Showing 24001 words to 27000 words out of 37591 words
Chapter 9 - FATIMA DA ZARAH NA AUTAR MARUBUTA.pdf
bari naje yanzu zan dawo in sha Allah."
Ta ce ."To Fatima Allah ya tsare ."
Fatima ta fita .
Nasir yana shirin tafiya makaranta ne wayar shi ta fara ringin yana dubawa ya yi murmushi ya
daga tare da karawa a kunne .
"Hello dan Alaji ka fito ke nan , nima ina hanya ."
Daga can bangaren Nasir yaji abokin nashi yana cewa.
"Kai gaye sha zamanka wallahi professor ba zai zo ba nima ka ganni ina gida ."
Nasir ya kwashe da dariya yana cewa.
"Alhamdulillah naji dadi wallahi ka ce kawai mu huta ."
Daga can ya ba shi amsa da cewa .
"Eh wallahi sai mun hadu kawai ."
Nasir ya kashe wayar yana murmushi yana cewa.
"Ahhhhh yau ba lecture ai kawai bacci zan ."
Ya hau gado tare da wayarshi .
Anan falo kuwa Hajjiya Binta tana ta yiwa Hajjiya Samira hira ba tare da tasan ma bata da lafiya
ba .
Lokacin Zarah ta shigo tana cewa.
"Mommy bari na shiga ciki na shirya kafin fatima ta dawo ko kina bukatar wani abin ne ."?
Hajjiya Samira ta kalli Zarah tana cewa.
" Bana bukatar komai 'yata Allah yayi miki albarka. "
Zarah ta yi murmushi ta nufi sashinta
Shigowar kira na biyar ke nan wayar Nasir, Abba Alaji ya dame shi da kira
Nasir ya girgiza kai yana cewa.
"Zan koya maka hankali Abba."
Kira na 6 yana shigowa Nasir ya daga ya kara a kunne .
"Hello Nasir wallahi yanzu zan shigo gidanku yunwa nake ji Allah."
Wani 'bacin rai ne ya daki zuciyar Nasir yayi ajiyar zuciya yana cewa.
"Abba kai wanne irin bakin maye ne mara ilmi mara zuciya, jahili kawai , to wallahi na rantse
maka idan ka taka kafa kazo , zan maka rashin mutuncin da tunda ubanka ya haife ka ba a taba
maka ba ."
Yana gama maganar ya kashe wayar ya kwanta cikin bacin rai
Suna cikin hira Nasir ya turo kofa
Ciki da mamaki hajjiya Binta ta kalleshi tana cewa.
"Kai kuma lafiya Abba wajen wa ka zo a wannan gidan."
Abba Alaji ya sosa keya yana cewa.
"Wajen Nasir mana ai a bokina ne ."
Hajjiya Samira da hankalinta bai kwanta dashi ba ta kalleshi tana cewa.
"To ai Nasir yana makaranta."
Abba Alaji ya dubi lungun-lungun gidan sannan ya lura da inda dakin Nasir yake sakamakon
lokacin da ya shigo dashi da dare
"Bari in shiga na duba ." Ya sha ta gabansu
Ya nufi dakin Nasir
Hajjiya Binta ta yi murmushi tana cewa.
"To idan ya shiga yaga baya nan ya fito ai ."
Hajjiya Samira ta hade rai tana cewa.
"Wane kuma wannan."
"Yanzu baki gane shi ba , yaron Alaji Sani ne fa yayana ."
Hajjiya Samira ta yi ajiyar zuciya
Cikin wayantar da zancen Hajjiya Binta ta ce .
"To Hajjiya d'an ko mini turare na kinsan kamshi ba a wasa dashi ."
Hajjiya Samira ta yi murmushi na yake tana cewa.
"Tom bari na shiga ."
Ta nufi dakin Fatima inda kayanta suke
Doctor zarah ta shirya , rigarta ta likitoci kawai zata sa ta fito .
"Uwarka ta yi asarar haihuwa Abba, ta haifo maye kuma annoba mara jin magani , wallahi ina
tabbatar maka da iyayenka sun san kai zasu haifa dasun kasheka tun kana ciki .
Na ce ka rabu dani ka bar rayuwata haka , amma kaki shege matsiyaci kawai."
Nasir yayi maganar cikin matukar hassala
Maganar ta batawa Abba Alaji zuciya hakan yasa ya kalleshi yana cewa.
"Ni kake fadawa wannan Nasir."?
Nasir cikin wata sabuwar fusata ya ce .
" Eh din ai takaita ma na yi domin kafi haka , idan kuma ka yi zuciya ka barni har abada. "
Cikin bacin rai da bakin ciki da takaici Abba ya juya ya fita cikin mahaukacin yanayi .
..............
Zarah ce da Hajjiya Binta kan Hajjiya Samira dake kwance a kasa
Cikin tashin hankali zarah ta fara kiran .
"Mommy tashi mommy mene ya same ki."
Yadda suka ga yanayin nata yasa su matukar tashin hankali
Hajjiya Binta ta kwallah kara tana kallon Zarah da cewa .
"Shi ke nan kin kasheta , kin kasheta hankalin ki ya kwanta ."
Ta rushe da kuka
Zarah ta kalli kwalbar turaren da Hajjiya Samira ta dauko daga gefe tana sake fashewa da kuka
.
Lokacin Kamal ya shigo tare da Hajjiya Amina wato mahaifiyarshi
Zarah wani
Tashin hankali taji ya ziyartar mata zuciya dajin abin da Hajjiya Binta take fada
Da gudu su Kamal suka yo kanta yana tambayar .
"Mene ya sameta mommy mene yake faruwa Zarah."
"Ta kasheta ta kasheta ."
Hajjiya Binta ta cigaba da fada tana kuka
Lokacin Fatima ta turo kofa daidai da sanda take maganar
Zarah mutuwar tsaye ta yi ta kasa cewa komai kawai hawaye ne suke zubo mata .
Da gudu Fatima ta karaso tana jefar da takardun hannunta
"Innalillahi mene ya faru da mommy mene yake faruwa."
Ta zube a kasa gaban mahaifiyar tata tana kiran sunanta tana jijjigata
Zarah ta sake fashewa da kuka
Fatima cikin kuka ta kalli Zarah tana cewa .
"Mene ya sameta dan Allah Zarah."
Kafin Zarah ta bude baki ta yi magna Hajjiya Binta ta sake fadin .
"Ta kasheta hankalin ta ya kwanta innalillahi wa inna'ilaihir raji'un ."
Fatima ta kalli Zarah cikin wani mummunan yanayi da matukar mamaki , Zarah ta kalli Kamal ta
sake fashewa da kuka
Sannan ta ce .
"Dan Allah kamal mu kaita asubiti bai kamata mu zauna ba ."
Ta fadi kasa tana cigaba da kuka
Hakan kuwa akai duk suka rankaya asubitin cikin mummunan tashin hankali.
Nasir kuwa yana daga daki yake jin komai, saidai tashin hankali ya hanashi fitowa , saida suka
tafi asubitin ya hau mota yabi bayansu .
Koda suka isa cikin asubiti Zarah bata shiga inda aka aje Hajjiya Samira ba
Dactor Ahmad ne cikin kwarewa ya shiga aikin shi
Suna cikin tsananin jiran fitowarshi ne , dactor ya fito
"Allan da ya baku shi ne ya amsa ina baku hakuri dactor Zarah."
Ya karasa maganar sanda Nasir ya shigo , tare kuma da kallon zarah.
Autar Marubuta
07040805269
WhatsApp only.
wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_ν Ύν΄²ν ΌνΏΌ
<><><ν ΌνΌΉ><><><>ν ΌνΌΉ<><><>ν ΌνΌΉ<><><><>ν ΌνΌΉ<><><><><>ν ΌνΌΉ<><
Editingβ
Page 32 & 33
Zarah kawai bangon dake gefenta ta fara bi tana zamewa cikin mugun yanayi ,
Nasir da ya kasa gane lissafin kamar kanshi ya buga yake ji
Hajjiya Binta kuwa sai kuka
Ita kuwa Hajjiya Amina innalillahi wa innailaihir rajiun take ta ambata .
Kamal shiru ya yi yana jinjina lamarin ubangiji
Fatima kuwa babu hawaye a idanunta amma tamkar zuciyarta ta fito take ji
Karfin hali ta yi ta kalli Kamal tana cewa.
"A yanzu komai ya kare Kamal a sanarwa da kowa mu koma gida ."
Zarah wani kuka ta ruruce dashi tare da zaucewa cikin wata murya da baza a gane me take
cewa ba ta kalli Fatima tana kauda kai tana fadin .
"Bani da idanun kallon ki Fatima. Fatima da idanun kallon ki Fatima."
Fatima ta fashe da kuka
Yanzu Alaji Mustapha da Alaji Mansur suke samin labari
Kafin ka ce komai kuwa zance ya isa saudiya.
Kowa aka kai masa labarin to zancen Zarah yana shigowa ciki
Dactor Ahmad ya tabbatar musu ba ciwon zuciyarta bane ya tashi har yayi sanadin mutuwarta ,
domin tun binciken farko da suka yi matakin ciwon shi ne dai harta rasu , kuma bai motsa koina
ba , bare ya yi sanadinta
Nan Hajjiya Binta take tabbatar musu Zarah ce ta bangajeta ta fadi bata motsa ba rai ya yi
halinsa
Alaji sale hankalinsu ya matukar tashi da samun wannan mummunan labari .
Karfe biyu Faruk da Murja,Ahmad da Najib suka iso Nigeria cikin matukar bakin ciki
Lokacin da suka zo , suka shigo cikin gidan .
Gida kuka wiwi na mutane ,har da su Barrister Khadija.
Haka waje karku ji yadda Alaji Mustapha yake kuka abin tausayi.
Zarah tana zaune idanunta sun yi jajir , tare da mahaifiyar ta
Faruk yana shigowa Fatima ta fada jikinshi tana kuka
Lokacin da Ahmad ya shigo ta koma jikinshi tana sake rurucewa da kuka .
"Daga kanta ta yi sama tana kallon yadda wata 'yar sanda ta shigo rike da ankwa
" Ina Zarah Sale ."
Cewar police din
Tashin hankali Fatima taji ya sake ziyartarta
Ta kalli Zarah tana ajiyar zuciya mai zafi
Zarah cikin kuka ta bar jikin mahaifiyar ta Hajjiya Sa'adatu tana tashi tsaye da cewa .
"Ni ce ." Tana kuka
'Yarsandar ta karaso gaban ta tare da ware ankwar tana shirin sa mata tana cewa .
"Muna zarginki da kisan kai , don haka zamu tafi dake domin bincike ."
Zarah kawai mika hannu ta yi , tana kallon mahaifiyar ta cikin mummunan yanayi
Hajjiya Sa'adatu ta fashe da kuka tana kiran sunan Allah
Fatima ta kasa cewa komai kawai kallon Zarah take Zarah ma tana kallon ta yayin da suka je
gaff da fita
Zarah ta yiwa Fatima murmushi mai matukar ciwo.
Fatima wani abu taji ya daki zuciyarta na bacin rai
Kawai ta sake fashewa da kuka
A lokacin aka fito da gawar Hajjiya Samira.
Gurin ya sake rurucewa da kuka .
Ahmad da Najib ma kukan ne ya ke ce musu suka yi waje , suna fita waje nan ma wani tashin
hankali ne , domin Alaji Mustapha suma ya yi
Faruk sam bai yi kuka ba , saida lokacin da ake sallatar gawarta lokacin ya ringa zuba nashi
kukan kamar mai shirin ham'budewa
Allah sarki Alaji Mustapha .
Kowa haka ne kawai lokaci muke jira , domin mutuwa guda daya ce , sanadi kawai ta tara, Allah
ka sa idan karshenmu ya zo mu cika da hasken imani .
Haka aka kai gawarta zuwa ....
Har dare ya yi wannan gida na Kamal kuka bai ragu ba .
Zarah kam tana nan a kulle cikin mummunan yanayi, domin su ma su Alaji sale da su Umar duk
hankulansu a tashe suke .
Bayan kwana biyu
Duk suna dai zaune a falon Fatima suna ta juyayi
Ahmad ya ce .
"Ba a tara sani ga Allah, mommy ashe ajalinki yana Nigeria da bamu barki kin zo ba ."
Cikin matukar tausayi da karayar zuciya ya karasa magana
Faruk ya yi ajiyar zuciya ya kalli Ahmad yana cewa .
"Gobe zaku shirya mu koma Saudiya, domin zaman mu ba shi da amfani , idan aka yi addu'ar 3
gobe tafiya kawai zami , ita kuma data kashe mana mahaifiya doka zatai aiki a kanta ."
Murjanatu ta ce .
"To Allah ya kaimu , ai baza ta ci banza ba, sai an kasheta , Allah ya jikanki yayata ."
Hawaye suka zubo mata
Kamal duk wani yanayi mara dadi yaji ya mamaye shi
Fatima ta kalleshi tana cewa .
"Kamal a kan wanne dalili ne zarah zata kashe mommy."
Kamal da hawaye a idanunshi ya tashi ya nufi daki
Ajiyar zuciya Fatima ta yi sannan ta tashi ta bishi
Washe Gari
Bayan an gabatar da addu'a, su Faruk suka fara shirin tafiya, domin har sun yi wa mahaifin su
sallama, nan yaci kuka ya ce su kula da kansu
Allah kuma ya basu hakurin rashi.
Umar da Faruk da Hajjiya Sa'adatu suna zaune a falo
Alaji sale ya fito cikin hanzari daga daki zuwa inda suke .
Duk tashi tsaye sukai ganin haka , kafin wani ya ce komai ya fara magana cikin masifa da
takama
"Wannan wulakancin ya ishe ni, an ce musu bana son Zarah ne , haukan banza dan anga na yi
shiru , kuma na yi shiru ne domin naga gudun ruwansu , ni na san Zarah baza tai kisa ba , dan
haka yanzu gidan kamal din zani a yita ta kare ."
Ya fita harabar motoci , Mahmud da Umar suka bi shi .
Bayan su Faruk duk sun shirya , sun d'ebo kayansu daga gidan Alaji
Komai ya yi musu daidai domin kawai sallama zasi su tafi
Ana wannan lokacin ne suka ji ana kwankwaso kofa
Nan suka bada izinin shigowa
Kamal yana ganin wanda suka shigo ya tashi ya nufi wajensu .
Alaji Sale ya dakatar dashi da hannunshi da kuma karin magana yana cewa .
"Ba gurin ka na zo ba ."
Kamal yaja da baya ya tsaya cikin matukar mamaki
Alaji Sale ya kalli Faruk yana cewa.
"Wajen ka na zo wato ma tafiya zaku yi tunda kun fa an rufe 'yar iska mara gata koh."
Faruk yaja baya ya jingine akwatin shi yana cewa da Fatima.
"Waye wannan."?
Fatima cikin hawaye ta ce .
" mahaifin Zarah ne ."
"Ohoooo ! Wato kaine wanda yarka ta kashe mana uwa ke nan ." Faruk ya fada
Alaji Sale ya doka masa tsawa da cewa .
"Shiru ! Karka kuma kiran 'yata da ta yi kisa, daman na yi shiru in ga iyakarku , to yanzu komai
ya kare ko ni ko koh."
Fatima ta fashe da kukan bacin rai da takaici.
Haka shima Kamal ya rasa inda zaisa kanshi
Faruk yayi murmushi yana cewa.
"Komai ya kare kuwa , dole a kashe Zarah yadda ta kashe mana uwa , domin rai bai fi raiba ."
Alaji Sale ya ce .
"Ni nasan a haife na haife ka , dan haka kawai mu hadu a kotu , zan ga dokar data isa ta kashe
mini yarinya."
Najib dai basu ce komai ba .
"Kana ganin zaka kayo lauyan da zai wanke 'yarka , to ai shi ke nan mu hadu a kotun ."
Ya kalli Fatima yana cigaba da cewa .
"Fatima zata tsaya mana a kan wannan shari'ar ka je ka shigar da kara duk inda kake so muna
jiran sammaci ."
Fatima ta sake fashewa da wani kuka mai matukar gwanin ban tausayi tana cewa .
"A'a, A'a Yaya faruk bana jin Zarah ta kashe mini mommy, zuciyata ta kasa amsar wannan
yanayi, bansan mene ya kashe mommy ba ."
Cikin sabon kuka ta cigaba da cewa .
"Ni na zauna da Zarah nasanta nasan abin da zata iya .
Don haka ku yi hakuri, ni bazan tsaya muku a kotu ba , zan tsaya kare Zarah ne Yaya, zan kare
Zarah a kotu shi ne abin da nake nufi ."
Dauuu kowa yaji zuciyarshi ta yi bugun mamaki da rashin gane inda maganar Fatima ta dosa.
Fatima ta cigaba da kuka
A wannan lokacin Ahmad ya dubi Fatima yana cewa.
"Ban gane mene kike nufi ba Fatima zaki kare wa ne ."?
Fatima cikin wannan kukan ta sake fadin .
" Idan har sai an shiga kotu , to ina nufin ku je ku nemi lauyan da zai tsaya muku, amma ni
Zarah ..."
Kuka ya kuma cin karfinta
Babu I zuciyar Faruk da yake jin matukar mamaki na abin da Fatima take fada
Shi kuwa Alaji Sale dasu Umar duk jikinsu ya yi sanyi .
Murja cikin kishin Hajjiya Samira ta jefawa Fatima kallo tare da tunanin
"An ya kuwa Fatima jininsu ce ."
07040805269
Autar Marubuta
FATIMA DA ZARAHν ΌνΎ
Na
Autar Marubuta
________________________________________
*AUTAR MARUBUTA CE*βν ΌνΏ»ν ½ν±Όν ΌνΏ»
ν ΌνΌΉ__________ν ΌνΌΉ_________ν ΌνΌΉ__________ν ΌνΌΉ_________ν ΌνΌΉ
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_ν Ύν΄²ν ΌνΏΌ
<><><ν ΌνΌΉ><><><>ν ΌνΌΉ<><><>ν ΌνΌΉ<><><><>ν ΌνΌΉ<><><><><>ν ΌνΌΉ<><
Editing β
Page 34 & 35
Najib ma wani matukar mamaki ne ya rufe shi dajin zancen yayartashi ,
Murja cikin mamaki d takaici ta so fara magana amma bata samu damaba sakamakon Alaji Sale
da ya fara cewa .
"Na gode Fatima, amma karki damu. Ni zan nemo lauyan da zai tsaya mini a wannan shari'a
karki damu."
Fatima taji ajiyar zuciya tana fadin .
"Ka yi hakuri Daddy, amma bazan bari ka kira wani lauyan ba domin ..."
Fesssss fessss Fatima ta ji an dauke