Showing 12001 words to 15000 words out of 39853 words

Chapter 5 - MIJI GOMA Book Complete By Sadiya Abdul.pdf

25 May 2025

7740

kayin nasu, tana tsaye a ƙofar gidan kusa da su, ta yaye hijjabinta ta
baya gabaɗaya bayanta a waje, ga shi riga da siket ɗin jikinta sun ɗame ta sosai, tsaye take a
kan yarinyar da take soya awarar siyarwa a ƙofar gidan, ta ɗauki ɗaya a cikin ɗan kwandon, ta
kai bakinta kenan suka haɗa ido da Nazifi wanda ya tsaya yana kallonta ransa a ɓace cike da
takaici.

Wani haushinsa ya kamata, ta tsaya tana ƙare masa kallo kamar yadda yake kallonta, Nazifi
dogo ne siriri, baƙi ba wani kyakkyawa ba ne, shi ba kuɗi ba, sai yau ma ta ji haushin kanta, ta
fara tunanin me yasa ma ta aure shi? Kamar wacce aka yiwa asiri, idonta ya rufe saboda ganin
son da yake yi mata.
Ta yi tsaki bayan ta karɓi awarar da yarinyar ta miƙo mata, ta juya ta fara tafiya, kamar ba ta san
wajenta ya zo ba.

Ya bi bayanta yana kiran sunanta, ta tsaya ba tare da ta juyo ba, ya ƙarasa ya tsaya a gabanta
yana kallonta zuciyarsa cike da sonta, ya ce"Amma Maryam kar ki manta yanzu ke matar aure
ce fa, bai kamata ki ɗage hijjabinki haka a titi ba, duk wanda ya kallar mini ke a haka wallahi ya
cuce ni".
Ta yi masa wata kafirar harara ta ce"Malam me yake tafe da kai?"

Ya daure ya yi murmushin yaƙe ya ce"Ango ya zo wajen amaryarsa a tambaye shi dalili? Zuwa
na yi mu tafi mana".

Ta gyara tsayuwarta ta ce"Nazifi kana son kanka da arziƙi? To ka taƙaitawa kanka wahala ka
sake ni, zan faɗa maka a taƙaice, wallahi ko sama da ƙasa za ta haɗe, ko uwata za ta taso
daga ƙabari ba zan koma gidanka ba, ka ga wannan bayanin da na yi maka? Indai ba ka
fahimce shi ba, to ba za ka taɓa fahimta ba, ka ga kenan ba ni da lokacin ɓatawa wajen
sauraronka".

Ransa ya ɓaci, a ɗabi'arsa shi mutum ne mai saurin fushi, amma yakan danne zuciyarsa idan
yana gaban Maryam, ya ce"Ki yi haƙuri Maryam, indai a kan Gwaggo ne ta amince da wannan
sharuɗan da kika kafa da farko, za ta dinga girkinta, kuma ta ce ma za ta kwashe kayanta daga
kitchen ɗin".

Ta yi wata shegiyar dariya ta ce"Yanzu da kuka ji uwar bari kenan! To sai ka koma ka faɗa mata
kun makaro, ita dama sau ɗaya take zuwa a rayuwa, da ace ka amince tun a lokacin da an yi
hakan, amma ka yi sake yanzu auren duka ya fita daga raina, kuma wallahi babu wanda ya isa
ya saka ni na ci gaba da yi, don Allah Nazifi idan ba takarda ka zo kawo mini ba kar ka sake
zuwa wajena, ni zan fi so ma ka turo min da sakin ta waya saboda ba na son ganinka".

Ganin ya daskare ya kasa cewa komai, sai ta yi tsaki ta shige gidan, ya rasa ma me yake yi
masa daɗi, me kuma zai ce mata ta yarda ta koma? Ya lura ita ma babarta ba son ci gaban
auren take yi ba, don haka ya yanke ba sai ya sake tuntuɓarta ba, kawai sai ya zauna a ƙofar
gidan yana jiran Babanta ya dawo, ya saƙa wannan ya ware wancen har aka kira magriba, ya
shiga masallaci ya yi, ya dawo ya zauna, babu jimawa kuwa sai ga Baban ya dawo.

Ya tashi da sauri, ya rusuna yana gaishe shi, Baba ya amsa yana cewa"Kamar Nazifi ko?"

Yana rusunar da kai ya ce"Ni ne Baba".

Baba ya ce"Sannu da zuwa".

Ya ce"Yawwa".

Ya ce"Wajen Maryam ka zo? Ka shigo daga ciki".

Nazifi ya ɗan sosa kai ya ce"Ai wajenka na zo, ita mun yi magana tun ɗazu, kai na zauna jira".

Baba ya ce"To shigo daga zaure".

Suka shiga, Baba ya shiga cikin gidan ya ɗakko tabarma, ya dawo ya shimfiɗa suka zauna,
Baba ya ce"Wai mene ne yake faruwa tsakaninku?"

Nazifi ya zayyana masa komai, sai Baba ya ji akwai ragi a maganarsa ba kamar yadda Uwani ta
faɗa masa har da dukan Maryam mahaifiyarsa ta yi ba, ya ce"Sun sanar da ni, to kai yanzu
wane mataki ka ɗauka?"

Ya ce"Ita Maryam ɗin tun farko ita ce ta ce ta yarda za su zauna da Gwaggo amma kowa ya yi
harkarsa, kowa ya yi girkinsa, to da farko ban amince ba, shi ne abin da ya tada tarzomar, duba
da ganin mahaifiyata ce, tana da cikakken iko a gidana, kuma ta cancanci mutuntawa daga
matata, amma da na ga hakan ya ƙi kawo maslaha sai na ce na amince da sharaɗin nata, ita
ma kuma Gwaggon ta amince, amma dai har yanzu Maryam ɗin ta ƙi ta nuna saki kawai take
nema".

Baba ya ce"Saki!? Kai ɗan yau ka haife shi ba ka haifi halinsa ba, ka ga ni fa shiyasa ba na
saka baƙincikin ɗan yau a kaina, sai su kashe ka a banza, kuma dama Maryam ta fita da ban da

ƴaƴan gidan nan, za ta aikata, auren ma da ya ta yi?"

Nazifi ya ce"Sai haƙuri Baba".

Baba ya tashi ya ce"Jira ni kaɗan".

Ya shiga cikin gidan ya ƙwalawa Maryam kira, har ta tashi Uwani ta mayar da ita ta zaunar tana
tsuke fuska ta ce"Malam lafiya?"

Ya shigo ɗakin yana cewa"Uwani wannan wane irin shirme ne haka? Ya za ki ɗaurewa yarinya
ta samu saken cewa ba za ta koma ɗakin mijinta ba?"

Maryam kamar za ta yi kuka ta ce"Baba ni fa wannan zaman ba zai yiwu ba".

Ya ce"A kan me? Ba matsalar babar shi ba ce? Ai ya karanta mini komai, ya ce zai bi sharaɗin
da kika kafa da farko, ku zauna da uwar tashi ba ruwan kowa da kowa, sai kace wasu facaloli,
kai Allah Ya shirya yaran zamani, maza saka hijjabinki ki wuce ku tafi".

Uwani ta ce"Haba Malam don ka ga ba ni na haifi yarinyar nan ba, shiyasa ba za ka ƙyale ni na
ƙwatar mata ƴancinta ba?"

Ya ce"Ko wacce kika haifa ce haka zan yi mata, ni ba na ma taɓa sakawa a raina ba ke kika
haifi Maryam ba, tun da ba kya wani abu na nuna bambanci, amma kin san wannan zaman nata
ba shi da wata fa'ida".

Ya kalli Maryam ya ce"Ba ki tashi kin saka hijjabin ba?"

Ta tashi a zabure kamar wacce za ta kai wa wani duka, tana turo baki da haɗe gira ta saka
hijjabin ya fita ta bi bayansa, ya ce"Ina akwatin?"

Ta ce"Gobe a kawo mini".

Uwani takaici ya rufe ta, sai take jin kamar da zuciyarta za ta tafi, sam ba ta so hakan ba, so ta
yi a yita ta ƙare, auren nan ya mutu a cikin satin nan, duniya ta shaida.

"Maryam!" Ta ƙwala mata kira murya a shaƙe.

Ta koma ɗakin tana share hawayen da ya zubo mata, idan ta tuna haka za ta tsufa cikin bauta
da rayuwar ƙunci sai ta ji har gara mutuwa a kan gidan Nazifin.

Uwani ta ja hannunta har ƙuryar ɗaki ta ce"Ba kuka za ki yi ba, ki koma ɗin amma ki ɗaura
ɗamarar yi musu gashin ƙuma shi da uwar tashi, kada ki sake ki saurara musu, musamman ita
uwar, saboda idan ta ga abun ba na ƙare ba ne, ita ce za ta saka dole ya sake ki, sannan kada

ki sake yarda ku haɗa shimfiɗa, idan kuma kin je kin sakar masa jiki kin samu ciki kin ga kanki
kika cuta, ki yi zaman zawarci da ciki".

"Ke Maryam!" Muryar Baba ta katse musu tattaunawar.

Wannan karon tare suka fito Uwani tana cewa"Allah Ya ba da sa'a Maryam".

Suka tarar da Nazifi a zaure, Baba ya ce"Tashi ku tafi Nazifi, Allah Ya rufa asiri".

Ya tashi ya naɗe tabarmar yana cewa"To Baba na gode, Allah Ya saka".

Ya yi gaba, Maryam ta bi bayansa, sai da suka ɗan yi nisa da gidan suka kusa kai wa titi sannan
ya tsaya har ta ƙaraso, saboda su samu damar jerawa.


08028966015
[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...*
_(BA UBA GOMA BA NE)_



*SADIYA ABDULRAZAƘ*


*Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne
hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman
aure?*

Marubuciyar
ZUCIYAR MACE
WUTAR ƘAIƘAYI
DA WALAKIN...
WANI AUREN
IYA RUWA
MATAR SHIGE. da sauransu

*FIRST CLASS WRITERS*

PAGE 6

Yana ɗan murmushi ya ce"Ki yi haƙuri Maryam komai zai wuce in sha Allah!".

Ta yi banza da shi. Ya ce"Ni fa ba nufina kawowa Baba ƙararki ba, da na san ma zai tilasta miki

ki koma da ban zo ba, na fi so ki dawo mini ta daɗin rai ba dole ba".

Nan ma dai ba ta kula shi ba, sai ma ƙara sauri da ta yi, yana biye da ita har suka ƙarasa titi, a
ranta tana ayyana zai gane kuskurensa na kafewa sai ya zauna da ita, a cikin adaidaita sahu
ma da ya kamo hannunta fizgewa ta yi tana aika masa mugun kallo, ya ce"Kin ce abinci kuwa?
Ko na tsaya mu siya?"
Ta yi kamar ba ta ji shi ba, sai ya kama kanshi ya ƙyale ta, ya ciro waya ya kira Gwaggo, ya
ce"Gwaggo na siyo miki tuwon ko sai na zo na dafa mana wani abun?"

Ta ce"La ai ni yau na yi tuwona, ina ka tsaya ne?"

Ya ce"Ga ni nan a hanya".

Ya ajiye wayar yana kallon Maryam wacce ta haɗe fuska tamkar ba ta taɓa dariya ba, shi
mamaki ya ƙi barinsa yadda soyayya take neman rikaɗa ta zama ƙiyayya, sun sauka a bakin titi,
sai ya tsaya don ya siya mata wani abun, ita kuwa ba ta jira shi ba ta wuce gidan, a buɗe ƙofar
take ta tura ta shiga ko sallama babu, har tana cin karo da kofin sulba da Yasmin ta bari a
tsakar gidan, tana jin Yasmin ta ce"Gwaggo kamar wani ya shigo".

Gwaggo ta ɗan ɗaga murya ta ce"Wane ne a nan?"

Ta ce"Ƙila tumakai ne, je ki kora su".

Haushi ya kama Maryam, wacce ta ja ta tsaya a ƙofar ɗakinta, saboda mukullin yana wajen
Nazifin, Yasmin ta fito ta haskata da fitila ta ce"Au!" Sai ta koma ta ce da Gwaggo"Maryam ce fa
ta dawo".

Gwaggo ta ce"Au kuma shi ne babu sallama?"

Daga nan Nazifi ya shigo da sallama, Gwaggo ta amsa daga ɗaki, ya ƙarasa wajenta ya miƙa
mata ledar hannunsa guda ɗaya, ta kau da kai gefe ba ta karɓa ba, sai ya ajiye su a ƙasa ya
ciro mukulli ya buɗe mata ɗakin, ta shiga, ya ɗakko ledar ya ajiye mata ɗaya, ya ɗauki ɗayar ya
shiga ɗakin Gwaggo, ya zauna yana cewa"Sannu da gida".
Ta ce"Yawwa, ashe ɗakkota ka yi".

Ya ce"E wallahi, kun gaisa?"

Gwaggo ta ce"Ba ta shigo ba".

Ya ce"Bari na kira ta".

Ta ce"Nazifi ba na son tada zaune tsaye, me gausuwarta za ta yi mini? Tun kafin a haife ta ake
ta gaishe ni, kuma har yau ban rasa masu gaishe ni ba".

Ya ce"Ki yi haƙuri Gwaggo".

Ta ce"A'a haƙuri ita ya kama ai, ga tuwonka nan" Ta ƙarasa tana miƙa masa kulolin da suke
ajiye a gefe.

Ya ce"Bari na yi sallah tukunna, kin ga har an shiga". Ya fito ya yi alwala ya tafi masallaci.

Kafin ya dawo Maryam ta fito ta yi alwala ta yi sallah, ta rufe ƙofarta, ta saka sakata, ta ɗauki
ledar, tsire ne a ciki da lemon jarka, ta cinye tass ta sha lemon ta kwanta, tana ta tsara nau'in
wulaƙancin da za ta fara aiwatarwa a gidan har bacci ya ɗauke ta.

Shi kuwa yana dawowa daga masallaci ɗakin Gwaggo ya shiga, ya zauna suna fira yana cin
tuwon, har tara ta gota, sannan ya tashi ya yi mata sai da safe. Ya ga Maryam ta rufe ƙofa bai
kawo komai ba, a zatonsa turo ta kawai ta yi ba ta saka sakata ba, amma sai ya tura ya ji ta a
rufe, da mamaki ya fara ƙwanƙwasawa ya ji shiru, ya fara kiran sunanta ƙasa-ƙasa don kar
Gwaggo ta jiyo shi ta gane halin da ake ciki, ƙarshe ya kira wayarta tana ta ringin ba ta ɗauka
ba, ya rubuta mata gajeren saƙo ya ce"Don Allah ki buɗe kar a fahimci wani abun". Shiru babu
amsa, da ya sake kira ma sai ya ji wayar a kashe, haka ya shige falo ya rufo ƙofar ya kwanta da
kayan jikinsa, a ransa yana ta mamakin kalar zuciyarta, da ƙyar bacci ya ɗauke shi.

Da asuba da ya dawo daga masallaci ya yi zaton zai ga ɗakin a buɗe, amma sai ya gan shi a
rufe, har ya yi tunanin ko ta makara ne? Sai kuma ya ga alamar ruwan alwala a takalminta da
yake ƙofar ɗakin, ya jinjina kai ya shiga falon ya zauna, yana ta saƙa da warwara har gari ya
waye, ya ji motsin Gwaggo ta fito hura wuta, sai ya fito ya gaishe ta, ya kalli ƙofar ɗakin har
yanzu ba ta buɗe ba, ita ma Gwaggo ta kalli ƙofar don a zatonta yana ciki bacci suka koma, ta
bi shi da kallo ganin ya koma falo.

Har takwas ta gota Maryam ba ta buɗe ƙofa ba, shi kuma wanka yake so ya yi ya canza kaya
ya tafi kasuwa, ya kira wayarta, yanzu ta shiga amma ba ta ɗauka ba, ya yi mata text ya
ce"Maryam wai mene ne haka? Ki buɗe mini ƙofa mana, wanka zan yi na tafi kasuwa".

Can anjima ya ji ƙarar buɗe ƙofar, yana fitowa yana banko ƙofar ta rufe, ya bi kayan da ta jeho
waje da kallo, duka jakar kayan shi ne, dama bai samu nutsuwar jera su a cikin sif ɗin ba,
mamaki ya daskarar da shi, sai ya yi saurin ɗaukar jakar ya shige falo don kar Gwaggo ta
fahimci wani abu, ya ajiye ya fito ya yi wanka ya canza kaya, ya shiga ɗakin Gwaggon, ta miƙo
masa kofin kunu da ɗumamen tuwo a roba, ya ce"Alhamdulillah Gwaggo".

Ta yi masa wani kallo ta ce"Kana nufin haka za ka fita ba ka ci komai ba? Ko teburin mai shayi
za ka je?"

Tun da ta ce hakan ya san ta gane wani abu a tsakaninsa da Maryam, don haka ya sha kunun,
ya ba ta ɗari biyar ta yi cefane ya yi mata sallama, ya tafi, ta bi shi da kallon tausayi don zuwa
yanzu ta gama saddaƙarwa ɗanta bai yi dacen mace ta gari ba, tana fatan idan da alkhairi a
zaman nasu Allah Ya daidaita, idan kuma babu alkhairi Allah Ya kawo rabuwar cikin sauƙi,
amma ta ji haushin rufe ƙofar da aka yi wa ɗan nata mai haƙuri.

Ransa babu daɗi ya je kasuwa ya kama harkokinsa, komai yake yi yana tunanin me zai yi ya
shawo kan Maryam su daidaita? Saboda yana sonta shi bai shirya rabuwa da ita ba, ko sati ba
a yi da aure ba a ce a rabu? Sau ɗaya rak suka haɗa shimfiɗa da ita, kenan duk kuɗin da ya
kashe daga neman auren zuwa auren ya yi asararsu a banza? Gaskiya ba zai yiwu ba, ko ta
kama dole zai rabu da ita sai ya mori kuɗinsa tukunna.

Maryam sai ƙarfe goma ta fito, shi ma yunwa ce ta fito da ita, ta ga Gwaggo a tsakar gida tana
wanke wake, don gyara shi take yi ta yi garinsa saboda yin ƙosai da safe, kallo ɗaya ta yi mata
ta ɗauke kai, ta shige kitchen, ita ma Gwaggon ba ta kula ta ba, ta tsaya tana ƙarewa kitchen
ɗin kallo, babu sauran kayan Gwaggo a ciki, ta ƙarasa ta dafa shayi da indomi, ta gama ta fito ta
koma ɗaki, yanzu ta bar ɗakin a buɗe, tana gama karyawa ta fito ta share iya ƙofar ɗakinta,
sannan ta shiga wanka da guntun tawul ko kunyar Gwaggo ba ta ji ba a matsayinta na
surukarta sai ma ita ce ta kau da kai, tana Allah Ya kyauta a zuciyarta.

Tun da ta shiga ɗaki ba ta fito ba sai azhar ta fito za ta yi girki ta ga babu kayan miya, ta saka
hijjabi ta je ta fita, ta yi ta yawo a unguwar har ta samu inda ake siyarwa ta siyo ta koma gida,
daidai lokacin Nazifi ya sauka daga adaidaita, hannunsa ɗauke da ledar cefane, da bai yi niyyar
kawo mata cefanen ba saboda abin da ta yi masa, sai kuma ya duba ya ga ai haƙƙinsa ne, ya
kamata shi ya sauke nashi ko da ita tana tauye masa, kuma maslaha yake nema bai kamata ya
yi abin da za a ce ga laifinsa ba, shiyasa ya yo cefanen, sai kuma ya ganta a waje.

Kallo ɗaya ta yi masa ta kau da kai za ta shige gidan, ya tare hanya yana cewa"Maryam daga
ina kike?"

Ta harare shi za ta gota ta gefen shi ta wuce, ya ce"Tambayarki fa nake yi, ina kika je babu
neman izini?"

A fusace ta ce"Kenan ba ka yarda na gama aurenka ba, shiyasa har kake tunanin idan zan yi
wani abu sai da izininka!".

Yana saita ɓacin ransa ya ce"Mu shiga mu yi magana".

Ya matsa ta shige, ɗakin nata ya dosa, yayin da ita kuma ta shiga kitchen ta fara gyara kayan
miya,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login