Showing 21001 words to 24000 words out of 110071 words
gyada masa ya rufo kofar. Dama a tsaye take saboda yanayin jikinta. Gadon da yake cikin ofishin Dr. Tani ta nuna mata tace ta kwanta.
Yaya dai tana gefe Dr. Tani ta tsaya a gaban Mawadda tana dubata. Yanayin da taganta yasa jikinta yayi matukar sanyi ba kadan ba. Wane dabba ne yayi mata wannan mugun aikin haka. Da kyar ta iya hadiyar yawu saboda tashin hankali. Musamman da taga ko yaya ta tabata sai ta runtse ido ko hawaye ya fito.
"Har yanzu wurin da ciwo ko?"
Kai ta gyada kawai zuciyarta tana kuna. Tasha tambayoyi sosai sannan tace ta sauko. Yaya ta kalla tace ta kirawo Baban yarinyar.
Da sauri ya suri silifas dinsa ya bi bayanta suka sami wuri suka zauna ita kuma Mawadda tana tsaye.
"Bawan Allah garin yaya kuka yi sake 'yarku ta sami kanta a wannan yanayin?"
Gajeren bayani yayi mata tace "a gaskiya lalurar yarinyar nan ba kasafai take faruwa ba idan anyi fyade. Amma kuma ana samu a daidaikun lokuta. Yawanci tsabar tashin hankali ke zaburar da mace idan haka ta sameta motsi kadan sai ya firgita ta har ta kasa rike fitsarin. Yanzu zan rubuta mata gwaje-gwaje da nake so ku samu kuyi zuwa gobe in sha Allah. Sai na ga sakamako zan san wane irin mataki ya kamata na dauka"
Baba ya rinka mata godiya tamkar ance Mawadda ta warke ta gama. Ta dakatar dashi.
"Zan bata gado saboda ciwon nan yana bukatar kulawa kada ya zame mata wani abu a gaba. Dadin dadawa ina bukatar sanya mata ido domin na gano wasu abubuwa da zasu taimaka wurin magance wannan matsalar ta fitsari."
Su Baba to kawai suke cewa ta kirawo wata ma'aikaciyarsu ta wakilta taje a bawa Mawadda gado a bangaren mata. Sannan a tabbatar anyi gwajin da ta rubuta a yau.
Cikin dan lokaci kadan an basu gadon a dakin can gefen taga. Kafin likitan ta iso haka taje ta yayyafawa jikinta ruwa tayi sallah saboda wucewar lokaci ga rashin kayan canjawa. Ganin haka Yaya ta karbi kudi a wurin Baba ta koma gidan Barira. Ta dauko musu kaya da zannuwa da kuma abin rufa da tabarma. Barira ta hada musu abinci suka koma tare.
******
Shirye shiryen fara karatu ya kankama a wurin Dahiru. Ya kira su Baffa ya fada musu aikin da ya samu duk sunyi murna. A nan kuma yake jin tahowar su Mawadda Kano. Duk da su ma su Baffan basu san me kuma yasa suka chanja asibiti ba amma ansan ba lafiya ne.
"Kana nan akan bakanka na aurenta har yanzu?" Baffa ya tambayeshi.
"In sha Allahu. Yanzu haka ma ina jiran Yayanmu Bilya ya dawo zamu fara duba gidajen haya"
"Dahiru ina jiye maka ga karatu, ga aiki sannan ka hada da aure. Auren ma irin wannan ba na dadin rai ba. Kada garin neman suna komai ya baci fa"
Murmushi yayi kamar Baffan na kallonsa "Baffa addua kawai zaku tayani da ita saboda ni dai don Allah nake son aurenta ba komai ba."
Bai kara cewa komai ba ya kashe wayar. Yasan yanzu kowa zaiyi kokarin cusa masa ra'ayin rabuwa da Mawadda. Sai dai ya shirya toshe kunnuwansa indai iyayensa suka saka masa albarka. Bai taba son wani yadda yake sonta ba. A halin yanzu yana ji a ransa tausayinta har yafi son da yake mata yawa. Bazai taba iya barinta ba saboda yanzu ne ma take bukatar kulawa da dukkan wani gata da shi ko wasu masu sonta zasu nuna mata.
Da yamma suka fita neman gida don yafi son ya samu da wuri.
******
Ranar lahadi washegarin da aka kwantar da Mawadda su Ade suka taho. Kafin isowarsu an kaita wurin gwaji inda aka debi fitsarinta da jini. Tun daga nan Baba ya fara sarewa da lamarin asibiti saboda kudin da yaji zai biya na wannan kawai. A haka ma wai don asibitin na gwamnati ne.
Da suka dawo ta samu dan bacci har su Ade suka iso bata sani ba. Sunyi sa'a karshen sati dama da wuri ake barin 'yan dubiya su shiga.
Tana cikin bacci ruwan hannunta ya kare Nos namiji ne a kusa aka kira shi yazo zai cire mata. Bude idon da zata yi ta ga namiji a kanta ta kwala ihu iyakar karfinta ta tashi a firgice.
"BB ka rufa min asiri kada ka cutar dani. Wayyo Allah Babana ka taimakeni"
A rude take gabadaya tana ta sambatu. Baba yana waje da kaninsa sai su Ade da Iya don Yaya ma ta tafi gidan Barira karo zannuwan da Mawadda zata rinka chanjawa.
Da kyar suka iya kamata idanunta akan Nos din tana kuka.
"Ade kada ku bari ya tabani wallahi akwai ciwo"
"Babu me tabaki kinji ki kwantar da hankalinki" ta amsa mata
"To kice ya fita"
Iya ta kalle shi da alamun roko. Shi tausayi ma yarinyar ta bashi ya fita sai Nos mace ce tazo ta cire mata allurar don ta goce.
Wani baccin ne ya soma fizgarta ta kwanta a jikin Iya.
"Allah dai ya kwashewa wannan tsinannan yaro albarka. Dubi yadda yasa ta tarawa kanta 'yan kallo saboda yadda ta firgita. Allah Ya kaimu a sallameta ko zan sayar da gonata ta gado sai mun shiga kotu da yaron nan"
"Kayya dai Iya da kin bar maganar nan. Dame zamu tunkari shari'a da wadanda suka fimu. Sannan daga lokacin kowa zai san sirrinta duk inda ta zaga a nuna ta"
Wani tsaki Iya tayi mai kara sosai "amma kin bani mamaki. Wane sirri ne ya rage mata bayan a garin namu babu wanda bashi da labari yanzu. Kuma da kike batun za'a nunata an dade ba'a nuna ta ba. Iyaka ace ga wadda aka taba yiwa fyade ba wadda taje yawon ta zubar ba ko. Kai! Ni kam kuna bani mamaki abu mai girma kamar wannan ya faru ayi ta kubi-kubi dashi wai kada ya fito duniya ta sani"
"Yanzu Iya ba kya jin yadda rayuwar mata irinta take tagayyara?"
"Me zai hana ta tagayyara kuwa iyaye sai su rufe magana abar yarinya ita kadai tana fama da bakinciki. Yanzu da tayi shiru bamu sani ba haka zata rinka zabura muna banka mata hayaki ace mutanen boye ne. Kinga idan baza kiyi komai a kai ba ni ki barni. A ganina shirun da akeyi da rashin daukar mataki shine yake bada damar gobe ma a sake. Sannan yana daga abinda yake sa matan su ga kamar sune masu laifi ba matsiyatan da suka cutar dasu ba"
Shiru Ade tayi don ko kadan bata maraba da a kai maganar kotu a yiwa Mawadda tonon silili.
Sake kallon Iya tayi tana ta fada ta jinjina kai. Wannan karfin hali nata ga talauci ga rashin wayewa amma baya dakusar da ita akan niyyarta.
Suna nan zaune sai ga Baba ya shigo da Dahiru da Bilya. Ade na hango su ta dubi Iya.
"Don Allah kada ki ce musu komai"
Iya tayi guntun tsaki "ku kuka sani, mutane sunyi sanadiyar tona sirrin da kuke ta boyewa ya fito har akwai wani abu na mutuntawa tsakaninku kuma"
Da suka karaso sun gaisa dasu tare da tambayar mai jiki.
Ade zata amsa Iya tayi saurin katseta "jiki da saukin musulunci gata tana bacci. Raunukan zahiri dai suna ta warkewa amma kwarewa a tsegumi yasa an dasa mata wani tabon a kahon zuci. Uhmm ko da wane idon jama'ar gari zasu rinka kallon jikata kuma Allahu Ya'alamu"
Duka su biyun kai suka sunkuyar a kunyace don sun san dasu Iya take. Bilya ne ma ya iya bada hakuri sannan ya kara da cewa "muna nan muna neman gidan da zasu zauna ba a kauyen zai ajiyeta ba"
Tsananin farinciki a take ya kama Iya ta kalli Bilya ta koma tana kallon Dahiru.
"Kai yaro rantse, kace Allah Dahiru zai aureta"
Ledar lemo da ayaban da suka zo da ita Dahiru ya ajiye ya fice ganin su Baba duka shi suke kallo. Bayan fitarsa Bilya ya fada musu halin da ake ciki na dangane da samun gurbin karatu da aiki da zaiyi.
"Nifa shiyasa tun ranar da aka gabatar min dashi nace in anyi duniya dan Manzo Mawadda bata da miji bayan Dahiru. Zuri'ar gidanku ba daga nan ba ni shaida ce ra'ayil aini. Aure a wannan yanayin wallahi sai dan kwarai da ya haifu cikin uwa da uba."
Ade dai kasa cewa komai tayi Iya ta saka ta jin matsananciyar kunya. Amma anya iyayensu Dahiru sun sani kuwa? Shi kuwa Baba fita yayi yabi bayan Dahirun. A can gefe ya hango shi zaune. Ganin Baban yasa ya taso da sauri.
Kaunarsa ta sake shigar Baba ya yi masa murmushi "Dahiru nasan kai yaron kirki ne kuma ko gobe ka nuna kana son wata cikin kannen Mawadda zan baka. Amma ka hakura da ita, tata kaddarar kenan hakuri da aure"
Yana jin kunyar Baba gaskiya amma baya jindadin yadda kowa yake ganin rabuwa da ita shine alkhairi garesu.
"Baba don Allah ku sa mana albarka kawai. Na fadawa su Baffa kuma sun amince"
"Bazan so kaina ba Dahiru. Ko a yanzu ma mungode sosai da kulawa. Amma ka dauketa a matsayin kanwarka kawai. Idan ma saboda magana ta fito ne duka babu komai ko me za'ace za'a gaji a bari"
Magiya sosai Dahiru ya soma yi har ya bawa Baba tausayi. Amma don ya kara nuna masa illar auren duk kuwa da cewa ransa yana so ya sanar dashi dalilin zuwansu asibiti.
Dan nazari Dahiru ya soma har Baba yaji jikinsa ya kuma yi sanyi kada ya fasa da gasken sai kuma yaji yace "Baba haka zamuyi ta hakuri har ta sami lafiya amma aure in sha Allah ba za'a daga ba."
Kwalla ce ta taru a idon Baba. Ya sani wannan ba karamin abu bane. Ko dansa ne haka ta faru da wadda zai aura da wuya fa ya amince. Baya jin zai taba mantawa dashi ko auren bai yiwu ba yasan ya so 'yarsa kuma yaso rufa masa asiri.
"Nagode amma ka jira zamuyi magana da shi Mal Isiyaku kaji."
Bilya ne ya leko yace Mawadda ta tashi suka nufi hanyar dakin Dahiru yana rokon Baba akan su taimaka kada a fadawa iyayensa lalurar da ta kamu da ita yanzu. Baba ya ji shi ne kawai amma fada ya zama dole musamman yadda ya kara yarda da wuya ake boye abu a duniya. Bazai so a zargesu ba a gaba.
Tun shigowar Nos dinnan namiji har yanzu da Mawadda ta farka hankalinta bai gama kwanciya ba. Shiyasa su Dahiru basu wani dade ba suka tafi. Iya kuwa ta rinka mata fada akan ya kamata ta soma sakin jikinta da mutane.
Da yamma Dr. Tani ta shigo ta sake dubata. Sakamakon gwajin ta fadawa su Baba
"Sakamakon urinalysis da aka yi mata ya nuna bata kamu da wata kwayar cuta ba irin wadanda suke kama mafitsara. Saboda haka zan dorata akan magunguna sannan akwai abubuwan da nake bukatar ta kiyaye. Ku dan bamu wuri zanyi mata bayani"
Su Iya ne akan gaba wurin fita. Dr Tani ta kalli Mawadda tana dan murmushi. Yarinyar ta bata tausayi sosai har labarin abinda ya sameta ta bawa iyalinta.
"Kina jin saukin jikinki yanzu?"
"Eh" ta amsa murya can kasa.
"Abinda nake so dake shine na farko bana so kina zama da fitsarin nan duk da na kula ana chanja miki zani akai akai. Ga auduga nan za'a baki sai ki rinka sakawa ko da ya digo bazai taba miki kaya ba. Abu na biyu ina so duk lokacin da kika ji fitsari kiyi kokarin rikonsa na kamar minti biyar....ke security! kirawo min mahaifiyar yarinyar nan dai"
Yaya ce ta shigo Dr ta cigaba da bayanin yadda take so a kula da Mawadda. Idan taji fitsari su rinka dubawa da agogo sai bayan minti biyar da soma jinsa zuwa goma zata je tayi. Kuma ta dage sosai wurin rikonsa kada ya digo. Abu na biyu idan sun je tayi ta tabbatar ta gama sai ta sake dagewa ta kuma matso duk wanda yayi saura. Kada ta tashi sai ta tabbatar a karo na biyun ta sake yin wani komai kankantarsa. Tana so suyi haka na kwana uku domin horar da jijiyoyin wurin. Idan ta gamsu da cewa Mawadda tana yin yadda aka umarceta zasu sallameta sai ta dawo bayan sati daya a dubata amma dole zata cigaba da yin yadda tace din.
"Sai lamari ya baci ake yin aiki wanda bana fata muzo haka dake. Saboda haka ki dage sosai ki bi abubuwan da nace. Magunguna kuma za'a bawa babanta takarda ya siyo da wuri domin a fara amfani dasu."
Wasu cikin magungunan babu a pharmacy din asibitin aka kwatantawa Baba wani a waje. Ya samesu duka amma an kashe kudi kusan dubu hamsin. Yau ba don Iya da Ade ba da kila ko bara ce ta kama yayi zaiyi. Me za'ayi da talauci. Sai yayi huluna suyi sati yanzu ko tayawa ba'ayi balle kuma a saya. Gonar da yake dan nomawa yanzu amfanin da ake samu ba kamar da ba ita ma.
Da nannauyar zuciya ya koma ya kai magungunan. Suna ta fatan Allah Yasa a dace.
Abubuwan da Dr. Tani tace ta kula dasu na yanayin fitsari kuwa ta fara gwadawa iyayenta suna karfafa mata gwiwa.
******
Maigadi ne ya fito jin ana ta buga gate din. Yasan fuskar matar da ya gani duk da bai san sunanta ba amma yasan tana zuwa wurin Haj Mara.
Bude mata yayi suka gaisa ta tambayi Hajiyar yace tana ciki. Da sallama ta shiga. Da Haj Mara taji muryarta wani mugun tsoro ne ya kamata. Murmushi ta kakalo na dole gabanta na faduwa.
"Hajiya Gambo kece a gidan namu?"
Gambo dillaliyar masu aiki tayi dariya "ai ku ne hajiyoyi. Yaya gida da kujiba-kujibar yau da gobe? "
"Lafiya kalau"
Shiru Haj Mara bata sake magana ba tana jira taji me ya kawo Gambo. Ita kuma jira take Hajiyan ta turo mata Mawadda kamar yadda ta saba. Gajiya tayi da jiran tace
"Hajiya ina Mawadda ne? Yarinya na kawo nan Malali shine nace bari na leko mu gaisa."
Haj Mara ta hadiyi wani mugun yawu saboda yadda ta tsorata.
"Mawadda ai ta tsufa a gida"
"Ban fahimta ba"
"Rana daya kawai tasa min kuka tana son tafiya. Tun ina bata hakuri na gaji da kaina na mayar da ita"
Gambo tace "Mawaddan? Ni duk cikin yaran da nake kawowa ma ai tafi sauran hankali. Tasan cewa zan dawo na tafi da ita da kaina. Dama yau karfin zuwan nawa zanyi miki maganar bikinta ne da ya matso. Shine nace gara na fada ko zaki nemi wata. Ita idan nazo na kaita hutun sallah bazata dawo ba"
"Ni na hakura ma da masu aiki hakanan Gambo. Aikin nawa yake gida sai mu uku"
"Haba Hajiya da kanki"
"Ai dole, Gambo bazan boye miki ba Mawadda ta bani mamaki. Ta difga min sata ta ban mamaki shiyasa ta dage zata tafi"
Ran Gambo kuwa ya baci. Ta saba da ace ta kawo yarinya tayi sata amma batayi zaton haka daga Mawadda ba.
"Hajiya kada ki damu nawa ta satar miki? Wallahi da kaina zan dawo miki da kudinki don gidansu zani. Wannan sai su kashe min kasuwa azo ana ganin kamar hadin baki muke dasu"
BB yana kitchen yazo shan ruwa yaji Hajiyarsa tana karya don ta rufa masa asiri. Wata dariyar shakiyanci yayi ya fito falon.
"Hajiyata kenan, Allah Ya barmin ke muci karenmu ba babbaka"
Gambo ta bisu da kallo Haj Mara ta wayance tace ta bar maganar satar ita ta hakura.
Gambo na fita wayar Baba ta kira tunda tana da ita. Duk lokacin da tazo karbar kudin Mawadda da layin take kiransa ta hadasu su gaisa. Ko tasha bata karasa ba ya dauka ta soma fada masa abinda Haj Mara tace.
"Ince ko Kano zaki sauka idan kin taho."
"Eh dama gobe nayi niyar zuwa Tariwa din"
"To ki daure ki shigo asibitin Malam sai ki kirani"
Daga haka ya kashe wayar ya barta da mamaki. A tashar unguwa uku ta sauka ta wuce gidanta da niyar gobe zata je asibitin tunda dare yayi.
******
Haj Mara tun zuwan Gambo hankalinta ya kasa kwanciya. Matar nan dai tasan gidanta. Idan ta dawo tare da iyayen Mawadda fa yaya zata yi?
Alh Sule har ya fuskanci tana cikin damuwa yayi kwafa.
"Tun ba'aje ko ina ba kin fara zurfafa a tunani akan barnar da yaron nan yake yi ko? To kadan ma kika gani. Ina me tabbatar miki idan bazaki kaini gidan iyayenta mu gyara lamarin nan ba to ki tanadi abin tarar hawaye nan gaba"
Ya gaji da magiya harda barazanar saki duka a banza tace bazata kaishi gidansu Mawadda ba.
Tsoron dawowar Gambo yasa ta dauki waya bayan ya fita daga dakin ta kira kawarta.
Saita muryarta tayi tamkar babu komai kafin ta soma magana da aka dauka
" 'yar boko matar dan boko"
Dr Tani tayi dariya
" 'yar kasuwa matar dan kasuwa jiya ina ta nemanki waya a kashe. Ya ya mutan gida"
Dan barkwanci da tsokanar juna suka taba irin na kawayen da suka tashi tare. Sai kuma Haj Mara ta tattaro nutsuwarta.
"Tani kwana biyu ina ta tunani nace bari dai na fada miki naji ra'ayinki. Cewa nayi me zai hana in turo Babawo yazo su daidaita da kanwarsa Qareeba?"
A zahirin gaskiya Dr. Tani bata da burin 'yarta tayi auren nesa saboda zaman su Haj Mara a Kaduna. To amma ta gaji da gorin dangin miji gashi Qareeban duk gayunta samari basa dadewa ta rasa dalili. Shekara ashirin da biyar gara tayi aure ko zata huta da surutu.
"Amma kinyi tunani mai kyau Marakisiyya na amince. Zanyi magana da Daddynsu sai na fada miki yadda muka yi"
Ajiyar zuciya Haj Mara tayi. Gara Babawo yayi aure kila zata sami saukin wannan bibiyar matan da yake yi.
******
Da kwatancen da Baba yake mata Gambo ta iso dakin da aka kwantar da Mawadda. Kafin tayi tambayar me suke a nan Yaya ta labarta mata komai. Idanunta jazur saboda kuka da takaicin rainin wayon da Haj Mara tayi mata jiya tace da zasu bata hadin kai da an kaisu kotu.
Iya tayi dariya "Allah nagode maKa na sami mai goya min baya. Mun yarda mun amince don ko wadannan basa so..." ta nuna su Baba "ni bazan yafe ba."
Sake kallon Mawadda tayi taji kamar ita ta jawo mata da bata tsananta bincike akan gidan ba. Ji yadda ya sabauta musu yarinya ta fada kumatu ba tsoka sai hakwara gayau da idanu.
[08/01 8:32 pm] Biebie: *GUMIN HALAK...*💰7
*Batul Mamman*💖
Bayan Sati Daya
Aikin Dahiru a gidan Dr. Tani ya kankama kuma Alhamdulillah komai yana tafiya daidai. Matsalarsa daya ce a gidan Qareeba