Showing 1 words to 3000 words out of 37591 words

Chapter 1 - FATIMA DA ZARAH NA AUTAR MARUBUTA.pdf


FATIMA DA ZARAH

Na

Autar marubuta




Wannan kagaggen labari ne dani Autar marubuta na zauna na kirkire shi .Ban kuwa yi dan
kowa da komai ba, idan ya yi kama da tsarin rayuwar wasu ma auratannn, tom ni dai kawai
arashi ne mai kashe auren wawa.


Editing d'in ma a wannan karan bai samu ba

________________________________________

*AUTAR MARUBUTA CE*✍
______________________________________
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_
<><><><><><><><><><><><><><><><><><><><






Page 1 _5






SAUDIYA

Dawowarsu ke nan daga asubiti , Najib da Ahmad tare da mahaifiyar su da bata da lafiya, eh
tabbas wannan iyalin kana iya ganin tsantsar soyyayar mahaifiyar su , bama dai wannan ba
tafkeken gidan da suka shiga ga wasu motoci a zube a harabar gidan .





Gida Nigeriya ✔




"A duniya bani da burin da ya wuce na mallaki Zarah,tabbas rayuwata dan ke aka yi ta , wayyo
Zarah , Zarah ina kaunar ki sama da dukkan ma'anar kalma ina miki san da babu misali , Allah
ya bani ke matsayin matata habibty."


Wani saurayi ne had'ad'ad'd'e mai kimanin shekaru 29 yake zayyano wannan kalamai yana
daga kwance a kan gadonshi .

Ba tare da ya sani ba mahaifiyarshi tana ta saurararshi , da abin ya ishe ta , ta fara kiran
sunanshi
"Kamal , Kamal."

Sam bai ji kiran mahaifiyar tashi ba ya zurfafa cikin matukar kewar Zarah , sai da mahaifiyarshi
ta sa hannu ta dungure 'kafar shi da ya jinginar jikin bango sannan ya dawo hayyacinsa .

Murmushi ya yi kafin ya tashi zaune yana sosa 'keya

"Mommy ina kwana ." Kamal ya fad'a yana sunkuyar da kai kasa


"Bazan amsa ba mara kunya , tun yaushe na shigo d'akin , kana can kana zantukan hauka a
kan wannnan yariyar ." Mommy ta yi maganar kamar mai shirin kaiwa d'an nata duka



a Kamal mi'kewa tsaye yana ri'ke hannunta yana cewa, "Yi hakuri dan Allah mommy, wallahi
bansan kin shigo ba haba masoyiyata uwata ta kaina."


Mommy ta yarfe hannunshi daga hannunta cikin muryar saukakawa ta ce, "Ba shakka tun da ka

mai dani kakarka , sai ka fito break fast."

Tana gama maganar ta fita tana murmushi tare da godewa Allah da wannan yaro da ya bata .

Shima bayanta yabi kafin ta 'bace masa suna isa teburin cin abinci Hajjiya ta zauna a kujerarta
ta kusa da Alaji Mansur


Kamal ma ya ja kujera dake tsakanin 'kannenshi biyu Nasir da Laila sannan ya zauna .



Alaji mansur ne ya fara tashi daga karin kumallon bisa godiya ga Allah ya shiga ciki

a wannan lokacin ne Nasir ya yi maza ya koma kujerar Alaji.



Wani kallo mommy ta jefa masa tare da cewa ,"Me ya sa baka da kunya ne Nasir , ka raina
kowa mene haka ne ."


Sum-sum ya tashi ya koma inda ya bari yana cewa, "A yi hakuri mommy."



Kamal dariya ya yi sannan ya dubi fuskar Nasir da duk babu annuri yana cewa, "Karka damu na
gidana idan na yi aure d'akinka guda wallahi a gidana."


Mommy ce ta yi dariya tana cewa, "Eh tabbas kuwa ya kashe auren ."



Dariya laila ta kwashe da ita harda tuntsurawa, fuskar Nasir kuwa sam yaki sakinta



Bayan Laila ta shanye dariyarta da 'kerrr ta dubi kamal tana cewa, "Yawwa Yaya Kamal ni fa
ban ta'ba ganin Aunty Zarah ba."

Kamal da jin maganar Laila ya wani yi mutuwar farin ciki a zaune yana murmusawa
Ba tare da ya cewa Laila komai ba ya fara dunmiyawa tunanin Zarah.




Iyalan gidan Alaji Mansur ke nan tsohon soja ,babban mutum mai magana guda .

Yana zaune da matarshi Hajjiya Amina wato mahaifiyar Kamal , tare da d'ansu guda daya tilo
shi ne Kamal, sai kuma Laila wacce ta taso a gidan tun tana karama sakamakon rasuwar
mahaifiyarta 'kanwar Alaji Mansur.

Sai Nasir wanda Hajjiya ce ta d'anko shi daga kauye tun yana sheakara 18 a wajen yayanta da
suke uba daya.Ya dawo nan suna zama tare.







Anan cikin wani katafaren gida kuwa yasha ban-ban da wancen suma dai suna zaune kan
teburin cin abinci irin nasu na gayu suna karin kumallo .


Da gani babu tambaya zaka gane wane mai gayya mai aiki mai wannan gida a cikinsu , sanye
yake da jallabiya fara babu far'a a fuskarshi yana shan shayi
Duk da kuwa tarin kayan abincin dake kan teburin bai d'auki komai ba ,
Daga karshe yaja dogon tsaki ya tashi ya bar wajen



Wasu manyan mata ne fara da ruwan tarwad'a da suma suke zaune suka kalli juna ,
Yayin da kowacce taci gaba da cin abincinta.



Gidan Alaji Mustapha ke nan , shima tsohon soja ne ,sannan babban aboki ga Alaji Mansur, sai
dai shi Alaji Mustapha iyalinshi ba kamar na Alaji Mansur ba ne , kusan kullum 'bacin rai yake
'kunsa a wajen matansa .

'Ya'yanshi guda 6 ne wanda duk suna raye sun girma, guda uku suna nan Nigeria a kusa dashi ,
Khalid da Habib wanda su ne mazan , sannan sai Fatima wacce ita ce kad'ai mace da Allah ya

ba shi .


Hajjiya Binta da Hajjiya Rukayya, a halin yanzu su ne matan Alaji Mustapha, wanda kowacce
tana da yaro guda daya



Sai kuma uwar gidanshi matarshi ta farko kafin su rabu , Hajjiya Samira wacce ita ce mahaifiyar
Fatima, sannan kafin Fatima tana da wasu yaran maxa su uku wanda kusan su ne manyan
'ya'yan Alaji Mustapha

Amma a halin yanzu basa Nigeria, suna can Saudiya wajen mahaifiyar su
ita kuma fatima tana gaban mahaifinta



Duk da cewa Hajjiya Samira mahaifiyar Fatima bata gidan Alaji bata kuma kasar , hakan bai
hana su Hajjiya binta cigaba da kishi da ita ba ,
Sakamakon yadda ta fisu 'ya'ya da kuma yadda Alaji yake yawan yabon ta har yau musamman
idan yaga d'iyarta Fatima.


Zan so kiran dukkan 'ya'yan Alaji Mustapha yanzu domin gabatar mana da kansu , sai dai duba
ga tafiyarmu da nisa da kuma tsawon jiran da zami na saudiya su zo yasa na fara cewa daku


Faruk shi ne d'an Alaji Mustapha na farko wanda yanzu haka soja ne a saudiya , sai kuma
Ahmad wanda yake kasuwanci shima a can kusa da mahaifiyar su, sai Najib d'an jarida
Sannan autar Hajjiya Samira Fatima wacce take nan Nigeria tana aikin lauya


Sannan Habib dan Hajjiya binta , soja ne , tare da Khalid dan Hajjiya Rukayya duk sojoji ne .
Wannan su ne iyalan Alaji Mustapha.







Gida ne na alfarma wanda ya gaji da had'uwa tabasss an zuba daula a wannan gida , domin
gida ne da ake yawan misali da shi

wannan gidan bana kowa bane face gidan Alaji Sale mashahurin mai kudi da yake da hanyoyin
samu bila a dadin masha Allah

Daga cikin falon gidan wata kyakykyawar halitta ce zubin karshen hutu take kwance kan d'aya
daga kujerun alfarmar falon na farko


Ga dukkan alamu dai chatin take , sai dai idanunta na kaiwa kan agogo tai sauri ta tashi ta
shige wanka

Babu jimawa ta fito tana zun'buro baki gaba , musamman ma ganin mahaifiyarta Hajjiya
Sa'adatu ta shigo

kamar kuwa yadda tai tsammanin jin mahaifiyartata zata mata magana haka taji .

"To ke kuma lafiya Zarah kike fushi."?

Hajjiya Sa'adatu ta tambaya

" Mommy na gaji bana son suna asubiti da rana wallahi. " Zarah tai maganar kamar za tai kuka


Kawai dariya Hajjiya ta yi mata kafin ta ce , "Wallahi wannan mitar ce bana so , shi ya sa kawai
nake jiran ranar da zaki tafi gidan Kamal na huta ."

Da jin haka Zarah taji wani shauki mai hade da kunya ya ziyarce ta , hakan ya sa ta nemi kofar
dakinta da gudu ta shige



Dariya Hajjiya Sa'a ta yi ta samu guri ta zauna , zaman ta ke nan sai ga Alaji Sale ya shigo ,
yayin da wasu samari kyawawa masu kama da Zarah suka biyo bayanshi


Alaji Sale salisu duk wata hanyar samun kudi ba ya bari , haka ya d'ora yaranshi a kai , hakan
ya sa arziki kullum gudana yake



Babban d'anshi Mahmud, wanda ya yi nisa a kasuwanci , sai Zarah da tai karatu a kasar misira
, wanda yanzu haka likitan zuciya ce , sannan d'aya daga cikin marubuta masu matukar hazaka
da masoya

Sai ’karaminsu Umar shima dai ....





Anan cikin gidan Alaji Mustapha, farin ciki ya ishe shi sakamakon ziyarar Alaji Mansur da ya
kawo masa


Bayan sun ci abinci sun sha sannan suka fara hira suna ta'bo 'bangarori da dama


Ana cikin hirar ne Alaji Mansur ya ce ,"Ni kam ya maganar matarka Samira ne ."


Dariya mai cike da ya'ke Alaji Mustapha ya yi kafin ya ce ,"Ka ji ka Alaji da wani zance , ka ce
dai tsohuwar matata mutuniyar kirki, ai wallahi na yi rashin mace ta gari kawai sai dai Allah ya
maida alheri ,ka ga shekaru nawa da rabuwar mu amma tana zuciya ta."




Cikin tausayi Alaji Mansur ya kalleshi ya ce ,"To Alaji Mustapha ni bama wannan ba , ya Fatima
take akwai maganar da nake son yi a kanta ."


Numfashi Alaji Mustapha ya aje kana ya ce ,"Fatima ai wallahi tana shan wahala , yarinyar nan
ta girma ,tarbiya da mutunci ba a magana , amma duk da haka su Hajjiya Binta basu da abin
wulakantawa kamar ita."


Alaji Mansur ya ce ,"Shi ya sa na zo maka da wani zance Alaji domin kasan Fatima 'yata ce."

Murmushi Alaji Mustapha ya yi yana cewa ,"Fad'a mini kai tsaye Alaji Mansur. "



Haka Alaji Mansur ya sanar da Alaji Mustapha abin dake ranshi , nan take farin ciki da sabuwar
kaunar juna ta rufe su , musamman Alaji Mustapha abin dai ba a cewa komai


Lokacin da Alaji Mansur ya tashi tafiya , har bakin get wajen mota Alaji Mustapha ya rakoshi

sa'ilin da yake cewa ,"A gaskiya na jima ban ji farin ciki irin wannan ba , ka gama mini komai
Alaji, wannan shi ne abota , Allah ya bar zumunci."



Cikin farin ciki shima Alaji Mansur ya fara cewa ,"Karka damu ai kawai mu fara shiryawa domin
babu abin da zai lalata mana wannan zumuncin ,kawai Allah ya kaimu ranar ." Alaji Mansur ya
karasa maganar yayin da driver ya bude masa mota ya shiga .


Sannan sukai sallama da juna , driver ya tu'ka motar suka tafi .



Fatima ce kwance kan gado tana kokarin yin bacci gefe guda ta kalli wasu curin takardu tana
tsaki

"Allah ka bani hutu , yanzu na dawo daga office, kaina ciwo yake wallahi ya kamata na yi bacci ,
ni koma ya jikin umma."

Ta karasa maganar tana daukar wayarta domin kiran Ahmad


Amma tana d'auko wayar sai ga kiran Najib ya shigo , babu jira ta d'auki kiran tana cewa
,"Yanzu nake shirin kiran Ahmad. "


Daga can cikin larabci ya fara mata magana yana cewa, "'Yar Nigeria ya aiki ya Nigeria, daman
mommy ce ta ce zaku gaisa."


Murmushi Fatima ta yi , kana cikin yaren Hausa ta fara cewa ,"Aiki kalau kuma haka kasarku
Nigeria tana lafiya , wallahi ina kewar ku."



Najib ya yi dariya sannan ya canza harshe ya koma Hausa yana cewa, "To ya shari'ar ko ba a
yi."


Fatima ta yi ajiyar zuciya tana cewa, "Dan Allah ka ba mommy na wayar , ina matukar mutuwar
son jinta yanzu."

Najib ya yi dariya sannan ya bawa Hajjiya Samira wayar .


"Assalamu alaikum ."

Fatima ta amsa sallamar mahaifiyar tata cikin matukar kewar ta

"Mommy fatan kinji sauki sosai wallahi ina kewar ki mamana."


Murmushi ta yi sannan ta ce ,"Naji sauki Fatima, ai banso suka sanar dake bani da lafiya ba ,
sun d'aga miki hankali. "




Fatima ta ce ,"Haba mama ke fa uwa ce a gare ni , bani da fatan da ya wuce ki samu lafiya , in
sha Allah ciwon zuciyarki sai ya zama tarihi ."



Hajjiya Samira ta ce ,"Fatima ke nan , to ya mutanen gidan , nasan zaman hakuri kike Fatima,
aita hakuri wata rana sai labari ."



A jiyar zuciya Fatima ta yi kafin ta ce ,"Babu wani zaman hakuri mommy, ni kawai kewar ku
nake , kuma ina nan zuwa ."



Hajjiya ta yi murmushi tare da cewa ,"Fatima ke nan nifa nasan ba rayuwar farin ciki kike ba
kawai dai bakya son fada mini ne."



Fatima cikin wayantar da zancen ta ce ,"Ni fa mommy gaskiya zaku gànni wajen shekara biyu fa
banganki ba , sai dai video call, dasu yaya Faruk da Ahmad, ina aunty Murja ."


Hajjiya Samira ta sanar da ita kowa lafiya kuma komai daidai

Bayan sun gama wayar ne sai ga Murjanatu ta shigo wato 'kanwa ga Hajjiya Samira....







Yadda Fatima taji kewar mahaifiyar ta da yadda idan ta tuna yadda take rayuwa a gidan
mahaifinta ya sa ta fad'a gadon nata ta fashe da kuka , kuka take mai gwanin ban tausayi abin
ta


Yayin da taji ana mata bugun kofa ne ya sa ta tashi da sauri tana share hawayenta , sannan ta
bud'e kofar



Hajjiya Binta ta gani tsaye tana kallonta

wata harara ta jefawa Fatima sannan ta ce ,"Kin dawo daga office, shi kuma wanke-wanke da
girkin daren wane zai mana ko so kike aiki ya kashe mu ne ."



Ajiyar zuciya Fatima ta yi tana cewa, "Dama mommy yanzu nske shirin fitowa ."


Hajjiya Binta ta juya tana cewa, "Ya dai fi." Sannan ta koma falo inda Alaji Mustapha yake zaune
tare da Hajjiya Rukayya






Fatima kanta yana matukar ciwo ta fito , tana nufo falo ta ga Alaji shima yana zaune ta nufi
bangaren madafa wato d'akin girki , kafin ta sa 'kafa ta shiga taji muryar mahaifin nata yana
kiran ta


Hakan ya sa ta juyo ta nufi wajen shi , tana isa ta zauna a kasa cikin matukar tsoro da fargaba ,

domin tasan tunda ta ga wannan makiran matan nasa biyu to tabbas sun had'a ta da mahaifinta



'Tashi ki zauna a kujera ."Alaji Mustapha ya fad'a cikin takama


Fatima ta aiwatar da umarninsa kamar yadda taji

"Mene zaki a dakin girki ."?
Ya tambaya cikin jiran amsa


" Daddy zan yi abu ne ."


Jin amsar Fatima ya sa Alaji Mustapha wani murmushin takaici yana dariya mai ciwo


Yayin da kuma ya fara cewa ,"Fatima ke ce kawai Allah ya bani 'ya mace , hakan yasa koda
muka rabu da mahaifiyar ki Samira ban bari ta tafi dake ba .


Amma sai dai Allah ya jarabe ki da zama cikin azzaluman kishiyoyin uwa da basa kaunar ki ."


Cikin mamaki Hajjiya Binta da Hajjiya Rukayya suka kalli juna


Hajjiya Rukayya ta tari numfashin Alaji tana cewa, "Haba Alaji, duk kokarin da muke wa yarinyar
nan baka gani , ai ko 'yar muce ....."



"Yimin shiru." Alaji Mustapha ya katse ta cikin matukar fushi , sannan ya d'ora da magana


"Duk kallon ku nake tarrrrr wallahi, Fatima tana shan wahala a hannunku matuka, amma na
zuba muku idanu domin ganin gudun ruwanku , tsawon lokaci yarinyar nan ko sau daya ba ta
ta'ba kawo karar ku ba . Amma dake baku da imani ko a jikin ku."

Cikin huci Alaji Mustapha ya dubi kowacce a cikinsu yana cewa, "To daga yauuuu kar wacce ta
sake saka Fatima aiki a cikin gidan nan , komai mene ne na haramta .


Mene ne amfanunku , duk wacce baza ta iya ba ga hanya Allah ya tsare."


A karo na biyu suka sake kallon juna



Alaji Mustapha kam ya ci gaba da fad'an shi yana cewa, "Tsinke idan Fatima ta sake d'auka a
cikin gidan nan zaku ga yadda zami daku , ai wallahi kawai shiru nake muku babu irin kissar ku
da munafunci da ban sani ba tun lokacin Samira , Samira ta fiku komai kawai kaddara ce ta
raba mu .

To wallahi kun yi na farko kunyi na karshe , kun yi na marmari ya gundire ku , an yi walkiya na
gama ganin ku , kuma ni da ku shege ya fasa ku tashi ku bani waje mutanen kawai."





Zumbur suka tashi Hajjiya Binta na gajeren tsaki wanda Alaji bai ji ba


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login