Showing 21001 words to 24000 words out of 37591 words
kunbura da gani babu
tambaya wannan duka ne da wani abin aka masa
"Me ya sa me ka haka ."?
Ya tambaye shi da mamaki
Abba Alaji cikin haki da wahala ya ce .
" Daddy ne ya dake ni wallahi, badaban na gudu ba kashe ni ma zai ."
Nasir ya kwashe da dariya
Sannan ya kalli Abba yana fadin .
"Allah sarki daddy wato ka kai shi bango , toni yanzu da ka zo mene zan maka ."?
Abba Alaji cikin yanayin tausayi ya ce .
" Wallahi jiki na duk ba dadi Nasir, ka temakan na kwana a dakinka zuwa safiya na tafi ."
Nasir ya zaro ido cikin rainin wayo yana cewa.
"Tabbb amma ka rainan wayo , dakin nawa da yake a cikin gida, kawai wani kato da kai zaka
shigar musu gida , to gaskiya a'a 'kara gaba kawai ."
Abba Alaji cikin wata fuska ta matukar tausayi ya sake kallon Nasir yana cewa.
"Yanzu ina zani Nasir, ina zani dan Allah kai ne kawai zaka taimake ni , safiya na yi ko asuba
zan fito babu wanda zai sani ."
Nasir ya dan yi jimmm yana tunani
Abba ya yi shiru
Nasir ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce
"To shi ke nan , amma wallahi ba wannan shegen baccin naka zaka yi ba , asuba na yi zan
tashe ka , Yaya Kamal yana tafiya masallaci zaka fito ."
Abba ya ce .
"Naji na kuma yadda ."
Ya juya yabi bayanshi , a hankali suka shiga gidan suka rufe kofar suka koma daki .
Ya ba shi kaya ya canza , ya gasa jikinshi da ruwa , har magani Nasir ya ba shi , sannan Abba
aka kwanta aka fara bacci .
Kamar kuwa yadda su kai yarjejeniya asuba na yi Nasir ya duba ya ga ba kowa a falo , sannan
ya tusa 'keyar Abba ya fita.
Allah ya taimaka babu wanda ya ganshi.
Bayan kwanaki
SAUDIYA
Duk suna zaune cikin harabar gidan,
Kanwar Hajjiya samira ce ta ce .
"Wallahi aunty bada ban gidan abincin nan sabo ba ne da tare zamu tafi ."
Faruk ya ce .
"Gaskiya ne aunty kuma wallahi bana son mommy ta tafi Nigeria ita kadai , da Najib zai bita su
tafi ko a fasa tafiyar sai sabon wata mu tafi tare ."
Ya karasa magana yana kallon mahaifiyar shi .
"Lallai ma yaron nan tun kafin a haifeka nake zuwa Nigeria na dawo , shi ne yanzu zaka zo min
da wata magana ?
Shi Najib ba shi da aiki ne da zai bini, yaushe rabon na ga 'yata, kuma kwana daya zan yi kawai
."
Faruk ya ce .
"To mommy a gaida mana da mahaifin mu da kuma Fatima."
Hajjiya Samira ta ce .
"Za su ji in sha Allah."
Da yaren larabci ta yi magana
A lokacin Ahmad ya shigo yana cewa.
"Jirginku fa mommy sauran minti 30 ya tashi."
zumbur Hajjiya Samira ta yi ta tashi tana fadin .
"Bari na dauko jakata ." Ta shige dakinta
Faruk ya yi murmushi yana bin mahaifiyar tasa da kallo cikin matukar kauna
Tana shiga daki ta ji kanta ya matukar sara mata ga wani jiri yana dibar ta .
Da sauri ta samu bakin gado ta zauna tana haki ,
Ta dafa kirjinta tana cewa.
"Innalillahi wa inna..... ."
Tai dauriya ta tashi ta zuge jakar tafiyar ta, ta zaro magani ta sha
Ta yi ajiyar zuciya kafin ta ce .
"Ya Allah na shekara da yawa banga 'yata ba , ina rokonka da karka kashe wannan baiwa taka
ba tare da ka hada uwa da 'ya sun gana ba ya Allah, ka bani dama na kuma ganin Fatima a
rayuwa."
Ta jayo akwatinta ta fito cikin karfin hali , gudun kar su Murja su fahimci halin da take ciki su
hana ta zuwa .
Har suka kaita filin jirgi basu iya fahimci komai ba .
Allah ya kai ki ga Fatima lafiya Hajjiya Samira .
NIGERIA
Yau Fatima irin tsumudin da take se Allah, domin tunda satin zuwan mahaifiyar ta ya kama
kullum sai irga ake
Bari kuma yau da take da tabbacin tana hanya .
Ga shi Nasir ya tafi daukota a filin jirgi .
Fatima da Zarah suna zaune a falo duk sun kagu da shigowarsu Nasir
A wannan lokacin suka ji ana kwankwaso kofa
Da gudu Fatima ta mike har da bigewa da kujera da sauri ta bud'e kofar cikin shauki .
Tana budewa ba wai haushi taji ba , yake ta yi tana cewa.
"Sannu da zuwa Mama."?
Wacce ta kira da mama ta amsa tare da shigowa falon .wato Hajjiya Rukayya
A lokacin zarah ta kwashewa da Fatima dariya .
Alkalamin Autar
Marubuta
07040805269
WhatsApp only
FATIMA DA ZARAHν ΌνΎ
Na
Autar Marubuta
____________________________________________
*AUTAR MARUBUTA CE*βν ΌνΏ»ν ½ν±Όν ΌνΏ»
ν ΌνΌΉ__________ν ΌνΌΉ_________ν ΌνΌΉ__________ν ΌνΌΉ_________ν ΌνΌΉ
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_ν Ύν΄²ν ΌνΏΌ
<><><ν ΌνΌΉ><><><>ν ΌνΌΉ<><><>ν ΌνΌΉ<><><><>ν ΌνΌΉ<><><><><>ν ΌνΌΉ<><
Editingβ
Page 28 & 29
Iso ta yi wa Hajjiya Rukayya ta zauna a falo
Yayin da take cewa" basu karaso ba ne Hajjiya."?
Murmushi Zarah ta yi tana cewa.
"Wallahi basu karaso ba amma suna hanya ai shi yasa nake wa Fatima dariya ta yi zaton su ne
."
Ita ma Hajjiya Rukayya dariyar ta yi sannan ta ce .
"Hmmm".
Fatima ta gashsheta tare da tambayar mutanen gidan, nan ta tabbatar mata kowa lafiya ita ma
ta samu labarin zuwan Hajjiya Samira ne yasa ta taho domin mata Oyo yo.
Suna cikin hirar ne Nasir ya turo kofa rike da akwati a hannunshi yana yiwa Fatima murmushi.
Cikin tashin hankali na farin ciki fatima ta tashi tsaye tana jiran shigowar ta .
Cikin wannan'kaguwar ne kawai hawaye suka fara zubo mata, lokacin da Hajjiya ta sanyo kafa
zata shigo.
Da gudu Fatima ta nufi wajen ta fada jikin Hajjiya Samira, Hajjiya Samira ma cikin kewar gaske
ta rike 'yar tata a jikinta
Gamm suka rike juna cikin matukar farin ciki ,
Zarah duk abin ya burgeta ta tashi tsaye ita da Hajjiya Rukayya.
" Allah na gode maka ." Hajjiya Samira ta fada da larabci
Fatima ta kalli mahaifiyar ta idanunta cike da hawaye tana cewa.
"Na yi kewar ki sosai ."
Hajjiya ta yi mata murmushi, Nasir ya kalli Fatima yana cewa.
"To ga akwatin ta ."
Fatima ta juya suka karasa falon tare sannan ta samu ta zauna, Fatima ta jingine akwatin a gefe
ta zauna kusa Hajjiya
Lullubun dake jikin ta ta cire yayin da take duban yanayin tsarin gidan nasu
Sannan tai ajiyar zuciya tana cewa.
"Alhamdulillah." Tana hada ido da Hajjiya Rukayya
Murmushi hajjiya Rukayya ta yi mana kafin ta ce .
"Sannunki da zuwa Hajjiya, fatan kin zo lafiya ."
Hajjiya Samira da murmushi ta fara magana tana bata amsa .
"Na zo lafiya kalau Hajjiya Rukayya, fatan haka na same ku."
"Mommy sannu da zuwa ."
Zarah ta fada tana murmushi
Hajjiya Samira ta yi ajiyar zuciya tana kallon Fatima da cewa .
"Wannan ita ce Zarah, abokiyar zamanki."?
Fatima ta ce .
" Eh mama ita ce Zarah. "
Sannan Hajjiya ta kalli Zarah cikin murmushi tana cewa.
"Sannu 'yata Zarah fatan kuna lafiya ."?
Zarah ta ce .
" Lafiya kalau mommy barka da zuwa ."
Hajjiya ta kalli Nasir tana cewa.
"Sannu kai ma Nasir, wallahi ka girma, tun muna Nigeria ina matar Alaji lokacin kana dan
karami , kana zuwa kana komawa har Hajjiya Amina ta dawo da kai gidan ."
Nasir ya yi dariya yana cewa.
"Kuma ai ban manta ki ba Hajjiya."
Hajjiya ta yi dariya tana cewa.
"Kamal kam tunda na ganshi a video na biki duk ya girma ."
Hajjiya Rukayya ta yi dariya tana cewa.
"Girman dan mutum ba wuya ai ."
"Ina Hajjiya Binta da kuma sauran yaran ."?
Mahaifiyar fatima ta tambayi Hajjiya Rukayya
Bayan ta bata amsa
Ne ta dora da cewa .
" Amma dai wata guda zaki mana ko hajjiya domin an juma ba a haduba ."
Hajjiya Samira ta yi dariya tana cewa.
"Wata kuma ana zaune kalau , ai jirgin gobe zan koma Saudiya in sha Allah."
Fatima cikin matukar rashin jin dadi ta ce .
"Goben lafiya kuma Mama, yaushe rabon ki zo gaskiya a'a."
Hajjiya Samira ta kalli Fatima tana fadin .
"Gobe kuwa in sha Allah, daman ke na zo gank kuma ga shi na ganki to ai shi ke nan , to shi
Faruk ma cewa ya yi kar na zo ."
"Gaskiya mommy baza mu bari ki tafi gobe ba ." Cewar Zarah
Fatima ta ce .
"Gaskiya kam domin akwai guraren da zaki je har gidansu Zarah."
Hajjiya ta ce .
"To ai a goben ma zan iya zuwa , amma bazan wuce kwana biyu ba ."
Hajjiya ta ce .
"To ai kuwa idan na koma zan sanar da Hajjiya Binta ta zo ku gaisa karki tafi baku hadu ba."
Fatima ta tashi tana jayo akwatin cikin bacin rai ta nufi dakinta tana cewa.
"Gaskiya ba za ki tafi gobe ba ."
A lokacin kamal ya turo kofa ya shigo , yana nufo falon ya hada ido da sirikar tashi
Ya saki wani murmushi mai matukar kayatarwa .
Nan suka gaisa ana ta hira a kamo can a kamo can
Abin dai ya yi
Bayan d'an lokaci kuma Hajjiya Rukayya ta koma gida .
Bayan an yi sallar isha'i nan ma dai suka ringa hira kala-kala
Lokacin da Hajjiya Rukayya ta koma gida take sanar da Hajjiya Binta cewa gobe Hajjiya Samira
zata koma ai ko hakan yasa ta ce gobe da safe zata gidan su gaisa.
Misalin 12 na dare sunata hirarsu cikin farin ciki, a yi dariya a yi dariya a kamo can a kama can .
Abin da ya matukar ruda musu hankali suna cikin hira Hajjiya Samira ta yi dif idanunta suka
kakkafe
Nan hankali kowa ya tashi sukai kanta
Zarah ta bara dubata
"Amma tana da ciwon zuciya ne ."?
Cewar Zarah ta yi tambayar ga fatima cikin tashin hankali
Fatima ma cikin wannan tashin hankali ta kalli Zarah tana cewa.
" Tana dashi Zarah. "
Zarah ta kalli Kamal tana cewa.
"Karku damu mu tafi asubiti yanzu, domin babu wani kayan aiki anan ."
Kafin ka ce komai
Nasir har ya dauko mota suka nufi asubiti.
Suna isa aka bawa Doctor Zarah Sale daki tare da kayan aiki .
Hankali na Fatima ya matukar tashi hakan ya sa ta fara kuka
"Haba mana Fatima ki yi hakuri zata samu lafiya karki damu dan Allah."
Kamal ya yi magana yana rike hannayenta
Fatima kawai ta kauda kai ta cigaba da kuka
Kamal ya yi ajiyar zuciya yana kallon kofar dakin da aka shigar da Hajjiya Samira.
Nasir ma ya matukar damuwa sosai da halin da ake ciki .
Duk jiran tsammani suke .
Masu abu da abun su doctor Zarah ce ta fito daga dakin tare da wani doctor Ahmad
Murmushi ta sakar musu tana nufa wajensu
Suma duk kanta suka yo , duk da sun ga tana murmushi amma hankalin su bai kwanta .
"Ya jikin Mama Zarah."?
Fatima ta tambaya cikin matukar son jin amsa
Murmushi Zarah ta yi tana cewa .
" To mene na kukan kuma , ta fa samu lafiya ."
Doctor Ahmad ne ya kalli Zarah yana fadin .
"Bari na kira nurse a canza mata daki zuwa dakin hutu."
Ya fara tafiya
Zarah ta dakatar dashi da cewa .
"A'a dactor Ahmad, ba wani tsanani bane dan haka baza mu kwana a asubiti ba , zamu tafi gida
."
Dactor ya ce .
"To shi ke nan dactor." Ya wuce ya tafi
Nasir ya duba agogon hannunshi yana cewa.
"Yanzu karfe 1:35 fa , dare ya yi ."
Fatima ta kalli Kamal tana cewa.
"Tom ya kamata mu tafi ."
"Amma Zarah babu damuwa idan muka koma gida ."
Zarah da jin tambayar ta Fatima ta yi wani murmushi na kasaita kafin ta ce.
"Kin manta wace ni , dactor Zarah babu abin damuwa in sha Allah."
Fatima ta kauda kai da takaicin yadda ta samu amsar a gun Zarah.
Bayan sun dawo gida misalin karfe 2 daidai ne Hajjiya Samira ta ce .
Su barta a falo domin bata jin bacci
Haka suka so ta kwanta ta yi bacci amma ta ki
Har asuba ta yi tayi sallah, ta zauna a falon tare da carbi
A lokacin Fatima ta shigo, yayin dasu Kamal suka dawo daga masallaci.
Hajjiya ta kalli Fatima tana cewa.
"Fatima tafiyata fa na nan yau zan koma saudiya."
Kafin Fatima ta ce komai ma .
Kamal ya fara cewa .
"Haba mommy ta ya zamu barki ki tafi saudiya ko baki da gata ai sai haka , gaskiya babu inda
zaki je."
Murmushi hajjiya ta yi tana cewa.
"Duk na tada muku da hankula amma ina baku hakuri ."
Lokacin zarah ta shigo tana ajiyar zuciya da cewa .
"Haba mommy duk muna kaunar ki , babu wani abu a ciki , Allah muke fatan ya baki lafiya
kawai ."
Cikin jin dadin yadda Fatima ta ji maganar Zarah ta kalleta tana fadin .
"Na gode Zarah, kin yi mini komai bazan manta da hakan ba ."
Wata harara Zarah ta dokawa Fatima tana cewa.
https://chat.whatsapp.com/BxsOc6eKfrTAE5lgAlJQHQ
FATIMA DA ZARAHν ΌνΎ
Na
Autar Marubuta
_______________________________________
Editingβ
*AUTAR MARUBUTA CE*βν ΌνΏ»ν ½ν±Όν ΌνΏ»
ν ΌνΌΉ__________ν ΌνΌΉ_________ν ΌνΌΉ__________ν ΌνΌΉ_________ν ΌνΌΉ
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_ν Ύν΄²ν ΌνΏΌ
<><><ν ΌνΌΉ><><><>ν ΌνΌΉ<><><>ν ΌνΌΉ<><><><>ν ΌνΌΉ<><><><><>ν ΌνΌΉ<><
https://www.facebook.com/profile.php?id=61550626300848
Page 30 & 31
"An ce miki ke ce kawai kike son mommy ne ."
Hajjiya ta yi murmushi hira sukai ta yi har gari ya waye .
Zarah ta kawo abinci aka karya sannan ta danko magunguna ta bata .
Fatima ta ce .
"Gaskiya kishi nake duk kinbi kin rike mini mommy komai ke kike mata ."
Zarah ta yi dariya tana cewa.
"Wallahi Fatima ina kaunar mommy a cikin jini na ."
Kamal ya yi murmushi
Nasir ne ya tashi tsaye yana cewa.
"Bari na shirya na tafi makaranta, mommy Allah ya kara miki lafiya ."
Ta yi murmushi ta ce.
"Amin ."
Ya wuce daki domin shiryawa .
Kamal shima ya tashi tsaye yana cewa.
"Mommy bari naje gidan Alajin mu na dawo ."
Hajjiya Samira ta ce.
"To Allah ya tsare dan Allah ka gash she mini da Hajjiya Amina sosai d sosai ."
Kamal ya ce.
"In sha Allah zata ji , domin ma ba dadewa zan ba yanzu zan dawo in sha Allah."
Sannan ya kalli Fatima yana cewa.
"Ai da kin shirya na aje ki , tunda Zarah karfe 9 zata fita har ma kin dawo ki zauna da mommy."
Fatima ta ce.
"A'a kaje kawai Allah ya tsare , sukai sallama ya tafi."
Zarah ta kalli Fatima tana cewa.
"Yau kina da aiki ne daban ."?
Fatima ta ce .
" A'a zanje bada basu takardu ne kawai asa mini hannu ."
"Okay to kije ki shirya , zan shirya na jira ki , idan kin dawo na tafi asubitin ."
Cewar Zarah
Fatima ta ce .
"To."
Tana tashi tsaye Hajjiya Binta ta shigo da sallama.
Duk ran Fatima kawai ya baci
Zarah ce ta amsa sallamar, yayin da Hajjiya Binta tana hango Hajjiya Samira ta taho da gudu
tafa fadin .
"Oyoyo oyoyo Hajjiya ta ."
Ta rungume Hajjiya Samira dake zaune cikin karfin hali.
Murmushi ta sakar mata suka fara gaisawa , Fatima ta tabe baki ta nufi dakinta .
Zarah ta gaida Hajjiya Binta yayin data fara kwashe kayan abincin da suka ci tana kaiwa wajen
da ya dace .
A lokacin Fatima ta fito suka gaisa da Hajjiya Binta, har wani soyyaya take nuna mata wai dan
ta ga a gaban mahaifiyar ta ne .
Fatima kuwa abin duk kona mata rai yayi ta kalli Hajjiya Samira tana cewa.
"Mommy