Showing 36001 words to 37591 words out of 37591 words

Chapter 13 - FATIMA DA ZARAH NA AUTAR MARUBUTA.pdf

Advertisement

24 Jun 2025

1948

komai da zan biyaki Fatima, hatta kalaman da zan nuna miki matsayinki a guri na bani
dasu , ki gafarce ni."


Murmushi Fatima ta sake yi tana kallon Zarah, Zarah ma ta maida mata da murmushi tana
cewa.
"Wallahi Fatima ina kaunar ki matukar gaske dan Allah ki yafe mini duk abin dana yi miki wanda
baki ji dadi ba."

Dariya Fatima ta yi tana cewa.
"Jibeta dan Allah."

Nasir da yanayin ya masa dadi ya yi dariya



A lokacin aka fara kwankwaso kofar falon .
Kafin kowa ya yi motsi aka fara kallon -kallon domin basa tsammanin zuwan kowa a halin yanzu


Nasir ya tashi ya nufi kofar a domin budeta

Yana bud'e wa ya ga Faruk ya fara shigowa , yana shigowa ya kalli falon ya gansu duk a zaune
suna kallon shi

Lokaci guda kuma suna had'a ido da Alaji Sale.

Fatima ta mike tsaye

Sannan su Ahmad dasu Murja ,Najib suka shigo

Kamal ya tashi ya nufi wajensu yana musu nuni dasu karaso

Suka kalli juna , sannan suka nufo falon ,
Duk suka zazzauna , yayin da kujerun suka cika ne babu gurin zama shi kuma Faruk yana
tsaye .


Alaji Sale ya kalleshi tare da matsawa gefe yana ce masa
"Faruk karaso ka zauna ga guri ."


Ya kalleshi tare da tuna irin sa'insar da sukai kafin shiga kotu , sannan yayi ajiyar zuciya tare da
duba agogon hannunshi ya nufi wajen shi ya zauna.




Autar Marubuta
FATIMA DA ZARAHν ΌνΎ€
Na
Autar Marubuta
_______________________________________

*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
ν ΌνΌΉ__________ν ΌνΌΉ_________ν ΌνΌΉ__________ν ΌνΌΉ_________ν ΌνΌΉ
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_ν Ύν΄²ν ΌνΏΌ
<><><ν ΌνΌΉ><><><>ν ΌνΌΉ<><><>ν ΌνΌΉ<><><><>ν ΌνΌΉ<><><><><>ν ΌνΌΉ<><



Editing❌

Page 46 & 47 ________the end


Sannan ita ma Fatima ta zauna tana kallon kowanne su , shiru aka yi kowa yanata sake-sake
cikin ransa


Jin wannan shirun yasa Faruk ya kalli Fatima ya fara magana cikin sanyin rai .
"Ba ke ba ce lauyan mu , amma tamkar ke ce kika bamu kariya .
Bawai nufin mu shi ne tozarta Zarah ba , muna cikin radadin da yunwar rashin mommy hakan
yasa idanun mu suka rufe ."

Alaji Sale ya yi murmushi yana sake kasa kunne

"Komai ya faru cikin fushi ,hakan yasa na zo neman a fuwarki Fatima ki yafe mini da abin da ya
faru ."


Murmushi Ahmad ya yi na farin ciki yana kallon Najib

Fatima ta kalli murja kana ta maida ido ga yayan nata tana cewa.
"Babu abin da kayi mini Yaya faruk, ni ce na yi muku laifi dan Allah ku yafe mini ."

Murja ta ce .
"A yanzu muna matukar alfahari dake Fatima wancen rudanin muna cikin yanayi ne . "

Fatima ta ce .
"Karki damu aunty na , komai lokaci ne , kawai na shiga damuwar rashin ku da rashin mommy a
lokaci guda amma tunda kun dawo gare ni komai ya wuce ."

Ahmad ya ce .
"To alhamdulillah Fatita."
Ta masa murmushi

Sannan Faruk ya kalli Alaji Sale dake gefenshi yana fadin

"Ina mai baka hakuri bisa rashin jituwar da ..."

Alaji ya dakatar dashi yana cewa .
"Baka yi min komai ba, domin duk wani d'an na gari shi ne abin da zai yi a kan iyayensa , kuna
da kanwa jaruma babu abin da kuke bukata ."


Murmushi Faruk ya yi a karon farko kana ya ce
"Na gode Allah Allah ya sake had'a kan mu ."

Suka had'a baki suka ce .
"Ameen ."


Lokacin Murja ta ce .
"Tom mufa daga nan zamu wuce saudiya domin har gidan Alaji mun biya mun yi sallama."

Kamal ya ce .
"A haba dai aunty a yau kuma ."?


Ahmad ne ya fara ba shi amsa da cewa .
" In sha Allah kuwa nan da mintina jirginmu zai tashi ."


Zarah tai murmushi tana cewa.
"Dan Allah Yaya faruk ku yafe mini idan nayi muku laifi ."


Murmushi ya kuma yi a karo na biyu yana cewa da Zarah.
"Ba ki mana komai ba Zarah, mune zaki gafarta ."

Murja ta ce .
"Haka ne ."

Zarah ta kuma fadin .
"Hakika kuna da 'yar uwa ta musamman. Fatima mutuniyar kirki ce ."

Fatima tai saurin cewa .
"Ai ban kai ki ba ."
Zarah ta galla mata harara


Faruk ya tashi tsaye hakan yasa zugar shi duk suma suka mike , sannan kowa da kowa ya tashi

Lokacin Alaji Sale yake cewa.
"Ya kamata ku zauna mu yi addu'a."

Kowanne su ya zauna sannan suka gabatar da addu'a har aka sanya mahaifiyar su, suka yiwa
annabi salati suka shafa .

Sannan suka tashi

Fatima ce tace .
"A gaida mini da kowa dan Allah, su Abu Junaid da Habibullah da Hafiz da kowa da kowa
gaisuwa ta ta isa gare su kafin na zo ."
Murja ta ce .
"Zasu ji insha Allah."

Alaji Sale ya ce .
"Ai zamu zo saudiyan in sha Allah zamu kawo muku ziyara ."

Faruk ya ce .
"To Allah ya kawo ku muna ta zuba ido."

Sannan duk suka rankaya suka fita ,
Nasir ya hau mota guda a domin kaisu filin jirgi, nan aka sake sallama suka wuce .

Shima Alaji nan suka hau motarsu suka koma gida


Bayan...

Yau Burin Nasir ya cika , karatun da ya jima yanayi domin a bud'e masa company yau Allah ya
tabbatar, domin yau aka gabatar da taron bude wannan company

Bayan sun dawo gida suka zazzauna a falo , Nasir ya shige ciki

Sai gashi ya fito da katuwar jakarshi yana cewa
"Tunda mafarkina ya zama gaskiya yau zan koma gidan Alaji."

Duk suka zuba masa idanu a tare
"Lallai ma yaron nan tun yau zaka koma ."?
Cewar Kamal

Nasir ya yi dariya mai cike da farin ciki yana cewa.
" Tabbas kuwa Yaya zan koma kusa da mommy, daman karatu ne ya kawoni tom yau nima na
zama babba zan koma gida ina maka godiya Yayana."

"Ka bari sai gobe mana ka karasa shiryawa ." Fatima ta fada

Nasir ya kuma dariya yana cewa.
"Ai na gama shiri aunty tun jiya wallahi, kawai gida zan yi yau ."


Kamal ya yi dariya yana cewa.
"Har ka bani tausayi ka bari mu zo mu kai ka mana ."

Dariya Nasir ya kumayi yana fadin
"A'a Yaya kusha hutunku , domin nima mata biyu zanyi wannan rayuwar taku tana burgeni ,
mata biyu zan auro nima ."


Kamal ya tabe baki yana cewa.
"Kunji shi , to wallahi kar ma ka fara domin matan ba haka suke ba , ni ne dai kawai Allah ya
za'ba ya bani su , ka bari idan Zarah ta rubuta labari a kan mu , idan matan sun yi sanyi sai ka
auro gudu 4 ma ."


Dariya duk suka kwashe da ita dajin zancen na Kamal

Nan Nasir ya wuce ya tafi suna masa fatan alheri .


Zarah ta kalli Fatima tana cewa.
"Yanzu mun zama jini daya aunty Fatima, babu sa'insa ."

Fatima ta yi murmushi tana cewa.
"In sha Allah Zarah ta ."

Kamal ya rungumosu a tare yana cewa
"Ina alfahari daku matana fiye da rayuwata."

Suka had'a ido sukai murmushi



Bayan wasu shekaru

Zarah ce ta fara haifowa Kamal mace , wacce ta ci sunan Hajjiya Samira marigayiya.

Sannan ita ma Fatima ta sunlubo tata 'yar wacce aka sawa Suhaila

Shima Nasir tun tuni ya yi aure har matarshi ta haifo 'yan biyu Mace dana miji
Na mijin yaci sunan mahaifin shi , yayin da macen ta samu sunan mahaifiyar Kamal , wato
Hajjiya Amina .


Haka gidan Kamal ya cigaba da kasancewa cikin farin ciki da kwanciyar hankali, wadata da
girmama juna a tsakanin su .

ALHAMDULILLAH...
Komai ya yi farko zai karshe da ikon Allah
Anan ni Autar Marubuta na kawo karshen wannan kagaggen labari nawa mai suna
FATIMA DA ZARAH.


Godiya ga dinbin masoya a duk inda suke masu yin sharhi , Allah ya bar kauna.


Ina fatan sake kasancewa daku cikin wani sabon labarin nan bada jimawa ba in sha Allah.

A bin da ya faru na daga kuskure Allah ya ganar dani , wanda ya faru sanadin karancin ilmi
Allah ya haska mini a nan gaba, Allah ya bada ikon daukar darasin dake cikin wannan labari.


To anan zan barku ni Autar Marubuta na ke cewa Allah ya sada mu da alheri.🙏



07040805269
WhatsApp
____________________________ν ½ν²”

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login