Showing 18001 words to 21000 words out of 37591 words
Hajjiya Sa'adatu ce ta yi murmushi tana cewa.
"Ai dole , amma dan Allah idan ta zo karta tafi baki hada mu ba Fatima, domin bazan ji dadi ba
."
Fatima ta ce ."In sha Allah mommy zan hada ku , idan ta zo ."
"Ta shi mu koma Ahmad." Najib ya fada cikin yaren larabci
Duk suka tashi tsaye
"Haba dan Allah yaya wai tafiya zaku yi ."? Fatima ta fada da matukar haushi .
Ahmad ya CE ." In sha Allah, kina so mu kwana anan ne , karki damu nan da wata biyu zamu
zo mu yi sati a Nigeria. "
Ya karasa magana yayin da sukai sallama dasu Hajjiya da Mahmud
Kafin su isa bakin kofa
Kamal da Nasir suka shigo suna dariya suna hirarsu .
A wannan lokacin ne suka lura da irin manya manyan bakin da sukai
Kamal ya ma kasa cewa komai , domin ya rasa dasu waye ma zai fara magana
Da sauri ya karaso cikin falon yana cewa.
"Ka ce yau manyan baki mu kai , ai dana san zaku zo babu inda zan fita ."
Suka mika hannu suka gaisa da su Ahmad da Najib dake tsaye
Sannan ya karasa ya gaida Hajjiya suka kuma gaisawa da su Mahmud
Kamal ya kalli Fatima yana cewa.
"Yana gansu a tsaye ."
Fatima ta ce ..
"Wai tafiya zasi fa ko minti 30 basi ba ."
Kamal ya karasa gabansu yana cewa.
"A haba dai yaushe rabon ku zo , kuma ku ce zaku tafi Ahmad."
Ahmad ya yi dariya sannan ya ce .
"Wallahi zamu rasa jirgi dole mu tafi , tunda Allah ya yi zamu gaisa da kai ."
Najib ya ce .
"Gaskiya ne , sai wani lokacin kuma ."
Suka nufi hanyar fita yayin da Kamal da Zarah su kai musu rakiya
Bayan sun dawo ne Hajjiya take cewa .
"Ku tashi ku yi sallah muma mu tafi ."
Kamal ya dubi Fatima yana cewa.
"Wai ina Zarah ne , ko dai bata dawo ba ."
Fatima ta ce .
"Eh."
"Bari na kirata mana ." Ya dauki wayarsa
Hajjiya ta ce .
"A" a barta wallahi, Fatima ma tace zata kirata ni na hanata , ai baza mu jira ba gaskiya, in tana
son ganin mu ta zo gidan kawai ."
Kamal ya yi ajiyar zuciya ya aje wayar yana cewa.
"Ai ya ci a ce ta dawo ."
Hajjiya ta tashi ta dauro alwala , bayan suma su Mahmud sun yi sallah suka koma gida .
Next page in sha Allahí ½í¹
FATIMA DA ZARAHí ¼í¾€
Na
Autar Marubuta
________________________________________
*AUTAR MARUBUTA CE*âœí ¼í¿»í ½í±¼í ¼í¿»
í ¼í¼¹__________í ¼í¼¹_________í ¼í¼¹__________í ¼í¼¹_________í ¼í¼¹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_í ¾í´²í ¼í¿¼
<><><í ¼í¼¹><><><>í ¼í¼¹<><><>í ¼í¼¹<><><><>í ¼í¼¹<><><><><>í ¼í¼¹<><
EditingâŒ
Page 24 & 25
Lokacin da Zarah ta dawo ta yi matukar takaici na rashin samun bakin da akai .
Anan cikin gidan Alaji Mustapha kuwa
Hajjiya Binta ce , zaune a falo ita da Abba Alaji, sakamakon yau ya zo gidan
Kallon shi ta yi sannan ta ce .
"Yau kuma an tuna dani ke nan har an kawon ziyara ,
To ka gama makarantar ne ."?
Murmushi Abba Alaji ya yi sannan ya d'ago yana cewa.
" Tun yaushe ma kuwa ai sakamakon ya yi kyau ."
Dogon tsaki hajjiya Binta ta ja kana ta ce .
"Ka ji makaryacin banza , daman jin bakin ka zan , tun yaushe Alaji yake sanar mini , ka yi abin
da ka yi an kore ka ."
Abba Alaji ya d'ago yana kallon ta da idanunsa na rashin kunya yana cewa.
"Au to tunda kin sani mene na tambaya kuma ."
Hajjiya Binta ta yi ajiyar zuciya tana sake kallon takaici ga Abba tana cewa.
"Wallahi ka kiyayi duniya Abba, yayana yana iya yinsa don ganin ka zama mutumin kirki , amma
kai kullum kana yawo kana jawo masa magana ana zaginsa , to ka cigaba Allah ya gani ai idan
ka kashe shi sai hankalin ka ya kwanta ."
Abba Alaji ya d'ago da jajayen idanunshi yana cewa.
"Ke kinji ki Aunty ta ya Daddy zai mutu, ai kuma Daddy yana sona ."
Hajjiya ta ce .
"Dah ne yake son ka wallahi Abba da zaka zama mutumin kirki, ba karamin dadi za ka samu
wajen Alaji ba , amma kai ne can neman fitina iri-iri .
To wallahi daman ya ce komai ya ishe shi zai jire hannunshi a kan ka .
To tun kafin haka ta faru ka gyara halinka , ka zama mutumin kirki, ka dena shaye-shaye, yanzu
dubi irin askin dake kanka kamar ba d'an musulmi ba ."
Abba Alaji cikin bacin rai ya tashi tsaye yana cewa.
"Ke kinji ki , shi ya sa bana son zuwa gidanki wallahi , gara ma na tafi sai anjuma ."..
Ya nufi kofar fita tana kiran shi , ko juyowa bai ba ya fice abinsa .
Ta yi ajiyar zuciya tana cewa.
" Allah ka shirya mana wannan yaro ."
Yau su Fatima suka kai ziyara gidansu kamal, har suka gano kayan lefen Laila wanda biki
sauran sati biyu .
Misalin 9 na dare .
Duk su kamal suna zaune a falo suna kallo .
A lokacin Laila ta turo kofa ta shigo tare da sallama da wasu ledoji a hannunta.
Kamal ya yi ajiyar zuciya kafin ya ce .
"Yanzu a wannan daren Alaji ya barki kika fito , ba an ce ki bari gobe ki kawo kayanka ba ."?
Laila ta tabe baki tare da fara yo taku zuwa cikin falon tana cewa.
" Wallahi yaya bana son fita da rana ."
Kamal ya ja tsaki
Nasir ya ce .
"Ka ga wai ita amarya tabb , za a ga wani abu ."
Fatima da Zarah sukai dariya
Laila ta kalli Nasir tana cewa.
"Kai dai kaji kunya wallahi, kullum tsokana mtww."
Nasir ya yi dariya yana cewa.
"Naji dadi ma sanda zan dawo gidan ba kyanan ai gara ...."
Bai karasa magana ba kamal ya katse shi da cewa .
"Zaka bari ta yi abin da ya kawota ko kuwa sai dare ya kuma yi ."
Nasir ya yi shiru
, Laila ta masa kwalo , sannan ta zo ta zauna
"Aunty Fatima da Aunty zarah ga kayan zuwa dinner din ku , yau muka am so su har da nawa ."
Suka amsa suka bud'e nan suka yaba katafaren kyan da dinkin ya musu .
"To tashi Laila tashi maxa dare na yi ." Cewar Kamal
Laila ta tashi tana cewa.
"Haba yaya kamal daga zuwana ."
Zarah ta ce .
"Ai shi ne ."
Kamal ya ce .
"Ni wallahi bansan me ya sa su mommy suka bari kika fito ba ma ."
Ya kalli Nasir yana cewa.
"Tashi ka rakata har gida ."
Haka Nasir ya sa Laila gaba har suka isa gida
Zarah ce ta ce .
"Za'a sha dinner kam zamu sha liki ."
Fatima ta yi murmushi
Kamal ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce .
"To duk nasan halinku wallahi kar wacce taje ta lika sama da Naira , na dai fada muku ."
Ya tashi ya shiga ciki .
To Allah ya kai mu wannan biki , domin Alaji Mustapha ya yi matukar yin sa don samun farin
cikin Laila, yadda ya riketa bata taba kukan rashin iyaye ba , to haka ma a wannan biki ya aje
mata abin da zatai alfari dashi matukar gaske .
Kowa ya shiryawa wannan biki , musamman wajen dinner irin babban mawakin da aka gayyato
, ga baki duk sun hallara , 'yan uwan amarya dana ango gurin taro ya cika fall masha Allah.
Ga Alaji Mustapha da Alaji Mansur duk sun sha ado , su Hajjiya Amina iyayen amarya
Kamal ma an sha kyau matuka, ga Nasir da abokanshi , Fatima da Zarah sun sha kaya irin
daya sun yi matukar kyau
Kawayen amarya da manyan baki sai murna ake
A can daga saman stage ga Laila amaryaí ½í±°
Tare da angonta Dactor Sadiq sun hadu sosai sai jan hankali suke .
Mawakin da aka gayyato yana fara wakarsa , su Alaji Mustapha suka ja zugar su , domin yin
wani pati din da ya shirya don haka babu wasu manyan iyaye maza a gun
Gurin sai tashin kamshi yashe da walwali
A lokacin ne aka saki wakar da aka yiwa amarya ta fito ita da angonta suna takawa .
Kafin ka ce komai 'yan uwa suka fara zuba liki
Hajjiya Amina ce ta zo da wasu kudi dummm tuli guda zugar dubu-dubu tana likasu
Shima kamal ya kwaso nashi ya zuba musu ya koma
Fatima da Zarah suka taso
Zarah ta fara likin dari biyar biyar masu yawa ,
Fatima na ganin haka , ta maida kudin hannunta ta d'ebo dubu-dubu tana lika musu
Lokacin da Zarah ta fahimci hakan , sai ta zaro daloli a cikin jakarta tana rawa tana likawa
Ita ma Fatima wannan dalolin ta kwaso a jaka kawai tana watsawa .
Tuni guri ya rude , kowa hankalinshi ya koma gun su , maxa da mata kuwa ana fadin "matan
Kamal ne
Da Fatima da Zarah, daya lauya ce dayar kuma likita ce ."
Haka wanda basu san masoyiyarsu Zarah Sale ba suka ringa farin cikin ganinta .
Guri ya rude da dalolin dasu Zarah suke watsawa
Shi kam Kamal ranshi idan ya yi dubu , to duk sun 'bata masa shi
Ya matukar jin bakin ciki yadda suke gasar zubar da kudi a gurin nan ko a jikinsu .Bayan jan
kunnen da ya yi musu amma sun yi watsi da maganar sa.
Haka ran kamal ya sake matukar baci , kawai ya fita , ya hau mota ya nufi gida .
Yana tuka mota abin yanata damunsa a ranshi
"Yanzu me suke nufi ban isa dasu ba ke nan kome , kudi hauka ne , suna da ilmi amma vasa
amfani dashi ."
Cikin bacin ran nan ya koma gida , ya zauna a falo abinsa .
Anata cakarewa ana murna bayan an tashi suka nufo hanyar gida .
Nasir ne ya fara shigowa bai ma kula da Kamal ba , hakan ya sa ya nufi dakinsa.
Fatima da Zarah suka shigo suna magana , inda Zarah take cewa .
"Bari kuma gobe , ai wannan kudin ba komai ba ne , dan ma dear ya hana canza mota mai
tsada ."
Fatima ta ce .
"Zancen kike so an ce da gwauro ya iyali ."
Suka karasa falon a daidai wannan lokacin suna zama
Wani bakin ciki Kamal yaji ya sake turnike masa zuciya, wato ma ko nadama basa yi
Yadda Kamal yake jinshi zai iyay musu komai idan bai kai zuciyarshi nesa ba , don ji yake
kamar ya rufesu da duka .
Haka Allah ya hani kowacce a cikin su da ta lura da halin da Kamal yake ciki , bare si masa
magana .
"Aikin kawai dadin abin ni na canza mota , ke ce ta gagare ki." Cewar Fatima
Zarah ta ce .
"Dan kin canza mota ai ba .. "
Kafin Zarah ta karasa magana taji saukar mari a kuncinta , kafin Fatima ta kula da abin da yake
faruwa ta ji ita ma an sauke mata wannan mari .
Kamal ne a tsaye a kansu idanunsa sun yi jajir , jijiyoyin kanshi duk sun tashi , sai wani huci
yake , ka ce wani zaki.
Ya kalli kowacce dake rike da kuncinta cikin mamaki da suke kallon shi
"Ku wanne kalar marasa tunanine da rashin hankali.
Ni ban isa daku ba , duk irin maganar dana fada muku , bayan kun aikata abin da kuka gadama
a wajen dinner kun zo gida kuma zaku tayar mini da hankali."
Yaja dogon ajiyar zuciya mai zafi sannan ya cigaba da magana .
Next page
07040805269
WhatsApp only.
FATIMA DA ZARAHí ¼í¾€
Na
Autar Marubuta
________________________________________
*AUTAR MARUBUTA CE*âœí ¼í¿»í ½í±¼í ¼í¿»
í ¼í¼¹__________í ¼í¼¹_________í ¼í¼¹__________í ¼í¼¹_________í ¼í¼¹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_í ¾í´²í ¼í¿¼
<><><í ¼í¼¹><><><>í ¼í¼¹<><><>í ¼í¼¹<><><><>í ¼í¼¹<><><><><>í ¼í¼¹<><
EditingâŒ
Page 26 & 27
"Ina hankulanku suke , ko daman babu ne ."?
A wannan lokacin Fatima ta sunkuyar da kai wasu hawaye suna zuraro mata
"Kun bani kunya , kun bakantan zuciya da rayuwa, tun a gida na sanar daku bana son
almubazzaranci amma dake ni ba komai bane a wajen ku , kuka ture magana , kun nuna ban
isa daku ba koh."?
Ya jefa musu tambayar yana zare jajayen idanunshi.
" To daga yau zan dau mataki a kan ku , tunda aikin lauya d Likita kuke takama dashi duk zaku
janye shi , zan yi maganinku ."
Ya nufi kofar dakinshi cikin huci .
Zarah ta cire hannu a wajen marin tana ajiyar zuciya.
Anan gidan Alaji Mustapha kuwa
Suna falo tare da Hajjiya Binta da mahaifin Abba Alaji wato Alaji Sani
Bayan Alaji Sani ya gaisa da Alaji Mustapha, nan suka gaisa da kanwarshi Hajjiya Binta
"To Alaji yanzu babu wata makaranta da aka samawa Abba Alaji ne ."?
Hajjiya Binta ta tambayi yayanta .
Alaji Sani murmushi na ciwo ya yi sannan ya ce .
" Dan Allah ki dena mini zancen Abba, Allah ya gani na yi abin da zan yi akanshi , na gaji
wallahi, Allah ma ya sani , idan ba so yake ya kashe ni ba,
Yaron nan zan aje kudi na , kudin mutane duk ya kwashe , a'a wallahi na gaji , in ya shigo
hannuna ai wallahi sai dai a kwace shi ."
Cikin bacin rai ya aje magana.
Alaji Mustapha ne ya ce .
"Ai hakuri za kai Alaji Sani , hannunka ba zai ribe ka yanke ka yar ba , kawai addu'a zaka
runguma komai zai wuce in sha Allah."
Alaji Sani ya sake murmushi na takaici yana cewa.
"Addu'a ta nawa kuma Alaji Mustapha, kuma idan hannuka ya rube dole kuwa ka yanke ka yar
."
Alaji Mustapha ya ce .
"A dai cigaba da addu'a zai shiryu in sha Allah, Allah ya shirya mu ya shirya kowa da kowa ."
Hajjiya Binta ta ce .
"Amin ya Allah."
Alaji Sani ya tashi tsaye , yana cewa.
"To bari na koma ga shi kuwa dare ya yi ."......
Washe Gari da safiya ta yi
Kamal babu wacce ya ce da ita komai, ko abinci bai saurara ba ya fara shirin tafiya company.
Ganin haka yasa Fatima da Zarah suka tare shi suna ba shi hakuri .
Samm Kamal ba shi da niyyar hakura ,
Amma da suka fahimci duk laifunsu ne da suka kai shi bango har kuka suka yi suna ba shi
hakuri.
A lokacin zuciyarshi ta karaya , ya tabbatar musu ya yafe musu , domin ma saida ya karya
sannan ya fita .
Sannan aka samu saukin rayuwa a cikin gidan .
Misalin karfe 1 na dare kowa ya kwanta,
Gama karatun Nasir ke nan zai fara bacci yaji wayarshi na ringin yaja dogon tsaki ya katse kiran
" Abba Alaji ko mara zuciya, uban me zan masa ma a wannan daren , ni bansan ma me yasa
ban goge number shi ba ."
Nasir ya aje maganar yana tsaki
Yayin da kiran Abba Alaji ya sake shigowa .
Nasir ya dauki wayar cikin masifa yana cewa.
"Mene kuma a wannan lokacin."
Nasir daga can kasa ya jiyo muryar Abba Alaji cikin jigata yana cewa.
"Dan Allah Nasir ka fito ka taimaka mini , ina kofar gida ."
Nasir yaja tsaki ya kashe wayar
Mamaki yaji ya kamashi yadda yaji muryar Abba cikin wani hali
Hakan yasa ya tashi ya bude kofar shi ya leka falo , yaga babu kowa , sannan ya fito cikin
sanda ya bude kofar fita a hankali ya fita ba tare da ya rufe ba
Ya fita waje
Yana fita yaga Abba Alaji da farar singlet jikinshi duk jini, fuska duk ta