Showing 9001 words to 12000 words out of 37591 words
wallahi sauran kwana kad'an , muje ana d'aura aure
mu dawo ."
Bashir ya ta'be baki yana cewa. "Allah ya sauwake muna exam a lokacin zamu je kano mu
dawo, wallahi baza ni ."
A lokacin Abba Alaji ya ban kad'o kofa ya shigo , alamun ya sha ya bugu , yana shigowa ya
fad'a gado ya fara bacci .
Ran Khalifa ya matukar baci ya kalli Nasir yana cewa. "Wallahi wataran sai na yiwa Abba
shegen duka ."
.Su ka kwashe da dariya .
Alkalamin
Autar marubuta ne .
FATIMA DA ZARAHν ΌνΎ
Na
Autar Marubuta
_______________________________________
*AUTAR MARUBUTA CE*βν ΌνΏ»ν ½ν±Όν ΌνΏ»
ν ΌνΌΉ__________ν ΌνΌΉ_________ν ΌνΌΉ__________ν ΌνΌΉ_________ν ΌνΌΉ
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_ν Ύν΄²ν ΌνΏΌ
<><><ν ΌνΌΉ><><><>ν ΌνΌΉ<><><>ν ΌνΌΉ<><><><>ν ΌνΌΉ<><><><><>ν ΌνΌΉ<><
Editingβ
Page 12 & 13
Duk ana ta shirye-shiryen biki , 'kanwar Hajjiya Samira, Murja sun zo ita da sauran yaran Alaji
Mustapha
Domin gobe ne d'aurin aure
Alaji Mansur ne a zaune a falo, yana waya
A lokacin Kamal ya shigo ya zauna a kasa
."To Alaji Musa bari. , sai kun shigo goben, dan Allah a sanar dasu ambassador da Malam
Mu'azu ."
Alaji Mustapha shiru ya yi sakamakon abokin nashi daga can barin yana magana , bayan ya
gama Alaji ya ce ."To shi ke nan , na gode sosai sai mun had'u."
Sannan ya aje wayar cikin farin ciki ."To ya maganar gidan naka ya yi maka ."?
Alaji ya tambayi Kamal
Kamal cikin girmamawa ya ce ."Daddy ya yi babu wata damuwa ."
Alaji ya ce ."To alhamdulillah,
Abin dana ke son ka sani Kamal, wannan sabuwar rayuwa ce zaka fara , ka sauke hakkin
Fatima, kar ka cutar da Fatima, matukar ka cutar da ita ka cutar dani duniya da lahira ."
Da sauri Kamal ya kalli mahaifinsa cikin mamaki ."Haba Daddy, wallahi bazan cutar da Fatima,
ka za'ba mini Fatima, kuma naji na gani na amince kuma Daddy samm bazan baka kunya ."
Murmushi Alaji Mustapha ya yi kana ya ce ."To gaskiya naji dadi kamal, Allah ya yi maka
albarka ya sa ka gama da duniya lafiya. "
Kamal ya ce ."Amin daddy. "
Sannan Alaji ya sallami Kamal ya tafi , yana fita ya nufi arabar motoci sannan ya hau mota ya
nufi gidansu Fatima
Isar shi ke nan suka gaisa da mai gadi sannan ya shiga ciki
Bayan ya gaisa da Hajjiya Rukayya, suka gaisa da Murjanatu nan ake sanar masa kanwar
mahaifiyar Fatima ce
Cikin girmamawa ya gaisa dasu faruk da Ahmad nan ake ta farin ciki
Bayan ya tashi tafiya ne Fatima ta rakoshi har wajen motarshi yayin da ya zuba mata idanu
Ta yi wani kyau matuka irin na amare sai sheki take
."Uhm lafiya kuwa Kamal. "
Fatima ta fad'a yayin da ta ga kallon ya mata yawah
Ajiyar zuciya Kamal ya yi sannan ya fara cewa ."Lafiya mana Fatima , ko lefi ne dan na kalli
amaryata ."
Wani yammm Fatima taji sakamakon karan farko da ya fara nuna mata irin wannan yanayi
Ta masa murmushi
Sannan Kamal ya ce ."Fatima ina son sanar dake na shirya rayuwa dake komai tsanani , zan
kula dake ga dukkan iyakar kulawata , duk yadda Allah ya tsara maka rayuwa shi ne daidai , a
domin haka ina son ki sani ina son ki , ina kaunar ki , domin kin zamanto mini wani babban
sashi lokaci guda a rayuwata, son ki ya kamani a yanayin da ban yi tsamani ba, wallahi Fatima
daga zuciya ta ne wannan sakon yake zuwa gare ki ."
Murmushi Fatima ta yi na matukar jin nauyin Kamal
Sannan ta kau da kai tana cewa ." Masha Allah Kamal, hakika naji dadin jin wannan. "
Shima Kamal murmushi na farin ciki ya yi yana cewa ."To yanzu mene ne kike da bukata."..
BAYAN AURE
Kamal da Fatima tuni ansha biki , komai ya yi matukar kyau , an sha shagali sosai da sosai , har
mutanen saudiya sun koma , auren Kamal da Fatima babu wata matsala.
Hajjiya Amina ce da Alaji Mansur a zaune suna hira
Sallamar Kamal ce tasa su duk shiga wani farin ciki
Nan ya durkusa ya gashshe da iyayen nasa
."To ya 'yar tawa ."?
Alaji Mansur ya tambayi Kamal
Murmushi Kamal ya yi yana cewa. "Tana lafiya Daddy."
Hajjiya Amina ta ce ."To masha Allah, Allah ya kara zaman lafiya ."
Alaji ya kalli kamal yana cewa. "Mene yake tafe da kai ne , domin tun jiya kake zuwa kuma
akwai magana a bakin ka ."
Kamal ya durkusar da kai yana sosa 'keya.
Alaji ya yi dariya yana cewa. "Ai ni na sani ,wannan yaron naki akwai maganar da take kawo shi
ya kasa yi ." Ya karasa magana yana kallon Hajjiya
Hajjiya ta ce ."Ai Alaji a kan maganar auren yarinyar nan ne Zarah yake son kasa baki a kai ."
Alaji Mansur ya 'bata rai lokaci guda yana cewa. "Wanne irin Zarah kuma , wata kuma zaka
kuma aura ? Yaushe ka auri Fatima."
Jin hakan ya sa hankalin Kamal tashi tsaye , take ya shiga wani hali
Ya d'ago cikin maraicewa ya ce ."Daddy dan Allah, ka duba ."....
Alaji ya dakatar dashi yana cewa. "Ka yi min shiru Kamal, karka sa yanzu na bata maka rai."
A take yaji kanshi yana sara masa ya kalli mahaifiyar tashi Hajjiya Amina cikin matukar damuwa
da shiga wani hali .
Cikin takaici Hajjiya Amina ta kalli Alaji tana cewa. "Haba Alaji , Kamal kuwa bai cancanci haka
ba wallahi, ka dubi yaron nan yadda ya maka biyayya a auren Fatima, bayan ba shi da ra'a
yinta , amma saboda ganin girmanka da tasiri ya amince , amma yanzu ya zo da zance a ce
masa ba haka ba , ai kuwa wallahi Kamal bai cancanci wannan ba daga gare mu ."
Babu annuri ta karasa magana tana ajiyar zuciya ta takaici
Shima Alaji Mansur ajiyar zuciya ya yi yana cewa.. "Alhamdulillah Hajjiya Amina, kin yi gaskiya,
shi ya sa nake sake kaunar ki , da zarar na bar hanya kike dawo dani daidai .Allah ya miki
albarka."
Ya kalli Kamal yana cewa. "Kamal Allah ya maka albarka kai ma , kuma wannan yarinyar
Zarah take ko wa , in sha Allah zaka aure ta ."
Wani farin ciki ne ya rufe zuciyar Kamal da Hajjiya Amina
Bari ma Kamal ya kasa rufe baki
"Daddy na gode Allah ya saka da alheri ." Kamal ya fad'a yana washewa mommy baki
Alaji ya ce ."A'a dena godiya, ka wuce haka , babanta naji kamar ana cewa Alaji sale ne ko ."?
Kamal ya ce ."A Dad shi ne ."
Alaji Mansur ya ce ."To masha Allah. "
Bayan wasu kwanaki
Kamal ne zaune a cikin falo , ya d'auki wayarshi ya kira Zarah, bugu daya ya yi ta d'auka bayan
sun gaisa ne
Fatima ta shigo falon ita ma ta zauna, nan kamal ya cigaba da wayarshi da Zarah suna ta
soyayyarsu
Fatima kuwa tana ta danna wayarta
Bayan ya gama ya dubi Fatima yana cewa. "My love ya ya aka yi ne , wai ko kishina ba kye yi
koh."
Dariya Fatima ta yi tana cewa ."Kishi kuma , ai ni wallahi dear na matsu Zarah ta shigo gidan
nan ."
Kamal yaja ajiyar zuciya yana cewa. "Tabbb gaskiya kina bani mamaki , amma ai shi ke nan .
Na ji kina zaki je office to ki shirya nima zani company sai na aje ki , sannan na biya gidan
Hajjiya."
Fatima ta ce ."Dah ka bari na tafi a mota na ."
Kamal ya galla mata harara yana cewa. "An ki , ni fa ko kad'an bana so kina nesa dani , kishirya
idan ma zaki dawo ni ne zan d'auko ki."
Bai jira ta ce komai ba ya tashi ya koma kujerar da take zaune
Sannan ya karbi wayar dake hannunta ya aje gefe yana cewa. "A karon farko dana kalli
shari'arki kin sani jin sabon alfaharin da nake yi dake matata .Kin iya aikin ki my life, na yi
matukar farin ciki sosai Fatima ina kaunar ki ."
Murmushi ta yi tana sake damke hannayenshi tana cewa. "Ina alfarin zamowa matarka Kamal
nima ina kaunarka ga dukkan yaki nina."
Junansu suka rungume cikin matukar shaukin juna
Sannan Kamal ya ce ."Kuma ki shirya ina nan zan aikata 'barna domin nasan zaki wanke ni a
kotu ."
Fatima tsare shi tai daga jikinta tana kallon shi da cewa ."Kana aikatawa zan aje aiki ."
Dariya ya kwashe da ita yana cewa. "Oho dai gara ma ki shirya , domin shari'ar dazan jayo miki
me wahala ce , kuma dole ki karbo ni Barrister Fatima ta ."
Dariya ta yi tana cewa ."To mu shirya kafin lokaci ya 'kure ." Ta yi maganar cikin harshen turanci
Minti 30 suka bata da suka fito Kamal ya aje Fatima a wajen aikinsu
Yayin dashi kuma ya karasa gidansu
Kamal yana shiga tunkan ya karasa falo ya fara jin muryar mahaifiyar tashi , sama-sama sai
fad'a take
Yana shiga ya yi sallama , Laila ta amsa ya shigo ya sa mu guri ya zauna
Yadda ya kalli Nasir ya tabbatar mommy shi ne takewa fad'a
Lokaci guda Kamal ya canja ya karbi bakin mommy
."Wai kai wanne irin yaro ne Nasir, kullum sai ka 'batawa mommy, yaushe ma ka baro
makarantar. "
Mommy ta amshe da cewa ."Rabu dashi kanshi ya yi wa asara gashi nan an kore su a
makarantar ai. Ba shi ke nan ba ."
Cikin mamaki kamal ya ce ."Mommy kamar ya an kore su a makaranta."
Autar marubuta.
FATIMA DA ZARAHν ΌνΎ
Na
Autar Marubuta
____________________________________________
*AUTAR MARUBUTA CE*βν ΌνΏ»ν ½ν±Όν ΌνΏ»
ν ΌνΌΉ__________ν ΌνΌΉ_________ν ΌνΌΉ__________ν ΌνΌΉ_________ν ΌνΌΉ
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_ν Ύν΄²ν ΌνΏΌ
<><><ν ΌνΌΉ><><><>ν ΌνΌΉ<><><>ν ΌνΌΉ<><><><>ν ΌνΌΉ<><><><><>ν ΌνΌΉ<><
Editingβ
Page 14 & 15
Mommy kawai ta kauda kai cikin takaici
Kamal ya kalli Nasir cikin fushi ya kuma fad'in. " An kore ku kamar ya ?Wanne rashin mutuncin
kuka aikata ."?
Nasir yaja doguwar ajiyar zuciya na takaicin wannan yanayi , sannan ya kalli Kamal cikin nuna
damuwarshi yana cewa
."Wallahi yaya Kamal, ba abin da muka yi , Abba Alaji ne ya yi laifi duk ya shafe mu , daman
suna neman hanyar rage d'aluban , amma bami komai. "..
Kamal ya dakatar dashi yana cewa." Yi min shiru dan Allah, zan cen banza , Abba Alaji ubanka
ne ko ran ka ne da baza ka barshi ba . To wallahi na yi abin da zan iya maka , saboda karatun
ka ne har yau bamu bud'e sabon company ba , zan nemi wani kawai , kaje kai ta rashin
mutuncinka ."
Cikin sauri Nasir ya kalli Kamal idanunshi sun ciko da hawaye yana cewa. "
Dan Allah yaya karka mini haka , wallahi ba a san raina komai ya faru ba , na yi iya yina don
gudun hakan ."
Ya share hawayen da suka zubo masa sannan ya cigaba da cewa ."Ka yi hakuri dan Allah ka
sake bani wata damar ka nema mini wata makarantar ko anan kano ne , in sha Allah bazan
baka kunya ba Yaya. "
Kamal ya sunkuyar da kai kasa bai ce komai ba
Ganin haka ya sa Nasir kallon Hajjiya Amina yana cewa ."Mommy dan Allah, wallahi ina yin
komai dan in gyara gobe na ki roka mini Yaya Kamal dan Allah. "
Laila cikin jin tausayin yayan nata ta kalli Kamal tana cewa. "Yaya ka yi hakuri."
Hajjiya Amina ta kalli Kamal tana cewa. "Shi ke nan Kamal, ka masa kokari , amma idan ka
nema masa makarantar ya koma gidan ka da zama nima na huta ."
Kamal ya d'ago yana aje ajiyar zuciya sannan ya ce da Nasir. "Shi ke nan amma dole ne ka
rabu da wannan mahaukacin abokin naka ."
Nasir ya ce ."In sha Allah zan yi iya yina Yaya Kamal na gode. "
Barrister Fatima ce zaune cikin office, tana duba wasu takardu da zatai shari'a a kai
A lokacin wata barrister Khadija ta shigo tana shigowa ta dubi Fatima tana mata dariya ,sannan
ta nemi guri ta zauna .
Fatima kallon ta ta yi ba tare da tace komai ba , sannan barrister Khadija ta ce .
"To Fatima ya kika ga shari'ar zaki karba ne ."
Ajiyar zuciya Fatima ta yi tare da rufe kundin tana cewa. "A'a gaskiya Khadija, domin wallahi
bana son shari'a me wahala yanzu. Kawai zan karbi shari'ar Alaji Muhd zan tsaya masa
" Tabbb sannu ." Cewar Barrister Khadija
Sannan ta cigaba da cewa ."Kawai dai kice aure ya sangartaki , wannan shari'ar wallahi baza ta
miki wuya ba , shari'a nawa kika yi wacce tafi wannan wahala, sai yanzu zaki ce wani-wani
.Kawai dai Kamal ya sangartaki kuma zan masa magana ."
Ta karasa magana tana wani jujjuya fuska
Dariya Fatima ta yi sannan ta juya suka gaisa da wani Barrister Aminu
Barrister Khadija cikin kasa-kasa da murya ta kalli Fatima tana cewa
."Yawwa barrister Fatima, zancen da nake ji gaskiya ne wai. "?
Fatima ta zubo mata idanu tana cewa
." Wanne zance ke nan ."
Barrister Khadija ta ce ."Wai Kamal zai kuma aure, har invitation fa na gani ."
Barrister Fatima ta yi murmushi
."Au haka ne mana Barrister Khadija, aure Kamal zai kinji daidai ."
Yadda Fatima ta aje maganar babu wata damuwa a fuskarta , sai jawo wasu takardu da take yi
gabanta tana shirin fara aiki a kan su .
Ajiyar zuciya Barrister Khadija ta yi tana kallon Fatima a wannan yanayi kana ta ce
."Wai ke da kanki Fatima kike fad'in haka , yaushe kuka yi aure da Kamal da har zai kuma wani
.
To wallahi karki yadda, wannan ai cin mutunci ne da rainin wayo ."
Barrister Khadija cikin takaici ta aje maganar
Dariya Fatima ta yi tana kallon Barrister Khadija.
"Au dariya ma zaki mini Fatima, ai wallahi akwai sake ."
Khadija ta kuma fad'a
Barrister Fatima ta marairaice tana cewa. "To yanzu mene mafita ke nan ." Ta kasa kunne tana
jiran abin cewa daga Barrister Khadija
Barrister Khadija ta kalli Fatima cikin kissa da kasa da murya tana cewa.
"Tashi zaki ki hana auren wallahi, abin sauki ki hanashi sukuni a kan me zai miki kishiya ,hauka
ake ."
Dariya Fatima ta kwashe da ita cikin yanayi na nishadi
Sai da taci dariya sosai , sannan ta kalli Barrister Khadija
Sa'ilin da ta fara cewa ."Sannu fa Khadija, wallahi dama so nake na bigi cikin ki ."
Ta sake kwashewa da dariya , sannan cikin harshen turanci ta cigaba da cewa .
"To ni wallahi Khadija ban'ki kamal ya aura mata 4 ba nan gaba , ko a jikina to sai me
Barrister Khadija.
Ni dai nafi 'karfin kallon banza wallahi, bani da lokacin wata, kuma sannan bugu da 'kari
Zarah Sale zai aura fa ."
Barrister Fatima ta canza harshe zuwa Hausa kana ta cigaba da cewa
."Kuma tun kafin ni suke kaunar juna , a kan me zan shiga tsakaninsu , ni fa ba shi ne ya
kawo ni duniya ba ."
Barrister Khadija ta tashi tsaye tana tabe baki , sannan ita ma da yaren turanci ta ce .
"Abin kunya dai , kin bani haushi wallahi, bari na koma ki dage dai ki yi aiki a kan wannan
shari'ar ."
Barrister Khadija ta juya ta nufi hanyar fita , Barrister Fatima na yi mata