Showing 1 words to 3000 words out of 46340 words
Chapter 1 - ARNAN DAJI Book 1 By Feedeen Bash.pdf
[9/11, 22:29] +234 810 679 5647: ?*ARNAN DAJI*?
FAREEDA ABDULLAHI
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI INAFATAN
ALLAH YA TEMAKENI YABANI IKON RUBUTA WANNAN LABARI DANA DAKKO BA AKAN
WANI KO WATABA KAGAGGEN LABARINE WANNAN SHINE LABARINA NA FARKO
INAFATAN ALLAH UBANGIJI YABANI IKON YINSA CIKIN AMINCI KUBIYONI DAN KUGA IRIN
SALON DAYAZO DASHI*
NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA MAHAIFIYATA WADDA TA RAINENI TA KULA
DANI TSAWON SHEKARU MASU YAWA JINJINA GAREKI MAHAIFIYATA
1-5
Garin kuguru dajine wanda wasu mutane ke rayuwa a cikinsa basu dawani addini dayawuce
bautar wani katon gunki Wanda duk shekara sai anyanka masa mutane guda biyar yasha jini
sukuma mutan garin suci naman suna bikinsu na al'ada duk shekara suna fita iyakar garinsu
suna kama mutane duk Wanda Allah yasa tsautsayi yashigo dashi dajin suna kamasu su
dauresu sai karshen shekara suyankasu subawa gunkinsu jinin sugasa naman aci asha burkutu
basu da wata sittira sai dai susa fata ko ganyaye su rufe gabansu da ita matan Kuma su dan
kara a mamansu idansun zama yammata suna daura auren duk wata budurwa a karshen
shekara a abikinsu na shekara shiyasa ba karamin gagarimin taro akeba sarkin garin
azzalimine bashida imani ko kadan idan kuma kikai haihuwar fari za a dafa dan acinyeshi
Wanda sai anfara kaiwa sarki naman wannan kenan.
Tenkwai tenkwai way kina inane kije kidebo mana ruwa a rafi kinsan gidan nan bamu da ruwa
ko kadanko ko sai dare yayi kinsan garin nan almuru na kawo Kai ba a zuwa rafi saboda
mugayen abubuwan dake hanyar,Kai lamunde ganinan bara nabiyawasu rama, da aduke,sai
mutafi yauwa kuyi sauri dai karku jima,tenkwai tasa kai da tulunta a hannu tana tafe tana wasa
tabiyawa rama da aduke suna tafe suna hirar wasan daza ay na wannan shekarar aduke tace
tenkwai wayko meyasa haryau kinki kisaurari ja'ene yakamata izuwa yanzu kibashi hadin kai
tunda kinga har yanzu baki Sami Wanda ya kwanta mikiba tenkwai ta kalleta tace nifa banasan
wannan rayuwar ta mutanen garinmu kawai Dan bansan yadda zanyiba amma gaskiya wannan
yanka mutanen banasansa duk fa jinsunmu daya irinmu guda kuna kallo idan aka rasa
mazanmu ake yankawa kanaji kanagani za a yanka abunda kahaifa Dan rashin imani ba afita
agarin nan bame shigo mana duk wanda ya shigo sunansa matacce inafatan sanji yazo mana a
wannan gari nisam bansan ja'e saboda dan sarkin garinnan ne shima bashi da imani tamkar
mahaifinsa kinsan Kuma insarki ya fadi shine sarki amma zankara tunani akai zanyi shawara
da lamunde.
Anan suka nemi waje suka zauna sunata hiarsu da hirar yanda wasansu na wannan shekarar
zekaya yarda ake wasa da wuta awajen da macizai aduke tasa tulunta tana debo ruwa tanata
basu labarin saurayinta tace tana dagowa saitaga kamar wani abu na yawo asaman ruwa
tazabura ta firgice ta kwalawa tenkwai wani razanannen Kira dubamun kamar abu nake gani
asaman ruwannan menene wannan tenkwai jaruma batada tsoro zuciyarta adake take amma
akwaita da tausayi ta matsa kusa rama da aduke sai ja da baya suke tasa kafarta tashiga ruwan
tana jawowa saitaga wani abu tasaki wata razananniyar kara wadda ta furgitasu gaba dayansu
suka zura da gudu sukabarta a wajan tana maida wani irin numfashi saboda bata taba ganin
irinsaba tunda take a rayuwarta.
Shin me tenkwai taganine daya furgitata kubiyoni a page nagaba.
*Feedyn bash*
[9/11, 22:29] +234 810 679 5647: ?ARNAN DAJI?*
*?KAINUWA WRITERS?? ASSOCIATION??*
{United we stand and succed;our ambition is to entertain &motivate the mind of readers}
FAREEDA ABDULLAHI
10-15
NASADAUKAR DA WANNAN PAGE DIN GA MASOYA WANNA BOOK NAWA INAJIN DADIN
YADDA BOOK DINA YA KARBU GAREKU JINJINA AGAREKU MASOYA ????????????
A guje lamunde ta karasa kanta kafin ta isa micijin ya gudu tarasa yadda zatay ga tenkwai
a kasa a kwance ga wani mutum daya firgitata ta rasa yadda zatay tadinga zagaye chan ta tuna
tajanye mutumin zuwa wani surkukin chan cikin dajin tausayinsa ya ratsata ta dawo kan tenkwai
taruke ta idonta yasanja kala yay kore shar aguje ta direta tabazama dawa akwai wani masanin
micizai cikin dajin shiyasan kan dajin tana zuwa ta zube ta rushemasa da kuka durka
katemakamun diyata na tsakiyar daji maciji ya sareta katemakamun a firgice ya Mike ya dakko
jakar maganinsa ta fata ya biyo bayansa suna zuwa yana kallonta yace wannan kububuwace
waddata addabi mutannen Bata taba saran wani be mutuba itama wannnan diya taki ba saranta
tayiba hucintane amma yanzu zan mata magani ya dukufa nan da nan cikin sa a tadawo
hayyacinta lamunde tadinga zabga masa godiya ya tashi ya koma dawa jiki b kwari yana ina
lamunde yana ina kitemakamun munemoshi mutemakeshi banaso suganshi sukamashi
lamunde ta toshe mata baki nina noyeshi Dan kar me magani yaganshi tashi muje mu dakko shi
takamata suka mike da kyar take tsaiwa amma haka ta karfafi jikinta suka nitsa dawa lamunde
ta dagashi dakyar tenkwai ta temaka mata suka fara tafiya saboda gari harya fara haske
Ana idar da sallah ta kwalawa me aikinta Kira ke maryama zonan aguje tafito saboda
masifar tsoronta datake zan fita asra da ansar basu tashi ba idansun tashi ki kula dasu ki hada
musu abinci ki shiryasu su tafi makaranta ni natafi tasa Kai tabar gidan oh ko ina zata da duku
duku haka Allah ya kyauta ita mijinta ya Bata amma ko ajikinta wani farin cikima takeyi tasa Kai
ta koma dakinta a guje take tukin kamar zata tashi Sama tana zuwa kofar gidansu afra tadinga
danna mata horn takirata kefa nake jira gani nan jarababbiya uwar rashin hakuri fitowa zanyi
tana fitowa ta shiga gaban motar kawata baki da hakuri da rayuwa duk wannan abun da kikai
be ishekiba sai kin hada da boka yazama dole kodan muci kudi hankalinmu kwance amma da
suhail ya tara kudi iya kudi yahanamu mu wala bayasan yabarni naje wasu kasashen shi kawai
sai wata saudia nagaji da zuwa sai Egypt itama sai dai banda lafiya suko yara kina kallo sai dai
akaisu jidda inaso inzama big madam yaki yanzu ay kinga yaywa kansa yana barzahu mukuma
muci kudi mi wadaka muje kasar damukeso mu wataya hhhhhhh suka kyalkyale da dariya kina
wutaaa wallahi inabinki da gas chewar afra sai wajen goma suka shiga garin zariya saboda sun
hadu da cinkoso a hanya nan suka dauke hanyar makarfi suka nutsa cikin wani daji suka tsaya
inda mota take tsayawa nan suka fara tafiyar kafa suna hawa dutsuna suna sauka saida sukai
tafiyar awa guda sannan sukazo bakin wata katuwar tsamiya nan sukaji wani amo mara dadin
saurara nan aka kyalkyale dawata mahaukaciyar dariya muguwa Yar gidan muguwa kinyo gado
gado ba karambaniba naga komeke tafe dake abu guda dayane tsofaffinnan bazasu manta da
dansuba bazasu dena masa addu a ba abu daya za'ay zamu cire musu tunaninki aransu
bazasu kara zuwa wajenkiba bazasu karayi miki maganarsuba Amma sai kin maida musu da
yayansa shi kuma kaninki angama dashi ga wannan kije tsakar rana karfe daya kidinga turare
kina ambatar sunansu tsawon kwana uku to boka ga wannan a asiyawa aljanu shanu su sha jini
ta ajiye bandir din yan dubu dubu guda goma hhhhhhh kufita da rarrafe aka daka musu tsawa
da rarrafe suka taho suna tahowa sunzo dai dai wani dutse suka hada ido da ita suka zubaa
mata ido cikin tsananin mamaki a matukar razane ta kallesu.
(Anan zan dakata fans sainaji ra ayoyinku yawan comment dinku shike kara mun karfin gwiywa
cigaba da rubuta wannan littafin nice taku a Koda yaushe )
*Feedyn bash*
[9/11, 22:29] +234 810 679 5647: ?ARNAN DAJI?*
*?KAINUWA WRITERS?? ASSOCIATION??*
(United we stand and succed;our ambition is to entertain &motivate the mind of readers)
FAREEDA ABDULLAHI
5-10
Cikin firgici ta kara kallonsa taganshi kwance lankwam cikin ruwa Bata taba ganin mutum me
kyau irinsaba tabbas wannan badan yankinsu bane ruwane ya kodashi nan gabar to amma
kamar fa be mutuba tasa iya karfinta tajawoshi saitaga kansa a fashe yanata zubar da jini tasa
kunnenta akan kirjinsa taji yana numfashi ta jawoshi gefe taboyeshi abayan bishiya yadda ba
wanda zeganshi ta shiga daji tadebo ganyayyaki na tsaida jini tasa a wajen dayay rami ta dinga
danna cikinsa ruwa yanata fitowa ta hanci ta baki amma be farfadoba yanata dai attishawa,
Da gudu aduke tashiga gidan tana Kiran lamunde yau mushiga tara badu ya temakemu tenkwai
tana bakin ruwa tayi gamo lamunde ta dora hannu ta dinga runtuma ihu Kira take badu
katemakeni ka kubutarmun da yata ita kadaice dani banda kowa banda komi sai ita kadai badu
ka kawon temako rama kuwa tuni tagarzaya gidan sarki tana zuwa abakin shiga tagamu da ja e
tazube tana haki fadi take jinjina gareka magajin kaho badu ya temakeka tenkwai na bakin ruwa
tayi gamo inaga zuwa yanzu ba tenkwai kaimun aikin gafara sarkin gobe yana jin wannan
magana ya mike a zabure ya saki wani ashar nan da nan ya kira fadawa suka dunguma sai daji
suna bakin ruwa suna tafe sunata zage zage.
Tana zaune ta dora kansa akan cinyarta tajiyo kamar hayaniya daga chan nesa da sauri ta tashi
tajashi chan chiki wajen wata bishiya tayi nesa da bakin ruwan tay maza tadawo bakin ruwa
tana fitowa suka karaso ja'e ya kalleta ta kalleshi yace inayake meyasameki a gigice yake
tambayarta tace ba komai naga jini a jikinki meyasamekine me kike boyemun bakomai
nagayama wani dabbace tafito daga ruwa Amma na kasheta ba abunda yasameni kintabbata
tace hakane yadakawa fadawan wata mahaukaciyar tsawa yace Kai kuduba lungu da sako
kuga bawani abu nacutarwa anan nanda Nan suka bazu cikin dajin da gefen koshin suna lalube
hankalinta yay masifar tashi dataga daya ya durfafi wajen data boye shi tadinga addu ar badu
yatemaketa har ya kusa zuwa wajen ja'e yakwalo masa Kira yace kai kuzo mutay ku dakko
wayan nan tulunan dukansu yasata agaba sai wayensa take suna tafe ja'e yanata mata hira
Amma Sam hankalinta baya kansa yace ki amince dani bikin shekarar bana tunda yakusa a
daura mana aure mutum daya ake nema daga nan zuwa wata biyu masu zuwa za agabatar da
bikin ki amince dani ina Sam Bata San meyake cewaba hankalinta yana kan wannan mutum
data tsinta abakin ruwa tana fatan karya farka ya shigo gari akamashi tunda dama mutum daya
ake nema hankalinta yatashi gashi ba a shiga wannan dajin da daddare yanzu yazatay meye
mafita sai da ya tabota sannan rayi firgigit Koda wata matsalane a a ko tunanin aurenmu kike
tay yake yace karki daga hankalinki duk wata wahala ni zan dauke miki ita baku da matsala
tace kabari zanyi magana da lamunde yadda mukayi zangayama ya bata rai ita zata zauna dani
toko kinasona ko bakyaso kishirya aure a wannan shekarar nagaji da binki danake kina mun
wasa kinsanni kinsan halina nine magajin garin nan Dan haka dole na samu abunda nakeso
ban taba nema abu na rasaba bazan Fara akankiba nagaya miki dankinga inasanki a fusace ta
juyo ta kalleshi tsakar ido saboda bata da tsoro tace bance bazan aurekaba amma baka isa
kaimun dole ba sai nayi shawara Dan ba a karkashin kanakeba balle kaimun zalincinka daka
saba ransa a matukar bace yace ni kike gayawa haka ya daga hannu ze mareta tarike hannun
tace karka Fara Danni ba sakarya bace tawuce tabarshi rai bace.
Laminde na zaune kawai taga tankwai ta shigo kamar anjehota tana huci da gudu lamunde
taringumeta tana kuka tace akacemun wani abu ya kamaki a bakin ruwa ki kwantar da
hankalinki ba abunda yasameni ina cikin kwanciyar hankalina duk inda nake badu yana tare
dani kawai tsorone irin nasu aduke tace nifa nagafa abun asaman ruwa amma kice ba komai
dagaske nake gaya miki banga komai ba kawai wata dabbace a ruwa kuma na kasheta ku
kwantar da hankalinku ga shi chan ankai muku tulunanku gida maza kuje kar anemeku nagode
maku.
Way lafiyarki tunda kika dawo kin kasa magana ki zubawa waje guda idanu ko dai kinyi
gamone tenkwai dakefa nake magana lafiyarki kuwa ta girgizata sannan ta dawo hayyacinta
laminde ke babatace bazan iya boye mikiba na tsinci wani mutum a cikin ruwa na boyeshi a
cikin daji banasan wani abu yasameshi saboda ba irinmu bane ba dan nan garin bane idansuka
ganshi zasu kasheshi yabani tausayi kitashi mu shiga daji mu dakko shi heyyy tenkwai meyake
damunkine kinfi kowa sanin gagarimar matsalar dake cikin dajin shin way ma waye shine kinsan
idan aka kamamu munshiga tara wajen sarki kaho kawai kibarshi har y tashi achan tunda
kintemakeshi ya koma inda yafito ta cikin ruwa tun kafin yan gari su farga dashi su cimmasa
lamunde haka baze yiwuba inajin tausayinsa Dole muje mutemakeshi to kobari da duku duku
kafin gari ya idda wayewa sai mu tay muzo dashi Amma inajin tsoro sosai karki damu lamunde
ba abinda zefaru inajin hakan a jikina cewar tenkwai.
Momy momy ina daddy na yau kwana biyar banganshiga kince zedawo daddy beta Mana
haka ba ko baya kasar nan yana kirana Kuma har yanzu kince ze dawo wallahi asra zanci
ubanki yana chan yayi tafiyarsa yawon iskancinsa zaki dameni matsa kiban waje karna
hambareki asra tasa kuka takama hannun ansar kaninta suka shige dakinsu sunata kuka da
begen daddynsu kai tsaye ya sawo kai cikin falon yana wani mugun wari na Yan maye cike da
maye ya kalleta komai ya kammala kimanin kwana biyar mun batar dashi daga doron kasa mu
kasheshi mun cilla gawarsa cikin ruwa hhhhhh ya sheke d wata mahaukaciyar dariya dan haka
kibamu rabonmu nida abokaina a wulakance ta kalleshi kai yahuza nifa yayarkace baka da
mutunci wlh Dan kunmun wannan Dan karamin aikin sai na biyaku a wajenku wannan ba komai
bane Kuma kasan idan wayannan tsinannun iyayen nasa sukaga nafara wadaka da kudi zasu
dago wani abu kanagani sun kasa tsaye sun kasa zaune neman mafita kawai suke naji labarin
angano motarsa a bakin titi inda kuka daukeshi dazu al ameen kaninsa yazo yake gayan shima
zasu tsananta binkice akansa sunata addu a kasansu kabari ba yanzuba sai komai ya lafa sun
hakura ke kin isa cewar yahuza wallahi Jeddah kinyi kadan koki bani ko yanzu ki bishi inda yaje
ba mijinki bane ba dukiyarku bace dallah malama bani ko yanzu na farke miki ciki kiga Yan
hanjinki a waje na dibi abinda zan diba Jeddah jiki na rawa tace baya ajiye kudi a gida kasani
kudin gidan duka bazasufi dala dari biyu b to wallahi sai dai ki hadon da sarkokin ki masiyar
shegiya me rowar tsiya uwarkima ba Bata kike ba duk da itama shegiyar ita take daure Mana
gindi (wa iyazubillah fans kunji fa uwa dakanta Allah Kai mana kyakykyawan karshe kabamu
iyaye nagari) bare mu kannenki ke kanki kin mallaki dukiya me tarin yawa saboda mijinki ya
sakar miki komai Amma saboda San zuciya irin naku keda uwarki duk da mora mata kikeba
kuka yanke masa wannan hukuncin kuma Ni kinsan dole a biyamu wlh tashi ki dakkon kudi
yadaka mata tsawa da gudu tashiga daki ta hado duka sarkokinta ta dakko masa duka kudin
dabatasan adadinsuba Amma daloline Dan tasan halin yahuza bashi da imani kanintane cikinsu
daya amma besan wani abu way shi tausayi ba tana kawo masa ya sheke da dariya yace
shegiyar kaya ganin kabari mesa a tuna Allah ya warce ya kara gaba yana fadin zan dawo Dan
ba wannan ne kawai kasonaba yana fita talalubo wayarta ta dakowa kawarta Kira tana dagawa
tace afra kina ina maza maza kizo muje wajen boka akwai matsala wannan shegen yaron
yahuza zeban matsala da wayannan dattijawan iyayyen na suhail wallahi basu isaba maza kizo
haba Jeddah la'asar fa tayi koso kike sai dare zamu isa kiyi hakuri zuwa asuba sai kibiyo
kidaukeni kinsan hanyar Bata da kyau shikenan amma Dan Allah ki shirya da wuri bamatsala
sai goben nagode
Tenkwai kwance tana ta juyi takasa bacci kawai hoton wannan mutumin take gani tunda take
Bata taba ganin mutum me kyansaba ya burgeta yanada kyau me daukan hankali ita tunda take
Bata taba ganin mutum me kyansaba wacece tenkwai yace awajen lamunde da aska mahaifinta
ya rasu tun tana shekara tara ita kadaice wajensu lamunde ba wata kyakykyawa bace ta tashin
hankali tanada dai kyanta dai dai nata sai dai fa akwai dukiyar fulani ga maka makan maxaunai
ga hips Kai abundai ba a magana idan tana tafiya Dole ka shagala da kallonta saboda
takuntama abun kallone tana taku day sai jikinta yay wata girgiza me tadawa maza hankali kaf
garin kuguru ba wata matashiya budurwa me diri irin nata sai dai afita kyan fuska gata da kyan
hali uwa uba nutsuwa da tarbiyya kamar ba mutuniyar daji ba tana da tarin masoya saboda
Allah yay mata farin jinin samari duk cikinsu b wanda take kulawa sai gashi Dan sarki kaho ja e
yana nemanta shiyasa kowa ya janye sabod masifar tsoronsu da akeji a gari bashi da imani ze
iya sawa a fillema Kai baruwansa tayi juyi takasa bacci kawai burinta gari ya waye lamunde tayi
juyi