Showing 30001 words to 33000 words out of 37591 words
07040805269
WhatsApp only
FATIMA DA ZARAHν ΌνΎ
Na
Autar Marubuta
________________________________________
*AUTAR MARUBUTA CE*βν ΌνΏ»ν ½ν±Όν ΌνΏ»
ν ΌνΌΉ__________ν ΌνΌΉ_________ν ΌνΌΉ__________ν ΌνΌΉ_________ν ΌνΌΉ
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_ν Ύν΄²ν ΌνΏΌ
<><><ν ΌνΌΉ><><><>ν ΌνΌΉ<><><>ν ΌνΌΉ<><><><>ν ΌνΌΉ<><><><><>ν ΌνΌΉ<><
Editingβ
Page 38 & 39
A nan suma su Faruk sun shirya tsaf domin tunkarar kotun da za a shiga
A yanzu haka suna zaune da Barrister Nuhu suna tattaunawa
Murja ce ta kalli barrister da cewa .
"Wannan shari'ar zata dau lokaci kuwa barrister."?
Barrister Nuhu ya kalli Murja a domin bata amsa .
" Banajin hakan matukar ba wani babban lamari ne ya bayyana ba daga su wanda muke kara ."
Faruk ya ce .
"Gara mu yi mu gama mu bar kasarnan domin Wallahi zamanta ya ishe ni ."
Barrister Nuhu ya yi murmushi
Su dai su Ahmad babu abun da suke cewa rashin mahaifiyar su ma kawai ya ishe su .
........
A yau aka gabatar da zaman kotu na farko , kotu ta cika ma'kil da al'umma sai dai ba wani
fafatawa akai ba alkali ya ce za a sake zama a ranar 17 ga watan da ake ciki .
Anan cikin gidan Alaji Mustapha duk iyalan nasa suna zaune ana ta hira domin har su Faruk
yau sun kai wa mahaifin nasu ziyara , duk ya yi ya yi dasu kan su dawo gidan su zauna akwai
isassun d'akuna amma suka 'ki saida suka je suka kama waje , haka ya hakura da su .
Su Habib da Khalid sun yi farin ciki sosai da ganin 'yan uwansu an sha hira an more , sannan
suka koma gida .
Ranar kotu
Daga nan falo Kamal yana zaune yana jiran fitowar Fatima a domin su tafi
Cikin cikakkiyar shigarta ta fito ta yi matukar kyau sosai .
Kamal ya mike tsaye yana murmushi yana fadin.
"Ohhh my life , idan kika sa kayan nan matukar kwarjini ki ke mini wallahi, ina fatan nasara a
gare mu ."
Fatima ta yi murmushi ta ce .
"In sha Allah, mu tafi kar mu makara."
Suka shige suka tafi
Mutane har sun fara shiga ciki , wasu kuma suna waje , ga 'yan jarida duk sun hallara ,a lokacin
ne aka zo da Zarah , babu jimawa alkali ya karaso babu bata lokaci kotu ta fara gudana.
Nan Barrister Nuhu ya tashi ya mika gaisuwa ga alkali tare da gabatar da kanshi da
mataimakansa .
Ita ma Barrister fatima ta mika gaisuwa da gabatarwa tare da abokin aikinta Barrister Muhd
Nan alkali ya yi rubutu cikin takardar dake gabanshi sannan ya d'ago yana fadin.
"Kotu ta shirya sauraran 'bangarori ."
Barrister Fatima da Barrister Nuhu suka hada idanu , sannan barrister Nuhu ya tashi tsaye da
wasu takardu a hannunsa ya fara magana lokaci guda ya na mika takardun ga alkali .
"Ya mai girma mai shari'a.Dukkan alamu sun nuna Zarah Sale wacce ake tuhuma ita ce ta
kashe Hajjiya Samira, sannan daga bangaren lauyan dake kareta babu wata shaida da suka
bayyana mana da zata kore haka ."
Barrister Nuhu ya gyara tsaiwarsa ya cigaba da cewa .
"Ya mai shari'a Hajjiya Samira marigayiya tana dauke da ciwon zuciya, sai dai likitoci sun
tabbatar mana wannan ciwon nata bai tashi ba har ta rasu , sannan shaidarmu wacce komai ya
faru a gabanta Hajjiya Binta ta tabbatar min yadda komai ya faru kamar yadda za tai wa kotu
bayani.
Duba da wannan bayanai ya mai shari'a, muna rokon kotu mai albarka da ta biwa Hajjiya
Samira hakkinta a domin hukunta Zarah sale."
Barrister Nuhu ya matsa kusa da Zarah da take tsaye cikin akwatin tuhuma yana fadin.
"Zarah Sale mene ya sa kika kashe Hajjiya Samira."?
" Ina da ja ya mai shari'a. " Barrister fatima ta yunkuro ta fada da babbar murya
Alkali ya ce .
"Kotu ta amsa Barrister Fatima."
Fatima ta ce .
"Barrister Nuhu yana kokarin razana wacce nake karewa tare da shirin sanya mata magana a
baki ."
Alkali ya kalli Barrister Nuhu yana fadin.
"Ka gyara barrister Nuhu ."
Barrister Nuhu ya ce .
"To na gode ya mai shari'a."
Barrister Fatima ta koma ta zauna
Barrister Nuhu ya baro gaban Zarah ya fuskanci alkali yana cewa.
"Ina son wannan kotun mai albarka ta bani damar gabatar da shaida ta gaba ."
Alkali ya sunkuya ya gabatar da rubutu sannan ya d'ago ya kalli Barrister Nuhu da cewa .
"Kotu ta baka dama Barrister."
Barrister Nuhu ya bukaci da Hajjiya Binta ta fito zuwa akwatin tuhuma
Bayan ta fito ne ya kalleta yana fadin.
"Hajjiya Binta shin mene alakarki da marigayiya Hajjiya Samira."
Hajjiya Binta ta yi ajiyar zuciya kana ta fara magana .
"Ni da ita miji guda muka aura tsawon wani lokaci kafin Allah ya rabamu , ma" ana kafin Alaji
Mustapha ya sake ta ."
Barrister Nuhu ya ce .
"Alhamdulillah kina nufin dai abokan zama ne a dah ."?
Hajjiya Binta ta ce ." Eh ."
Barrister Nuhu ya ce .
"Hajjiya Binta ki sanar da kotu yadda wannan lamarin ya faru har ya kai ga hajjiya Samira ta
rasu , wato ma'ana yadda komai ya faru a gaban idonki ."
Hajjiya ta gyara mayafin dake jikinta kana ta fara cewa .
"A wannan ranar na kaiwa Hajjiya Samira ziyara sakamakon ta zo daga saudiya kuma zata
koma da wuri , ana cikin haka sai Fatima ta tafi wajen aiki wanda ita 'yace ga marigayiya Hajjiya
Samira, dama shi mijinsu Kamal ban same shi a gidan ba ,
Sai ya zama babu kowa cikin gidan sai mu 3 , ni da Hajjiya muna hira a falo, har na ce mata ta
dauko mini tsarabar turare na , sai ta tashi a domin ta kawomin ,
Ita kuma a wannan lokacin Zarah ta fito daga dakinta ta tsaya mini a ka tana hararata, sai ga
Hajjiya ta fito tare da turaren da taje kawo mini ."
Hajjiya Binta ta aje ajiyar zuciya sannan ta cigaba da cewa.
"Kawai Hajjiya Samira tana yiwa Zarah magana , sai ta fara mata rashin kunya ta hankad'eta ta
fadi . Shi ke nan rai ya yi halinsa
Amma na tabbatar cewa ita Zarah batai tsammanin abin zai kai ga mutuwa ba ."
Barrister fatima ta yi wani murmushi na takama da mamaki
Zarah ta sunkuyar da kai dajin yadda Hajjiya Binta ta tona mata asiri
Barrister Nuhu ya kalli alkali yana fadin.
"Ya mai girma mai shari'a, wannan shi ne abin da muke son sanarwa kotu , ina rokon wannan
kotu mai adalci data gaggauta yankewa Zarah sale hukunci .Na gode ya mai shari'a."
Cikin takun isa ya koma ya zauna
Alaji Sale ajiyar zuciya ya sauke yana kiran sunan Allah
Shi kam Kamal ba a cewa komai.
"Barrister Fatima shin kina da abin cewa ."?
Alkali ya jefawa Fatima tambaya
Cikin girmamawa Barrister ta tashi tsaye tana cewa.
" Ina da abin cewa ga Hajjiya Binta ya mai shari'a. "
"Kotu ta baki dama." Alkali ya mayar mata
Barrister Fatima ta karaso gaban Hajjiya Binta
Sannan ta fara cewa .
"Ya mai girma mai shari'a, wacce ake zargin Zarah ta kashe da mommy take kiranta , sannan a
daren da marigayiya ta zo Nigeria , to ciwon zuciyarta ya tashi kuma Zarah da ake tuhuma ita
ce likitan data duba lafiyarta a cikin dare ."
Barrister fatima ta gyara rigarta ta cigaba da cewa .
"To me yasa idan Zarah tana son kashe Hajjiya Samira bata kasheta tun a asubiti ba?
Sai da aka dawo gida , kuma ta rasa yadda zata kasheta sai ta hanyar da Hajjiya Binta ta bada
bayani ."?
Alaji Mustapha ya girgiza kai tare da cigaba da saurara
" Ya mai girma mai shari'a, ina rokon wannan kotu mai adalci data sake komawa baya domin
bibiyar wasu zantuka na kuskure da Hajjiya Binta ta yi yayin had'a labarin ta ."
"Ina da jah ya mai shari'a."
Barrister Nuhu ya yi saurin kai farmaki
"Mene Barrister." Alkali ya tambaya
Cikin sauri ya fara cewa .
"Barrister Fatima tana shirin karya mana hujja tare da danganata da kagaggen labari ."
Alkali ya kalli Barrister Fatima yana fadin.
"Ki gyara barrister Fatima."
Barrister ta yi godiya ga alkali ta cigaba da cewa .
"Ya mai shari'a, ina rokon kotu data dubi kyakykyawar alakar dake tsakanin marigayiya da
Zarah , domin ko kallan banza Zarah bata ta'ba yiwa Hajjiya Samira ba .
Amma ina rokon kotu data bani damar tambayar Hajjiya Binta domin sanin mene ne ya kawo
Zarah ta yi wa Hajjiya rashin kunya, wato muna son ta sanar da kotu da wanne irin kalamai
Zarah ta yi amfani dasu yayin rashin kunyar da kuma irin martani da ita marigayiya ta yi wa
zarah har ya sa Zarah fusata ta bangajeta ."
"Ina da jah ya mai shari'a."
"Tun da aka ce rashin kunya kowa yasan rashin kunya barrister Fatima na shirin ja mana shari'a
ta yi nisa bayan komai ya bayyana."
Inji barrister Nuhu
Alkali ya ce .
"Barrister Nuhu korafinka bai ansu ba ."
Alaji Mansur ya yi murmushi na farin ciki yana sake kasa kunne a domin sauraran wannan
shari'a
Alkali ya kalli Fatima yana fadin.
"Kotu ta baki dama ."
Barrister Fatima ta yi murmushi tana kallon Hajjiya Binta da cewa .
"Kotu na sauraranki Hajjiya kuma malama Binta."
07040805269
WhatsApp only
FATIMA DA ZARAHν ΌνΎ
Na
Autar Marubuta
_______________________________________
*AUTAR MARUBUTA CE*βν ΌνΏ»ν ½ν±Όν ΌνΏ»
ν ΌνΌΉ__________ν ΌνΌΉ_________ν ΌνΌΉ__________ν ΌνΌΉ_________ν ΌνΌΉ
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_ν Ύν΄²ν ΌνΏΌ
<><><ν ΌνΌΉ><><><>ν ΌνΌΉ<><><>ν ΌνΌΉ<><><><>ν ΌνΌΉ<><><><><>ν ΌνΌΉ<><
Editingβ
Page 40 & 41
Hajjiya Binta kawai ta fara kuka tana kuma shirin fara magana
"Ni-ni ni Allah ya sani na shiga tashin hankali." Ta kuma fashewa da kuka harda majina
"Na shiga rudani babu abin da zan iya tunawa."
Wani takaici Barrister Fatima taji ya sokar mata zuciya ta kalli Hajjiya Binta tana cewa
"Kotu na sauraran ki ."
Hajjiya Binta ta cigaba da kukan ta
Lokacin Fatima ta baro gabanta ta fuskanci alkali tana cewa.
"Ya mai shari'a Hajjiya Binta akwai wani abu da take boyewa kotu , sannan wannan kotu ta tuna
cewa babu babu kowa cikin gidan sai su biyu .
Amma ya mai shari'a me yasa ZARAH ce kawai zata zama abar zargi , shin ita Hajjiya Binta
kotu ta yadda da ita ne ? Hajjiya binta muna da bukatar ta bude baki ta yi wa wannan kotu
bayani. Amma hakan ya gagara , da haka nake rokon wannan kotu mai adalci data sake bamu
lokaci a wani zaman domin samun hujjoji ga wacce ake kara .Na gode ya mai shari'a."
Ta yi godiya ta koma ta zauna
"Lauyan wanda yake kara kana da ta cewa ."?
In ji alkali
Barrister Nuhu ya ce .
" Eh ya mai shari'a. "
Ya nufi gaban Zarah yana cewa.
"Shin Zarah kuna da 'yar aiki a gida ."?
Zarah ta kalli Fatima, sannan ta ce ." A'a babu."
"Me gadi fa ."?
Ya sake jefa mata tambayar
Zarah tai ajiyar zuciya ta kuma cewa .
" A'a babu ."
"To me ya sa babu ? Bayan da cewa duk mazauna gidan fita kuke yi , sannan akwai motoci
akallah guda shida a cikin gidan amma babu mai bude get ."
Zarah ta kalli barrister Nuhu tana cewa.
"Bamu da ra'ayinsu hakan ya sa bamu d'auka ba .Kuma mene alakar wannan da shari'ar."?
Barrister Nuhu ya kalli alkali yana cewa.
" Na gama ya mai shari'a. " Ya koma ya zauna
Bayan alkali ya yi rubutunsa ya d'ago yana cewa.
"Wannan kotu ta d'age shari'a zuwa kwana uku, a tare da hakan wacce ake tuhuma Zarah Sale
za a maida ita zuwa gidan gyaran hali kafin sauraran shari'a ta gaba."
Alkali ya fad'a tare da mikewa
Kuka Zarah ta fashe dashi tana kaiwa kasa , yayin da Mahmud yaji matukar tausayinta ya sake
rufe sa , sai da yaji wasu hawaye sun gangaro masa
Haka Fatima dauriya kawai tai duba da dandazon mutane , ga 'yan jarida , ga shi bata da wata
hujja da zata tunkari kotu a zama na gaba .
Bayan Kamal ta bi da ya fice waje , domin ya ga an yi waje da Zarah za a sata a motar gidan
yari wacce aka kawota a ciki .
Kawai kuka ya fara yana rungume mahaifin shi Alaji Mansur, Alaji Mansur wani yanayi na
matukar tausayin d'an shi yaji ya fara keta masa zuciya.
Lokacin Fatima ta karaso inda suke , babu annuri a fuskarta ko kad'an
"Fatima yaushe shari'ar nan zata kawo karshe ."?
Alaji Mustapha mahaifin ta ya yi mata tambayar
Sai da taja dogon numfashi sannan ta kalli Kamal , kana ta kauda kai cikin tsananin tausayinshi
ta kalli Barrister Nuhu da yake tsaye can nesa dasu Faruk suna zantawa ta ce .
" Barrister Nuhu na yi shari'a dashi sosai Daddy , koda yaushe ni nake nasara , amma bai taba
karaya ba , a wannan karan yana tafe sosai domin ya karbi bangare me saukin hukunci ."
Wani tashin hankali Kamal ya sake rufe masa zuciya da jin kalaman Fatima harda kuma
hawayehawaye
"Ban ce Nasara baza ta samu ba Baba amma koma mene zai faru zama na gaba kotu zatai
hukunci, domin ba shari'a ce me sarkakiya ba ."
Alaji Sale ta kalla cikin rurucewa da kuka tana sake fadin .
"Idan kotu ta yankewa Zarah hukuncin kisa , sai dai mu daukaka kara."
Fatima ta tsuguna kasa tana kuka , wani firgici ne ya ziyarci kowanne su , babu kamar Alaji sale
da Kamal
Kamal ya saki hannun mahaifin shi ya durkusa gaban Fatima yana kuka
"Kina nufin kin karaya kuma Zarah kasheta za ai."?
Idanunshi sun yi jajir Fatima ta kalleshi cikin matukar damuwa ba tare da tana da niyyar cewa
komai ba
Alaji Mustapha ne ya durkusa ya jawo hannunshi suka taso
Sannan ya kalleshi yana cewa .
" Ka yi hakuri dan Allah Kamal , duk muma fa muna cikin wannan tashin hankalin, ita shari'a ai
mace ce me ciki , ba a san mene zata haifar ba , Allah ya kaimu zama na gaba kawai mu
cigaba da addu'a Allah zai bayyana gaskiya. "
Alaji Mansur ya ce .
"Wannan gaskiya ne ."
Kamal ya zare hannunshi ya nufi mota
Haka kowa ya kama hanya aka koma gida .
Yana sauran kwana 1 za a koma kotu
Kamal duk yabi ya sake lalacewa dashi
Fatima tana zauna a falo
Ta zurfafa matuka cikin tunani domin har Nasir ya shigo ya zauna bata sani ba
A lokacin ya yi ajiyar zuciya yana cewa.
"Aunty Fatima lafiya kuwa."
Fatima ta kalleshi ba tare da ta ce komai , sannan Nasir ya sake fadin
"Na shigo baki sani ba kina ta tunani haka."
Ajiyar zuciya ta yi sannan ta gyara zama tana cewa .
"Gobe za a koma kotu Nasir, bani da wata hujja, bani da kwarin gwiwa, dole rayuwata baza tai
mini dadi ba ."
Nasir shima ya yi ajiyar zuciya yana cewa.
"Aunty, akwai abin da zan fada miki , wata kila ya zama wani abin daban ."
Da sauri Fatima ta kalleshi tana cewa.
"Ina jinka Nasir."
Ajiyar zuciya ya kuma ajewa me zafi sannan ya ce .
"A ranar da abin nan ya faru aunty Fatima ina gida babu inda naje , ina tsoron zama abin zargi
shiyasa ban yi bayani ba , amma wallahi bansan komai game da mutuwar mommy ba duk da
ina cikin gidan."
Da sauri Fatima ta gyara zama tana fadin .
"Karka damu Nasir ka sanar dani duk wani abu da ya faru wanda ka sani , kuma wanne dalili ne
ya hanaka zuwa makaranta a wannan ranar bayan ka tafi ."
Nasir ya fara mata bayani filla- filla kamar yadda take da bukata .
"Haba Alaji dan Allah yanzu haka gobe za a koma kotu , kana gani wannan yarinyar tana wani
tsare Hajjiya Binta da tambayoyi harda rashin mutunci a kotu ."
Hajjiya Rukayya ta fada tana kallon Alaji Mustapha
Ita kam Hajjiya Binta kawai ta sunkuyar da kai
"Ya kamata a yi wani abu akai Alaji amma wannan bai kamata ba , kuma duk fatima tana zargin
Hajjiya Binta ne da zata