Showing 30001 words to 33000 words out of 39853 words

Chapter 11 - MIJI GOMA Book Complete By Sadiya Abdul.pdf

25 May 2025

7749

taya ta
kishi, don ban faɗa miki ba ne ba ma, amma Sauda ta yi yaji tana can gidanmu, kuma Innar ta
goya mata baya ta ƙyale ta, sannan akwai wasu ƙananun maganganu da suke yi, wai ai ba
zaman aure kike yi ba, ko na aure ki za ki fita, sai dai kin toshe kunnuwanki gaskiya".

Jikin Maryam ya ɗan yi sanyi ta kasa cewa komai ta tafi duniyar tunanin kalar zaman da za su
yi.

Alhaji ya ce"Maryam kin yi shiru, ina son ki, kuma sannan zan kwatanta adalci daidai
gwargwadon iyawata a tsakaninku, ba zan ga wata ɓaraka na ƙyale ba, amma kin san komai
sai kin yi haƙuri kafin ki ci riba".

Ta ce"To Allah Ya ba mu zaman lafiya bakiɗaya".

Suka yi sallama Maryam ta shiga gida a sanyaye, da a da ne da tuni ta juyewa Uwani komai,
amma a yanzu sai ta yi shiru ta bar abun a cikinta tana fatan Allah Ya ba su zaman lafiya.

Washegari ƴan kawo lefe suka zo, mata ne su biyar, suka kawo akwati guda huɗu, kuma babu
laifi ya saka mata kaya sosai, duk da sun rage a cewarsu ai wannan kayan bai cancanci
bazawara ba, ƴan'uwa da aka gayyato karɓar lefe da ƙawayen Uwani suna ta ɗaga kaya suna
cewa"Ma sha Allah! Kaya sun ce".
Wata cikin masu kawo kayan ta taɓe baki ta ce"Iyyi kaya sun yi fa! Sai fatan Allah Ya sa kunun
banza ya ƙare a farau-faru ɗin banza".

Wata ta ce"A to, tun da dai amaryar an ce ba mazauniya ba ce a gidan aure".

Wata cikin dangin babar Maryam ta ce"Daɗin abun dai shi ya gani ya yaba, sai a bar shi da
zaɓin shi".

Wata ta ce"Kuma mutuwar aure ai ƙaddara ce, ƙaddara kuwa tana kan uban kowa, ko a yau
idan uban mutum ya kwanta ya mutu uwarsa ta zama bazawara".

Wata cikin masu kawo kayan ta hasala ta ce"Kin ga kar ki zage ni, wallahi kar ki sake, dama an
faɗa mana ba gidan arziƙi ba ne, ƙaddara ce da biyewa zuciya ya kawo shi".

Nan aka fara maganganu, hayaniya ta kaure a gidan, aka rabu baran-baran dutse a hannun
riga, ko tukuici ba a samu damar ba su ba, suka tafi.

Wannan abu da ya faru ya ƙarawa Maryam baƙinjini a wajen dangin Alhaji Haruna, musamman
mahaifiyarsa da ta cika ta yi fam kamar za ta yi bindiga, musamman idan ta kalli Sauda da
yaran a gida, a cewarta ya zaɓi wata mara tarbiyya ya watsar da matarsa ta ƙuruciya da
ƴaƴansa, don haka fushi take yi da shi sosai.
A haka dai Alhaji ya toshe kunnensa, suka yi ta hidimar gabansu shi da Maryam, har ranar
auren ta zo, aka ɗaura aurensu, an yi yini a gidan su Maryam saɓanin shi da babu abin da aka
yi, ko abincin ƴan ɗaurin aure a can gidan matar baban shi aka yi, shi dai yana ta zumuɗin
zuwan amarya babu abin da ya dame shi.
Bayan sallar isha'i aka ɗauki Maryam aka kai ta gidan miji a karo na huɗu, wanda take fatan ya
zama na ƙarshe da za a sake ɗaura aurenta, ma'ana wannan aure ne ta yi na mutu-ka-raba.



(To fa! Ya kuka hango zaman Maryam a irin wannan gidan?)

Littafin nan na kuɗi ne a kan naira 500 kacal!
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay


08028966015
[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_



*SADIYA ABDULRAZAƘ*


*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne
hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman
aure?*

Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu

*FIRST CLASS WRITERS*

https://chat.whatsapp.com/BuEB69AOiqBKg0PMiBzdG3

PAGE 14


Suna ƙule a ɗakinsu baban nasu ya dawo, Maryam ta tare shi ranta fess, ta haɗa masa
ruwan wanka ta kai banɗaki, abin da ba ta taɓa yi wa sauran mazan da ta aura ba, ko ruwa a
buta ba ta taɓa zuba musu ba, amma shi wannan da yake zaman gaskiya ta zo ta ɗaura
ɗamarar yi masa hidima iyakar iyawarta, tsaf ta taya shi shiryawa bayan ya fito, sannan ta ja
hannunsa kamar wani ɗanta zuwa falo, ta kawo masa tuwon, tana ba shi a baki suna ta firarsu
cike da nishaɗi, har ya yi mamakinta saboda shi kansa ya san kafin auren ba wani son shi take
sosai ba, kiran sallar magriba ne ya tashe shi, ya yi alwala ya tafi masallaci yana jin shi fess da
shi, ya manta rabon da ya samu kulawa da soyayya irin wannan, sautari sai bayan magriba
yake yin wanka saboda sai ya ce Sauda ta dafa ruwan take dafawa, wataran ma a haka yake
kwanciya ko ya yi da na sanyi, sannan Momy ce mai kai masa abinci dining, idan ma ya shiga

ɗakinsa yana wani aikin ko kuma ya shigo da wata damuwar, babu ruwan Sauda da zuwa ta ji
dalilin ƙin fitowarsa, sai dai ta aiko masa da abincin ɗakin nasa, sannan babu ruwanta da
tambayar shi fita unguwa, indai ka ga ta tambaye shi sai dai idan nesa sosai za ta je, gidan Inna
kuwa idan za ta je tun rana idan ta tafi sai dare idan ya je yi mata sai da safe su taho tare, babu
ruwanta da me zai ci ranar, babu dai wata kulawa akwai matsaloli birjik, wanda shi ne dalilinsa
na son ƙara auren, kuma tun yau ya fara tunanin za a samu canji in sha Allah!

Ya dawo daga masallaci Maryam ta ga bai yi maganar yaran ba, ta dai leƙa bayan fitarsa ta ce
duk su yi alwala su yi sallah.

Ta ce"Alhaji dama ina so mu yi magan a kan yaran nan".

Ya ce"To, wasu yara?"

Ta ce"Yaranka".

Ya ce"Me ya faru? Ba za ki samu matsala da su ba in sha Allah! Kin ga ma yara ne, uwar ma
don Allah ki kau da kai ga matsalolinta".

Ta ce"Ba wata matsala ba ce, ka ga yau taliya na dafa da safe, na ba su suka ce wai ba sa cin
taliya, sai kowaccensu ta shiga zaɓar abin da take so, ni kuma na ga ba zao yiwu na yi girki har
kala huɗu ba, ko hakan bai zama almubazzaranci ba ai ka ga ni ma ina buƙatar hutu, tun da ba
bautarsu na zo yi ba, sannan ba ma tarbiyya ba ce yara su dinga zaɓin abin da za su ci, na ce
su tsayar da guda ɗaya, suka ce tuwo, shi ne na yi, loma ɗaiɗai suka yi suka ce mini ba daɗi,
ƙarshe sai suka sha golden morn suka ƙule a ɗaki".

Alhaji ya ce"Ikon Allah! Wai kina nufin su yaran suna gidan nan? Waye ya kawo su?"

Maryam ta ce"Wai dama ba ka sani ba? Daga makaranta mai adaidaita sahu ya kawo su".

Ya ce"Yanzu suna ina?"

Ta ce"Suna ɗaki".

Ya shiga ƙwala musu kira ransa a ɓace, suka fito, Kausar da Momy suka haɗa baki wajen
faɗin"Abba yunwa muke ji, ba mu ci komai ba".

Ya daka musu tsawa da faɗin"Ku nemi wajen zama!".

Suka zauna duk suka sha jinin jikinsu, saboda Abban nasu ba mai yawan faɗa ba ne.

Ya ce"A cikinku waye ba ya cin taliya? Yaushe kuka daina cin taliya?"

Duk suka yi shiru suna raba ido.

Ya ce"Wato ku har kun yi girman da za ku yiwa babba rashin kunya? Ku sa ta yi tuwo ku ce
babu daɗi?"

Ya kalli Maryam ya ce"Idan akwai ki sako musu".

Ta tashi ta je ta ɗakko shi a yadda suka bar shi, ta ajiye, ya saka su a gaba sai ga shi sun cinye
tass, har da ƙari, ya yi mamakin dalilin da ya sa suka yi mata haka, ya zaunar da su ya yi musu
nasiha sosai, ya nuna musu ita ma Maryam babarsu ce, duk abin da suka san ba za su yiwa
babarsu ba to kar su yi mata, suka ce to, sannan ya saki jiki da su suka yi fira, Maryam ta ce su
je ta yi musu wanka, ba su yi musu ba suka wuce, sai a lokacin ma ta sa suka yi home work,
ƙarfe takwas Abba ya ce su je su kwanta, ita kuma Maryam ta kwashi unifom ɗinsu ta tafi
wankewa, sai ga shi sun yi wankin a tare da Alhaji suna yi suna fira.

Ita kuwa Momy suna shiga ɗaki ta ɗauki wayar ta sanarwa Sauda duk yadda aka yi, Sauda
ranta ya ɓaci matuƙa ta ji kamar ta taso ta taho gidan yanzu, ta fara tunanin wato daga zuwanta
za ta sa ya tsani ƴaƴansa har yana yi musu faɗa? Nan gaba ai sai duka, kenan ya goyi bayanta
nan gaba ko ita ce da laifi tana kallo za a tauyewa ƴaƴanta haƙƙi, ai kuwa ba zai yiwu ba, ta fara
tunanin hanyar da za ta bi don ta hana su cin amarci, sai dai yaran sun yi ƙanƙantar da za ta
saka su yi wata kissar, don haka kawai ta yanke gara ta dawo su fara gabza yaƙin, ta ce wa
yarinyar ta yi haƙuri su kwanta, amma kar su sake bari ta yi musu wanka, ita ta yi da kanta
sannan ta yiwa ƙannenta.

Washegari haka Maryam ta yi sammakon tashi saboda yaran, don tun a daren ya faɗa mata
girki biyu ake yi da wanda za su ci, da wanda za su tafi da shi, ta dafa shayi ta soya doya da
ƙwai ta saka musu a lunch box ɗin, sannan ta tafi ɗakinsu, ta tarar Momy ta yi wanka za ta fara
yiwa sauran, Kausar tana cewa ita ba za ta yi mata, ta ce"Ya za a yi ki yi musu? Ke ma ai ba
wuce wankan kika yi ba, ku wuce na yi muku".

Momy ta ce"Mu fa Ummanmu ce kawai take yi mana wanka".

Maryam ta ce"Tun da yanzu ba ta nan ai dole ku bari na yi muku".

Ta ce"Mu dai a'a".

Maryam ta juya ta fita, ta sanarwa da mahaifinsu, da mamaki ya ce"Ha'a, wai me yasa yaran
nan suke haka ne?"

Ya fito ya zo ɗakin, ya ce"Ke Momy! A kan me ba za ta yi muku wanka ba?"

Ta ce"Ummanmu ta ce kar mu yarda da ita".

Maryam ranta ya ɓaci ta ce"Ai shikenan". Ta juya ta bar ɗakin.

Ya ce"Ummanku? Au haka ta tsara muku? Abin da ta turo ku ku yi kenan? To zan haɗu da ita!
Ku saka kayan naku a haka ku tafi, idan ta damu sai ta dawo ta dinga yi muku wankan".

"Maza ku saka ku fito, mintu uku na baku". Ya ƙarasa a tsawace yana jin dole ya takawa Sauda
burki don ba za ta lalata masa tarbiyyar yaransa ba.

Yana fita Momy ta shiga banɗaki ta kira Sauda ta sake faɗa mata, ai kuwa ta hasala tana ta
zage-zage.

Suka fito kowaccensu babu sakewa, sai a lokacin suka gaishe shi, ya amsa kafin ya ce"Kun
gaishe da Antinku?"

Duk suka yi shiru, sannan suka gaishe ta ɗaya bayan ɗaya, suka karya mai adaidaitansu ya zo
suka tafi makaranta.

Sun gama karyawa ya ce da Maryam"Don Allah ki yi haƙuri, yara ne kin san duk yadda aka
tsara musu ba za su yi nazari ba, amma zan same ta na yi mata magana, idan ba za ta barki ki
yi yadda ya dace da su ba, to ta zo ta zauna da su".

Maryam ta ce"Allah Ya kyauta".

Kafin ya tafi kasuwa ya tsaya a gidan nasu, ya gaida Inna, ya samu Sauda tana karyawa, ko
kallon shi ba ta yi ba, ya ce"Yawwa Sauda na ga kin aiko mini yarana, ina son ki sani Maryam
za ta iya riƙe su fiye da yadda kike kula da su, sai dai ki sani indai kin bar mata su to fa sai dai ki
koma gefe ki yi kallo, ba zai yiwu tana tufka kina warwarewa ba, saboda shirme kin zauna kina
tsarawa yara shirmen banza, to matata uwa ce a gare su, ya zama dole su yi mata biyayya tun
da ni na haife su!".

A hasale Sauda ta ce"Ita ta haifar mini su? Wallahi babu shegiyar da ta isa ta tsarawa ƴaƴana
yadda za su yi, yarinyar da ba ta samu tarbiyya ba tun daga tushe, har kana kallona kana faɗa
mini kalmar matarka?"

Sai kuma ta saki wata dariya mai kama da ta tsantsar baƙinciki ta ce"Heee masu mata manya!
To a yi mu gani idan tusa za ta hura wuta, yarinyar da ba ta zaman aure har wata abar alfahari
ce? To sai ka jira ka ga zaman ya yiwu kafin ka fara wulaƙanta ni ka watsar da ƴaƴanka!".

Ya ce"Ni dai na faɗa miki, idan kuma kin ƙi ji ba kya ƙi gani ba!". Ya fice ya barta tana ta
bambami.

Inna duk a gabanta a ka yi komai, ba ta ce wani abu ba, dama idan da sabo ta saba da faɗan
nasu, sai da ya fita ta ce"Sauda a nan fa ba ki da hujjar da za ki saka yara su raina matarsa,

idan har ba kya son ta shiga sabgar yaranki to ya zama dole ki koma kansu ki ci gaba da kula
da su, kin ga dai yadda ya gigice a kan yarinyar nan yake rawar kai, kina nan a zaune za ta
gama mallake shi da kissarsu ta zawarawa, irin wannan gogaggun yaran da suke yin aure-aure
wallahi ki kiyaye su,sai kin tashi a tsaye kin ɗaura ɗamara, saboda haka ni yanzu umarni nake
ba ki ba shawara ba, ki kama hanya ki koma ɗakinki a yau, ki kula da ƴaƴanki, sannan ki yi iya
yinki na ganin ba ta mayar da ke bora ba, kar ki yarda ta ƙwace miki mijinki da gidanki".

Sauda ta ce"Shi kenan Inna an jima zan koma".

Inna ta ce"Ko ke fa, wannan ai kina nuna mata ta fi ƙarfinki ne ba za ki iya da ita ba, saboda
haka ki koma ki nuna mata gida naki ne, kuma miji da ƴan'uwan shi ma naki ne!".

Sauda ta jinjina kai cike da gamsuwa, ta tashi ta shige ɗaki.

Zama ta yi ta kira ƙawarta a waya ta sanar da ita za ta koma, ta ɗora da faɗin"Don Allah ya za a
yi ki haɗa ni da wannan mai maganin? Na san shegiyar tana nan ta gigita shi, bazawara ana
marari za a samu miji".

Aliya ta sheƙe da dariya ta ce"Alhamdulillah! Allah na gode maka da ka nuna mini ranar da
Sauda za ta nemi maganin gyara zama".

Sauda ta ce"Au shaƙiyanci za ki yi mini kenan".

Ta ce"To ai ke ce kullum cikin kuri kike kina da ni'imarki ba sai kin sha komai ba, yanzu kika
dawo hanya Hajiyata, zan turo miki lambarta".

Sauda ta ce"Malama yanzu fa nake so, zai yiwu ta aiko mini kayan a yau?"

Aliya ta ce"In sha Allah!".

Tana turo mata, ta kira ta a waya, suka yi ciniki gabaɗaya irin wanda ake cewa ban da me
kishiya su ta siya na dubu ɗari, kuɗin gudunmawa ne dangi suka haɗa mata don ta yi gyaran
dama, da yamma aka aiko mata da kayan, ta gama shirinta tsaf jira kawai take yi ya zo yi wa
Inna sai da safe ta bi shi su tafi.
Yau ɗin Maryam shinkafa da miya ta yi, da alama yaran ba ma su taurin kai ba ne, don kuwa
yau babu wanda ya yi magana a kan abinci, kowa ya ci, sannan sun tsaya ta yi musu wanka,
ban da babbar da ta ce ita ce take yi da kanta dama, sai ta rabu da ita, amma dai sam sun ƙi yin
fira da ita, don haka ita ma ta ke ta harkar gabanta.
Da yamma da ya dawo sai da ya tambaye ta yaran, ta ce babu wata matsala, ya yi wanka ya ci
abinci, ya fita sallah ya dawo, dama idan zai fita sallar isha'i da mota yake fita saboda daga can
yake wucewa gidan Inna ya yi mata sai da safe, don haka yau ma ya wuce, ya ɗan zauna

bayan sun gaisa, hat yanzu ta ƙi dawo masa kamar baya, babu wata fira haka dai babu yabo
babu fallasa, ya tashi zai tafi ta ce"Ka zauna".

Ya zauna yana sauraronta.

Ta ce"Sauda za ta bi ka ta koma kan ƴaƴanta, saboda haka kar na ji kar na gani, ka zama mai
adalci a tsakaninsu, kar sabo ya sa a watsar da tsoho, ta farkon dai ita ce dahir ɗinka, ba zan
ɗauki wulaƙanta mini ƴa ba wallahi, don haka ka ja kunnen yarinyar nan, ta kula ta kiyaye, tun
da zuwa ta yi ta tarar da ita da ƴaƴanta, ba ta san faɗi-tashin da aka yi kafin ka kai matakin da
kake a yanzu ba".

Ya ce"To Inna za a kiyaye in sha Allah!".

Ya tashi ya fita yana yi mata sai da safe, ya ɗan jima a motar kafin Saudar ta fito da akwatinta,
ta buɗe motar ta shiga ya ja suka tafi, babu wanda ya ce wa wani ƙala har suka ƙarasa gidan,
lokacin yaran suna ɗaki, Maryam kuwa tana hakimce a babban falo cikin wata fitinanniyar rigar
bacci, suka shigo da sallama, niyyarta idan ya shigo ta je yin oyoyo amma sai ta yi turus ganin
shi tare da wata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login