Showing 39001 words to 42000 words out of 46340 words

Chapter 14 - ARNAN DAJI Book 1 By Feedeen Bash.pdf

addu ata agareta haske ya
haskaka rayuwarta zuciyarta a cunkushe Jin an amabaci wadda tafi tsana naji lamunde ya jikin
naji sauki ya mijin naki Yana nan nibanda miji zaman daukar fansa nake Amma nafasa saboda
makiyana su Sha haushi ta fada tana hararar waje



Murmushi kawai lamunde Tai Ina iya Kuna zaune kalau dai kowa lafiya da kyar ta kalleta idonta
ya ciko da kwalla Ina mado tunda ya tafi ban sake sa shi a idonaba cike da kuka abunda ya
kawoni kenan lamunde Inasan mado kunsani gabanta ya shiga faduwa haryanzu baki hakura

da shiba kiyi hakuri kizauna a dakin ki kawai kuka tasa na rantse da KABARIN babana bazan
yarda ya auri Rama ba Dan ita yakeso ya aura sai dai duk mu mutu Bata karasa ta lura iya tafita
daga hankalin ta numfashinta ya tsaya cak ta kwalla Kara



Da gudu Rama ta shigo taga lamunde a sankame ta shake Tenkwai me kikai Mata tadinga
zabga Mata Mari Bata taba sanin Rama nada karfi hakaba sai yau me kikai mata idanke bakya
San rayuwarta mu muna bukata muna kallon ta amatsayin uwa agaremu Nan itama ta shake ta
fada ya kaure kowa cike da Jin haushin kowa a haka Aduke ta rarafo tagansu ku kashe kanku ki
huta akan namiji kafin ki kashe kanku bara na Fara kashe kaina Ni ta daga wuka ta daba dai dai
kahon zuciyarta suka fasa wata Kara dukansu sukai kanta



Tofa ga lamunde a kwance ga Tenkwai da Rama na Bala I kan mado ga Aduke zata kashe
kanta




Suhail ne ya Kira jeddah leko gani kofar gidanku tuntsire da dariya bayan ta ajiye wayar ba Dole
ba na daga maka hankali nasan Dole kadawo Kuma bazan Bari kasha minti ba sai dai na
kwakuleka nabarka fanko (tofa dama mace na kwakule namiji)ta fito tana kwarkwasa ransa ya
biya Amma ya basar ta karaso ta kwanta a kirjinsa ya tureta ranta ya baci Bata hakuraba ta
hada fuskarsu gu daya ya janye kasan zuciyarsa tsanarta yakeji Amma wannan tasirin maganin
ya Hana ya aiwatar da komai ko ya gane tsanace ya bada dubu dari biyar ki turon account
number dinka zanmiki transfer



Kigayawa umma tasanar zasuje a wannan satin adamawa Kai komai na aure sati biyu masu
zuwa biki Dan haka karku takurawa kanku da komai komai akwai ko tsinke bana bukata sai ke
ya dankamata kudin ransa a hade kiyi lissafi duk abunda kike bukata na fanninki Ni dinner
kawai zanyi gaba dayanku keda haleema zaku halarta ranta idan yai dubu ya baci batace komai
ba yayi Mata sallama tana tsaye ta kasa cewa komai yaja motarsa ya tafi ransa Kal shima ya
Bata Mata ya Rama taje tajika jikinta muguntar datai masa Kuma Allah ya isa



Da gudu ta shige gida tasa kuka menene umma tafito ta kwashe komai tagaya Mata mtsww
lefinkine akanme Dan bakin ciki ke kin kawo shi kihanasa kawowa sai ki shirya kinwa kanki ki
Masa list din million biyu zakice ya baki baki ta tabe ta wuce daki ranta a bace ta Kira afra kizo

Inasan ganinki akwai matsala ke nasamo Mana wani boka me gani har hanji heeyy suka saki
shewa suka dinga ihu Amma kibari sai gobe zanzo Ina gida yau



Washe gari alhamis saiga afra da wuri Nan suka hau lissafi faty na kala bakwai za ai harda na
dare harda Wanda za ai a club Abu kala kala za a lalace a wannan bikin hankali kwance ta tura
Masa account number dinta ya kirata naga sako nawa 2 million ok kawai yace ya kashe Bata
Gama rufe bakiba taji alert a haukace suka mike suka dinga tikar rawa 3 million ya turo kamar
zasu Suma Dan Dadi



Muwuce wajen boka kawai a a gsky ki Bari sai min dawo daga adamawa zanje nasami baba
Dole yai hakuri mu wuce harke suka saki wata shewa muje kasuwa miyi siyayya komai da za a
bukata na kawo kefe kar a arainamu suka mike ta bawa umma dubu dari biyu tarike a hannunta
jikinta har rawa yake sai guda take saki suna Tai Mata dariya suka fice


Ankai Kaya ko wane bangare akwari goma Sha biyu aka kaiwa ko wacce ba bangaren da aka
samu matsala ko Ina anyi komai a mutunce ango ya shiga busy haka amare ita haleema ba
abunda zatai sai dai bayan anakaita zatai waleema Jeddah ko ba sauki Dan gudun mawa ta
karbeta a gun samarinta tasamu kudi na tashin hankali magani kullum anemansa take Amma
tana sawa idan yayi kamar ya matse sai gaban ta koma ya saki




ANAN ZAN DAKATA SAI NAJI COMMENT DINKU GASKIYA BAKWA COMMENT SOSAI KO
YADENA DADINE NADENA TYPING????




NICE TAKU AKODA YAUSHE ME KAUNARKU MESAN FARIN CIKIN KU





*FEEDYN BASH*
[9/11, 22:29] +234 810 679 5647: *?ARNAN DAJI?*

*NA*


*FAREEDA ABDULLAHI*




*_?KAINUWA WRITERS?? ASSOCIATION_*??
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




*WANNAN PAGE DIN FANS DINA MASU YIMUN COMMENT WANDA YAJI SUNANSA DA
WANDA BEJIBA INDAI KANA COMMENT TOKASA ARANKA NAKANE KAYI YADDA KAKESO
DASHI NAKUNE*


MUHSEENAT
ZYNABA
K,SDK
NURSE IKRAM
UMMU ABDALLAH
MOM ARFAT
UMMU SHUREIM
QUEEN MEENERLY
UMMU HANAN
*DASAURANSU KUNADA YAWA DAN ALLAH KUYI HAKURI KUNSAN BAZE YIWU DUK
MASU MUN COMMENT SAI NA SASUBA SABIDA ABUN DAYAWA DAN ALLAH KUDENA
KORAFI SISTER ANA TARE FA INA YINKU IYA WUYA*




*BISSIMILLAHIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JIN KAI GODIYA TA TABBATA
GA ALLAH (S.W.T)*

*INA MIKA GODIYA GA MASOYANA AKO INA SUKE INAJIN DADIN YADDA KUKE KARANTA
BOOK DINA NAGODE*









115-120




Suna fitowa ya hango Jeddah dunkuke tana ta sharar kwalla ta fiffisge kwalliyar har tuntube
yake ya karasa gunta wani magana dison Santa najansa Yana zuwa ya kamota ta fisge
haleema naganin haka ta kyalkyale da dariya ta shige motar abokin suhail mutafi jafar bazan ga
bacin Rai ba yaja suka tafi hankalinta kwance


Da kyar ya lallabata ta taso dakansa yaja motar besaurari kowaba sai da sukaje yai Mata
shopping sai Sha biyu da rabi ya maidata gida ta kalallame shi da zance sharri faruk yai Mata
Dan tace Bata sansa bazata aure Shiba yai Mata haka yadinga lallashinta Yana Bata hakuri
ransa Banda tafasa ba abunda yake idonsa idon faruk Allah kadai yasan meze faru


Yana ajiyeta yai gida ya Danna Kai get din gidan su faruk a fusace ya nufi dakinsa to shi bacci
ma yake hankali kwance dake yanada key din side din faruk din ya bude ya shiga ya tarar Yana
bacci cikin bacin Rai ya dakko ruwa me sanyi ya tsilalamasa gashi garin da sanyi a firgice ya
farka jikinsa na kyarma


Suhail ya gani Rai bace shima sai ya tamke fuska lafiya malam zaka shigomun daki harka
zuban ruwan sanyi lafiyarce ta kawo haka wato bakin ciki kakemun shiyasa kaje zaka
tarwatsamun taro to ta Allah ba takaba Kuma Jeddah tawace baka Isa ka rabamu ba har abada

Dan takika ta Soni kake jifanta da miyagun kalamai harda sharrin bariki to ahir Dinka kafita
hanyar iyalina



Ya sheke da dariya baka da hankali suhail kasan duk macen dazaka ganni da ita farat daya Yar
hannuce wallahi ba haka wannan tsinanniyar ta barka me sadiya mezeyi da wacchan jakar stop
ya fada da karfi jikinsa har rawa yake karka Kara fada Mata wannan kalmar nafada Kuma
wallahi ko kanaso ko bakaso sai anyi gwajin jini natabbatar ita ta birkita ka rannan kazo zaka
mace Mana saboda Sha awa



Jikinsa Kuma sai yai sanyi Amma tasirin asiri baze barshi ya fuskanci komai ba naji Ni naji
nagani Dan haka ka fita hanyar iyalina ya kyalkyale da dariya zan fita Amma sai anje anyi
gwajin jini tukun naji za aje Dan Allah karka gayawa hajiya komai kuma saina baka mamaki duk
matana sainayi irin abunda sai na sawa kowacce farin kyalle Dan kaji kunya tunda kazubarmun
da mutunci wajen abokanmu



Ya kyalkyale da dariya Amma nayi murna za asha haushi hajiya ko ai ta Dade da sani kasan ko
bangayamata ba Dole labari zeje kunnenta abunda naiwa jakar chan Kuma tasan naje Dan
Dana dawo naje nagaya Mata komai Kuma tasamun albarka ya kyalkyale da dariya in wuta
suhail ya jefa faruk Yana huci ya dakumo shi idanunsa sunyi jajur


Narantse wani Abu ya samu aurena da Jeddah na yanke duk wata alakata dakai kabar ganin
tare muka tashi komai namu tare na rabu dakai har abada akan jeddah ya cika shi ya fice Yana
huci ko motarsa be tsaya daukaba anan ya barta da kafa ya karasa gidan abun mamaki mutane
Yan biki kamar Rana suna ta hayaniya agidan yai tsaki ya wuce daki Kota kan haleema bebi ba
Yama manta da ita tunda suka hada jiki da jeddah



Hankalinsa a tashe yai wanka yai brush ya kwanta barci me nauyi ya dauke shi makara yai
sallar asuba da kyar ya tashi yai sallah ya Fara shiri saboda yau take daurin aure faruk ne ya
shigo ya wulla Masa key din motarsa naji nagode da abunda kaimun jiya mace ta SHIGA
tsakaninmu ta rabamu kamar yadda kace Ni nafita daga rayuwarka nabarka da matarka zan
koma Istanbul zanyi PhD Dina nagode da zaman da mukai tare na tabbata wata Rana zaka
tuna nagayama GASKIYA

Ya fice jikin suhail yai sanyi akan wannan maganar zebar kasar Amma ya kasa dakatar dashi
aransa yanaji ze iya hakura yabar Masa Jeddah Dan yasan be kyautawa abokinsa ba shiya
Fara Santa daga gaisuwa sai ya kwace Masa ita guri yanema ya zauna jabar cike da Jin nauyin
aminin nasa borin kunya kawai naima nasani Umar sarkin zuciya nasan bazaka saurareniba sai
ka huce Yana wannan tunanin jafar ya shigo kai fa muke jira yai turus daya ganshi a haka lafiya
kake zaune haka



Yai firgigit yai murmushi ya Mike yasa kayansa yayi mugun haduwa dama ga kyau wow Masha
Allah Kai sauri kasan a masallaci daya za a daura ancika iya cika jiki a sanyaye suka fita gaba
daya hankalinsa baya jikinsa abun mamaki faruk ya hango Yana jiransa ya saki murmushi ya
shiga yaja suka tafi Amma yasha kunu ba Wasa


An daura auren haleema da suhail Jeddah da suhail ko wacce akan sadaki dubu dari biyar waje
ya cika yai makil bikin Dan gidan gadon kudi damma matan bawasu yayan manya bane ba
yadda abokan mahaifinsa basiba yaje yaga Yaya yensu ai gashi ya bige da auren yayan
talakawa amma suna bakin ciki daba Yaya yensu bane zasu shiga gidan gadon kudi ba


Anyi reception me kayatarwa anci ansha cikin farinciki jeddah Ina ruwa Tasha tasan itace
uwargida Dole a gidan suhail tana tunanin irin mulkin dazata shimfida da yadda zataci uwar
haleema da kafarta ta gudu base wani ya koretaba tunda tanada sanin suhail yazama nata Dan
tasan asirin datai yafara kamasa tun dazu yake Mata waya ta shirya adakkota Amma Taki sai
dare akanme sai kace wata Mara class



Bangaren haleema Yan daurin aure na dawowa aka Fara Shirin Kai amarya Nan aka farai Mata
fada iyaye da Yan UWA kowa da abunda yake fada rabi duk nasihace ba abunda take sai kuka
dakyar aka bambareta daga jikin mamanta Kuka suke dukansu ita kadaice yarta a duniya tana
Haifa suke mutuwa haleema ce kawai ta rayu tasami tarbiyya sun shaku da kyar aka bambareta
daga jikinta




babanta da kansa ya dauketa a motarsa wadda suhail ya bashi da Yan rakiya gwaggon ninta

sukaje aka kaiwa hajiyar suhail Tai Mata fada me shiga jiki da ratsa zuciya tabata addu oi ita
haka kawai take kaunar yarinyar saboda tarbiyyar ta gata yarinya karama tana tausaya Mata
Zama da kishiya irin wadda faruk yagaya Mata ita tasan ba banza ba take kin yarinyar tace tayi
hakuri kafin Yan walima suzo tunda a gidan tace zatai walima nayi murna daxakije a uwargida
Allah yasa kija girmanki akai addu oi aka dakko ta sai gidanta



Tsayawa Gaya muku girman gidan sai nacika page guda bangarenta aka kaita akace ta shiga
da addu a da addu oi a bakinta ta shiga da kafar dama wani Ni imtaccen kamshi ya bigeta dakin
da babanta yai Mata aka kaita gadone royal da kujeru a falon komai ash ne da silver a dakin
komai na burgewa ya sata Mata ancika Mata daki da Kaya bangaren suhail ko yadda yai wa
bangaren Jeddah komai iri daya zuba musu sai bambanci kala kowa side dinsa daban side
dinsa a tsakiya ko wacce ta side dinta zata gangaro nasa idan tana bukata



Ja'e ne ya shigo meze gani iya rungume da Tenkwai tanata kuka da gudu ya cincibeta sai gidan
me magani shikansa kuka yake karki tafi ki barni Tenkwai kece rayuwata ke kadai nakeso karki
mun haka yanata kuka ya Karasa gidan me magani Nan da Nan yafara cire Mata dafin yakushin
masu Shan jini ne sukaso shanye nata sunzuba Mata dafin kayi gaggawar kawota da wuri da
jininta ya tsotse duka



Kuka kawai yake da gudu aka garzayo Kiran me magani daga gidan Ja'e amarya ba lafiya sai
sukaga Ja'e suka gaya Masa anga amarya na murkususu a waje cikinta da kibiya me mugun
dafi jinkinta duk a fashe da gudu ya bisu suka rankaya Dame maganin tunda Tenkwai tasamu
yasa Mata magani bacci take Dan Ja'e yanasan amaryar sa ba lefi ta iya soyayya


Suna zuwa suka Tarar harta mutu Ja'e ya fada kan gawarta yanata kuka sai ga Yan kungiyarsu
suna zuwa suka Fara ihu shugabarsu ta mutu dayar tace saida nagaya Mata ta kyale Tenkwai
tafi karfinta karta Sha jininta Amma Taki ji gashi ta kasheta Nan suka dinga tonawa kansu asiri
kowa Yana mamaki a wajen Ja'e ya tashi cike da tsanarsu duka har amarya sai yanzu yasan cin
naman mutane ba karamin Bala I bane



Gashi har wata kungiya sukayi Ashe harda matar sa ake Shan jini itacema shugabarsu duk
matansa ta cinyesu kaho be musu adalciba shida badu gashi suna cikin halin tashin hankali
yaza ai ahana mutane cin naman Yan uwansu besan hakan nada illaba sai da akazo kan

Tenkwai hhhhh



Rai bace yasa aka damkesu gaba dayan su yace aje a kullesu sai ya gama yanke hukuncin
daza ai musu yace kowa ya tafi yasa aka dauki gawar amarya ransa ba Dadi akaje aka yarda
kamar yadda aka Saba kafin kace meye wannan zance ya baza gari dama garin ba wani girma
ba kowa Yana tofa albarkacin bakinsa


Mutane ko sai tururuwa suke wajen duba Tenkwai dai ta kawo karshen wayannan masu shan
jinin mutane wayanda basa Bari fita da daddare ga sabon sauyi daga Ja'e sunsan duk itace ta
Hana shi kashe mutane da cin namansu suna sa ran tahana muguwar dabi ar cinye musu jarirai
Dan ransu na Kuna basaso


Duk wannan abun yajewa badu yayi rantsuwa sai Ja'e ya rabu da Tenkwai Dan ita tasanja Masa
tsarin da baze yarda ba Dole ya rabu da ita baze iyaba dansa jal Wanda ze gaji sarautar garin
kuguru ace Yana tsoron mace ze sa rabu da ita ya aika har gida akashe su dukansu Dan zasu
bashi matsala wata Rana abunda suka boye ze iya bayyana saukin ta dayama ita macece
Amma wannan zata iya kwace sarautar ta koma musu kamar da Dan haka baze yiwuba



Na rantse da badu Dole mu raba wannan auren mu kasheta da mahaifiyarta Dan ita zata Gaya
Mata cewa sune masu sarautar garin nan Dan haka Dole su mutu yadda kowa ze manta dasu
Ja'e Dole ka koma halinka nada Dan Kaine sarkin gobe a ranar bikin shekara zasu mutu
dukansu a fusace ya Mike sai sashen it's fadawa na take Masa baya

Ja'e saki wannan la ananniyar idan nine mahaifinka yasa kuka itace rayuwata itako Tenkwai
kamar yasata a aljanna duk da ciwon datakeji nemarsa Tai ta rasa cike da farinciki ta mike ta
cire komai na aure dake jikinta Nina warware shi dakaina Ja'e ya rungumeta Yana wani irin
kuka Bata taba Jin tausayin Ja'e ba sai yay wani Abu ya daki zuciyarta Wanda batasan meyeba itama ta rungumeshi tana zubar da kwalla



Sabo kenan tirken Wawa kullum suna tare su kwana tare su tashi tare tabbas Ja'e nasanta karki
tafi kibarni Tenkwai ta kinsan kece rayuwata kayi hakuri idan da rabo zan dawo gareka Amma
bazan zaunaba a yanzu zanje na jarraba sa a ta kozan samu abunda nakeso Jin haka jikin

kaho ya Fara rawa kajiko sarauta takeso la ananniya bazakiba har abada sai kin mutu besan
sanda yake wannan furucin ba ta dago ta kalleshi



Kaho kake kowa meye hadina da sarautar ka Kuma niba Yar sarauta ba Dan haka karna karajin
ka Fadi haka akwai Wanda nakeso ba danka ba idan narasa shi zan zauna da danka Dan
nasan Yana Sona cike da rashin tsoro take magana ya hango tsantsar rashin tsoro da jarumta a
idon ta tamkar mahaifinta iya ko kuka take kowa kuka yake sunaji suna gani ta fice Ja'e ya
yanke jiki ya Fadi kaho yai kansa a sukwane




*TO MAKARANTA ANAN ZAN DAKATA SAI KUNJINK NICE

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login