Showing 6001 words to 9000 words out of 37591 words

Chapter 3 - FATIMA DA ZARAH NA AUTAR MARUBUTA.pdf

,"A gaskiya na gode Allah da wannan a hali daddy, matukar tsanar
Kamal naji ta rufe ni kafin wannan maganar taka
Na gode daddy, ina fatan na zamo tamkar haka , yayin da damuwa ta samu 'ya'yanmu mu juya
musu kaddararsu zuwa nasarori ."



Mahmud ya yi ajiyar zuciya yana cewa, " Gaskiya ne Zarah, babu iyaye kamar namu mu
godewa Allah, sannan ina baki shawara ki d'auki maganar Daddy, domin amfaninta yana tare
dake duniya da lahira ."

Murmushi Zarah ta yi tana kallon yayan nata tana cewa, " Daddy, mommy na rungumi kaddara ,
amma ina san ku sani ina san Kamal, ina bukatar addu'oinku idan kamal alheri ne gare ni Allah
ya bani , idan aka sin haka ne Allah ya nisanta mu dashi." Ta karasa magana tare da radadin
rashin Kamal hadda wasu hawaye a idanunta

A lokacin hajjiya ta ce ,"To alhamdulillah Allah ya muku albarka."


Umar ya ce ,"Amin mommy. "

Zarah ta koma ta kwanta kafar Hajjiya tana ajiyar zuciya, lokaci guda kuma tana yiwa Umar
murmushi yayin da suka had'a idanu .



Fatima kuwa tun da gari ya waye babu wani sukuni a tare da ita domin yau Kamal zai zo , haka
kawai take jin kamar Kamal zai zo mata wulakanci ne , haka dai ta runga zullumi a karshe ta
shirya tunkararshi da dukkan irin fuskar da zai zo mata .




Hajjiya Amina ce zaune a dakin Kamal, yayin da Kamal yana tsaye yana sanya agogo bayan
wata hula da ya sanya wacce ta hau kan fatar shi sosai , sannan ya matsa bakin mudubi yana
fesa turare.

Yana gamawa ya juyo ya kalli mommy yayin da take masa murmushi

Murmushin ya'ke ya mata yana cewa, "Mommy zan tafi Allah ya sa ina zuwa wannan yarinyar ta
ce ban mata ba da naji dad'i wallahi mommy."

Hajjiya Amina dariya ta yi tana kallon yaron nata wanda duk ya rame ya yi wani dogon wuya
tana cewa

,"Banda abinka Kamal, ai ba yarinyar da zata ganka ta ce baka mata ba , ni dai kawai abin dana
ke so da kai , kar ka yadda wani abu ya faru wanda ran mahaifinka zai 'baci, ka yi hakuri komai
mai wucewa ne ."


Kamal ajiyar zuciya ya yi kamar mai shirin kuka yana cewa. "In sha Allah Mom bazan baku
kunya ba , ko dan girman darajarku , zan rike wannan kaddarar na tunkareta a duk yadda ta zo

min , zan nunawa daddy ya isa dani mommy."


Hajjiya wani dadin gaske taji dajin zancen Kamal
Hakan ya sa ta bud'i baki tana cewa. "Allah ya yi maka albarka, wannan umarnin na mahaifinka
shi ne farin cikin mu."




Cikin wani yanayi Kamal da matukar tausayin kanshi ya ce. "Yanzu mommy shi ke nan na rasa
Zarah."


Ita ma Hajjiya wani matukar tausayin d'an nata taji ya kamata lokaci guda, amma cikin kwarin
gwiwa ta ce dashi


.In ji waye Kamal, Allah ne yasan mene ya tsara maka , rabon kwad'o baya hawa sama Kamal,
ko ya hau sai ya sakko .Dan haka karka damu ."



Kamal ko kad'an zancen Hajjiya bai kwantar masa da hankali ba , haka suka fita daga d'akin
suka nufi babban falon yayin da mommy take kara ja masa hankali a kan abin da ya dace .



Suna karasawa sai ga Nasir da Laila sun fito daga 'bangaren Alaji Mansur
Nasir sanye da wata babbar jaka a bayansa ta 'yan makaranta.



Mommy ce ta ce ,"To har ka fito Nasir ."?

Nasir ya ce ." Yes mommy na fito , dan Allah a cigaba da mana addu'a domin satin biyu zami
mu fara jarabawa .Kuma kin san mu manyan yarah idan muka fad'i akwai damuwa mommy. "



Hajjiya ta'be baki ta yi tana cewa. ."Ka ga Nasir , kawai ka dage da abin da ya kai ka , kuma
wallahi ina jan hankalinka kan yaran nan marasa tarbiya 'yan shaye-shaye , matukar kana so
gobenka ta yi kyau dole ka barsu ."

Kamal ya girgiza kai alamun haka ne , sannan mommy ta cigaba da cewa

."Yanzu dai kamar wannan yaron na gidan Alaji Sani ai ba aboki ba ne ."

Hajjiya Amina mamaki ne ya rufe ta gani dajin yaron da take magana ya shigo kai tsaye cikin
falon

"Ina kwana maman Nasir ." Abokin nashi ya fada cikin harshen turanci da muryar shaye-shaye
idanunshi jajir dasu


"Haba Abba Alaji ya zaka shigo babu sanarwa." Nasir ya fada cikin takaici da haushi


Tsaki Kamal ya ja yana cewa, "Kai me ya sa baka da hankali ne , to wallahi duk ranar da ka
sake zuwa gidan nan iya ka cinka can waje , zan matukar 'bata maka rai wallahi."


Abba Alaji ya sunkuyar da kai yana 'kun'kunai

"Ka fita waje ka jira ." Kamal ya sake fada cikin haushi


Abba Alaji ya bud'e kofa yana kallon Nasir da cewa . "Ka yi sauri fa ka fito ." Sannan ya fita



Tsaki Hajjiya ta yi tana fad'in ."Kun gani ba , Allah ya kyauta."


Nasir ya yi ajiyar zuciya yana cewa. "Ku yi hakuri mommy."

Kamal ya ce ."Ba dai wata matsala ko ." Ya yi maganar yana kallon Nasir


Nasir ya ce. "Babu komai Yaya Kamal na yi sallama da Daddy, zamu tafi ."

Nan su kai sallama baki dayansu , sannan Nasir ya fita ya samu Abba Alaji sannan suka d'auki
hanyar Ibadan

Laila ita ma ta shige ciki, yayin da Kamal yake cewa da mommy. "Bari na tafi mommy."

Mommy ta ce ."To Allah ya tsare hanya , a dawo lafiya."

"Amin mommy." Kamal ya fada yana fita waje


Yana fita yaje bakin motarshi ya tsaya cakkk , sannan ya yi ajiyar zuciya yana cewa. "Kai
rayuwa karki mini haka mana , amma ba komai ta bakin mommy din wataran sai labari komai
zai wuce , duk abin da hakuri bai baka ba tashin hankali ba zai kawo shi ba. "


Ya shige motar tashi yana ajiyar zuciya, yayin da mai gadi ya bud'e masa get .





Bayan Kamal ya isa kofar gidansu Fatima mai gadi ya bud'e masa get , yayin da ya shigo ya yi
burki ya fito

Mai gadi da gudu ya taho yana cewa. "Barka da zuwa Alaji, sannu da zuwa bakon barrister
fatima."


Cikin mamaki da duhun maganar da mai gadin ya yi Kamal ya nanata cikin ranshi ."Barrister
kuma ."

Sannan ya kalli mai gadin yana cewa. "Wato kasan da zuwana ke nan ."?


Mai gadin da shegen surutunshi ya kuma cewa ." Ai yalla6ai bani da aiki sai bacci , sai a zo ai ta
hon bana ji .Hakan ya sa barrister fatima ta sanar min da zuwanka domin kar nai bacci , domin
tasan hali na ."Ya karasa magana yana yankare baki yana dariya.



Shima Kamal dariyar ce ta kamashi , sai dai ya kasa gane mene ya sa ake kiranta Barrister


Daga can gefe Kamal yaji murya tana cewa. "To sarkin surutu Haruna mai gadi ."

Kamal ya juya da murmushi dan ganin waye

Alkalamin
Autar marubuta ne.



FATIMA DA ZARAHν ΌνΎ€

Na
Autar marubuta


________________________________________

*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
ν ΌνΌΉ__________ν ΌνΌΉ_________ν ΌνΌΉ__________ν ΌνΌΉ_________ν ΌνΌΉ
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_ν Ύν΄²ν ΌνΏΌ
<><><ν ΌνΌΉ><><><>ν ΌνΌΉ<><><>ν ΌνΌΉ<><><><>ν ΌνΌΉ<><><><><>ν ΌνΌΉ<><


Editing❌





Page 10 & 11






Habib ne ya karaso cikin far'a suna gaisawa da Kamal
Yayin da mai gadin yake masa kirari ."Ka ga daya daga cikin sojojin mu , ka ga jarumi Habibu
dan Alaji. "

Habib ya ce ."Dan Allah Haruna ka tafi ." Kamal yana dariya
Sannan mai gadin ya koma bakin aiki yana sake musu kirari



"To ya na same ku bro ."?

Kamal ya fad'a yana kallon Habib cikin farin ciki

A lokacin Khalid ya shigo yana tura kofa , yayin da me gadin shima yake masa kirari


Kai tsaye Khalid ya nufo wajensu Kamal yana cewa." Ahhh Habib bako ka yi ne ."
Yayin da yake mikawa Kamal hannu suna gaisawa

"Kaji ka Khalid, tom sirikin mu ne ." Habib ya bawa Khalid amsa



Cikin mamaki Khalid ya ce ."Au haba dai , ai wallahi ban gane shi ba." Ya sake mika hannu
suna gaisawa


Wani farin ciki Kamal yaji ya rufe shi da ganin 'yan uwan fatima



Haka sukai masa jagora har cikin babban falo suka zauna
Nan Habib ya kawo musu kayan motsa baki , kafin kace komai kuma hira ta 'barke tsakaninsu

Wajen minti biyar ke nan su kamo can su kamo can cikin farin ciki , kamal duk sai yaji ba abin
da yake damun shi



Lokacin da Habib yake basu wani labari suka ke ce da dariya , sai ga Alaji Mustapha ya shigo
falon


Girgiza kai ya yi alamun mamaki yayin da ya fara takowa wajen su ya fara cewa

."Sannunku jarumai , yanzu dama Kamal d'in ne ya zo amma kun sa shi a gaba kuna ta wani

dariya , maimakon ku sanar da fatima amma kuna ta masa surutu."


Kamal ya zube kasa yana gaida Alaji Mustapha cikin girmamawa

Bayan sun gaisa Alaji ya ce ."Yi hakuri fa Kamal, wai nan duk sojoji ne , amma babu kai ."


Dariya ce duk ta kusan kwace musu dajin zancen Alaji


Habib ya mi'ke yana cewa. "A yi hakuri Daddy bari a kira masa Fatiman."



"Wacce Fatima kuma zaka kira , yanzu lokacin kun cinye shi , dan haka ku tafi masallaci ku
dawo tukun ."



Habib ya ce ."To Daddy bari muje kafin mu rasa sallar ."



Alaji ya dubi Khalid da Habib yana cewa. "Saura idan kuka dawo ku sake sashi gaba kuna
zance, kuna dawowa ku sanar da Fatima."



Khalid ya ce ."In sha Allah Baba. "



Sannan suka wuce suka d'auro alwala suka tafi masallaci .







A 'bangaren Zarah babu abin da ya canza , domin yanzu tana tafe cikin motarta ta nufi asubiti,
tana zuwa babu jira ta fara duba marasa lafiya .

Bayan su Habib sun dawo daga masallaci, suka shiga ciki suka kira masa Fatima, yayin da
suka shige ciki.




Minti biyar ke nan Kamal yana zaune, kafin daga nan yaji sautin tafiya daga saman bene ,
wanda hakan ya tabbatar masa da cewa wannan Fatima ce take zuwa




Idanu ya zuba mata kafin ta karaso , tsayinta daidai dana Zarah, wannan tafi Zarah hanci da
manyan idanu , ta sanya bakar riga tare da ash din mayafi , cikin fatar hutu da kyau


Numfashi yaja yana kauda kanshi kafin ta fahimci yana kallon ta , ya yi ajiyar zuciya




Lokacin da Fatima ta karaso gaban Kamal duk yabi ya rude ya kid'ume sakamakon wani
kwarjini da take masa



"Assalamu alaikum." Fatima ta yi sallama tare da zama cikin nutsuwa



'Dago kai ya yi ya kalleta , maimakon ya amsa sallamar da tai ,cikin kidumewa ya ce


."Baku da yarah ne a gidan ."


Murmushi Fatima ta yi domin tabbas ta fahimci halin da ya shiga da ganin ta

Kamar za tai dariya ta ce ."Bamu da yarah , fatan ka zo lafiya ."




Sa da ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce ."Lafiya kalau wallahi tun d'azu nazo muna ta hira dasu
Khalid har mun je sallar mun dawo ."



Murmushi ta sake yi a karo na biyu yayin data kasa cewa komai ta durkusar da kai kasa


Shima haka Kamal ya gaza magana domin duk ya rasa kalmomin da zai magana dasu




Wajen minti guda kowa yana sa'ke-sa'ke a cikin ranshi



Sannan Kamal ya yi kokari ya ce ."Malama Fatima, nasan kin san iyayen mu sun saka ranar
auren mu .
Nan bada jimawa ba zasi mana aure. "




Fatima ta d'ago kai tace dashi ."Haka ne."


Sannan Kamal ya yi ajiyar zuciya yana sake cewa ."Rayuwa kaddara ce , a matsayinmu na
musulmai dole mu amshi kaddarar , a ko yaushe ta zo ." Ya karasa magana yana kallon Fatima



Murmushi Fatima tasa kana ta fara magana."Gaskiya ne , ina son karka mini karya a kowanne
yanayi ka sanar dani gaskiya komai muninta da zafinta ."

Kamal ajiyar zuciya ya yi daga bisani ya kalli Fatima ya fara cewa ."Najin dadin jin hakan ,
kamar yadda kika sani suna na Kamal, aikina a company ne , sannan ina da Zarah wacce
kullum ita ce mafarkina da nake son aura , amma Allah ke ce ya zaba mini ."



Ya kalli Fatima tare da sake cewa ."Sai dai banajin koda na aure ki bazan auri Zarah ba , ina
son Zarah kuma in sha Allah idan Allah ya so ita ma zan aure ta ."




Fatima wani zafin kishi taji ya dakar mata zuciya, amma lokaci guda ta share shi ta fuskanci
kamal tana fad'in


."Eh to yin Allah shi ne daidai ."

Murmushi ya sake mata a karo na ba adadi yana cewa
."Amma ni ban san komai game dake ba ."


Ita ma murmushi ta yi sannan ta d'aga idanunta tana kallon Kamal


Sannan ta fara magana. "Uhm .

Na yi karatun lauya a yobe , ni 'yar kasuwa ce , sannan kuma a halin yanzu ni lauya ce , ina
kuma fuskantar kowacce irin shari'a."





Murmushi ya yi har sai da hakoranshi suka bayyana

Sannan cikin ranshi yake cewa ."Okay yanzu kin fiddani duhu barrister. "

Sannan ya fito fili yana cewa. "Barrister Fatima.

Tabbas kuwa zan aikata abin dana ke so ko."?

Dariya Fatima ta yi sannan......






Hajjiya Amina ce zaune a falo ita da Laila
Laila ce take cewa ." Mommy kin ga har yanzu Yaya Kamal bai dawo ba ."


Hajjiya ta ce ."Ai duk inda yake yanzu yana hanyar gida ."



Laila ta sosa 'keya ta kalli Hajjiya, sannan ta fara cewa ."Mom Ahmad ya ce fa zai turo ."



Kallon Laila ta yi tana cewa. "Wai me yake ci na baka na zuba , yanzu ta auren Kamal ake , ya
bari a gama tukun ."



"To mommy a had'a mana dana yaya da namu ."

Hajjiya ta kalli Laila cikin mamaki tana cewa
."Eh gaskiya ne zamani ya lalace , to sannu Laila da wannan 'karfin halin , to kije ki sanarwa da
Alaji mana ai shi ne zai miki auren ."



Dariya Laila ta kwashe da ita tana kwanciya a kafar Hajjiya

Ita ko Hajjiya tana sake jin mamakin zancen Laila ta ce ."To ai kuwa ana yin na kamal zan sa
Alaji ya kawar dake tunda kin fara tuna ....."


Bata karasa magana ba , sallamar Kamal ta katseta

Kamal ya karasao ya zauna tare da cire hular kanshi

."Sannu da zuwa Yaya Kamal. " Laila ta fad'a
Yayin da ya amsa mata


."Mommy na dawo kuma Fatima tana gaidaku ."
Kamal ya fad'a yana cire agogon hannunshi


Murmushi najin dadi Hajjiya ta yi, ganin yadda d'an nata yake ta farr 'a


Kafin ta ce komai ya tashi yana cewa. "Bari na watsa ruwa Mom." Ya nufi sama




Bayan wasu kwanaki



IBADAN

Samari ne su uku suna zaune suna karatu a cikin dakinsu cikinsu kuwa har da Nasir , duk babu
wanda yake cewa da kowa komai , duk booklet ce a hannunsu


Sautin kawai Bashir ake ji , da yake yin karatun a zahiri

Tun d'azu Khalifa yake gallawa Bashir harara , sannan yaja tsaki

"Wai Khalifa idan baza kai karatun nan ba ka ajiye mana , sai tsaki kake mana ."


Nasir ya yi magana yana aje handout nashi



Cikin haushi Khalifa ya ce ."Wannan banzan ne mana Bashir ya yi karatu a zuciya ya'ki sai
damuna yake. "

Dariyar 'keta Nasir ya kwashe da ita .

Yayin da Khalifa ko sauraransu bai yi ba , ya cigaba karatun shi


Haushin hakan ya sa Bashir fisgar handout din yana jefarwa gefe


Nasir ya sake fashewa da dariya , kawai Khalifa yaja tsaki yana fad'in

."Ka kiya ye ni fa , ni wallahi ma inajin nan da sati zanje gida ."




Nasir ya ce ."Ka bari sai bikin Yaya Kamal

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login