Showing 27001 words to 30000 words out of 37591 words

Chapter 10 - FATIMA DA ZARAH NA AUTAR MARUBUTA.pdf

fuskarta da mari har guda biyu lokaci guda


Kamal duk ya rasa me yake masa dadi a wannan rayuwa.

Kowa kallon Faruk ya yi da yake huci , dalilin marin da ya ajewa Fatima

"Tunda haka kika ce , mu zuba mu gani duk inda zaki je ki dawo mu ne jininki , mun gode da
butulci ."


Murja a lokacin ta samu damar magana ta fara cewa .
"Rabu da ita Faruk , asararriya mara kishin mahaifiyar ta , rashin zaman da kika yi da ita yasa
kike jin tamkar ba mahaifiyar ki ba ."



Lokacin Fatima ta fashe da wani kuka mai radadin gaske , dajin irin zancen da 'yan uwanta
suke a kan ta .

A wannan yanayi ta fara magana cikin kuka tana cewa.
"Shi ke nan aunty, ku yi duk abin da kuke so ,amma ina so ku sani zan koyi da bayan Zarah ,
idan kun so ku dauko lauyan da zai sanya a kashe Zarah a zaman farko , ni kuma zan yi iya
yina domin bayyana muku gaskiya, cewa Zarah ba tai kisa ba duk da bani da hujja , amma
Allah ya sani kuma zai bayyana gaskiya."
Faruk ya ce .
"To shi ke nan sai mun hadu a kotun , amma ina tabbatar miki karki sake kukan rashin
mahaifiya, kuma karki sake tunanin kina da wasu 'yan uwa a wannan duniya." Ya karasa
magana cikin matukar zafi da fusata


Sannan ya kalli su Ahmad yana cewa .
"Ku tashi mu tafi zamu samu gida mu zauna, har zuwa kammala wannan shari'ar ."

Wani zafi Fatima taji ya daki zuciyarta dajin cewa zasu bar gidanta

Kamal ya fara basu hakuri amma Faruk ya tasa su a gaba tare da kayansu suka bar gidan.

Wani kuka Fatima ta sake rude wa dashi tana cewa.
"Ya Allah , yanzu mene laifi na dan kawai ina son bayyana gaskiya."

Ta kai kasa tana kuka mai matukar ban tausayi

Duk su Mahmud suka ji tausayinta ya rufe su , bari ma Nasir da hawaye suke zubo masa .
"Allah sarki aunty Fatima, dalilin Zarah dubi halin da take ciki ta rasa mahaifiyar ta kuma 'yan
uwanta duk sun tafi sun barta , Allah Ka kawo mana dauki ."

Nasir ya karasa maganar a cikin zuciyarshi yana gangaro da hawaye .



.....
Kotu ta sanya ranar fara sauraran shari'ar Zarah da ake tuhuma da kisan kai , wannan zance
yana matukar yawo a tsakanin masoyan rubutun Zarah Sale Salisu


A halin yanzu Fatima tana hanyar zuwa gidansu sakamakon kiran da Alaji Mustapha ya yi mata
.


Cikin gidan Alaji Mustaphan kuwa Abba Alaji ne zaune a falo shi da Hajjiya Binta.
Abba Alaji ansha wasu manyan kaya , har da hula , saidai kayan ba wani kyau sukai masa ba ,
saboda bai saba sawaba kuma wannan halayyer tashi da 'yan shaye -shaye bai dena ta ba .

Hajjiya Binta ta kalleshi d murmushi tana cewa.
"Haba kai kuwa Abba wallahi har ka fito ka yi kyau , ai idan ka dore a haka Alaji zai ji dadi ."


Abba Alaji akai dariya kafin a ce .
"Ai in sha Allah na tuba aunty."
Ta ce ."To Allah ya tabbatar. "

A lokacin Hajjiya Rukayya ta shigo tana murmushi nan ita ma taji dadin ganin Abba Alaji a
wannan yanayin .

Daga nan kuma su kai sallama ya tashi ya tafi

Nan su Hajjiya suka cigaba da hira yayin da Fatima ta shigo tare da sallama

Babu wacce ta amsa mata sallamar a cikinsu
Sai Hajjiya Rukayya dake cewa .

"To mene kuma aka zo yi mana gida , ai muma yanzu dole mu nisanta dake a kashe
mahaifiyarki amma ko a jikinki banza mara ilmi ."


Fatima ta sunkuyar da kai cikin rashin jin dadin jin maganar ta hajjiya Rukayya.

Hajjiya Binta ma dorawa tai da cewa .
"An dai yi asara ma'asaranciya ."

A lokacin Alaji Mustapha ya fara sakkowa daga saman bene , yayin da ya hangi Fatima a kasa
ne ya dakata da sakkowar yana cewa.
"Au Fatima ashe kin karaso to bismillah hawo sama ."

Ya juya ya koma , Fatima ta wuce ta barsu suna harararta suna tsaki


Tana karasawa saman ta samu guri ta zauna a falo , sakamakon nan ta ga mahaifin nata yana
zaune .
"Ina yini Daddy."?


Ba tare da ya amsa ba ya ce da ita .
" Tashi ki hau kujera Fatima. "

Babu musu ta mike ta zauna

Bayan sun gaisa sai Alaji Mustapha yake cewa .
"Da gaske ne kun yi fada dasu Faruk kuma kin zabi kare zarah a kotu ."???

Ya jefa mata tambayar lokaci guda

Wani faduwar gaba Fatima ta ji ya ratsa mata zuciya

Cikin daburcewa da kame kame ta fara cewa ." Daman Daddy daman ."..

Alaji Mustapha ya dakatar da ita cikin gaggawa yana fadin .
"Dakata kawai amsata eh ko a'a ce ."


Cikin kwarin gwiwa Fatima ta ce .
"Eh haka ne ."

Ajiyar zuciya ya yi sannan ya fara cewa .
"Allah ya bayyana gaskiya ki je kotu ki yi abin da ya dace Fatima, domin ni yanzu na yarda da
ke , kuma komai zai wuce Allah ya kare ki ya bada sa'a Allah ya jikan mahaifiyar ki ."


Fatima wani farin ciki taji ya rufe ta dajin yadda mahaifin ta ya goya mata baya ,

Cikin kauna ta kalleshi tana cewa.
"Daddy na gode da goyan bayanka , hakan yake nuna tabbatar zan samu nasara , babu wanda
ya fahimce duk a cikin su , hakika Daddy ina kaunar 'yan uwana amma yanzu duk sun juya mini
baya ."


Murmushi Alaji Mustapha ya yi yana kallon Fatima da cewa .
"Karki damu Fatima, ai komai lokaci ne , kuma gaskiya zata bayyana karki sa komai a ranki,
idan Zarah ce ta kashe mahaifiyar ku , to tabbatar dole za a hukuntata amma Allah ne mafi
sanin daidai."


Ajiyar zuciya ta yi tana fadin.
"Gaskiya ne Daddy , bani da shaidar cewa ZARAH bata kashe mommy ba , amma babban
amincin yana daga zuciyata domin Zarah baza ta aikata ba ."



Alaji Mustapha ya ce .
"Allah ya sa mu dace Fatima."..






Fatima tana komawa gida ta samu kamal a zaune a falo , duk ya wani rame dashi yayi baki
kamar ba shi ne ba


Murmushi kawai ya yi mata sanda ta yo sallama, saida ta karaso ta zauna sannan ya amsa
sallamar.



" Daddy yana goyon bayana Kamal, har naji komai zai tafi daidai tabbatar

Yanzu na samu kwarin gwiwa."


Murmushi ya kuma yi na jin dadin batun nata yana fadin .
"Ai Daddy mutum ne mai fahimta Fatima hakika ina alfahari dashi matuka."


A lokacin Barrister Khadija ta turo kofar falon tare da sallama


Ta karaso
Nan suka gaisa da Kamal ta sake masa ta'aziyya sannan ya tashi ya shiga ciki .


Nan suka gaisa da Fatima tare da sake mata gaisuwa


Barrister Khadija ta kalli Fatima tana cewa.
"Duk kin rame wallahi Allah ya jikan Mom."


Fatima ta yi murmushi tana gyara zaman rigar jikinta tana cewa.
"Amin Khadija, to ya shari'a kin kammala ne ."?



Barrister Khadija ta yi ajiyar zuciya tana cewa.
" A wallahi.
Dama wani zance nake ji da ban gane kanshi ba , zaku shiga kotu sannan kuma kin tsaya
domin kare Zarah Sale kin bar 'yan uwanki ."


Ta aje maganar tana wurgawa Fatima kallon takaici

Fatima ta yi murmushi tare da gyara zama tana kallon barrister Khadija.





Alkalamin Autar
Marubuta ne

FATIMA DA ZARAHν ΌνΎ€
Na
Autar Marubuta
________________________________________


*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
ν ΌνΌΉ__________ν ΌνΌΉ_________ν ΌνΌΉ__________ν ΌνΌΉ_________ν ΌνΌΉ
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_ν Ύν΄²ν ΌνΏΌ
<><><ν ΌνΌΉ><><><>ν ΌνΌΉ<><><>ν ΌνΌΉ<><><><>ν ΌνΌΉ<><><><><>ν ΌνΌΉ<><


Editing❌



Page 36 & 37


Fatima haka kawai taji ta kasa cewa da Barrister Khadija komai
Hakan yasa ta kuma ajiyar zuciya

Gani da jin haka ya sa Barrister Khadija cewa .
"Okay ashe gaskiya ne ai dole ki rasa abin cewa , amma wallahi kin bawa ahalinki kunya ,
sannan kuma ina sanar miki Barrister Nuhu suka d'auka , sai ki shirya kare me laifinki da gaske
."


Barrister Khadija ta tashi tsaye tana cewa.
"Na tafi Allah ya kyauta sai mun hadu a kotun ."


Ta fita ba tare da Fatima ta iya cewa komai ba
A take a gun Fatima taji wani ciwon kai ya risketa mai matukar radadi

Kawai kujerar da take zaune ta kasheta ta fara bacci

Anan kuwa Alaji sani ne zaune a falo shi da matarshi

Matarshi Hajjiya Nana ta kalleshi da fadin
"Wai Alaji yau na ga duk farin ciki ya same ka , ko kuma ma batun yau na kula da hakan ba ."


Alaji Sani dariya ya yi yana cewa.
"Haba Hajjiya Nana kema dai kinsan farin cikina ba zai wuce Abba ba , kamar yadda bakin
cikina ba ya wuce shi ne sula."


Dariya Hajjiya Nana ta yi tana fadin .
"Wannan haka ne muna godiya ga Allah da ya fara shirya mana shi ."

Alaji ya ce .
"Ina son yaron nan wallahi Hajjiya, halinshi ne bana kauna amma yanzu alhamdulillah."

Hajjiya Nana ta yi dariya tana kallon agogon dake dakin yayin da take kuma sauraran kiran
sallar la'asar .




Fatima har yanzu tana falo tana bacci a lokacin Kamal ya fito daga daki yana kallon inda take
kwance cikin mamaki

Da sauri ya karaso ya fara tashinta
Lokacin da ya ga ta bud'e ido tana mammatsa idanu tare da dafa goshi ya fara cewa .
"Haba Fatima kin san zamu je gurin Zarah, ga shi kwanaki kad'an ya rage shiga kotu amma kin
kwanta bacci haba dan Allah idan na rasa Zarah ya zanyi ."


Wani abu Fatima taji ya sake tokare mata zuciya cikin bacin rai ta sakko ta tashi tsaye yayin da
kanta ya ke sara mata ta fara cewa.

"Mene haka dan Allah, kowa ba ya iya fahimta , sanin kanka ne ina cikin tashin hankali kamal
na rasa abubuwa da yawah saboda Zarah."


Wasu hawaye ne suka zubo mata cikin kuka da karyayyar zuciya ta cigaba da cewa .
"Ya zan yi ne dan Allah ni kam ."

Shima kamal cikin karyewar zuciya ya rungume Fatima a jikinsa yana ajiyar zuciya tare da cewa
.
"Yi hakuri Fatima, wallahi ina cikin tashin hankali bana ga ne yanzu waye zan yi wa fada komai
na babu dadi Fatima, dan Allah ki yi hakuri."


Fatima ta janye jikinta tana cewa .
"Bari na shiga na shirya sai mu tafi ."
Ta wuce ciki

Kamal ya zauna , a lokacin Nasir ya fito daga dakinshi yana isowa falo

Yayin da Kamal ya kula dashi ya fara cewa .
"Kai dama kana ciki ."?

Nasir yayi murmushi yana cewa.
" wallahi Yaya Kamal ina ciki , na rasa mene yake mini dadi , shi ya sa na fito domin na tafi
gidan Alaji. "


Kamal ya ce .
"To shi ke nan muma muna nan zuwa ."


Nasir ya nufi hanyar fita yana fadin .
"To sai kun zo ."



Bayan Fatima ta shirya suka nufi police station suna isa barrister Fatima ta tabbatar musu ita ce
lauyan da zata kare Zarah kuma tana da bukatar ganinta .



Nan DPO ya bada umarnin a fito da ita .

Lokacin da aka taho da Zarah, Kamal da Fatima hankalinsu ya matukar tashi ganin wani mugun
yanayi da take ciki


Da gudu ta karaso gaban Fatima ta zube a kasa tana kuka
Fatima cikin matukar dauriya ta sunkuya ta d'agota tsaye

Kamal kawai kauda kanshi gefe ya yi yana zubar da hawaye daga bisani ya sharesu ya dawo
da hankalin shi gare su


"Ki dena kuka Zarah."
Cewar Fatima

Zarah cikin kukan ta fara cewa .
"Fatima Daddy ya zo ya kuma fadan ke ce zaki kareni a kotu , ina cikin mugun yanayi Fatima
mara dadi , mommy fa ake zargin na kashe Fatima, dan Allah karki tsaya mini mahaifiya ba
wasa ba ce." Ta sake fashewa da sabon kuka

Kamal ya share hawayen da baisan ma sun zu bo masa ba

A lokacin Fatima ta yi murmushi tana rike hannayen Zarah tana fadin .

"Haba doctor zarah, ko kin manta mommy kike kiran mahaifiyar mu , sannan kika bata kulawa
yayin da ciwonta ya tashi .
Ni kuma kawai sai na zama kamar kowa ?
Kawai abin da nake so dake ki samu kwarin gwiwa ina tare dake , ki amsan dukkan
tambayoyina Zarah ."


Zarah ta sake damke hannayen Fatima tana fara magana .
"Wallahi bansan komai ba Fatima, ina zaman jiran ki dawo na tafi asubiti, ina cikin daki na gama
shiryawa, sai na fito falo , ina fitowa na ga Hajjiya Binta a kan mommy dake kwance a kasa tana
kiran ta tashi tana jijjigata , da sauri naje wajen domin ina tunanin ko ciwonta ne ya motsa ."


Zarah ta yi ajiyar zuciya ta cigaba da cewa .
"Ina sa hannuna a jikinta , shi ke nan Hajjiya Binta ta fashe da kuka tana fadin na kasheta , har
hakan ya yi sanadin zuwana nan Fatima ki dubi halin da nake ciki ." Ta sunkuyar da kai tana
kuka



Fatima ta kalli Kamal , Kamal ya sunkuyar da kai

Fatima ta maida hankali ga Zarah tana cewa .
"Zarah mawuyacin abu ne ki kwantar da hankalin ki , ni na sani , amma ina tabbatar miki
wannan shari'ar baza tai tsawo ba komai zai bayyana , domin yadda aka shirya komai cikin
sauki ne , kuma Hajjiya Binta dole abar zargice ."

Fatima taja ajiyar zuciya tana kallon idanun Zarah da cewa.
"Bazan ce ki kwantar da hankalin ki ba , idan har wannan kalaman nawa basu sa kin samu
sukuni ba ."


Zarah ta yi murmushi tana cewa.
"Har yanzu kina nan da halinki koh ."?

Fatima ta yi dariya ta ce .
" Kwarai kuwa dactor Zarah. "


Murmushi Zarah ta kuma yi tana kallon fuskar Kamal shi ma ya mata murmushi



Bayan Fatima ta gama komai suka dauko hanya suka dawo yayin da suka tsaya gidan Alaji
Mansur.





Duk suna zaune a falo ,Alaji ne kawai bayanan, domin ita ma Laila ta zo


Kamal da Fatima suna shiga aga gaggaisa
Fatima ta ce wa mommy.
"Mommy ina Daddy na fa ."

Hajjiya Amina ta yi murmushi tana cewa.
"Baban naki da baya son zama waje guda , ai yanzu haka zaki iya ganinshi ya dawo ."


Nasir ya yi dariya yana cewa .
"Daddy manya ke nan Allah yaja kwana ."


Hajjiya Amina ta ce
"Fatima yaushe ne za a shiga kotun ne ? Allah dai ya bayyana gaskiya."

Fatima ta yi murmushi na ya’ke tana kallon Kamal sannan ta ce .
"Ai mommy komai zai zo da sauki ku ta ya mu da addu'a domin bani da wata hujja a hannu ."


Laila ta ce .
"Kaiii aunty kuma haka za a shiga kotun ."?

Murmushi na ya'ke Fatima ta sake yi sannan ta ce . " In sha Allah Laila ai zamu samu hujjojine
daga lokacin da shi lauyan da zai tsaya musu zai gabatar da nashi hujjojin tom zamu samu
makama ."




Nasir ya ce .
"Tabb Allah dai ya temaka .Lamarin naku sai ku aunty, a ce zaku shiga kotu amma vabu hujja ."



Kamal dai ya yi ajiyar zuciya tunda dai suka gaisa bai sake cewa komai ba .


Laila ta kalli mommy tana cewa.
"Wallahi mommy karki ga yadda masoyan Zarah suke matukar damuwa a social media , har
wani program nake saurara a gidan redio da suke yi a kanta ."



Hajjiya ta ce .
"To ya za ai , haka Allah ya so .kowa da irin tashi jaraftar ."


Ta kalli Kamal tana sake fadin .
"Ka kwantar da hankalinka Kamal karka sa damuwa a rai ta maka illa duk wannan abin masu
wucewa ne ."


Kamal ya kalli mahaifiyar tashi yana cewa.
"In sha Allah mommy." Yayin da suka hada ido da Laila sukai wa juna murmushi.

Sannan ya kalli Fatima yana fadin .
"Mu koma Fatima."

Kafin Fatima ta ce wani abu ne Hajjiya ta ce
"A'a dama ba wuni za ku yi ba ."?


Kamal ya tashi tsaye yana cewa.
" Eh mommy gida muka yi ga shi har zamu tafi Daddy bai dawo ba , a gaidashi ."



Hakan ya sa Fatima ta mike , nan sukai sallama sannan suka koma gida .




Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login