Showing 21001 words to 24000 words out of 46340 words
Chapter 8 - ARNAN DAJI Book 1 By Feedeen Bash.pdf
gashi duk Wanda yay magana a cikin su sai ta
daga Masa hannu Bana bukatar tambayar kowa a yanzu Amma kamar yadda nai alkawari gaba
dayanku ku taru ranar zan Baku tarihin mu Nan da wata biyu masu zuwa kowa yai shiru an rasa
me magana
Nayarda ki auri Ja'e Amma kamar yadda iyar sa ta fada Ina bukatar zamanki a sashen ta Dan
nasan baza ta taba Bari ya cutar min dake ba kuta shi kuje kuduba Mara lafiya suka mike suka
koma dakin da Mara lafiyar yake duk yana jin meke faruwa a waje ya Kura musu ido yana binsu
da kallo daya bayan daya
Iyar Ja'e ce ta shigo dakin mado kowa yay shiru ta karasa kusa da shi sunan ka mado kasamu
rashin lafiya ne Amma Kai bawana ne a gidan sarki Ni matar sarki ce Babar dansa Ja'e magajin
garin Nan a sashina kake Dan haka ka shirya komawa bakin aikin ka zan sanar wa da matarka
da danka rashin lafiyar ka bansan inda kasamo wannan kayan ba ba irin namu bane Dan haka
yadda kaga shigar mu take Kai ma taka zata koma haka kana da kyan jiki da wuri zaka warke
Yai Mata shiru yana ta tunani tabbas yanada Mata da da Amma kamar ba a Nan suke ba ba
irin wannan kayan suke sawaba Amma baze iya tunawa ba Tom shikenan Ina Mata ta da Dan
nawa inaso zan gansu zan koma wajen su har na warke Inasan su zan zauna dasu
Ranta kal tace suna gida kabari kaji kwari Nan da kwana biyu saika koma Amma zan dawo
gobe na dubaka naga ya jikin naka yake sai na taho ma da kayan naka kasa a jikin ka muba ma
amfani da wannan inda kasamu lalurar ne suka sama Amma mu da wannan mike amfani bana
so kasanarwa da kowa kowa ya tambayeka kar kace komai Koda ko matar kace kar kace nice
nasa aka Fara dubaka
Gaba dayan su mutuwar zaune sukai jin wannan batu kamar almara me take nufi zata tafi dashi
su cinye kenan hankali tashe tenkwai ta bude baki zata Fara magana ta daga Mata hannu muje
Inasan magana daku ta fice suka bi bayanta suka shiga dakin lamunde har da aduke data ke
takawa da kyar ta dinga basu hakuri su rufa Mata asiri su rufe wannan sirrin ta zayyane musu
duk Shirin ta jikin su yai sanyi da wannan tunani nata tabbas suna Kama da mado ba me
ganewa idan aka turashi tunda Suma wasu na tirin baza a ganeba Kuma wannan ce kawai
hanya daza a tseratar da rayuwarsa
Rama tace iyar Ja'e na Miki alkawarin zan tira shi kafin ranar daze koma wajen ki nayi alkawarin
kula da lafiyarsa har ya warke kafin tunanin sa ya dawo bazan janye ba ki dauke Ni matsayin
me kula dashi yadda matar mado bazata zargi wani Abu ba bare har asirin ki ya tonu
Cike da farinciki iyar Ja'e tace tabbas kinyi gaskiya naji Dadi da kuka fahimceni kinga kema
baze Miki nisa ba ta dubi tenkwai duk San da kike son ganin sa zaki gan shi tunda bayina Ni a
bangarena suke banasan siyi nisa dani a Daren yau mado Dole ze bar gari duk da hatsarin
dake tattare da tafiyar say Amma Dole yase da ransa bamu San me wannan mutum yazo dashi
ba bamusan alherin dake tare dashi ba sai ya warke
Cike da farinciki ta baro gidan tana zuwa kofar shiga gidan wazata gani sarki kaho fuskar Nan a
tamke daga Ina kike munafika kinje wargaza auren gudan jinina ko to baki isaba in Banda kece
mahaifiyar sa da tuni nasa anbatar dake Dan nasan bakya kaunar mu nida shi zan iya kashe ki
akan Ja'e
Ta sheke da dariya kaho kenan da bakin ka kace nice mahaifiyar sa Dan haka baka Isa Kai min
shamaki da Dana ba ba tsoron kasa a kasheni nake ba zan dai gayama ne kawai Dan ra ayina
shawo kan yarinyar naje yi abun da ka kasa sai nuna Isa da iko akan Wanda ba danka ba ko
danka baka iya tankwara shi bare Dan wani kuma sai gashi Ni makiyarsa na Samo Masa
farinciki sabanin Kai masoyinsa daka kasa yarinya ta amince saboda Ni zata auri Dana Dan
haka kaga karshen kiyayya kenan
Gashi dai magana tagaya Masa Amma kamar ta sashi a aljanna Dan farin ciki tabbas ta bashi
farinciki be taba tunanin zata iya nemar wa Ja'e aure ba sai gashi ta fada karya ba dabi arta
bace balle yace ita tayi ransa Kal ya kalleta
In dai ko hakane ki Fadi duk abunda kikeso zan Miki bansan kina San gudan jinina ba sai yau
me kike bukata ai miki kinyi abunda mu muka kasayi Dole kema a faran ta Miki
Bana bukatar komai sai yarinyar ta zauna a sashena Dan haka take da bukata Ni Kuma farinciki
shine namu Dan ta Mana halacci yarinyar
Hhhhhh in dai wannan ne an Miki Ankara muku bayi Mata guda goma sannan anhada muku da
kyautar shanaye guda goma hhhhhh kin kyauta muna godiya masoyi yata a shirya yau a
bangaren ki zan kwana
Tai tsaki a ranta base kazo ba badu yaja da ranka shanu Kuma mu bazami komai dasu ba
gwara bayi kodan ita amarya Dan haka kabar shi karya kike Dole dake zan kwana yau Kuma
baki ISA nayi kyauta ki dawon da itaba
Har zatai magana ya juya ya tafi fadawan sa suka rufa masa baya wata zuciyar tace karshema
tun nakune suke ta albarka ki karba kici gaba da kula dasu harsuyi yawa kidawo da yawan
shanunku ta share kwallar data zubo Mata saboda tunawa da iyayenta tabbas sai ta dau fansa
akan sarki kaho ta juya ta nufi sashen ta
Ummata albishirin ki bukata fa ta biya suka rungume juna sunata ta murna umma harda
guda afra Bata San wainar da suke toyawa ba batasan akan me ake maganar ba tace wai farin
cikin me kuke ne abani Nima Nasha adara Dani ba a barni abaya ba Yar uwa
Cike da farinciki tace wallahi sis nayi babban kamu wannan dakika ganmu tare suhail ne Dan
gidan alhaji ibrahim gadon kudi shine ze aure Ni Nan bada dadewa ba sai ki Fara shiri daga yau
Ido waje aure Jeddah aure yanzu kinsan a tsarinmu ba aure yanzu yaushema har kukai
maganar aure dashi baki gayan ba a Ina kuka hadu baki taba gayan ba dama bazaman Amana
kike Dani ba Ni bana iya boye Miki sirrina kece ke boyen naki
Mtsww kina da matsala wlh jiya muka hadu Kuma yace yana San aurena sai anjima zezo zami
tsaida magana kinsan ba Wanda ze Fara ji sama dake Kece zaki gayawa wasu ma kece fa
Babar kawa sai yadda Kika yi Sai abunda kikace a wajen bikin Nan
Hmmm shikenan yanzu naji zance Amma aranta Bata so ba Bata so Jeddah zatai aure ta barta
ba tafiso siyi ta gantalinsu tare Dan Jeddah ita tabude Mata ido sosai gashi zata tafi tabar ta
gaskiya bata ji dadin hakan ba ita kuma gsky yanzu karatu ma takeso ta koma Dan gayen jiya
yy Mata alkawarin daukar nauyin ta
Cike da murmushi tace Tom kawata Allah yasan ya alkhairi yakaimu ranar Amma fa Dole mu
jijjige zamu jajige muja magana wannan ranar ai Dole ne kawata kema aikin ce kinyi babban
kamu jiya kema kawai ki aure shi ki huta kayya karatu zan koma gsky ayke kina da kwakwalwar
karatu sai ki ta fama Amma Ni ko London ze kaini banaso Dan kin San yanzu ba kasar daba
zan zaga ba a duniya suka sheke da dariya suka tafa
Aini saudiyya zaki Fara kaini Yar albarka in dawo inzama hajiya ai ban haifi tsiyaba arziki na
Haifa Kuma shi zan ta karba har abada kema ki dage kisamo irin na Jeddah Dan Ina alfahari
daku yayana nakai na sai umman mu suka fada cike da dariya suka mike suka koma dakin
jeddah Bari inyi bacci kafin yamma tayi Dan nayi karya a gida nace anan zan kwana nagayawa
baba kinsan kallon wata muguwar nutsatstsiya yake Miki kece kin iya badda Kama
Hhhhhh ba Dole ba ay indai ka goge da bariki Dole kasan hannunka saboda tsaro ba yadda
za'ai ka Bari manya su ganoka ai sai kasamu matsala yanzu kinga Koda anzo bincike na
hankali kwance Dan inawa tsofaffin layi ihsani
Suka Kuma kecewa da dariya shegiya Jeddah kinsan ta kan tsiya Dole a Sara Miki danga kyau
ga fari komai zam zam diri dai sai dai agani a jikin ki shape kamar ke Kika kera kanki Dole maza
sudinga ridewa Amma Dole zamuci uwar sabada a bikin ki kamar a mafarki Dan gidan gadon
kudi zaki aura chab wai garin Yaya har Kika yarda da wuri haka tagama fasa Mata kai Nan ta
zayyane Mata yadda akai tun daga farkon haduwar su har zuwansu wajen malamin
Suhail kasa tabuka komai yai faruk ne yajasu suka koma gida Dan yakasa control din kansa a
hanya Dole faruk ya karbi kan motar suna zuwa gida ya wuce yabar faruk shi Kuma ya fice da
motar ya tafi gantalinsa y a zube a daki ba abunda yake tunani sai ita surarta Amma tabbas ba
Santa yake ba to meye shibe taba yaba kyan wata ba ko surarta sai Yar jaririyar sa haleema
Tunaninta ya cika Masa kwanya Dole yaje ya ganta koya huta da wannan tunanin Kobe ce Mata
komai ba ya ganta tome ma zece Mata shida besa ba Hira da mata barkatai ba shi duk tarin
masu zuwa wajensa da masu Kiran sa basa gabansa Amma wannan ta tsaya Masa arai Dole
yaje yaganta ba shiri ya Mike ya zari wani key din motar kirar anaconda Fara Kal Tasha tintac
ya dau hanya be tsaya ko inaba sai Dan gwauro
Yama rasa mezece yajeyi shiba number dinta ce dashi ba ya dai yi shahada ya Kira wani
almajiri Dan Allah shiga kace Jeddah tazo suhail nasan ganinta zebata wani sako to wane sako
zebata shi kansa be saniba yaron ya fito tace tana zuwa ya zaro dubu guda ya bashi yaran
tsorata ya ki karba ya falfala da gudu sai yasa dariya abunma dariya ya bashi
ANAN ZAN DAKATA GASKIYA COMMENT YAI SANYI YANZU KO YADENA DADINE BOOK
DIN NICE TAKU
*FEEDYN BASH*
[9/11, 22:29] +234 810 679 5647: *?ARNAN DAJI?*
*NA*
*FAREEDA ABDULLAHI*
*_?KAINUWA WRITERS?? ASSOCIATION_*??
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA MAHAIFIYATA ALLAH YAJA KWANA YA RAYA
ZURI A*
*NASADAUKAR DA WANNAN PAGE DIN GA DUMBUN MASOYANA WANDA NASANSU DA
WANDA BANSANSUBA AKO INA SUKE INA MUSU FATAN ALKHAIRI DAFATAN UBANGIJI
YATEMAKEMU GABA DAYA YA BIYAMANA BUKATUNMU NIDA KU*
*JINJINA GA KAINUWA WRITERS ALLAH YA KARA WA ZUMA ZAKI DAN MASU SAI DA
SUGA SUSHA HAUSHI????*
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JIN KAI*
70-75
Jeddah ta dalawa afra duka tashi kawata yazo wallahi yana waje narasama wane irin
kwalliya zanyi wane irin kaya zan sa Dan na burge shi na tafi da zuciyarsa gaba daya tabbas
malam yayi gaskiya suhail yazama nawa Ni kadai
Maza tashi ki shirya kina shegen zance sai ya tafi kinsan ba karamin mutum bane cewar umma
data ke sawo Kai umma wanka zanyi ke banasan shashanci wankan ubanki zira Kaya ki gyara
fuskar ki fita afra ko ta kasa magana kawai binsu take da ido ta rasa wannan San zuciya na
umma da Jeddah ita dai Bata burin auren asiri tafi San na soyayyar gaskiya Dan shine ginshikin
rayuwa Allah ya kyauta tafada a ranta
Cikin hanzari tasa wani less me kalar ja da ratsin ash dinkin Riga da siket ya karbeta duk
halittun ta ba inda be fito ba tayi kyau na mamaki batayi wata muguwar kwalliya ba ta daura
Dan kwalinta ta fito tashiga dakin umma Nan da Nan jiki na rawa tahau bulbula Mata turaren ita
kanta jitai yana hawa Mata Kai ya isa Dan Allah umma wannan turaren ba Dadi kamar na Yan
bori Dan Allah barshi haka karya kadani
To uwar kinibibi koma na meye shige ki tafi karki Mana asara ba malam ne yace yana shakar
Saba sai dai wani bashi ba Kuma kinsan irin tsadar maganin nan maza ki wuce Yar albarka ki
shigo dashi mu gaisa ta balla Mata harara ke kin cika rawar jiki wallahi daga zuwan farko zezo
wani ki gaisa ko kunya bakya ji jibi fa yadda kike mtsww tayi ficewar ta
Ai tana dosar wajen sa yai mutuwar tsaye wani masifar kyau yaga ta kara fiye da dazu tana
zuwa kusa dashi wani kamshi ya dake shi ya dafe kansa yafi minti biyar be dago ba itama Bata
tanka ba gabanta yanata faduwa kodai zaton ya yahau Masa Kai sai taga yadago idanunsa
sunyi jajur ya kalleta tadan firgita ita kanta dataga yadda idanuwansa suka Sanja kala suka rune
Nan da Nan
Cike da kasala ya Fara magana Jeddah inasanki sai da tsigar jikin ta tashi Ina kaunarki zan
aure ki a lokaci kankani Nan kusa zan aureki ki amince min zuciyata zata fashe bazan iya jurar
kallon kiba batare da kinzama mallakina ba banasan auren mu ya wuce wata daya kiyi magana
Dan Allah kar na mutu kirjina
Kamar zata zuba ruwa a kasa Tasha Dan murna zuciyarta Kal bukatarta ta biya me Kuma zata
nema a duniya yanzu ta Gama samun duniya amma sai ta basar aure suhail aure kace fa
bayan kasan faruk ke sona Kuma cikin wata guda Ni marainiyace Banda mahaifi sai mahaifiya
mu masu karamin karfine kafi karfina kanemi dai dai dakai kawai nasan iyayenka nazasu yarda
ka auren ba
Ambatar sunan faruk datai kamar ta watsa Masa ruwan dalma a zuciyarsa saboda masifar
kishin daya yunkuro Masa Amma ya danne bakinsa har daci yake faruk ba aurene a gabansa
ba yanzu ki bani dama na nuna Miki nafi kowa sanki a duniya zan aureki cikin lokaci kankani
iyayena basu da matsa ba dukiya nakeso ba ke nakeso zaman lafiya nafi bukata sama da kudi
wane irin kudine bamu mallaka ba daza a karbe duk abunda na mallaka abani ke nafi bukatar
hakan akan komai ya wani marairaice Mata
Itako dake tasan komai ta wani basar chan tayi shiru kamar bazata Kara maganaba shikenan
suhail nizan koma ciki Amma kaje Kai shawara da iyayenka Nima zanyi danawa Amma kagaya
musu mu bamu da komai talakawane mu masu rangwamen gata Banda mahaifi sai danginsa a
adamawa ta shiga matsar kwallar farinciki shi Kuma yadauka tunawa da mahaifin tane ko Kuma
talaucin dasuke ciki ya kudiri aniyar ciresu daga kangin talaucin
Yakara narkewa a tausayin ta shike Nan zan gaya musu insha Allah cikin satin Nan za a Gama
komai atsaida Rana kigayawa mamanku tasanar da danginku zan turo ga wannan ba yawa ya
zaro rafar dubu dari ya Bata sai na dawo gobe ko kabar shi Dan Allah wallahi sai kin karba
harda rantsuwa Tom nagode besan sutafi bukataba shikenan shiga gida dama sakon kenan
yanata murmushi tashiga gida shi Kuma ya tada motar ya bar wajen
Yana tafiya yana tunanin Anya ma ko shine tayaya za ace yaje wajen wata ba haleema ba
harda maganar aure tabbas idan be auri jeddah ze iya mutuwa ita yakeso da ita ze rayu ahaka
ya karasa gida ya shiga sashen hajiyarsa yai sallama ya shiga suna tarema da alhaji ko tsoro
Babu bare fargaba aransa ya shiga falon
Yauwa naji dadin ganin ku tare hajiya dama magana ce nakeso miyi daku daddy aure nakeso
nayi cikin lokaci kankani cike da farinciki hajiya tace to candy Dinma bazaka barta tayi ba
takarasa a dakinta saura shekara daya fa tagama kayi hakuri Mana suhail bansan ka da wutar
ciki ba alhaji ma yai dariya kabari takarasa mana ko babban mutum ko dai kafara matsuwane
ya fada cike da murmushi
Yai shiru ya numfasa hajiya ba haleema bace wata ce daban wannan mun hadu da ita a wajen
bikin abokina Inasan ta sosai Amma talakawane shine nake Kara tausaya Mata so nake Nan da
wata daya ai auren nan da sati daya nakeso agama komai sai asa bikin sati biyu kitemakamun
Dan Allah yai rau rau kamar ze kuka
Hajiya jin abun take tamkar mafarki Kai suhail baka da hankali ko kafara shaye shayen zamani
karka