Showing 21001 words to 24000 words out of 39853 words

Chapter 8 - MIJI GOMA Book Complete By Sadiya Abdul.pdf

25 May 2025

7743

nasarar tsayar da jinin, suka ba ta gado, sai a lokacin
Umman ta kira Hamza a waya, ta faɗa masa asibitin da suke, ya ce ga shi nan zuwa, a ransa
yana addu'ar Allah Ya sa cikin ya zube.


08028966015
[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_



*SADIYA ABDULRAZAƘ*


*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne
hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman
aure?*

Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu

*FIRST CLASS WRITERS*

PAGE 9

https://chat.whatsapp.com/G08KLEmlF3gJ3X4npkfIee


Lokacin da ya ƙaraso asibitin Maryam tana kwance luf an saka mata ƙarin ruwa, ya shigo
yana cewa"Umma wai me yake faruwa?"

Ta sake sanar masa a yadda Maryam ta zo, ta ɗora da faɗin"Kai ina ka shiga?"

Ya ce"Yanzu shikenan cikin ya zube?"

Ta ce"A'a Allah Ya taƙaita, amma ga scanning sun rubuta a yi".

Ta miƙa masa takarda, ya karɓa jiki a suluɓe yana jin babu daɗi na rashin cikar burinsa.

Maryam ta ce"Ina wayata?"

Ya ciro daga aljihu yana miƙa mata ya ce"Dama na ga cajin ya yi ƙasa kuma ba su kawo wuta
ba, shi ne na kai miki".

Ta ji sam ba ta yarda ba, ta ce"Amma Hamza wannan lemon da ka ba ni akwai wani abun a ciki
ko?"

Ya kalli Umma da ta kafe shi da ido, ya fara muzurai ya ce"Kamar ya? Ban gane ba".

Ta ce"To ya za a yi a ce daga shan lemo sai ciwo?"

Ta kalli Umma ta ce"Dama fa ba son cikin yake ba, ya ce na zubar na ƙi yarda, kuma ma na
manta rabon da ya shigo min da ɗan wani abun motsa baki, sai yau ɗin ya kawo min balangu
da lemo, kin ga tun da ba son cikin yake ba ai zai iya saka min maganin ma".

Hamza ya fara zabure-zabure ya ce"Wai kamar ya? Me kike nufi ne?"

Umma ta ce"Lallai biri ya yi maka da mutum, za ka aikata Hamza, na sanka dama ba son
haihuwa kake yi ba, amma kuwa idan haka ta tabbata sai dai na ce Allah Ya shirye ka, Ya ganar
da kai gaskiya! Ke kuma Allah Ya saka miki".

Ya ce"Wallahi Umma ban zuba mata komai ba".

Ta ce"Allah Ya san komai".

Sai ya fice ya bar asibitin.

Umma ta je gida ta kwaso ƴan abubuwan buƙata tun da sun ce sai gobe za a sallame ta,
ƙanwar shi ce ta kwana da ita, washegari da safe aka yi scanning aka ce cikinta lafiya ƙalau,
ashe ma ƴan biyu ne, kowa ya cika da farinciki ban da Hamza da ya ƙara sarewa da lamarin,
mai ɗa ɗaya ma ya aka cika ballantana biyu? Ai kwamacala kawai za a yi masa a gida kafin su
girma, ya kasa ɓoye baƙincikinsa har sai da Umma ta gane, ta san halinsa ta san haihuwa ba ta
dame shi ba, ta zaunar da shi ta yi masa nasiha sosai, ya ce shi fa bai ce ba ya son haihuwa
ba, da aka sallame su ƙanwarsa ce ta zauna a gidan har sati biyu, ba ta faɗawa Uwani wannan
abun ya faru ba ma, har ta warware, laulayin ma yanzu ya tafi sai amai da ba ta daina ba har
yanzu, da ta yi masa zancen zuwa awo ma cewa ya yi wannan awon kawai yawo ne, sai da ta
haɗa shi da Umma sannan ya barta ta fara zuwa.

Da daɗi da ba daɗi cikin Maryam ya shiga wata na tara, idan ka ganta kamar ba ita ba, ta
kumbura ta cika fam, hanci ya bubbuɗe, duk ta gaji da cikin, ko fita ba ta son yi sai a filin tsakar
gida take ɗan zagaye tana tattaka ƙafarta, Hamza idan ya kalle ta wani mugun haushinta yake
ji, shi kam inda ya san haka za ta samu ciki da wuri har gara ma bai yi auren ba, babu wani
amarci da ya sha sai na laulayi. Wataran tana zaune a falo ya zo ya zauna ya ce"Maryam ya
kamata ki tafi gida haihuwa ko? Tun da an shiga watan".

Ta yi wani murmushin takaici ta ce"Hamza ba don cikin jikina ba a cikin maza kai ba kowan
kowa ba ne a wajena da har sai ka kore ni zan bar maka gidanka".

Ya ce"Ni kike faɗawa haka?"

Ta ce"Bari dai Allah Ya sauke ni lafiya sai mu tattauna, ni ba wannan ba, ban ga fa wani shiri da
kake yi na haihuwar nan ba, ko riga ɗaya b a siya ba, me kake nufi?"

Ya ce"Kin ga kin haihu ban siya ba?"

Ta ce"Sai na haihun? To cikin kayanka sai ka zaɓo wanda ƴaƴan za su saka na tafi da shi a
sibiti kafin ka siyo musu".

Ya ce"Kin ga ni na riga ma na faɗawa babarki gobe za ki koma gida, kuma zan bada kuɗin
kayan yaran kafin ki haihu".

Bai jira cewarta ba, ya tashi ya fice.

Ta ɗauki waya ta kira Uwani, suka gaisa ta ce"Kin gama shiryawa?"

Maryam ta ce"Shiri na me?"

Uwani ta ce"Ba mijinki ya ce yau za ki dawo gida ba?"

Ta ce"E, yanzu zan tashi na shirya".

Ta ce"To sai kin ƙaraso".

Ta haɗa kayanta a akwati, ta ɗauki waya ta kira Hamza, ya ɗaga ta ce"Na gama shiryawa zan
tafi".

Ya ce"To ki gaida gida, ki biya ta gidan Umma ki ajiye mini mukullin".

Ta ce"Kana nufin ba za ka zo mu yi sallama ba? Kuma haka zan tafi ziƙau-ziƙau ko ɗan kayan
shayi ba za ka siya mini ba? Sannan ma ni ko kuɗin adaidaita sahu ba ni da shi".

Ya ce"To wane kayan shayi kuma sai ka ce wacce za ki tafi daji ba gida ba? Su a gidan naku
ruwa ake sha? Kuma ni ban da ko sisi".

Ta ce"Ka ga Hamza dakata mana! Kar ka sake ka zage ni ballantana iyayena!".

Ya ce"An zage ki ɗin me za ki yi?"

Ta ce"Ramawa zan yi fiye da wanda ka yi mini, don kai mijina ne ba ubana ba!".

Ya yi tsaki ya kashe wayar, ta mayar da akwatinta ɗaki, ta zauna ranta a ɓace tana mamakin
wai ita ce namiji yake yi mata haka, kamar wanda ya asirce ta, ji take har yanzu ba ta son
rabuwa da shi, kuma babu wata hujja da zuciyarta take ba ta sai na cikin nan na jikinta, don
haka ta bari har zuwa ta haihu ɗin ta gani, shin da gaske cikin ne sila ko kuwa Hamza ne ya
samu nasarar canza mata tunani?

Azhar ta yi ta tashi ta ɗora girki, saboda ta yi alƙawarin ba za ta tafi ba sai ya yi mata siyayya
kuma ya ba ta ɗan kuɗi ta riƙe a hannunta, ta gama cin abinci ta yi wanka ta kwanta baccinta,
sai la'asar ta tashi, ta idar da sallah Uwani ta kira ta a waya, ta ce"Ya na ji shiru? Ko sai
yamma?"
Ta ce"Ai na fasa tahowa yau".

Ta ce"To! Sai yaushe?"

Ta ce"Sai yadda ta yiwu".

Ta ce"A kan me?"

Ta ce"To ya ce ko kuɗin babur ba shi da shi, ballantana ya yi min ƴar siyayyar tahowa gidan,
sannan ko tsumma bai siya ba, babu rigar da za a tafi da ita asibiti, sai na zuba masa ido?"

Uwani ta ce"Kayyasa! Amma wannan yaron akwai mara kirki, kodayake laifinki ne ɓa wallahi, ni

na rasa irin son da kike yi masa ba".

Maryam ta ce"Ta ya zai zama laifina?"

Ta ce"To akan me ba za ki yi masa kaca-kaca ba? Wannan wane wulaƙanci ne a ce ciki har ya
shiga watan haihuwa ba a sayi komai ba? Haihuwar fari fa za ki yi Maryam, ko so kike mutane
su samu abun faɗa a kanki? Wallahi da ki haihu ya zo ya ja mana abun kunya, gara ma mu san
auren ya mutu wannan an san dama ba mijinki ba ne, ke ba ki ga Murja ba haihuwar fari yadda
ta dinga tatso kuɗi a jikin mijinta hatta yajin da na yi mata da kuɗinta ne, to ba ki Murja komai
ba? Shi kenan ki yi ta zama da wannan ƙaddararren auren".

Maryam ta ce"Ai shiyasa na ce ba zan taho ba sai ya zo".

Uwani ta ce"Ki miƙe tsaye ki tada masa da hankali kar ki yarda ki dawo gida haka hannu na
dukan cinya".

Ta ce"To bari ya dawo".

Suka yi sallama, kalaman Uwani sun ƙara tunzurata don haka ta cika ta yi fam tana jiran
dawowar shi, ƙarfe tara ya dawo unguwar, ya biya ta gidansu don ya karɓi mukullin gidansa,
Umma ta ce"Wane irin mukulli kuma? Ina Maryam ɗin ta tafi?"

Ya ce"Au ba ta kawo mukulli ba? Gida ta tafi ai, kin ga ta yi nauyi idan ta haihu ta yi arba'in sai
ta dawo".

Umma ta ce"Ikon Allah! Ku mazan zamani da ba kwa yarda mace ta tafi goyon ciki? Hamza
anya kuwa? Kuma da sai ta tafi haka ko sanar da ni ba za ka yi ba?"

Ya ce"To ai ga shi yanzu kin ji, kuma goyon ciki ai ba komai ba ne".

Ta ce"Amma ni dai da ta haihu a ɗakinta, idan aka yi suna sai ta koma gidan".

Ya ce"A'a ta je ɗin kawai babu komai".

Ta ce"To Allah Ya sauketa lafiya".

Ya yi mata sallama ya fita. A ƙofar gida ya tsaya ya kira lambar Maryam,har ta fara bacci ma, ta
ɗaga cikin muryar bacci, ya ce"Mayam kina ina?"

Ta ce"Ina gida mana".

Ya ce"Wane gidan?"

Ta ce"Gidanka mana".

Ya ce"To me ya hana ki tafiya?"

Kawai sai ta yi tsaki ta kashe wayar, ta tashi ta je ta cire sakatar ƙofar ta dawo ta kwanta.

Babu jimawa ya shigo gidan, ya same ta a ɗakin ya ce"Wai ni me ya sa ba ki tafi ba?"

Ta yi kamar ba ta ji shi ba, tana jin takaici wai ita miji yake nunawa yana son ta yi nesa da shi
ƙiri-ƙiri babu sakayawa.

Ya ce"Magana fa nake yi miki".

Ta tashi a fusace ta ce"Hamza idan ka yi haƙuri zan bar maka gidanka har abada, amma sai na
haihu, kuma dalilin ƙin tafiyata ai na faɗa maka sai ka yi mini siyayya, sannan ka sayi kayan
jarirai".

Ya ce"Amma ai ce miki na yi zan aiko ko?"

Ta ce"Don ka yi magana dole ne na amince? Idan ji ya zama dole ai babu inda yarda take zama
dole".

Ta juya ta kwanata.

Ya fice daga ɗakin yana tsaki.

Da ya ga dai har ta ƙara kwana uku ba ta da niyyar tafiyar, sai ya same ta suka zauna ya
ce"Wai me da me kike buƙata?"

Ta ce"Za ka siyo kayan shayi na gwangwani fa ba irin wanda kake kawo mini ba, sannanza ka
siyo kwalin indomi, da golden morn, sannan kayan jariran wanda mace da namiji za su iya
sakawa kala uku, ka ga kenan shida za ka siya tun da su biyu ne".

Kalmar biyun nan ta saka gabansa faɗuwa, saboda har yanzu kuɗin abun yanka ma ɗaya ya
tanada, shi ma lissafinsa tunkiya zai siya haka ƴar madaidaiciya.

Ta ci gaba"Ka ga za ka siyo tawul masu kyau kowa biyu, sai saitin kayan sanyi da saitin man
shafawarsu, wannan su za ka siya kafin na haihu, idan na haihu aka ga me aka samu sai a san
yadda za a haɗa kayan barka".

Ya ce"Wannan lissafin nawa ya kama?"

Ta ce"Oho! Ka ba da dubu ɗari sai a je a ji".

Ya yi mata wani mugun kallo mai ɗauke da manufar ba ki da hankali, ya ce"Dubu ɗari?"

Ta ce"To ka je ka siyo mana".

Ya tashi ya fice, a ranar ya siyo komai da ta lissafa, amma duk masu sauƙin kuɗi ya zaɓo, ya
kawo mata ya lallaɓata ta tafi.

Uwani da ta ga kayan ta rafka tagumi har sai da Maryam ta tsargu, kafin ta ce"Maryam wane
irin miji ne wannan da kike son rayuwa da shi? Wannan kayan tsohon ya yi masu mugun arha
ya siyowa ƴaƴansa na fari? To sai dai mu ce Allah Ya kyauta".

Maryam dai ba ta ce komai ba.

Daga nan kuma sai Uwani ta tsiri saka ta ta cewa Hamza ya siyo mata nama, ko kayan
marmari haka, idan ta kira shi ta faɗa masa sai ya fara masifa yana cewa shi fa ba shi da kuɗi,
wataran zai kawo, wataran kuma ya ƙi kawowa, Uwani kuwa ta samu abun mita, ta yi ta masifa
tana tsinewa auren, a haka dai har aka cika sati biyu, ranar tsakar dare Maryam ta fara naƙuda,
Baba ya ce ga maƙotansu wani matashi yana da adaidaita sahu a kira shi su tafi asibitin, amma
fir ta ƙi ta dinga kiran Hamza a waya, shi kuwa yana ganin kiran jikinsa ya ba shi ba lafiya ba, ya
san dai ƙarshen zance cewa za a yi Maryam za ta haihu ko kuma ta haihu, don haka ya ƙi
ɗagawa, sai ma ya saka wayar a silent ya ci gaba da baccinsa, dole dai aka bi maganar Baba,
suka tafi asibitin a hanya tana ta zagin Hamza Baba yana kwaɓarta.

Sai da asuba Maryam ta haihu, ƴaƴanta mace da namiji, sai dai macen ta zo babu rai, sai
namijin ga shi nan ma sha Allah, sai da gari ya waye ta kira lambar babar Hamza ta bawa
Uwani, ta faɗa mata an sauka lafiya, ta ce"Ki sake kiran shi shi ma".

Uwani ta ce"Kin san kira nawa na yi masa jiya? Yanzu da ya tashi sallah ai zai ga miss call idan
shi mutumin kirki ne ai sai ya kira!".

Bakwai da rabi Hamza ya zo asibitin tare da babar shi, suka kawo musu abun karyawa, a
gaban babar shi Uwani ta caccake masa tass na rashin ɗaga wayar, ita kuma tana ta ba ta
haƙuri, aka tafi da gawar yarinyar aka binne, sai da yamma aka sallami Maryam ta koma gida.

Sun ga tijara kafin ranar suna ta zo, don yanzu Uwani karɓar lambar shi ta yi, abu kaɗan ta kira
shi ta ce ana buƙatar abu kaza, ranar da bai kawo ba ta yi ta tsine masa ƴaƴanta suna yi mata
nasiha, amma kamar suna zugata.

Ranar sunan ma sai da ta raina abun yankan, kayan fitar suna ma kala ɗaya ya yi mata, wata
atamfa ce aka sako ta a cikin kayan barka, don haka ita Maryam a ranta ta ƙudure wannan
zuwa gidan da ta yi, ta zo kenan babu zancen komawa, don wannan idan ta ci gaba da zama
da shi gorin Uwani ma kawai ya ishe ta.

08028966015
[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_



*SADIYA ABDULRAZAƘ*


*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne
hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman
aure?*

Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu

*FIRST CLASS WRITERS*

PAGE 10


https://chat.whatsapp.com/G08KLEmlF3gJ3X4npkfIee


Hamza sai ya bushi iskarsa yake leƙowa gidan har aka yi arba'in ɗin Al'ameen, ga wani raini
da ya yiwa Uwani, saboda yawan roƙon shi da take yi, da yadda take raina ƙoƙarin shi, har wani
kallon gani-gani yake yi mata idan ya je gidan. Uwani tana sane ta ce Maryam arba'in biyu za ta
yi, saboda ta dinga ja masa rai har ya gaji auren ya sire masa, ba ta san kamar an zuga
zugagge ba ne, don shi ma ba son ci gaba da zaman yake yi ba, Baba da ya yunƙuro a kan sai
ta koma ɗakinta Uwani ta sanar masa ba ta da lafiya fa, ɗinkin da aka yi mata sanadin haihuwar
nan bai warke ba, kuma likitocin sun yi gargaɗi da kakkaurar murya a kan kar ta koma sai
bayan wata uku, su kuwa yaran zamani masu do a tsakar ka idan ta koma sai dai komai ya faru,
don haka Baban ya ƙyale su ya zuba ido.

Watanta biyu a gida Hamza ya zo da daddare, sun gaisa yake cewa"Maryam yaushe za ki

koma ne? Sannan ina ga fa sai dai ki koma gidanmu da zama..."

Ta katse shi da faɗin"Ban gane ba!".

Ya ce"Ai ganar da ke nake yi".

Ya ce"Kin ga dama kuɗin hayar ya ƙare, kuma ni ba ni da kuɗin da zan sake biya, sannan ma
ina son tafiya wata ƙasar neman kuɗi, ana kan yi mini hanya, kuma ko ba wannan ba ni dama fa
a zamanmu haƙuri kawai nake yi da ke, saboda tsakani da Allah ba ki da kunya, ba ki da
tarbiyya ba ki san girmana ba a matsayina na mijinki".
Maryam ta yi mamaki sosai, don ko da wasa ba ta taɓa tunanin gidan nan ba na shi ba ne,
sanda yana neman aurenta ya ce mata na shi ne ya gina tun da jimawa sai ya saka ƴan haya a
ciki, yanzu ya tashe su tun da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login