Showing 3001 words to 6000 words out of 37591 words
Bayan sun fita Alaji ya yi ajiyar zuciya, yayin da Fatima ta kalli mahaifinta tana cewa ,"Dan Allah
Daddy ka yi hakuri."
Alaji Mustapha ya ce ,"Karki damu Fatima ba zaman lafiya suke so ba ,
Ke yarinya ce mai tausayi da hakuri kamar mahaifiyar ki .Allah ya yi miki albarka."
Fatima ta amsa da ,"Amin Daddy. "
Alaji Mustapha zama ya gyara yana kallon Fatima da niyyar fara sabuwar magana
"Sannan kuma Fatima akwai al'amarin da nake son sanar dake , domin ina da tabbacin baza ki
bani kunya ba."
Ta ce ,"In sha Allah Baba. "
Jin haka ya sa ya cigaba da cewa ,"Na yi magna da mahaifiyar ki , sannan na sanar da ita na
tsayar da ranar auren ki."
Cikin mamaki da tashin hankali Fatima ta kalli Alaji
"Aure kuma Daddy." Cikin mamaki
Ya kalleta cikin sake jaddadawa ya ce ,"Eh Fatima aure , baki da mahaifin da ya fini , kuma zan
yi domin farin cikin ki , duk inda zan shiga in fita domin sama miki farin ciki shi ne burina Fatima,
kuma zan shiga dukkan hatsari domin baki kariya, wannan shi ne za'bin da na miki a matsayina
na mahaifin ki Fatima. "
Ya yi shiru yana jiran Fatima ta ce wani abu
Jin bata ce komai ba ya sa shi cewa ,"Baki ce komai ba Fatima. "
Murmushi ta yi sannan ta d'ago kai tana cewa ,"Daddy ni fa 'ya ce a gare ka , na yi imani kana
son farin ciki na , ka yi mini komai Daddy, wallahi na amince da wannan auren har cikin zuciya
ta."
Wani abu Alaji Mustapha yaji ya takure masa ran sa na farin ciki da matukar tausayin Fatima
Cikin ajiyar zuciya ya fara sabuwar magana ,"Ban yi zaton abin dana shirya zaki kar'ba ba , ban
yi zaton farin cikin da nake hangowa zan samu ba ." Kawai Alaji kuka ya fashe dashi cikin wani
yanayi mara dadi
Hakan yasa Fatima tashi tsaye cikin tashin hankali tana cewa, "Dan Allah ka dena kuka , Baba
ka haifa ne mene amfanina idan ban share maka hawaye ba kawai ka dena kuka dan Allah na
roke ka."
Ajiyar zuciya ya yi mai zafi sannan ya share hawaye ya dubi Fatima
"Dole na yi kuka Fatima, domin a wannan zamanin akwai wahalar samun 'ya kamar ke, Allah ya
yi miki albarka ya sa ki ciki da Kalmar shahada."
"Amin ya Allah Daddy." Abin da fatima ta fad'a ke nan
Kallon shi tai cikin kunya da son jin amsa ta ce ,"Da waye za ai Daddy. "
Sai da ya yi mata murmushi ya gyara zama kana ya ce ,"Zumunci mai kyau Fatima zamu
kasance har a aljanna tare , Yaron Alaji Mansur wato Kamal. "
Dauuuuuu
Abin da zuciyyarta ta fad'a ke nan , tasan dai da cewa Alaji Mansur guda daya ne kuma haka
Kamal shi ne d'anshi wanda ta sani
Murmushi ta yi kawai ba tare da cewa komai ba domin karta 'batawa mahaifinta yanayin da
yake ciki
"Allah ya faran ta maka Baba ya cika muradan ka."
"Amin Fatima ki fara shiryawa a sanarwa ga duk wanda ya dace , sannan kamal din yana nan
zuwa."
Wata zabiya ce ta rad'o sallama cikin falon , hakan ya sa maganar tasu ta dakata
Sa'arr Fatima ce ta shigo gidan cikin shiga da zamu iya cewa matar aure ce
Nan ta durkusa suka gaisa da Alaji cikin ladabi da biyayya .
Sannan su kai cikin daki da Fatima
Bayan sun gaisa Fatima ta kwanta kan gado kamar mai shirin bacci hakan yasa kawar tata mai
suna Fiddausi ta ce ,"Fatima ke nan hala dai kina da damuwa."
Sai da Fatima tai wani irin kashe idanu tana kallon Fiddausi sannan ta tashi zaune tana cewa,
"Rasss nake kawata , kawai dai ina sanar dake mun kusa shigowa sayun ku."
Ta karasa maganar cikin kasalalliyar murya
Dariya Fiddausi ta yi tare da cewa ,"Kina nufin fa aure ke nan ."
Nannauyar ajiyar zuciya fatima ta aje tana cewa,"Kwarai kuwa nan da wata guda ma."
"Abin mamaki wannan aure bakatatan haka Fatima, amma dan Allah waye angon."
Murmushi ta yi kafin bata amsa cikin nutsuwa Fatima ta fara cewa ,"Na shirya tunkarar
kaddarata ko wacce iri ce , bani da damuwa ko fargaba Fiddausi, duk yadda rayuwata ta juya
mini zan yi abin da ya dace ."
Ta aje maganar tana kallon Fiddausi, sannan ta d'ora da cewa ,"Kin san dai abokin baba Alaji
Mansur to d'ansa ."
Cikin mamaki matuka Fiddausi ta kalli Fatima
"Wai kamal kike nufi ."? Ta jefa mata tambaya da mamaki
Dariya Fatima ta yi , daga bisani ta ce ," Ke ma dai kinsan ba shi da wani d'ah banda Kamal. "
"Tabbbbb! Jan aiki kika d'auko ki ce ." Fiddausi ta fad'a tana ri'ke ha'bar ta
Bata jira cewar Fatima ba ta cigaba da magana ,"Wannan gayen da kowa yasan yarinyar da
yake so Zarah Sale .Wannan yarinyar da suke da uwar kudi da kadarori , sannan gata
marubuciya mai masoya , kuma likita ce fa.Me ya kai ki ke kuwa Fatima ga Kamal. "?
Tsaki Fatima taja najin haushin kalaman kawar tata hakan ya sa ta fara cewa ," Ke kika san
wata Zarah Sale da kike karanta novels, amma koma wace ita , ni Fatima na tabbatar baza ta
fini komai ba , kudin banza Fiddausi, muna da kudi muna da komai , dan haka shima Kamal d'in
ko ya yake santa shi ya sani ga zabin iyayensa ."
"Babbar magana." Cewar Fiddausi
"Ai ko dai da kina karanta novels zaki san Zarah sale Salisu.To wannan aure ni dai Allah ya
nuna mana ."
"Haka za ki ce kawai." Fatima ta fad'a tana hararar kawar tata.
07040805269
WhatsApp only
Alkalamin Autar marubuta ne .
FATIMA DA ZARAHν ΌνΎ
Na
Autar Marubuta
________________________________________
*AUTAR MARUBUTA CE*βν ΌνΏ»ν ½ν±Όν ΌνΏ»
ν ΌνΌΉ__________ν ΌνΌΉ_________ν ΌνΌΉ__________ν ΌνΌΉ_________ν ΌνΌΉ
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_ν Ύν΄²ν ΌνΏΌ
<><><ν ΌνΌΉ><><><>ν ΌνΌΉ<><><>ν ΌνΌΉ<><><><>ν ΌνΌΉ<><><><><>ν ΌνΌΉ<><
Editingβ
Page 6 & 7
Washe gari
Karin kumallo suke cikin hira da farin ciki
Hajjiya Sa'adatu kawai abincinta take ci ba tare da tana shiga hirar 'ya'yan nata ba .
"Alhamdulillah yau ba aiki sai zaman gida ." Zarah ta yi magna da farin ciki tana gyara zaman
Bluetooth d'in dake kunnenta
Umar ne ya ce ,"Hmmm aunty Zarah ke nan , kwana biyu kin dena rubutu."
Wani kallo ta jefa masa tana cewa ,"Yanzu na fi bawa gidan television d'in mu muhimmanci ,
dah ni za su tura Dubai wallahi na 'ki zuwa."
Mahmud kawai murmushi ya yi , sannan ya kalli Mommy yana cewa ,"Yau babu dadi breakfast
Daddy ba ya nan ."
Sai a lokacin Hajjiya ta d'ago kai tana cewa, "Yau ai sammako ya yi yana gidan gona."
Sannan ta kalli Zarah tana cewa, "Ya yi mini magana a kan ki da Kamal ya ce ki masa magana
a yi a wuce wajen babu amfanin 'bata lokacin."
Murmushin ya'ke Zarah ta yi tana kallon 'ya uwan nata
Yayin da sukai mata murmushi suma tabbas wannan rana Zarah ke jira ita da Kamal.
Haka suma gidan Alaji Mansur suna zaune suna jiran fitowar Alaji domin su fara cin abinci
"Laila ki temake ni ki mini guga dan Allah, kin ga na kusa komawa makaranta."
Cewar Nasir
Wata harara Laila ta buga wa Nasir tana cewa ,"Hmmm mommy kin ji shi yanzu fa ya gama
cewa bani da amfani , to wallahi bazan maka ba."
Hajjiya ta kwashe da dariya kafin ta ce ,"Ai gaskiya kawai aure zan had'a ku na huta , kuje can
ku 'karata.Shikenan tuwo na mai na ."
Nasir Cikin jin haushin maganar da Laila ta fad'a masa ya ce ,"Tabb mommy, ni me zan da
wannan yarinyar gata mummuna Allah na fita kyau tabb , waye ma zai aure ki."
Sai a lokacin Kamal ya yi dariya yana sake baza kunne yana sauraran hirar tasu , lokacin guda
kuma yana tunanin idan zai fita company zai biya ya ga Zarah.
A ajiyar zuciya Laila ta yi sannan taja tsaki tana kallon Nasir, "Ni wallahi gara ma ka koma
makarantar na huta ."
A lokacin Alaji Mansur ya fito cikin farin ciki ya samu guri ya zauna
Haka zalika suma duk sun kula da irin wannan gagarumin farin ciki da ya ke ciki
Bata abinci yake ba ma shi magana ya fara kamar haka ,"Gaskiya na ji dad'in ganin du duk
anan domin akwai magana mai daraja da muhimmanci da zami ko na ce da zan sanar daku ."
Kamal ya kalli mahaifiyarshi cikin murmushi, haka Nasir ya kalli Laila
Mommy ce ta ce ,"Ai ni Alaji tun jiya da kaje gidan Alaji Mustapha na kula da wani farin ciki da
kake , na ce mene ka ce kawai ni ma na gode Allah na yi murna bayan baka fad'a mini komai
ba ."
Wata dariya Alaji Mansur ya ke ce da ita
Hakan yasa duk su Nasir suma dariya
"Daddy dan Allah ka fad'a mana mene wannan farin cikin ." Cewar Laila
Alaji Mansur ya kalli Hajjiya yana cewa ,"Wato Hajjiya ina d'aki yanzu, sai Alaji Mustapha ya
kirani , to naji dadi sosai yadda Fatima ta nuna masa ya isa da ita , wato Fatima ta amince da
auren Kamal kun ji dai abin farin ciki. "
Dauuu dauuu kowa yaji a cikin zuciyarshi, duk suka canja yanayi zuwa rashin fahimtar maganar
Alaji
Babu wanda ya ce dashi komai , ya cigaba da cewa Hajjiya, "Wato kin san mun yanke shawarar
auren Kamal da Fatima."
A karo na biyu zukatansu suka sake shiga rudani ,"Wai wanne Kamal kake magana ne Alaji. "?
Hajjiya ta yi tambaya da mamaki
" Ahhhh kin jiki fa , akwai wani Kamal bayan wannan. "Ya nuna kamal da ranshi yake a rikice da
matukar tashin hankali
" Ai mun shirya tsaf ni da Alaji Mustapha domin samun cikakken zumunci."Alaji ya kara musu
bayani
Kallon juna suke da matukar mamaki , Kamal dauriya ya yi yayin da kanshi yake matukar sara
masa ya ce ,"Daddy wai Zarah kake nufi ko Fatima. "?
Murmushi Alaji ya yi yana cewa," Fatima dai 'yar Alaji, amma ai zaka iya kiranta da zaran idan
haka kake so , daman an ce fatimatuzzahara'u."
A take Kamal ya sake jin kanshi ya matukar sara masa idanunsa sun ciko da ruwa
"Haba Alaji, wacce irin Fatima kuma , yaron nan fa Kamal Zarah yake so 'yar Alaji Sale , amma
ka zo kana wata magana kuka."
Mommy ke nan
Lokaci guda Alaji Mansur ya fusata yana cewa, "Ni bansan wata maganar Zarah ba , Fatima na
sani kuma ita na za'ba."
Ya juya ya kalli kamal dake cikin matukar rudani yana cewa, "Karka yadda ka nuna mini ban isa
da kai ba , mene ai bun Fatima da zaka na kira mini wata Zarah, to wallahi Kamal ni ne ubanka
, kuma ba a canjawa tuwo suna , mun tsaida ranar auren ku , ban yi maka dole ba , idan kana
da hankali zaka yi abin da ya dace ."
Yana gama maganar ya tashi ya fita cikin fusata
Wasu hawaye suka zubowa kamal masu zafi ,kafin wasu su dire wasu na biyo bayansu
Laila da Nasir suka kalli juna da tashin hankali, Hajjiya ma haka taji wani ba'kon yanayi .
Tun da Fatima ta amince da auren Kamal, Alaji Mustapha duk ya canza mata farin cikin
matukar gaske , domin har sabuwar mota Alaji ya canza mata
Lokacin da 'yan uwanta suka kirata video call, nan suke bayyana mata irin shirye-shiryen da
zasi a wannan biki , zasi shagali sosai
Ita dai Fatima tana fatan auren Kamal alheri ne a gareta , ba samuwar wata sabuwar kaddarar
ba .
Lokacin da dare ya yi Alaji Sale da Mahmud Umar duk suna zaune a falo hadda Hajjiya suna
hira suna kallo
A lokacin Zarah ta shigo da gudu kanta babu d'ankwali ta fad'o jikin Hajjiya tana wani rurucewa
da kuka .
Kafff hankulansu ya tashi tsaye da jin irin wannan kuka na Zarah
Hajjiya ta d'agota a jikinta , amma Zarah ta'ki tashi ta fuskanci kowa kawai kukanta take
shekawa
"Mene ne ya faru ne haka."?
Alaji Sale ya tambaya da tashin hankali
Haka suma Mahmud da umar duk sun 'kagu su ji dalilin wannan kuka na yayarsu da basu ta'ba
ganin ta a irin wannan yanayi ba
" Mene ya ke faruwa ne Zarah." Mommy ta sake tambaya yayin da ta yi nasarar d'ago Zarah
Idanunta sun yi jajir yayin da wasu hawayen suke turereniya Zarah taso fara magana amma
wannan kukan ya sake shan kanta .
Cikin kokari ta d'ago tana kallon furkar mahaifiyar ta tana cewa ," Mommy amana ta yi 'karanci ,
mutane babu mommy Kamal aure zai ."
Wani tashin mamaki suka ji ya bugo musu zukata
Wasu sabbin hawaye suka sake zubo wa Zarah
Ta ci gaba da magana cikin takaici da bacin rai tare da hawayenta ,"Mommy nan da wata daya ,
wata zai aura ba ni ba , baban shi ne ya sama masa mata."
Ta karasa magna tana sake shiga wani hali tana kwanciya a jikin Hajjiya
"Innalillahi, kamal din ne ya ce miki zai aure? Kamal din ."? Mommy ta yi magana cikin mamaki
tana kallon Alaji sale
Alaji sale a wannan karan ma dai bai iya cewa komai ba
Har Zarah ta sake fashewa da kuka tana cewa," Mene ya sa haka mommy, me ya sa Kamal zai
barni , shi ne fa ya kirani yake fadan zai yi aure, shi ke nan na rasa shi mommy. " Ta aje
maganar cikin wani gwanin ban tausayi na kuka
A lokacin Alaji sale ya kalleta yana cewa ,"Ba za ki rasa shi ba ."...
Alkalamin Autar marubuta ne
Zasu same ni a WhatsApp a wannan number
07040805269
FATIMA DA ZARAHν ΌνΎ
Na
Autar marubuta
________________________________________
*AUTAR MARUBUTA CE*βν ΌνΏ»ν ½ν±Όν ΌνΏ»
ν ΌνΌΉ__________ν ΌνΌΉ_________ν ΌνΌΉ__________ν ΌνΌΉ_________ν ΌνΌΉ
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_ν Ύν΄²ν ΌνΏΌ
<><><ν ΌνΌΉ><><><>ν ΌνΌΉ<><><>ν ΌνΌΉ<><><><>ν ΌνΌΉ<><><><><>ν ΌνΌΉ<><
Editingβ
Page 8 & 9
Diff Zarah ta yi ta d'ago tana kallon Alaji sale,
Duk hankalinsu ya koma kan Alaji da jin wannan magana
"Mene ka ce daddy." Zarah ta tambaya cikin jajayen idanunta na kuka
Alaji cikin kwanciyar hankali da nuna kauna ga Zarah ya fara cewa ,"Allah ya halicceki da kyau,
sannan ya mahaifinki da mahaifiyar ki suna tare dake , sannan ga 'yan uwan ki masu baki farin
ciki ."
Jikin kowa ya yi san yi yayin duk suke sake kasa kunne domin sauran mahaifin nasu .
Haka Alaji ya cigaba da cewa ," Baki ta'ba neman abu kin rasa ba , amma ga shi a yau kina
kuka cikin bakin ciki sakamakon Allah ya jarabce ki da rashin Kamal. "
Zarah ta sauke kanta kasa cikin wani yanayi
Alaji sale ya ce ,"Idan Allah ya rubuta Kamal mijinki ne , to dole zaki aure shi , matukar Kamal
yana son ki , komai daren dadewa baza ki bar zuciyarshi ba ."
Zarah ta dago ta kalli mahaifinta cikin sabon hawaye
Ba tare da jiran komai ba , ya cigaba da cewa ,"To sai mene idan Kamal zai auri wata !Abin da
nake son ki sani , karki yadda duniya ta rudeki , karki yadda kibi rudin zuciyarki , wannan
lamarin kar ya shigar dake wani hali kiji kin tsani Kamal ko matar da zai aura , sannan matukar
kina son shi ko mata 3 ya yi ya ce zai aure ki cikon 4 karki yadda ki dubi wannan matan a
gabanki domin zaki halaka , ni a matsayina na mahaifinki duk san da Kamal ya zo min da
zancen auren ki , matukar kina son shi to babu makawa zami farin ciki , kuma mu yi shagali
sosai na bajin ta da nuna babban gida ne mu."
Ajiyar zuciya Zarah ta yi tana jin farin cikin kalaman mahaifinta
Hakan ya sa ta fara magana