Showing 33001 words to 36000 words out of 37591 words

Chapter 12 - FATIMA DA ZARAH NA AUTAR MARUBUTA.pdf

Advertisement

24 Jun 2025

1947

kashe hajjiya Samira .Amma ka yi shiru akai ."
Ta karasa maganar ta


Alaji Mustapha ya kalli Hajjiya Rukayya
Sannan ya fara cewa .
"Idan zaki ja da shari'a ne ga hanya , banda rashin hakuri irin naki ki bari gaskiya ta bayyana
mana, kuma fatima babu wani abu da ta yi ko kece abin da zaki ke nan ."


A lokacin ne Habib da Khalid suka shigo

Hajjiya Rukayya ta ce .
"Ai shi ke nan ."





"Kotu ta shirya cigaba da sauraran bangarori ."

Cewar alkali

Barrister Nuhu ya kalli Barrister Fatima
Barrister Fatima ta jefa masa murmushi😇






Autar Marubuta ce 😤


FATIMA DA ZARAH🎀
Na
Autar Marubuta
________________________________________

*AUTAR MARUBUTA CE*âœí ¼í¿»í ½í±¼í ¼í¿»
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><


EditingâŒ



Page 42 & 43




Barrister Fatima ta tashi ta nufi wajen Hajjiya Binta dake cikin akwatin tuhuma

Sannan Barrister ta kalli alkali tana fara cewa .
"Ya mai girma mai shari'a, kowa ya sani sanda aka kashe hajjiya Samira mutum biyu ne cikin
gidan, amma ya mai shari'a wannan a zahiri ke nan ."


Alkali ya sake gyara zama yana sauraran Barrister Fatima, tare da kowa hankalinshi yana
wajenta .

"Ya mai girma Hajjiya Binta ta boye mana cewa Nasir yana cikin wannan gidan , a baya da haka
ma d'an gidan yayan ita Hajjiya Binta ya shigo cikin gidan yayin da wannan kisan yake gafff da
faruwa."



Wani firgici ne ya mamaye zuciyar Hajjiya Binta, taji duk ta rude ta razana



Babban tashin hankalin ta ma saida Barrister Fatima ta matso kusa da ita tsoronta ya bayyana
a zahiri

"Malama Binta me yasa kika boyewa kotu wannan.Bayan kin sani sarai wannan ya sake
tabbatar wa akwai abin da kike boyewa kotu."

"Ina da jahh ya mai shari'a." Barrister Nuhu ya yi hanzari ya fada


Alkali ya kalleshi da cewa .
"Kotu ta baka dama."


"Barrister Fatima tana son dawo mana da shari'a baya ya mai shari'a, tare da shirin sanyawa
Hajjiya Binta maganar da bata da tushe cikin bakin ta ."
Barrister Nuhu ya 'kar'kare


Alkali ya mayar masa da cewa .
"Barrister Nuhu kotu guri ne na sauraran bangarori , ka bar barrister Fatima ta fito mana da abin
da take son kotu ta sani ."


Barrister ya koma ya zaunazauna



Fatima ta kalli alkali tana cewa .
"Ina rokon wannan kotu mai adalci data bani dama domin fito da babbar shaidar nuna cewa dan
Hajjiya Binta yaje wannan gida domin kare inkaren barrister Nuhu ."

"Kotu ta baki dama ." Alkali da babban murya ya fada


Nan Nasir ya fito ya tsaya, tun a gida kamar yadda Fatima ta bukaci kar yaji tsoro komai ya
tsaya cikin kwarin gwiwa , haka Nasir ya tsaya babu wani tsoro a tare dashi


Sannan ta matsa kusa dashi tana cewa .
"Malam Nasir shin mene ne tsakanin da Kamal ."?


Nasir ya ce .
" Shi yayana ne kuma gidansa nake zaune ."


Fatima ta ce .
"Alhamdulillah, kana nufin wannan kisan ya faru kana gidan ke nan ."?



Wani tsoro ne ya ziyarci Nasir dajin wannan magana ta Fatima


Yayi saurin fara cewa .
" A'a ba haka nake nufi ba. "


"Zaka iya sanar da kotu abin daka sani a wannan ranar , bayan kuma kana da lecture a
makaranta, amma ka kasance a gida ."


Ajiyar zuciya Nasir ya yi sannan ya fara magana .

"A wannan ranar kowa na gidan ya sani har ita marigayiya Hajjiya Samira cewa zanje
makaranta, domin a gaban idanunsu na tashi na tafi dakina a domin shiryawa , bayan na fara
shiri sai ga kiran aboki na yake tabbatar mini professor bazai zo makarantar ba .

Hakan yasa na fasa zuwa makaranta kuma nayi farin ciki da hakan


Ina kwance a daki sai ga kiran wayar abokina wanda shi kamar d'an yake gurin Hajjiya Binta
yake sanar dani cewa zai zo wai yana jin yunwa . Ni kuma nace kar ya zo amma yace sai yazo

."



Ajiyar zuciya ya yi sannan ya dora.


"Na fada masa zan masa rashin mutunci idan ya zo , amma saida ya zo hakan yasa ban fasa yi
masa rashin mutunci ba ya fita cikin fusata , wanda babu jimawa na jiyo kuka a falo, amma ni
sam bansani ba cewar ma Hajjiya Binta ta zo wannan gidan ."



Barrister Fatima ta kalli Nasir tana cewa .
"Nasir kotu zata so taji wanne dalili ne yasa baka son zuwan wannan abokin naka ."?


Nasir ya ce
" Saboda ya sha sa na rasa damammaki na cigaba a rayuwata, karatu na wanda sanadinshi
aka kore mu a makaranta, sannan yayana Kamal ya bani dama ta karshe , shi yasa nake gudun
wannan abokin nawa domin gina rayuwata. "


Fatima ta yi murmushi tana cewa .
"Kana son sanar da kotu ba abokin kwarai bane ke nan ."?


Nasir ya ce .
" Haka ne domin har shaye-shaye yana yi."


"Mene sunan abokin naka ."? Ta tambaya


A takaice Nasir ya ce .
" Abba Alaji. "


Barrister ta yi murmushi ta kalli alkali ta fara magana


"Ya mai girma mai shari'a, ina fatan wannan kotu mai albarka ta fahimci wannan sako na Nasir,
Hajjiya Binta tana falo Abba Alaji ya shigo , sannan tana falo ya fita , babu jimawa kuma kisan

ya faru ."


Ta kalli Hajjiya Binta tana cewa.
"Shin ko ke da Abba Alaji kuka kashe Hajjiya domin wata manufar."?


Cikin matukar hassala da babban murya Barrister Nuhu ya ce .
"Ina da jah ya mai shari'a.


Barrister Fatima tana yunkurin juya wannan lefi ga Hajjiya Binta har ma ga dan yayanta ."


Ya kalli Nasir yana cewa .
"Malam Nasir kana shaye-shaye."?

Nasir ya ce .
A'a ko cigare ban taba sha ba."


"To me yasa kake son cinnawa abokin ka wuta har kake kiran yana fita wannan kisan ya faru ,
shin kaima ba abin zargi bane ."?



Nasir kamar yadda yaji jan kunne na Fatima kan karya ji tsoro ya fara magana cikin kare kai

" Ita Hajjiya Binta shaida ce , tunda ta zo bata ganni ba , har Abba Alaji ya shigo ya fita bata
ganni ba ko da wasa , ta ya kuma zanzama abin zargi bayan wacce aka kashe tana tare da ita
."



Wani murmushi fatima ta saki najin dadin yadda Nasir ya bada amsa lokaci guda kuma tana
kallon ZARAH


Sannan ya koma gaban Zarah yana cewa .
"Shin kina ina sanda wannan yaron ya shigo ."?


Zarah tai ajiyar zuciya mai zafi kana ta ce .

" Ina cikin daki, sannan ban ma taba ganin shi ba , kawai sunanshi..."

Barrister Nuhu ya dakatar da ita da cewa" kin bani amsa ta ".



Sannan ya yi godiya
Barrister ya koma ya zauna





Fatima ta kalli Hajjiya Binta tana cewa.
"Zaki iya fada mana dangane da shigowar Abba Alaji cikin gidan, shin ya hadu da Hajjiya
Samira ko ya akai."?


Wani yanayi ne mai matukar wuya ya rufe Hajjiya Binta, kowa yana hangar wannan yanayi na
tashin hankali a tare da ita


" Kotu na sauraran ki ." Fatima ta sake tunatar da ita



Wani takaici ne ya rufe Barrister Fatima hakan yasa ta kalli alkali ta fara maganar da ta sake
tadawa Hajjiya Binta hankali.


"Ya mai girma mai shari'a
Hajjiya Binta tana tsoron bayyanawa kotu cewa ita ta kashe Hajjiya Samira, wanda nasan da
cewa da tasan Hajjiya Samira ciwonta ya tashi ,lokacin da ta zo Nigeria to da wannan zata fake
, amma rashin sanin hakan yasa ta dorawa Zarah Sale kazafi na kisa.

Me yasa kika kasheta."?



" Ina da jah ya mai shari'a. "


Barrister Nuhu ya fada

Kotu taki amincewa da jansa



Hakan ya sa Hajjiya Binta ta fara kuka tana cewa.
"Wallahi ba haka bane akan mene zan kashe Hajjiya Samira, babu abin da ta yi mini duk da
cewa mum yi zaman kishiyoyi, ni wallahi bazan iya kasheta ba ."



Barrister Fatima ta ce.
"To me yasa kike tsoron sanar da kotu cewa Abba Alaji shi ne ya kasheta. Tun da bake bace ,
shin kina tsoron a kashe shi ne ."?



Sabon kuka ta sake fashewa dashi


Tana cewa.
" A'a A'a ya mai shari'a, Abba Alaji ya shiryu.
Bani da burin da ya wuce naga wannan yaron ya samu rayuwa mai kyau , shima haka mahaifin
sa .


Kwarai da gaske Abba ya shigo a wannan ranar ."


Cikin sabon kuka ta sake cewa .

"Ya shigo a wannan ranar , muna zaune da Hajjiya a falo
Kai tsaye ya shige dakin Nasir, Ni kuma a wannan lokacin nake cewa hajjiya ta bani turare na ,

Ta shiga ciki domin ta dauko mini .


Da wowarta ya yi daidai da fitowar Abba daga dakin Nasir cikin fusata ya bangaje Hajjiya
Samira ta fadi."


Nan kowa zuciyarshi ta fara bugun ....

"Da sauri na nufi gunta , amma bata iya ko bude idoba , hakan ya bawa tunani cewa ta mutu .


A ranar naga tashin hankali a idanun Abba wanda ban taba gani ba

Ya ringayi mani magiya kan na rufa masa asiri daga yau ya dena komai ya tuba ,

Hakan yasa na amince ya tafi , saboda ko ba komai d'ana na daukeshi ."


Wani kuka take kamar mai shirin shidewa

"Hakan ya sa na nemi mafita , nasan da cewar Nasir baisan abin daya faruba ,
A wannan yanayi sai Zarah ta fito , shi ke nan na dora mana wannan laifi domin samin salama
ta da Abba Alajiiiiiii."

Ta kai kasa tana kuka


Dactor Zarah wani yanayi ne ya rufeta kawai ta fara kuka


Kotu aka barke da hayaniya , caaaaaa shaaaa wannan ya ce wannan ya mayar masa .


Alkali ya bukaci a yi shiruuuushiruuuu






07040805269
WhatsApp only




Autar Marubuta
FATIMA DA ZARAH🎀
Na

Autar Marubuta
________________________________________
*AUTAR MARUBUTA CE*âœí ¼í¿»í ½í±¼í ¼í¿»
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><


EditingâŒ

Page
44 & 45


Bayan kotu ta yi shiru , kawai kukan Hajjiya binta kawai ake ji

Zarah kuwa hawaye take

Nan alkali ya bada sammacin kawo Abba Alaji a duk inda yake

Aiko yana gida mahaifin shi yana shirin su tafi filin jirgi domin Abba zai koma makaranta, basu
kai ga tafiya ba
Aka kamo Abba Alaji aka taho kotu , nan Hajjiya Nana da Alaji Sani hankali su ya tashi suka
biyo bayansa.


Ana shigo da Abba Alaji ya kalli Hajjiya Binta yana cewa.

Cikin kuka
"Wato saida kika bayyana komai , bayan kin yi mini alkawarin rufa mini asiri , wannan ita ce
soyyaya da kike mini ,bayan na shiryu na dena kin yaudare ni ."


Kotu ta sake barkewa da ka ce, na ce , alkali ya bada umarnin shiru


Nan kotu ta karantawa Abba Alaji irin tuhumar da ake masa, nan ya amsa laifinsa bisa kuskure

Hankulan jama'a suka sake tashi sosai

Barrister Fatima ji take kamar ta fesawa Hajjiya binta mari domin wani abu take jin ya tsaya
mata a zuciya


Su kam su Faruk yau gasu ga makashin mahaifiyar su kawai hukunci suke jiran kotu ta yanke .


Zarah kukan farin ciki take yi da bakin ciki a hade, Kamal kuwa zuciyarshi cike da zumudi



Nan Alkali ya fara gabatar da irin tuhumar da aka yiwa Zarah Sale

Nan ya tabbatar wa al'uma kotu ta wanke Zarah Sale bisa wannan zargi da ake mata , sannan
kotu ta sallameta .


Abba Alaji bisa wani shashi na kundin tsarin mulki aka yanke masa hukuncin zama a gidan yari
har karshen rayuwarsa .


Sannan Hajjiya Binta bisa kazafi na kisa data dorawa Zarah Sale
Duba da wasu shashin kundin tsarin mulkin kasa
Alkali ya tabbatar mata da dangwama a gidan yari har karshen rayuwarta .


Sannan alkali ya sallami wannan shari'a tare da wanda bai yadda da wannan shari'a ba yana da
damar daukaka kara cikin watanni uku .



Khalid kuka ya fashe dashi na matukar tashin hankali dajin irin wannan hukunci da aka
yankewa mahaifiyar shi .


Da gudu Zarah ta nufi mahaifiyar ta da mahaifin ta tana rungumesu cikin wani kuka mai karya
zuciya



A wannan lokacin wasu zafafan hawaye suka zubowa Fatima sanda ta tuna da mahaifiyar ta

Kamal kuwa duk ya rasa inda zaisa kanshi farin cikin da yake ciki


Alaji Mustapha da Alaji Mansur ba a cewa komai

Suna gani aka sanya Hajjiya Binta a motar gidan yari tana kuka, Alaji Mustapha ya kauda
kanshi, yayin da ya hangi Khalid cikin mugun yanayi

Kawai ya tsinci kanshi shima cikin wannan yanayi

Alaji Sani abin ya yi masa yawah ga danshi ga kanwarshi , duk yabi ya susuce , to sai dai Allah
baya dorawa mutum jarabawar da zata fi karfin shi .


'Yan jarida kuwa sai neman labarai suke , sai dai samm basu samu damar magana da Zarah ba
.

Haka Fatima bata saurare su ba




Lokacin da Fatima take kuka ne Kamal ya rike hannunta

A lokacin su Faruk suka fito daga cikin kotun suka wuce ta gabansu

"'Yan uwana .'!

Fatima ta fada cikin muryar kuka

Su faruk suka dakata ba tare da sunce komai ba

Cikin wannan yanayin ta ce .
" Ina kaunar ku , bani da sama daku , duk shari'a ta gaskiya nake bi hakan yasa nake yin
nasara."


Faruk ya sa kai ya wuce , suka bi bayanshi suka tafi

Fatima ta sake fashewa da kuka tana cewa Kamal.
"Ina kaunar su sosai ."

Kamal ya mata murmushi yana cewa.
"Suma suna alfahari dake , kuma zaki gani ."

Ta masa murmushi cikin kuka


Sannan ta ce .
"Mu tafi gida kawai domin nasan Alaji sale tare da Zarah zasu tafi sun yi kewarta ."


Kamal ya kuma yi mata murmushi sannan suka wuce suka tafi



Alaji Mustapha ya matukar shiga wani yanayi, haka kowa na cikin gidan, Hajjiya Rukayya ma
abin yana matukar dukanta

Khalid ya matukar zautuwa haka Habib ba a cewa komai


Haka su Alaji Sale suka wuce gida cikin matukar jin dadi , Mahmud da Umar farin ciki ya ishe su
.



Washe Gari da wajen karfe 12
Sai ga Alaji sale da Hajjiya Sa'adatu da Umar, Mahmud da Zarah sun nufo gidan Kamal



Ai kuwa Nasir da kamal duk suna gida
Bayan su Alaji sun shigo sun zauna aka gaggaisa cikin farin ciki da wasa da dariya

Sannan Fatima ta kalli Zarah tana cewa.
Cikin harshen turanci
"Barka da dawowa likitan zuciya."

Kowa murmushi ya yi , Zarah tai dariya sannan ta ce .
"Hmm abin dai kamar mafarki a karshe gaskiya ta bayyana ."

Fatima tai murmushi tana fadin .
"Ai karki damu ki aikata duk abin da kike so."

Dariya kowa ya yi sannan Zarah ta ce .
"Kar dai ki cika mini baki naje nayo kisa ki barni a ciki ."


Dariya Fatima ta kwashe da ita sannan ta ce.
"Allah dai ya kyauta Allah ya jikan mommy na ."
Wasu hawaye suka gangaro mata

Zarah ta tashi ta koma kusa da ita , kana ta rike hannayen ta tana cewa.
"Ina matukar baki hakuri Fatima, ina jajanta rashin mommy, dan Allah ki yi hakuri amma ai
muna da wata uwar."

Zarah ta karasa maganar tana nuna mahaifiyar ta tana murmushi

Murmushi Fatima ta yi sannan ta had'a ido da Hajjiya Sa'adatu cikin wannan hawaye .



Hajjiya Sa'adatu ta fara mata murmushi tana fadin .
"Haka ne Fatima, ki dauke ni uwa , domin kin yi mana abin da bamu da abin da zamu biyaki .."


"Haba ,haba mommy dan Allah." Fatima ta fada tana share hawaye

"Zarah ce ta fara komai , ta kula mini da mommy matuka , hakan yasa zan iya sadaukar da
komai a domin ce to ta dan Allah kar ku yi mini godiya."

Ta aje maganar tana kallon Alaji Sale

Nasir ya yi murmushi yana kallon Kamal, kamal ma ya maida masa da murmushi na farin ciki.

Alaji Sale ajiyar zuciya ya yi sannan ya dubi Fatima ya fara mata magana .
"Bani da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login