ƴan'uwa, maƙotan dai duka ƙawayen Sauda ne, don haka gulma ce kawai take kawo su,
kowacce idan ta shiga ta ganowa idonta sai ta kira Sauda ta yi mata sharhi, wanda hakan bai
ƙara mata komai ba, sai baƙinciki da tsanar Maryam ɗin, ita kuwa Maryam dama ta yi tunanin za
a yi hakan, don haka babu wata mace da ta sakarwa fuska, kadaran-kadahan take karɓarsu.

Wajen ƙarfe biyu ta gama girki tana sallah ta ji ana buga gidan, an daɗe ana bugun saboda
tana tayar da sallar aka fara, da ta idar ta taho da sauri ta buɗe, sai ta ga yara ne su huɗu da
unifom a jikinsu, jikinta ya ba ta ƴaƴan mijinta ne, sai mai adaidaita sahun da ya ajiye su ya
ƙaraso da waya a kunnensa yana cewa"Ai ga shi ma ta buɗe".
Don kuwa da ya ga yaran suna ta bugawa ba a buɗe ba, sai ya kira Sauda ya faɗa mata, ta
kuwa harzuƙa ta miƙe tsaye tana zage-zage da cewar gidan ubanta ne da za ta hana su shiga?

Ya miƙawa Maryam babbar jakar dake hannun shi yana cewa"Ga shi mamansu ce ta ce na
kawo su".

Maryam ta karɓa ta ce"To ka gaishe ta".

Ta kalli yaran ta ce"Ku shiga, sannunku da zuwa".

Babu wanda ya amsa, ballantana su gaishe ta, wannan huɗubar mahaifiyarsu ce, suka shige
ɗakin kwanansu, Maryam ta biyo su da jakar kayansu ta ajiye tana cewa"Ku cire unifom, sai na
yi muku wanka ku canza kaya ko?"

Momy da take babbar ta ce"A'a, mun yi wanka da safe".

Ta ce"To ku canza kaya ku fito ku ci abinci".

Suka fara kiciniyar cire kayan, ban da Momy da ta ja ta tsaya tana ta ɓata rai, sai da Maryam ta
fita sanan ta fito da duka kayan cikin jakar, sai ga waya keypad ta bayyana, ta ɗauka ta shige
banɗaki, ta danna ta kira babarsu a waya, Sauda tana ganin kiran ta miƙe ta shige ɗaki, don ko
Inna ba ta san da wannan shirin nata ba, tana ɗagawa ta ce"Momy yaya aka yi?"
Momy ta ce"Ta ce mu yi wanka na ce mata mun yi, shi ne ta ce mu fito mu ci abinci".

Sauda ta ce"To ko me ta dafa ku ce ba kwa ci, kowa ya zaɓi abin da yake so ya ci, kin ji ko?"

Ta ce"To, amma wallahi Nana ce uwar kwaɗayi, na san ci za ta yi".

Ta ce"Ki gargaɗe ta, ki ce idan ta ci za ta mutu, ta ce doya take so ta ci, ku kuma ku zaɓi wani
abun kowa na shi da ban".

Ta ce"To"

Ta ce"Ki ɓoye wayar nan fa sosai, ki saka a ƙarƙashin katifarku, kuma kar ki fita ko falo da ita".

Ta kashe wayar ta fito ta faki idon ƙannen nata ta ɓoye, sannan ta ba su kayan da za su saka,

ta zaunar da su ta ce"To Umma ta ce ko me ta dafa kowa ya ce ba ya ci, ke Nana ki ce doya da
ƙwai za ki ci, ke Kausar ki ce shinkafa da wake, ke ke kuma Ummi ki ce shinkafa jollop, idan
kuma shinkafar ta dafa sai ki ce macaroni, wallahi Umma ta ce duk wacce ba ta ce haka ba sai
ta ci ubanta".
Duk suka gyaɗa kai, sannan suka fito a tare, Maryam tana falo tana chart, ta ce"Kun fito?".

Ba su ce komai ba, ta tashi ta shiga kitchen ta juye musu taliyar da ta dafa da miya, leda ɗaya
ce dama ta dafa ko ci ba ta yi ba, plate biyu ta yo ta kawo ta ajiye a gabansu tana cewa"Ku yi
maza ku ci".

Daidai lokacin kiran Uwani ya shigo wayarta, ta ɗaga tana gaishe ta, Uwani ta ce"Oh! Maryam
har na fara kewa, ya kike ya gidan?"

Ta yi ƴar dariya ta ce"Lafiya ƙalau".

Ta ce"Babu wata matsala dai ko? Kin san zama da kishiya".

Da a da ne sai ta faɗa mata ga shi har yaran shi sun zo, amma yanzu kuwa ta ce mata babu
komai, kuma ba ta ma faɗa mata uwar gidan ta yi yaji ba, ko da ƴan kai amarya suka zo ma duk
a zatonsu ɗaki ta shiga ta kulle saboda kishi.

Suna gama wayar ta juyo ta ga yaran ba su da niyyar sakkowa su ci abincin, ta ce"A'a! Ya ba ku
fara ci ba? Ko sunayenku ba ku faɗa mini ba ma, ku gama ci ku zo mu yi fira ko?"

Momy ta ce"Mu ba ma cin abinci a ƙasa sai a dining, kuma ba ma son taliya".

Ta ce"Ba kwa son taliya? Kwata-kwata ba kwa ci a gidan?"

Ta ce"E".

Maryam ta ce"To me za ku ci?"

Momy ta ce"Ni tuwo nake so".

Ummi ta ce"Ni kuma jollop ɗin shinkafa".

Nana ta ce"Ni doya da ƙwai".

Kausar ta ce"Ni shinkafa da wake, da mai da yaji da salak da tumatur da albasa, da cocomba".
Ta ƙarasa da karsashi, don dama Momy kowa abin da ta san ya fi so ta ce ya faɗa.

Maryam ta tsaya kallon su da mamaki, ba sai ta wahalar da kanta da tunani ba, saboda ba zai

taɓa yiwuwa ta biyewa yara ta yi girki kashi-kashi ba kamar wata ƴar aiki, girki kala huɗu?
Sannan wannan ai ba tarbiyya ba ce yara su dinga zaɓar abincin da za su ci, don haka ta
ce"Duk na ji, amma fa sai dai ku zaɓi abu guda ɗaya dukanku, saboda kun ga idan na yi girki
har kala huɗu na yi almubazzaranci, don haka ku tsayar da abu ɗaya".
Duk sai suka kalli Momy tun da ita ce shugabar tawaga, ta ce"To ai mu ba ma cin taliya".

Ta ce"Na ni ba za ku ci taliya ba, ku zaɓi kala ɗaya sai na dafa muku".

Ta ce"Sai dai a yi mana tuwon shinkafa miyar agushi".

Maryam ta ce"Ni ba ni da agushi, sannan ba zan takurawa babanku ba yana kasuwa, amma
akwai wake, zan yi muku miyar wake".

Da gaske Nana ba ta cin miyar wake, don haka ta taɓe fuska za ta fara kuka ta ce"Ni dai ba zan
ci ba".

Kausar ta ce"Nana ba ta cin miyar wake".

Maryam ta ce"Zan dafa mata indomi".

Ta wuce kitchen ɗin, a ranta tana mamakin yadda aka sangarta yaran, ita idan ƴaƴanta ne
gaskiya ba za ta saki fuskar da za su yi mata haka ba, amma su ma ɗin muddin a wajenta za su
zauna to kuwa tabbas sai ta saita su. Ta ɗora tuwon da yake ta tarar da komai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login