Showing 30001 words to 33000 words out of 110071 words
hannun abokan hamayya sannan ita ko kadan Mawadda bata ambaci sunan wani mai kiyos ba. Kanta ya kulle ta rasa me zatayi. Tashi tayi ta nuna bata gamsu da furucin Barista Dalhatu ba domin yana neman karkata akalar shari'ar kan wani daban bayan kuma har yanzu ba'a wanke Babawo ba.
Alkali ya karbi korafinta sannan aka bukaci Haj Mara ta taso. Hankali kwance taje ta tsaya.
Ajiyar zuciya Barista Shafa'atu tayi tana kallonta. Shigar mutumci tayi harda hijab fuskarta fayau kalar tausayi.
"Haj Mara a ranar shahudu ga watan Yuni kin koma gida kin tarar da danki ya yiwa mai aikinku fyade bayan mugun duka da yayi mata. Ke kika taimakata ma tayi wanka sannan tsoron tonon asiri duk da raunukan dake jikinta kika ki kaita asibiti. Dadin dadawa kika dauketa kika mayar gida batare da yiwa iyayenta bayani ba"
"As....as...sal...salam...as..."sai kawai kuka ya kufce mata mai sauti da tsuma zuciya. Ta kwashi wurin minti biyu tana kuka tana goge hawaye.
"Ku gafarceni, assalam alaikum. Ni dai sunana Marakisiyya kuma nice mahaifiyar Babawo. Nayi mamaki matuka ranar da sammacin kotun nan ya iso garemu har gani na rinka yi ko anyi kuskure ne."
Ta kalli Mawadda idanunta jazur "Mawadda me nayi miki a duniya zakiyi min wannan sakayyar? Tabbas nasan ni mutum ce mai zafi bazan boye ba. Amma hakan bai hanani rungumar duk wata maiaiki ba saboda nasan da na kowa ne. Me muka yi miki Mawadda har kika rasa wanda zaki kai kotu sai ni? Ni bazan tonawa kaina asirin zaman da mukayi ba balle na kwashe ladana da baki. Idan kotu ta kamamu da laifi ayi mana duk hukuncin da ya dace." Ta kare a raunane.
Mutane sai tausayinta suke ji. Mace kamar wannan wadda ko ba'a fada ba zaka san cewa arziki ya zauna mata take yiwa yarinya karama kuka.
Da kyar aka iya rarrashinta ta bada nata jawabin kamar haka.
"Banyi niyar tozartaki ba Mawadda amma kin nuna min da gaske ne da ake cewa kayiwa mutum inuwa shi kuma ya kaika rana. Ya maigirma mai shari'a yarinyar nan satar da take min bazata kirgu ba ina kawar da kai. Da zata tafi iyayenta shaida ne ba karamin tanadi nayi mata ba. Yaron da ake magana a kai wato Na'ibi, kiyos gareshi kusa damu. Daga aike a hankali na fuskanci ko ban nema ba sai tayi kwalliya tace min akwai aike? Idan nace babu sai tace zata dan fita. Ban kawo komai a rai ba nake kyaleta. Sai kawai wata rana aka kawo min zancen an ganta a dakinsa. Nayi kuka nagode Allah. Sakacina shine rashin mayar da hankali da na fuskanci ta fiye yawo amma banyi mata zaton yawon banza ba. Wannan abin shine ya daga min hankali nace gara ta koma gida kada a haifi da mara ido. Tayi kukan tayi magiya duk a banza don bazan boye muku ba ranar har dukanta nayi. Na hukuntata kamar yadda zanyiwa 'yar cikina. Ina fita ne ta shigar min daki sata Babawo ya kamata shima zuciya ta kwashe shi ya mareta. Washegari na maidata gida bamu sake jin komai ba sai kararmu da aka kawo"
Mawadda kuka iyayenta kuka. Hatta Baba hawaye yake yi sosai.
Alkali Dawud yace idan suna da shaidar da zasu kawo ana bukata. Waige waige suka soma yi ba Dr Tani ba dalilinta. Wani mai kaya irin na masinja ne ya fadi uzurinta cewa ta taho aka kirata patient din da ta yiwa aiki tana zubar da jini. Wannan dalilin ya sanya aka dage sauraron karar sai bayan kwana goma sha biyu.
A sanyaye suka tashi kafin su fita Barista Shafa'atu ta hau Mawadda da fadan me yasa bata yi mata zancen Na'ibi ba. Su Iya suka tsaya sauraronta tana fada mata cewa da gaske ne ya nuna yana sonta amma da wuri ta sanar dashi aure zata yi. Kuma duk wata kyauta da yake bawa Ramadan maigadi ko tsinke bata taba karba ba. Game da zuwa kiyos dinsa tun da ta gane yana sonta ta gwammace ta tsallaka titi idan an aiketa. Dama yawanci siyan katin waya ne yake kaita. Kafin faruwar wannan abu gareta kuwa yafi wata bata ganinsa. Kiyos din ma ya koma shagon renting din finafinan hausa shi kuma bata san inda yayi ba.
"Wato sun nemo wanda baya nan bare ya kare kansa shine za'a dora masa laifin da baiji ba bai gani ba" Barista Shafa'atu ta fada tana rubutu.
Mawadda ta kalleta "wallahi babu karya a duk abinda na fada miki"
Murmushi tayi "na sani Mawadda kuma in sha Allah sai an kulle BB an bi miki hakkinki"
"Idan ba mu muka ci shari'ar ba ni za'a kulle kenan?" Yadda tayi maganar da raunin murya yasa Baba fita hankalinsa duk a tashe yake ya rasa me zaiyi ya samarwa 'yarsa farincikin rayuwa.
Fitarsa waje ke da wuya yaji wasu suna tattaunawa suna aibata 'yan kauye a matsayin kwadayayyu wadanda basa iya rike talaucinsu.
"Tsabagen son zuciya ke dibarsu su kwaso rida-ridan 'yan mata a kawosu birni aiki."
Wani yace "sai ta kwabe musu ayi ta dauki ba dadi"
"Idan basuyi haka ba ai basu amsa sunansu na 'yan kauye ba. Da anyi magana sai ace an turo yarinya tara kudin da za'a yi mata kayan daki."
Zuciya ta kwaso Mal Fatihu, ransa ya kai makurar baci ya karasa gaban wadannan mazan cikin daga murya wanda ya janyowa kansa taruwar 'yan jarida yace
"Shi dan kauye ko talaka ba mutum bane? Meyasa idan dan birni ya nemi kudi ake jinjina masa idan dan kauye ya nema yake zama kwadayayye? Masu kudin da mutanen birnin me suke yi mana domin inganta rayuwa? Ko nan da Jigawa ban taba zuwa ba amma ina da tabbacin ko ina a fadin duniyar nan akwai masu kudi kuma akwai masu yi musu aiki talakawa kauyawa irinmu. Haka Allah Yaso kuma haka Ya tsara duniyar arzikin wani yana karkashin wani. Idan munyi bara kuce zukatanmu sun mutu idan mun nemi halak da guminmu ace mun kasa rike talauci. Wannan wane irin son kai ne da rashin adalci? Mune 'yan dako mune leburori mune masu kaskantacciyar sana'a amma duk ba'a gani. Talauci yasa yaro sa'an jikanka zai tsaya ka bude masa kofa ya shiga mota yana binka da harara. Mu maza mun nema a waje matanmu kuma su nema a cikin gidajen aure. Kuna da mata maaikata, suna bukatar masu tayasu raino, gyaran gida ko girki. Idan ba kaddara ta rabo mace da gidan mijinta ba ai dai bakwayi tsammanin matan aurenmu ne zasu baro nasu kananan yaran a kauye su fito aikatau ba. Dole yaran namu da suka kawo karfi zamu turo. Babu mai zurfafa tunani yaga cewa banda abinci muma fa muna rashin lafiya kamar 'yan birni waye zai bamu kudin asibiti, lalura da dama ta kudi tana taso mana. Kai da kake cewa muna turasu neman kudin kayan daki waye yace maka don muna kauye shikenan idan mun tashi sai mu aurar da 'ya mu kaita da tabarma? Haka al'adar bahaushe take waye yaki ya sami wani abu da zai taimaka masa yaji dadin rayuwarsa? Komai namu sai ya zama laifi saboda bamu da galihu. Mu yini muna muku aikin karfi ku sallamemu da dubu uku karshen wata har kuna ganin ba karamin karamci kuka yi mana ba. Yaranmu suna kauye da kokarinsu talauci yasa basa iya wuce sakandire idan sunyi sa'ar zana jarabawa. Ni Fatihu bazan boye ba kuma bazan fasa fada ba mu daku muna bukatar juna ne domin taimakekeniya ta rayuwa. A cikinmu da cikin kowacce sana'a akwai nagari akwai bata gari. 'Yata Mawadda da duk sauran masu zuwa aikatau ba kiyayya ko rashin sanin ciwon kai yasa muke turo muku su ba. Yanayi ne na kuncin rayuwa....Wallahil Azim bazan taba yafewa wannan yaro ba, babu wata riba da zamu tsinta don mun batawa dan wasu suna"
Kafin ya karashe maganar kuka ma yake yi sosai hawaye har gaban malun-malun dinsa ya jike. Masu daukar rahoto da 'yan kallo da dama sun zubar da kwalla. Haka zalika iyalansa da suke tsaye a bakin kofar kotun.
*****
Dahiru zaune gaban yayansa Bilya yana ta juya cokali cikin abinci.
"Kayi hakuri kada ka batawa su Baffa rai akan mace Dahiru komai mai wucewa ne"
"Na sani Yayanmu amma bazan taba iya cire Mawadda daga zuciyata ba. Yau aka fara shiga kotun ya dace ace ina tare dasu amma kaga banma san wace kotu bace"
Bilya yana tausayin kaninsa sosai amma Inna tayi masa gargadi mai karfi akan ya tsawatar masa da batun auren don bazata taba yarda ba duk runtsi.
Kasa cin abincin Dahiru yayi ya tashi ya fita wurin wani mai shayi a layin da suka saba zama. Ana ta hira ya zurfafa a tunani yaji muryar Baba a lokacin da yake maidawa wasu martani. Mai kawo rahoton yace hakika wannan mutumi ya nusar da mutane da dama abinda suka manta game da na kasa dasu a kowane matakin rayuwa. Komai talauci, rashin ilimi da wayewa mutum, mutum ne abin darajawa saboda haka zasu cigaba da bibiyar wannan shari'a da akeyi a kotu mai lamba biyar Court road domin jin yadda zata kaya.
Har kuka Dahiru yayi yana jin wannan labarai. Tashi yayi ya bar wurin da surutun jama'a ya ishe shi akan kukan me yake yi.
Washegari da sassafe yaje gidan aikinsa yayi shara da gyaran filawa ko sallama baiyi da kowa ba ya kama hanyar tasha. Yayi babbar sa'a su Mal Fatihu tun jiya suka koma Tariwa. Kai tsaye gidansa ya wuce sai ya tuna bata gidan ya kama hanyar gidan kakaninta.
Lokacin shadaya na safe yana tsaye yana jiran yaron da ya tura sai ga Baffa shima yazo. Da mamaki Baffa yace "Dahiru saukar yaushe?"
Gaishe shi yayi yaga bai amsa ba yace "isowata kenan"
"Shine ka fara zuwa nan? Ashe duk maganar da muke yi maka bayan kunnenka take bi. To billahillazi kaji na rantse ban lamunce maka auren yarinyar nan ba ka nemi wata. Garin nan kwana akayi ana zancen shigarsu kotu jiya shine nazo jajanta masa naje gidansa ance yana nan ashe rabon na ganka ne."
Kamar yayi kuka ya dan duka "Baffa don Allah kayi hakuri yanzu ne take bukata ta bai kamata na juya...."
"Dahiru kada ka bari na sauke maka bacin raina. Ka wuce muje jajen ma na fasa tunda shima ya kasa gane zuru da kawaici idan kazo maimakon yace ka dena zuwa aure tsakaninku bazai yiwu ba"
Duk yadda Dahiru ke rokon Baffansa haka ya saka shi a gaba suka tafi.
Mal Fatihu da ya dade a tsaye saboda yaron na cewa Dahiru ne ya kalli Mawadda da tayi shiru tana jiran taji ko za'a bata umarnin fita yace tayi hakuri a karo na karshe ta cire Dahiru daga ranta. Shima zai fita ya bashi baki ya bi maganar iyayensa. Kafin ya fito ne kunnuwansu suka jiye masa maganganun Mal Isiyaku. Wani irin zafi yaji a saitin zuciyarsa kamar ana daddaureta ya dafe kirjin ya koma ciki yana dafa bango.
[08/01 8:32 pm] Biebie: *GUMIN HALAK..*💰10
*Batul Mamman*💖
Su Inna da sauri suka karasa inda Baba yake kwance ko motsi baya yi tamkar babu rai a jikinsa.
Mutane suka yi dafifi a wurin ko iskar kirki babu. Mawadda tana durkushe tana kuka ta soma kokarin daga kansa wani dan sanda yace ta kyale shi kada wanda ya motsa shi. Waya ya shiga yi suka ji yana kwatanta inda suke da abinda ya faru.
Su Iya duk sun zagaye shi suna kuka Mawadda ta hango Haj Mara tana washe baki wasu mutane suna yi mata barka da arziki tana fada musu ai kudin tarar da alkali ya nema daga garesu ma sun yafe tunda gaskiya ta fito.
Yadda zuciyarta ke suya a lokacin duk wani tsoro ya fice mata. Tashi tayi da saurinta kada ta shige mota su tafi ta kutsa kai ta cikin mutanen ido a rufe ta samu ta damko hannunta.
"Ke meye haka?" Ta fada tana son kwacewa sai dai kusan janta Mawadda take yi tana son turjewa ta nuna hali amma tana tsoron kada ta bada kanta a gaban mutane.
Ba ita ta saketa ba sai da suka je inda Baba yake kwance Yaya tana masa firfita da mayafinta. Idanu jazur ta dubi Haj Mara cikin karaji tace
"Kinga hawayen da yake zuba daga idanun iyayena???"
Haj Mara ta tsorata da yadda Mawadda take dadinta daya suna fita ta danna BB a motar Dr Tani tace zata biyo bayansu idan ta gana da iyayen Mawadda. Ba komai yasa tayi hakan ba sai tsoron kada ya tona musu asiri a bainar jama'a.
Bangazar kirjinta Mawadda tayi ta sake maimaita tambayar. Mutane suka soma darewa ana mata kallon mara hankali. 'Yan sandan da suke wurin suka fara matsowa ta dago idanu wanda kallo daya zaka yi mata idan ba ka jajirce ba kaji firgici ya ziyarceka.
Sassauta murya tayi tace "Na gani Mawadda, kinga ki kwantar da hankalinki komai zai wuce kinji ko"
Iyayenta ta rinka nuna mata daya bayan daya hawaye yana bin kumatunta.
"Wannan hawayen nasu nake so ya zauna a ranki har abada Hajiya. Idan Babana ya mutu ne to shima ki samu wuri a zuciyarki ki ajiye saboda gaba"
Daga haka ta koma ta zauna a gefen Baba. Haj Mara ta kasa barin wurin sai mutane ne suke matsawa daga gareta. 'Yar wannan magana ta Mawadda tayi mugun tasiri a zuciyarta har tana ganin kamar har ta mutu fuskokin mutanen bazasu taba gogewa daga kwakwalwarta ba. 'Yan bani na iya tuni suka fara hasashen ko dai akwai wata a kasa ne.
Ba jimawa sai ga karar ambulance aka ajiyeta kusa da Baba. Cikin nutsuwa da kulawa suka dora shi akan gado akace mutum daya cikinsu ta shiga sauran su biyosu Aminu Kano bangaren emergency.
A gurguje suka fita suka tari adaidaita sahu yayin da Yaya ta bi Baba a cikin motar.
Lokacin da suka isa tana wajen reception tana bada bayanai kamar sunansa da shekaru. Shi kuma tuni likitoci sun amshe shi ana bashi taimakon gaggawa.
Duk wani abu da zasu yi na ceton ransa sunyi. Kusan awa biyu sannan aka tura shi dakin marasa lafiya idanu a rufe. Su Inna zuciya ta tsinke ganinsa a haka. Sai dai wata likita tace su kwantar da hankulansu in Allah Ya yarda zai tashi. Jininsa ne ya hau sosai ga dukkan alamu yana tattare da damuwar da tayi masa yawa.
Mawadda na jin haka taji ta tsani kanta sosai tana ganin ita ce sila. Mahaifinsu talaka ne amma mutumin kwarai wanda rayuwar kauye bata hana shi zama uba mai barkwanci da iyalinsa ba.
A gefen gadon nasa duk suka taru sai daga baya suka fara tafiya yin sallah. Ya rage Yaya kawai a wurin Mawadda ta fita siyo musu ruwan sha ya bude ido a hankali.
Yaya tayi maza zata fita kiran likita kamar yadda suka bada umarni yace ta dawo ta gyara masa kwanciya yaji kamar ya karkace.
Tana ta ce masa sannu ta shiga kici-kicin daga shi ta kasa.
"Malam ai ka sakar min nauyi dan yunkara mana"
Gwadawa yayi yaji ya kasa sai ga Ade ta shigo. Yaya tace tazo ta tayata. Dan turus tayi tana kallonsa Yaya tayi murmushi
"ni dai zo ki kama min jikin nasa yayi nauyi."
Tsohuwar kunya ce ta taso tazo ta kama sai dai duka sun kasa.
"Yaya Fatihu kaima baka motsawa"
Yaya tace "nima haka nace masa kafin ki shigo"
"Ku sakeni ragwaye" yace sannan ya dan yunkura amma kansa ne kawai ya motsa. Sake yunkurin yayi yaji da gaske bazai iya ba. Zuciyarsa ta buga da karfi don ya tsorata ya daure yace "Haule jeki ki kira min likita na kasa motsa ko ina banda wuyana"
Bai karasa ba ta fita a guje yayin da Ade ta soma kuka tazo tana cewa ya daure ya tashi. Likitan ya zo sai ga Iya da Inna tare da Mawadda. Gefe suka matsa ya dan dudduba shi sannan ya juyo yana fuskantarsu.
"Tun dazu da aka kawo shi munyi zargin haka amma bamu da tabbas sai yanzu da ya tashi. Kayi hakuri Malam ka sami shanyewar barin jiki"
"Innalliahi wa inna ilaihi raji'un" suka shiga fada wasu na salati. Kan kace kwabo sai kuka domin wannan abu ya dokesu ba kadan ba.
Likitan ya rinka basu hakuri sannan yace idan har zasu rinka kawo shi gashi ko bayan sallama to hakika bangaren hagunsa zai sami lafiya ko bai dawo daidai ba zaiji sauki.
Fita yayi ya barsu da jimami da kuka. Innar Fatihu ta kira kaninsa guda namiji da yake aikin dreba. Baya gari duk abinda akeyi a lokacin sunyi tafiya da ubangidansa tana kuka ta fada masa. Hankalinsa ya tashi ya kira mijin kanwarsu daya da yake da waya yace aje gidansu a sanar da Malam.
Kamar an tsikari Ade ta soma juye juye tana cewa ina 'yarinyar nan ne da ta farga Mawadda bata wurin. Kowa kuma sai lokacin ya lura Baba ya daure yace ta fita ta nemota.
Waje tayi kaf wurin reception din bata nan. Kofar shigowar ta kalla sannan ta fita, dubawar farko ta hangota tayi hanyar gate.
Kwala mata kira tayi iyakar karfinta amma Mawadda bata tsaya ba. Ganin tsayuwa bazata kai mata ba ta bita da sauri. Shima hakan baiyi ba don tafiya kawai take kai tsaya dole Ade tasa gudu tana kiranta. Tana zuwa gate Mawadda tayi gaba ta hau titi bata kallon gabanta. Kusan ma bata san me take yi ba da ya wuce kukan zuci na jin lalurar da ta kama mahaifinta.
Motoci ne suka taho suna ta horn da taka burki ganinta a tsakar titi. Wata mota ta taho da gudu mutumin sai taka burki yake abu yaki yi. Ade hannuwa ta dora a kanta kawai ta rufe ido tana kuka don ta saddakar sai an bigeta kawai.
Wani mugun burki mai motar ya sake ja tayoyin suka yi wata kara ya karkata motar ya daki jakin babangida. A fusace ya fito jibgege mutum yasha babbar riga yana zuwa ya dauketa da mari har biyu a inda tayi mutuwar tsaye.
"Baki da hankali ne zaki zo tsakiyar titi ki nemi jaza min masifa?"
Mutanen da suke wurin kowa ya tsorata aka soma zaginta wasu na cewa mahaukaciya ce kila. Kasa cewa komai tayi sai kalle kalle take yi kamar wadda ta tashi daga bacci. Ade ta taho ta kama hannunta tana bawa mutumin hakuri.
Yadda ya gansu cikin tsumma yasan babu abinda zai tsinta a tare dasu idan ma yaki