Showing 12001 words to 15000 words out of 46340 words
Chapter 5 - ARNAN DAJI Book 1 By Feedeen Bash.pdf
da karfi zan keta duk wadda naso nakuma
kasheta kaima yanzu zan kasheka hhhhhhh
Haka rayuwar gidansu jeddah takasance kowa abunda yakeso yakeyi saboda uwa ba
kwaba uba ya mutu a wannan lokacinne za ay bikin wata makociyarsu me suna ummi tare suka
taso da jeddah makaranta daya sukai Amma kowa da halinsa shiyasa basa shiri sosai sai dai
idan an hadu a hanya hy hy nan Jeddah najin labarin irin mijindazata aura sukai ruwa d tsaki a
harkar bikin ita da afra tunda ansan juna saboda mijin me kudine na gaske tayi musu gaba
daya ankon dinner din Dana bikin ita da aminiyarta afra sai da tasan yadda tayi suka shigewa
amarya har rabon cards da ita akai takoma babbar kawar amarya ita d kawarta afra tsabar
shishshigi anfara kamu washe gari dinner mijin d abokansa sun saki kudi shiyasa suke wadaka
gashi sun hadu da Jeddah me bala in wayo idon cin nera wadda tasan lakanin karbar kudi a
hannun namiji aranar dinner ta gaji da kyau Dan takusan fin amarya kyau Dan dai amarya
amaryace kodako ta buzuzuce tanayin kyau ranar bikinta sunyi dinner dinsu meena event
center dake longe road guri yayi guri anci ansha Nan aka Kira aminiyar amarya tabada tarihinta
aka Kira jeddah Nan ta taso dakyar kamar Yar governor tana fita akahau shewa da tafi Nan
camera tafara aikinta daukanta ake kmr baza a denaba gashi b turanci da hausa ta gabatar da
jawabin ta koma Nan aka Kira aminin ango nn akafara zuga kirari yaro d kudi abokin tafiyar
manya me kudi uban matsiyata Dan gidan kudi gadon kudi Nan y fito yana zuwa Nan fa
kowacce yarinya taraina kanta wa kuke tsammani suhail Ibrahim gadon kudi kenan nanfa yafara
larabci tamkar balarabe camera kamar zatay magana mata suka yanyabeshi mazako sai manni
suke masa Ana gamawa aka saki kida Nan da nan ya balle rafar dollars yadinga zuba kudi
tamkar besan ciwonsuba tamkar ya samu bolarsu nanfa mawaka suka samu nayi yi suke ba
kakkautawa amarya da ango sun fito guri ya kara rinchabewa anata watsi da nera
Jeddah kuwa mutuwar zaune tay tunda taga wannan matashin meji da kudi ta mutu a
zaune dama gata mayyar kudi Amma shi wannan soyayyace me cike da sha awa takamata
lokaci guda nan ta mutu a zaune duk rawar kan Nan nata Babu ita hankalinta be kara tashiba
sai yadda taga yana zuba dollars a tsakiyar fili dakyar taja kafarta ta koma filin tasan yadda tay
ta nanuka kusa dashi kawai kallonsa take bemasan tanay ba chan abokinsa ya lura da ita
yadda tazama kamar gunki shi Kuma tunda yaganta tay masa ta tafi dashi yasa aransa yaga
matar aure amma mace har mace Amma gaba daya ya lura ta tafi a duniyar San abokinsa
gashi shibamesan mata bane Dan betabajin yay masa zancen wata ba banda haleema
yarinyar dayake masifar so wadda ze aura Bata karasa candy bane yace besan manyan mata
da idanunsu y bude Yan gaba da secondary tayi karatun a gidansa behanaba yarinyace me
nutsuwa gata iyayenta masu rangwame gatane suna dai da rufin asiri har ansa musu rana da
ita tofa tirkashi muje zuwa
A tsorace baban rama ya fara ja da baya suka fara binsa Nan yafara gudu ya nutsa cikin
jeji suka dinga gudu gashi ya fara manyanta sukuma samarine masu jini a jika jinsu suke kamar
zakuna ga ARNAN DAJI dama karfafa samudawa bazato ya zabga uban tuntube ya Fadi kasa
warwas Nan sukayi masa chaaa aka sukayi masa dabaibayi suka daukeshi kamar kullin goro
suka juya da baya Dan cika umarnin ogansu magajin garinsu ja e sarkin gobe suna zuwa suka
cilla masa shi gabansa ya kece dawata mahaukaciyar dariya kagama gudun ina kaje bazaka
taba tserewa ukubataba Dole ka karbi hukuncin Dana shirya yima kokanaso kobakaso saboda
guduwar dakayi sainasa anganama azaba zuwa faduwar rana sannan mucinyeka hhhhhhh sai
sarki me jiran gado sukadinga ihu suna murna suna masa kirari suna kara zugashi Kai damusa
shiga cikin gari ka kawo Mana burkutu ku daureshi a wannan bishiyar haka yanaji yana gani
suka daureshi suka dinga dukansa suna gana masa azaba har kusan faduwar rana sannan
yasa akwance shi yasa akabashi wuka kakkaifa yasa suka danneshi yanaji yana gani sukay
masa yankan rago nan suka hau ihu da sowa harda tafi Nan da nan aka hada wuta aka farke
cikinsa suka fara cin kayan cikin danyu aka cire kan aka ajiyeshi agefen hanya akafara gasa
naman anaci ana hadawa da burkutu sunata ihu da murna hankalinsu kwance ta Fadi gasassa
Idan hankalinta yay dubu ya tashi har yanzu babanta be dawoba besaba dadewa hakaba
gashi ta tabbata aduke najin jiki gashi tanaso taje taduba mara lafiyan nan dasuke masifar so ita
da kawarta bara tabishi dajin taga ko lafiya tunda tasan inda yake zuwa batagayawa tenkwai
tafitaba saboda itama tazama kamar matacciya tayi tayi suje gida takiya kawai takyaleta tace
mata inazuwa tadau hanyar jejin datasan yatafi tana tafe gabanta yanata faduwa Amma Bata
kawo komaiba daga chan nesa ta hango hayaki tanadanjin kauri kauri kamar n mutum tunda
tasan yanayin kamshin mutum wannan bana dabba bane tome akeyi a dajine toke meye naki
wata zuciyar tace kije kinemo babanki kawai shiyafi Miki hankali kwance take ta tafiya tana kara
dosar inda wutar take tazo daf da wutar kenan harzata gifta tunda sina Dan cikin ciyayi basa
ganin giftawar mutum mezata hango kan mutum agefe a ajiye sunma manta dashi harzata
wuce tace Bari dai in sanda inga wakuma yau aka yanka tadaure takarasa cikin sanda tana
zuwa gabanta na cigaba da faduwa karsu ganta tayi tawuce lafiya tana zuwa harzata fasa
dubawa saitace Kai bara dai naga kan wane wannan tundasu sunbada baya sunata shagalinsu
tana dagawa wazata gani babantane batasan sanda tasaki wata gigitacciyar karaba jikinta y
sandare a fusace suka juyo wazasu gani ramace (chab dijan Nan Nima nasaki alkalamina
jikina yanata Bari tofa muje zuwa meze faru a wannan dajin kubiyoni kusha labari)
Inajin dadin yadda kuke nuna kaunarku ga littafina da yadda kuke comment akansa godiya
mara adadi agareku masoyana nice taku a kullum ako wane lokaci kuna Raina ina alfahari daku
masoyana
*FEEDYN BASH*
[9/11, 22:29] +234 810 679 5647: *?ARNAN DAJI?*
*NA*
*FAREEDA ABDULLAHI*
*_?KAINUWA WRITERS?? ASSOCIATION_*??
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
50-55
*GODIYA AGAREKU MASOYANA INA JIN DADIN YADDA KUKA NUNA KAUNA AKAN
LITTAFINA MUSAMMAN ARNAN DAJI FANS DA KAINUWA FANS GODIYA AGAREKU MARA
IYAKA ALLAH YA BANI IKON FARANTAWA MASOYANA INA JIN DADIN COMMENT DINKU
GARENI GODIYA MARA ADADI*
*JINJINA AGAREKU KAINUWA WRITERS ALLAH YA KARA DAGAKU YA ALBARKACI
RUBUTUNKU*
Tenkwai tasa Kai dakin data bar aduke mezata gani adukece a sassankame tana cikin
wani mawuyacin hali ta rushe da kuka nashiga tara badu ka kawon tallafi dame zanji abun yay
mun yawa bazan iya daukaba Nini kadaice bazan iyaba karki mutu kibarni haka tadinga kuka ta
kife akanta lamunde taji kuka yay yawa tana shigowa taga aduke a sankame
Da gudu takoma ta debo ruwa ta zuba mata Amma shiru kakeji saida tay wata dabara ta
danna Mata kirjinta saitin zuciyarta saita saki wata ajiyar zuciya cike da farin ciki tenkwai tayi
kanta ki tashi Yar uwata karki tafi kibarni kinsan ku kadai gareni tunda muka Kai aduke bamu
Kara komawa mun gantaba tana bukatar temako daga garemu nasani ki karfafa jikinki nasan
duk akan abunda akaiwa adukene natabbatar Miki dazan daukar Mata fansa nayi Miki alkawari
Tafara gyada Mata Kai kibarshi tenkwai bazaki iyaba babana Babu ya tafi baze dawoba
ankasheshi a daji sai yanzu tasami damar yin magana ya tafi shima Banda kowa saike a
wannan garin sai suka sake rungume juna sunata kuka me tsima Rai kuka nashin hankali.
Kigayan gaskiya Rama waya kashe babanki na tabbatar kashe shi akai Ja'e ne ze kashe shi
tabbas Kuma a yau base gari ya wayeba zanje na kashe Ja'e zan daukar Miki fansar abunda
yay muku keda aduke saboda duk sabodani yay muku duk kokarin da kuke akan naso shi na
aure shi gani yake kamar kune kuke zigani nakishi ayau koni koshi gaba daya jikinta sai rawa
yake jijiyoyin jikinta duk sun tashi rada rada cike da bacin rai tafice daga dakin tadibi kwari da
baka da kibiyoyinta masu shegen dafi saboda tenkwai ta kware a fannin harbi Bata taba saita
Abu Bata same shiba
Da gudu Rama tazo tarike kafarta tana gursheken kuka bashi bane nagaya Miki bashi
bane kubuwace ta cikin Daji Ina shiga naga gilmawarta ta yasar dashi a wajen kiyi hakuri kinsan
Ja'e yafi karfinki duk abunda kikeji dashi Ja'e yafiki zai iya hallakaki kema kinsan duhu yayi ba a
fita muje daki mu kwanta danta kautar da wannan maganar ya jikin Mara lafiyanki ya farka iceko
tenkwai tai shiru takasa magana tanata sake sake a ranta kome take sakawa oho
Tabbas rama jarumar macece wadda take iya jure duk wata damuwa datake ranta tayi
hakuri tasa dangana aranta tasan Bata da kowa yanzu ba uwa tunda tafaifeta ta rasu yanzu
Kuma uban nata datake jin dadinsa take ganin Bata da wani gata sai shi yau gashi Babu shi ta
tabbatar yanzu ita ja'e yake hari agaba yanzu yazatai tabbas bazata koma wannan gidan ba
tasan tunda yaganta sai ya kasheta maboyarta dayace gidansu tenkwai saboda yay masa
wahalar zuwa saboda zallar San daya kewa tenkwai da Kuma shayinta daya ke wannan kenan
Jeddah ta shiga bayan motar faruk yashiga gaba suhail yaja wani mugun tsaki ya figi
motar kamar ze tashi sama bakin cikin duniya ya ishe shi besan meyasa faruk beda hankali ba
Banda hauka daga ganin mace ka kwaso ta harda sa ta A mota to gidan uwar wa zashi da ita
cike da takaici ya cemasa ina mukayi madam Ina mukayi cewar faruk dangwauro what ya fada
da karfi niban San wannan unguwar ba cewar suhail
Ranta yay masifar baci tome wannan yake nufi a kauye take komai tai kwafa faruk yace haba
suhail gabanfa sa'datu rimi ne idan kawuce fly over ay ba wani nisa bane amaryar ma ai achan
take yay musu shiru be kara tanka musu ba zuciyarsa tamkar zata fashe Rai bace ya dau
hanyar dangwauro
Suna tafe tana masa kwatance har suka zo layin su tanuna musu dai dai gidan su yai
parking rai bace faruk meye sunan abokinka naga baya magana faruk yay dariya suhail kenan
ai miskiline baya magana sosai ran suhail in yai dubu ya baci dan Allah jibi yadda yadda yake ta
washe mata baki mtsww ya ja tsaki yadau waya yakira budurwarsa haleema cike da shauki
yake maganar ran gimbiyata yadade nasan nayi lefi tuba nake kiyimun rai karki fushi kinsan
kece rayuwata gaba daya
Ai jeddah jitai gaba daya ta muzanta ya gama da ita agabanta yake cewa wata itace
rayuwarsa a fusace ta bude motar ta fita faruk yai maza ya bita gimbiya ta yazaki tafi bamu
gama magana ba kaina ne yake ciwo zanje gida mayi magana wata rana baki ban no dinki ba
cewar faruk ka kyaleni Dan Allah bazan bakaba suhail ko ya gama wayar yana jinsu meko zeyi
inba dariya dariya yake kamar cikinsa ze kulle maganinka kenan na mamajo kowa kagani kana
so Jeddah tasa Kai ta shige gida ranta a kuntace ko sallama Bata iya yiba dama ba damun ta
tai ba da chokareren takalminta ta shiga dakin ta tana zuwa ta zube a katifar ta luntsumemiya
ranta a kun tace tana ta saka da warwara
Haka suka kwana zuciyoyinsu a jagule gari be gama wayewa ba sukaji kakarin mutum
yanata ruwa ruwa ay da gudu suka Mike suna Yar rige rige saboda duk cikin su ba Wanda yai
bacci kawai juyi suke cike da damuwa suka dai suka San abunda ke damun zuciyoyinsu gasu
suba musulmai b bare suyi sallah Kai musulunci yayi Allah ka kara Mana tsoronka da biyayya
agaremu ka kashe mu cikin bautar ka
A guje tenkwai tadebo masa ruwa Rama Kuma tai dakin tana zuwa ta tallafo shi sannu
sannu basu ya baka lafiya ya zuba Mata ido yana kallonta waye Kuma badu besan shiba
tenkwai ta shigo da ruwa jikinta har rawa yake kamar mazari Rama ta karba ta bashi Nan ya
kafa Kai sai da ta janye Dan karya kulle shi cikin sa ba komi yadinga binsu da kallo suwaye ku
Ina ne nan wanene ni cike da tausayinsa tenkwai ta ce tsintarka mukayi a ruwa waye Kai Ina ne
garin ku kayi bayani musaka a hanya idan suka ganka zasu kashe ka Amma Ni zan bika cewar
tenkwai ya kara kallonta kawai yakasa tuna komai na rayuwarsa bana iya tuna komai iya
abunda yace kenan Amma Nan ba iri na bane ku tabbas katuna Mana cewar rama shiru yay be
kara cewa komai ba
Rama ce ta mike zoki ji tenkwai ta mike ta bita tana ta waiwayensa wai shine ya tashi har
yake ta magana haka ranta kal burinta ya kusa cika Rama taja tenkwai gefe akwai damuwa
saboda ya samu cutar mantau sai kuka tabbas Rama bataso haka ba Amma tunda tagan shi
tasan sai anyi haka saboda ciwon dake kansa ya taba kwakwalwarsa gwarama mantau din Ana
dawowa akan ace hauka yake jagwab tenkwai ta zube tana ta kuka abubuwa sun musu yawa
wannan gari babu adalci cikin sa bazata bar shi ya rayu a ciki ba zata San yadda zatayi
Rama jaruma ta durkusa ta gogewa tenkwai hawayen ta nasan yadda kike ji a ranki game
da soyayyar wannan mutum wannan itace damar dazaki amfani da ita ki mallake shi tunda yana
cikin mantau baze iya tuna komai ba ze soki ya kaunace ki a hakan da muke a cikin jeji saboda
beda wani zabi a yanzu (gaskiya Rama kina burgeni jaruma ce ke kujifa wata sadaukarwa duk
da San da take masa kawance na gaskiya kenan)ta rungumeta kin kawo shawara me kyau
Amma Dole sai bayan na auri Ja'e na kashe shi sannan wannan alkawari ne saina cika shi
sannan tawa duniyar zatai mun Dadi um um kibi a hankali duk yadda kike tunanin Ja'e ya wuce
Nan karki fara kibi komai a hankali yanzu tashi muje muga aduke bekamata mu yasar da itaba
tun jiya bamuje mun Kara ganin taba gaskiya fa hakane bamu kyauta ba muje maza nasan tana
jin jiki gashi ba asa Mata maganin ba muje muganta sai mu wuce daji mudebo Mata maganin
Amma bazan je wanchan ba banaso naga gawar babana sai hawaye suka zubo mata muje na
chan gaba da gari hanyar beguwa
Suka fito suna tafe Rama tana ta hawaye saboda tunawa da abun da Ja'e yay wa mahaifinta
Yanzu fa shikenan ya cinye shi Kuma kashe shi yayi gwara ace mutuwa yayi taga gawarsa data
ga wannan bakin lamarin Amma yazatayi ba Wanda ya damu da damuwar wani a wannan garin
kowa ta kansa yake kanayin Abu kadan za a kashe bakin ciki yai wa mutan wannan dajin yawa
dame zasuji tana musu fatan su Sami chanji a rayuwarsu Koda bayan ta gushe ne a duniya
Dan tabbas zata kashe kanta rayuwarta Bata da amfani
Tenkwai ce ta kamota Ina zaki je meyake damun ki Rama nasan tunanin babankine kiyi
hakuri kinga kububuwace bamu da damar daukan fansa kaddara ce sanadin ciwon aduke
amma tabbas na Dora alhakin hakan akan Ja'e Dan shine ya janyo ko sunansa Bata so a Kira
suka sa Kai gidan suka shiga gari yayi haske tanga raran suka duba dakin farko ba kowa suna
dakin chan kenan suna sa kansu tenkwai ce a baya Rama a gaba me Rama zata gani inance a
daddatse yayinda ga aduke Kuma a mace Amma ita ba kasheta akai ba Dan ba yanka a jikinta
waye da wannan aikin Ja'e ne zuciyarta ta gaya Mata Bata San san da ta yanke jiki ta Fadi ba
tenkwai naganin haka itama tasa Kai mezata gani saita zunduma wani irin ihu daya jawo
hankalin mutanen da suka fara fitowa waje kafin su shigo itama taje kasa
Kumin afuwa fans anan zan dakata baku samu typing da wuriba yay wallahi ayyuka ne sukai
mun yawa Amma kuyi min uziri ga wannan nice taku har kullum