Showing 15001 words to 18000 words out of 37591 words

Chapter 6 - FATIMA DA ZARAH NA AUTAR MARUBUTA.pdf

Advertisement

24 Jun 2025

1975

ya akai haka."



Murmushi Fatima ta yi kana ta gyara zaman ta a kujera tana fadin

"Wallahi lamarin ne , amma in sha Allah ranar 20 ga wata za ai zaman karshe ."



Khalid ya ce .
"To masha Allah, fatan nasara ."

Fatima ta ce .

"In sha Allah yaya na gode ."


Ta kalli abincin da Zarah ta kawo musu tana cewa.

"Ku ci abincin mana yaya."



Habib ya ce .

"Keee mu fa ba yunwa muke ji ba kuma gashi min sha fruit."



Khalid ya kalli Fatima yana cewa.

"Ina Kamal d'in fa ."?



" Kamal bai dawo ba wallahi yana company. "
Fatima ta ba shi amsa





Kad'an sukai hira suka tashi kamar wanda aka muntsu suka tashi a tare .



"Haba Yaya muna hira kuma zaku tafi , to ku bari Kamal d'in ya dawo mana ai yanzu yana
hanya ."



Fatima ta yi musu maganar yayin da suke a tsatstsaye

Khalid ya ce .

"A'a fa sai wani lokacin, ki gashe shi kawai ." Suka isa wajen kofar



Tana taka musu zuwa wajen kofa tana cewa a gaida mutanen gidan.



Habib yana sa hannu zai bud'e kofar


Nasir ya turo kofar ma'kale da jakar makaranta, ga dukkan alamu daga makaranta ya dawo .


Yana hada ido dasu ya sakar musu murmushi.





07040805269
WhatsApp only.


FATIMA DA ZARAH🎀
Na
Autar Marubuta

________________________________________

EditingâŒ

Page 20 & 21



"Ka ga sojoji barkan ku wai har zaku tafi ."
Nasir ya yi magna a sanda yake shigowa ciiki


Suma duk murmushi sukai fara masa kafin

Habib ya ce .

"Ai kuwa har zamu tafi ya makaranta, ya mancewa damu ."


Nasir ya yi dariya kana ya ce .

"To wallahi makaranta ce take boye ni , domin so nake kawai na kammala karatun nan na koma
gidan mommy, yaya Kamal ya buden company na ."

Habib ya ce .

"To Allah ya taimaka Nasir."

Sannan ya basu guri suka wuce tare da sallama

Suna fita Fatima ta rufe kofar

"Aunty Fatima na dawo ."
Nasir ya yi magana da Fatima

Halinta na murmushi ta masa sannan ta ce .

"To sannu da zuwa ."

Ya shige dakinshi yana murmushi
Yana shiga ya aje jakar shi , sai yaji wayarshi ta fara ruri

Kafin ya cire takalmin kafarshi ya duba wayar don ganin me kira


Dogon tsaki yaja yana cewa.
"Abba Alaji ko mayen mutum wallahi."

Ya sake jan tsaki yana katse kiran




Kamal da Fatima ne zaune a falo suna kallo
Misalin karfe 8saura na dare

A wannan lokaci Zarah ta fito daga dakinta, sanye da rigar likitoci da jakah a hannunta

Fatima tana ganin haka ta kauda kai tana dariya

Zarah tana kula da hakan ta yi murmushi, kana ta ce da Kamal.


"Zan tafi saida safe."

Kamal ya d'ago yana cewa.

"Ohhh kina da night ko , to Allah ya tsare hanya."


"Mene kike mini dariya."?

Zarah ta tambayi Fatima

Fatima ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce .

" Shi kin ga aikina babu fitar dare , ga shi zaki barni da Kamal a gidan ." Fatima ta yi maganar
cikin son cusawa Zarah kishi


Zarah ta kauda kai , kawai ta fice cikin haushi


Kamal ya kalli Fatima yana cewa.
"Data kula ki baza ta tafi yanzu ba , ga shi ta samawa kanta samala ."

Dariya Fatima ta yi sannan ta ce .

"Wallahi ba 'kin kulani tai ba , nasan zata rama ne ."

Kamal ya ce .

"Wato Fatima ina alfahari daku ina san ku fiye da komai .
Amma wannan kace-nace d'in tsakaninku Allah ya nunan ranar dena shi ."

Fatima ta yi dariya.


Wasu kwanaki

Nasir da Kamal suna zaune suna kallo , Zarah kam tana duba wasu takardu
Babu sautin da ake ji saina gidan TV da suke kallo


Fatima ce ta turo kofa sanye da kayan lauyoyi da bakar jakarta ta gun aiki .
Cikin matukar far'a a tare da ita ta ce .


"Assalamu alaikum wanda nafi kauna a duniya ta ."

Jin hakan ya sa duk suka d'ago suna kallonta

Kamal ne ya fara murmushi yana cewa.
"Ga dukkan alamu an gama shari'a cikin nasara ."



Fatima ta saki wani murmushi ta samu guri ta zauna


Fatima ta kalli Kamal tana cewa .

"Wannan gaskiya ne dear ."


Sannan ta kalli Zarah cikin wannan farin cikin dai tana cewa .

"Wato Zarah yau na kammala shari'a cikin nasara ,kar ki ga yadda komai ya yi daidai a kotu ,
farin ciki matuka, zan so a ce kin shiga kotun an yi a gaban ki ."



Zarah ta tabe baki sannan ta ce cikin yaren turanci.
"Na ta ya ki murna ."

Sannan ta juya harshe zuwa Hausa ta cigaba da cewa .


"Allah kar ya nunan ranar da zan shiga kotu a rayuwata, domin bani da lokacin ta ."

Fatima ta yi dariya


Nasir ya ce .

"Aunty Fatima ni kam zan so watarana ki gayya ce ni kotu , nasan in dai ke ce zaki karbi shari'a
to tabbas dole a sara miki ."




Fatima ta yi murmushi sannan ta ce da Nasir.

"Kar ka damu akwai wata shari'ar ma ."




Kamal ya ce .

"Naji dadin nasarar ki sosai ."


Ta yi masa murmushi.

Fatima ta ce .

"Ya Allah na gode maka da wannan nasarori da kake jaraftata dasu ."

Zarah ta kalleta yayin da suka hada ido , ta kauda kanta .


Wayar Nasir ce ta fara ringin , ya yi sauri ya katse ta , aka sake kira ya yi sauri ya kuma
kashewa .


Kamal ya jefa masa wani kallon zargi , Nasir ya yi masa murmushin ya'ke



Bayan minti guda ya ji shigowar sako wayarshi .

"Ka fi to ina waje ."

Abin da aka turo ke nan

Ya yi ajiyar zuciya ta bacin rai ya tashi ya fita waje . Yayin da Kamal yake binshi da kallo


Fatima tana ta duba wani abu cikin fayil tana murmushi,
Ita ma Zarah ta na aikinta .
Nasir yana fita
Ya ci karo da Abba Alaji.


Cikin mummunan bacin rai Nasir ya fara masa magans .

"Wai kai uban mene kake bukata ne Abba , wallahi ka rabu dani abotar an dena ka rabu dani
mana ."


Abba Alaji ya ce .

"Haba Nasir ni ne fa , zuwa na yi mu gaisa , wai waye ya shiga tsakanin mu ne ."



Nasir ya ce .

"Wallahi ka kiyaye ni , babu ni ba kai , kai matsala ne mai haddasa annoba , duk sanda na fara
samun nasara kana nufoni komai ya ke lalacewa .


Wallahi ka kuma kirana ,ai yaya Kamal yana falo ka cigaba ."


Yana gama magana ya koma ciki bai jira cewar komai daga Abba ba .




Cikin wata fuska ta rashin gaskiya ya koma ciki , a wannan lokacin dai Kamal yana masa wani
kallo , har ya zauna , amma Allah bai nufe shi da ya furta komai ba .



Fatima ta rufe fayil din da take dubawa , lokaci guda kuma tana kai idonta kan TV

Nasir cikin son Kamal ya dena masa kallon zargi ya ce .

"Bikin laila fa ya zo .Ga shi ban fara aiki ba ."


A lokacin kamal ya yi murmushi sannan ya ce .

"Ai kai ne ka yi wa kanka , da tuni kana aikinka , yanzu ma idan ka yi wasa da damar ka babu
abin da zan iya maka .

To mene idan ka fara aikin mene zaka mata kake wani zance."



Nasir ya sosa kanshi , sannan ya ce .

"Wallahi yaya Kamal mota nake son siya ."


Zarah ta d'ago kai ta ce .

"In sha Allah nima kafin bikin zan canja mota ."


Fatima ta ce .

"Canza mota ai dole ne nima ."


Kamal ya ce ."Ai akwai motoci masu kyau wajen Alaji Mamman sai ku samu a can kawai ."


Zarah ta ce ."Eh tabbas akwai motoci masu kyau a gun shi , can zamu je ."


Fatima ta bata rai jin yadda Zarah ta yabi motors din

Sannan ta ce .

"A'a ni gaskiya bazan se mota a can ba , babbar motarshi bata wuce million 5 ba , dan haka
bazan siya a can ba ."



Ita ma Zarah ranta ya baci yadda taji Fatima na magana


"Me kike nufi Fatima."?


Fatima ta ce .

" Ina da kudin da zan se motar sama da million 5 don haka bazan siya anan ba , ba karama
nake so ba ."



Zarah ta rufe takardun dake hannunta ta aje su gefe sannan ta fara magana .


"Ke kin san ina da kudin da zan se motar da baki isa ki hau ta ba , kin sanni kin san mahaifina,
kinsan yadda na yi suna a harkar rubutu , to ki tabbatar dole kina baya na ."


Nasir ya zuba kunne cikin mamaki yana kallonsu


Yayin da ran Kamal ya matukar baci dajin abin da suke



Fatima ta yi murmushi na kasaita kafin ta ce .

"Kwarai kuwa nasan mahaifinki yayi suna , amma ina tabbatar miki ba zai nuna maka kudi ba ,
sanin kan ki ne su waye iyayena , mahaifiyata tana saudiya , tare da yayannina , kuma ina mai
tabbatar miki komai kudin ku , baza ku fimu ba , kuma ina da darajar da zan shiga wani guri ,
wallahi baki isa ki shige shi ba ."

Zarah ta ce.
"To shi ke nan , mu zuba ni dake muga wanda zai se motar da tafi karfin wani ."

Kamal ne ya tashi tsaye tare da daka musu wata tsawa yana cewa.


"Wannan wanne irin hauka ne ."


Duk suka sha jinin jikinsu




Autar Marubuta
07040805269
Ku ne meni a WhatsApp




FATIMA DA ZARAH🎀

Na
Autar Marubuta

________________________________________
*AUTAR MARUBUTA CE*âœí ¼í¿»í ½í±¼í ¼í¿»
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><
><><><>🌹<><


EditingâŒ




Page 22 & 23

Kamal cikin fushi da bacin rai ya cigaba da cewa .

"Kuna son nuna wa duniya ilmin ku , duk na banza ne ke nan , na yi muku shiru tsawon lokaci,
amma abin naku gaba yake yi ,

Mene amfanin hakan , almubazzaranci daidai ne ?

To wallahi duk wacce baza ta hau motar kasa da million 7 ba , duk na haramta muku siye , aikin
banza , wallahi zan yi maganinku ."


Ya wuce ya futa waje ya bar musu gidan .



Nasir ma ya yi ajiyar zuciya , ya tashi ya nufi dakinshi .



Fatima ce kawai a cikin gidan , sakamakon Kamal yana company tare da Nasir.
Zarah kuma tana wajen taron karawa wani marubucin abikinta girma .


Yau babu wanda yake da aiki a cikin gidan .

Gama girkinta ke nan , Fatima ta d'auka wayarta don ganin meke faruwa a duniya .
Sallama taji ana yo wa amma an kasa shigowa jin muryar mace ce ya sa ta fadin .


"Shi go ."

Hajjiya Sa'adatu ce ta fara shigowa sannan Mahmud da Umar suka biyo bayanta .


Murmushi na farin ciki Fatima ta saki , tai saurin tashi tana taro su .


"Oyoyo mommy sannu ku da zuwa ."

Su ma su mommy murmushi sukai mata , ta musu iso suka zauna

Bayan sun gaisa

Fatima take cewa .

"Mommy bari na kawo muku abinci domin yanzu na gama shi ."

Bata jira sun ce komai ba ta nufi dakin kirki .



Mahmud ne ya kalli mahaifiyar su hajjiya Sa'adatu yana cewa.


"Masha Allah mommy, suna zaune lafiya ."


Murmushi hajjiya ta yi sannan ta ce .


"Ai dama haka ake so ."


A lokacin fatima da murmushi ta kawo abinci, ta koma ta kawo lemo da ruwa .


"Tom mommy ga abinci, nasan wata kila kafin ku gama Zarah zata iya dawowa ."




Hajjiya Sa'adatu ta kalli Fatima sannan ta ce.
"Au bata nan ."


Fatima ta ce .


"Eh taje wani taro , amma bari ma na kirata ."


Ta dauki wayarta tana kokarin kiran lambar Zarah

Kafin ta kira ne hajjiya Sa'adatu ta ce .


"Ba sai kin kirata ba Fatima, ai dama lafiyarku muka zo gani , idan ta dawo kafin mu tafi sai mu
gaisa ai ."



Fatima ta yi murmushi tana cewa.

"Wallahi mommy da an kirata ."


"Ba sai kin kirata ba wallahi Fatima." Cewar Hajjiya


Fatima badan taso ba , ta fasa kiran Zarah.


Bayan su Hajjiya sun gama cin abinci ne , suka fara shirin sallah da zummar idan Zarah bata
dawo ba , zasu koma


A wannan lokacin ne ta ji ana kwankwaso kofar falon

Ta tashi ta nufi kofar tare da bud'e ta


Wani ihu ta kwalla ta rungume wanda ya fara shigowa wato mai sanye da kayan turawa wato
Ahmad

Sannan cikin farin ciki ta sake rungume dayan wanda shi ne Najib



"Haba matsala dake ke nan 'yar Nigerian nan idan kin yi kewar mutane baki iya hakuri ba ."
Ahmad ya fada cikin farin ciki yana sake shigowa cikin gidan , lokaci guda kuma yana hango su
Hajjiya Sa'adatu a zaune

"Wayyo Allah gaskiya kun yi mini zuwan ba zata Yaya ."

Ta yi magna cikin shagwaba da matukar shaukin kaunar su .



Suka nufo inda su Hajjiya suke zaune domin samun masauki



Hajjiya ta kalli Umar tana cewa.
"Su waye kuma su ."


Umar ya ce .
"Wallahi ban sani ba mommy."





Bayan sun zauna lokacin da Hajjiya ta kare musu kallo tabbas tana iya ganin kamanninsu da
Fatima.


Hakan ya sa ta saki fuska da jiki suka gaisa cikin girmamawa




Bayan sun gaisa ne Fatima cikin wannan fatin cikin ta kalli hajjiya tana cewa.


"Mommy wannan 'yan uwana ne daga saudiya ."


Ta nuna Ahmad tana cewa.
"Wannan shi ne Ahmad, ga kuma Najib ." Shi ma ta nuna
Shi



Lokacin hankalin Hajjiya ya sake kwanciya, suka sake sabuwar gaisawa tare da tambayar

mahaifiyar su .




Fatima ta kalli su Ahmad tana cewa.
"Wannan mahaifiyar Zarah ce , ga kuma 'yan uwanta ."



Wani farin ciki ya sake rufe su , suka fara hira

Umar ne ya ce .
"Kun sha hanya sannuku ."

Najib ne ya mayar masa da cewa .


"Ai dake ma muna can gidan mahaifin mu , kuma yanzu zamu koma domin nan da minti kad'an
jirginmu zai tashi ."



Fatima ta murtuke ranta matuka tana cewa.
"Wanne irin yanzu kuma yaya gaskiya ni wai mene haka ."?

Bacin rai ya bayyana a fuskarta .


Najib ya ce.


" yanzu kuwa , zamu koma ."


Hajjiya ce ta ce ."Fatima baki kawo musu komai ba , kina ta murna ."


Fatima ta dafa kanta alamun sha'afa tana cewa.


"Wallahi mommy na manta ."

Najib ya ce .
"Kar ki kawo mana komai domin daga gidan Alaji mu ke , kuma ba za mu bari mu rasa jirgi ba ."




Fatima ta sake hada ranta jin cewa da gaske tafiyar za si .



Ahmad ya kalleta kana ya ce.
"Wai ina Kamal din ne da Zarah."?

Tana cuno musu baki ta ce .
" Sun fita amma zaku jira su dawo ai . Me ya sa Aunty Murja bata zo ba ."?



Najib ya yi murmushi kafin ya ce .
"Zata zo ne , mommy na nan zuwa a sabon wata mai kamawa in sha Allah."





Wani dadin gaske Fatima taji tana sake bazo idanunta tana cewa.

"Allah ya kawota wallahi na yi kewar mommy na ."


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login