Showing 18001 words to 21000 words out of 110071 words
kasuwa.
"Ayi haka Iya gabadaya?" Yace a kunyace.
"Don kaniyarka ko ban haifi uwar Mawadda ba kai din ba dana bane? Ko matsayin nawa zaka nuna min eyee?"
Murmushi yayi yana bata hakuri. Ade ma tace kudaden da take tarawa na bikin Mawadda zata fito dasu idan yaso gobe da sassafe sai su wuce Kano.
*****
Da wuri Dahiru ya isa Kano saboda sammako da yayi. Rijiyar zaki ya nufa gidan Bilya. Da yake yasan da zuwansa dama yana gida yana jiransa. Abinci ya fara ci sannan suka zauna tattaunawa da dan uwan nasa.
Bilya ya nuna alhinin wannan al'amari bayan Dahiru ya gama bashi labari. Sannan suka koma batun gurbin karatu da ya samu.
"Kasan na fada maka yayan ubangidana na garejin mu ne ya sama maka adimishon din. To Alhamdulillahi jiya kana kira nayi maza naje na same shi. Munyi sa'a yace sai nan da sati biyar za'a fara zuwa karatu. Amma kafin nan akwai takardu da zan baka kaje ka cike su sai kasa suka hannu. Sauran bayani dai zaiyi maka tunda zamu je wurinsa"
Dadi ya kama Dahiru jin cewa bai makara ba. Bayan ya duba takardun da kudin da zai biya jikinsa yayi sanyi. Da gani wannan karatu za'aji jiki. Ga Bilya ba wani abin kirki gareshi ba shima ta kansa yake ga 'ya'ya biyu.
Ganin yayi shiru Bilya ya karbe takardun "kaga malam tunani ba naka bane. Tashi zaka yi muje wurin shi Oga Sani nayi masa maganar bamu da kudin karatunka sai ka nemi abin yi. Yace zai san yadda za'ayi idan ka zo"
A raunane Dahiru yace "Yayanmu Bilya ni kam me zan ce maka. Ka gama min komai nagode sosai"
"Me zaka ce kuwa da ya wuce idan an sami aikin ka rike amanar iyayen gidanka sannan kayi karatu sosai ka 'yan mana arzikin bokon a gaba. Kuma fa karatun injinniya yace ka samu saboda ya ga ka kware a lissafi. Baka ga dadin da naji ba" yayi maganar yana masa dariya.
Matar Bilya mai suna Furaira ta zo bayan Dahiru ya gama cin abinci tana masa tambayoyi kamar 'yar jarida game da Mawadda.
"Amma dai ka fasa aurenta ko?"
"In sha Allahu aure yana nan kamar yadda aka tsara tun farko"
"Kai kuwa me zaka yi da ita kamar dole"
"Ke!!! Ban fada miki ki rike bakinki akan maganar nan ba? Ina ruwanki idan yace zai aureta" Bilya ya daka mata tsawa.
Murguda baki tayi ta mike "gaskiya ce bakwa son fada masa. Allah na tuba wa ya sani ma ko 'yan ciwukan zamanin nan ta kwaso zai aura a hada shi da jafa'i"
Dahiru bai ce komai ba ya tashi ya saka takalmi. Yana jiyo hayaniyar Bilya da Furaira bayan ya bita dakin. Kaya ya chanja ya fito suka fita tare.
Garejin da Bilya yake aikin gyaran mota a bakin titin unguwar suka je. Sunyi rashin sa'a Oga Sani bai zo ba. Gefe Dahiru ya samu ya zauna yayin da Bilya ya sauya kaya zuwa kayan aiki ya shiga cikin abokan aikinsa kowa ya kama aikinsa.
Sai wurin karfe uku Oga Sani ya iso. Mutum ne na mutane mai faram-faram da jama'a da sanin hakkin na kasa dashi. Bisa wannan dalilin ne ma wata rana yaji Bilya yana fadawa wani abokin aikinsa burinsa Dahiru yayi karatu tunda yaci jarabawar shiga jami'a. Jin haka ya taimaka masa da kudi wanda da shi ne Bilya ya biya wa Dahiru yayi JAMB. Bai kuma tsaya haka ba ya kara da kaiwa yayansa da yake aiki a matsayin darakta a BUK din takardun gashi anyi sa'a ya sami gurbin karatu zai karanta Computer Engineering.
Yana fitowa daga motarsa gaban Dahiru yaje yana murmushi "wannan dai ko ba'a fada ba nasan kaina kanin Bilya mayen honda"
Dahiru yayi 'yar dariya yana kallon Bilya da ya taho wurin "Yayanmu sunanka kenan ashe"
Oga Sani yace "ashe bai fada muku ba. To ai idan kazo wurin nan ba ka ce Mayen Honda ba da wuya a gane shi. Kunyi kama sosai amma dai ka dan fishi kyau"
Shi dai Bilya sai murmushi. Sallah suka yi Oga Sani ya daukesu a mota yace ya yiwa yayansa bayani ga dukkan alamu Dahiru zai sami aiki a gidansa.
*****
A can asibiti kuma sun gama hada kayansu an basu takarda da zasu nuna mai dauke da duk wani bayani dangane da Mawadda.
Kafin Baba ya dawo su ma sun taho tunda zaman babu amfani. Jin tana fama da lalurar rashin rike fitsari ba karamin dagawa 'yan uwanta hankali yayi ba. Haka suka tafi dai kowa rai babu dadi.
Daga bakin titi da suka sauka daga bus har zuwa gida idanu da kananun maganganu suna biye dasu. Mawadda rufe fuskarta tayi gabadaya saboda yadda ake binta da kallo. Duk bakin Iya bata ce komai ba saboda kunya. Iyalin Baffa ne suka sha zagi tas a wurinta na Dahiru ya ma fi na kowa bayan sun isa can gidansu Malam da Innar Fatihu. Lokacin duk sauran 'yan uwan Ade da na Baba kowa yana gidan.
Sun tausayawa Mawadda sosai yawancin matan harda kuka. Shirin tafiya Kano suka hau yi 'yan uwa kowa da ya mika abinda Allah Ya hore masa a matsayin tasu gudummawa saboda basu san yaya zata kaya ba.
*****
Katon gida ne suka je a Sharada housing estate. Dahiru bakon birni sai bude baki yake bai taba ganin gida irin wannan ba.
Gida ne mai kyau ga filawoyi sun kawata shi. Can gefe kuma motoci ne wurin shida masu kyau da gani zasuyi tsada shine tunanin Dahiru.
A wajen maigadi Oga Sani ya barsu ya shiga ciki. Bai wani jima ba ya dawo ya kira su. Wata mata ce ta fito a daidai bakin kofa ta tsaya su kuma suna daga gefen matattakalar da za'a taka mai gudu shida ya isa inda take tsaye. Gaisheta suka yi a mutumce ta amsa tana faman yatsina.
"Sani wanne ne zaiyi aikin a cikinsu?"
Dahiru ya dan dago kai yayin da Oga Sani ya dafa kafadarsa "wannan ne sunansa Dahiru"
Kallonsa tayi ta dan tabe baki "Aikin share farfajiyar gidan nan da gyara flower zaka yi. Sai kuma duk asabar zaka rinka yi mana wanki nawa da na yaran gidan. Ranar lahadi ka goge ko babu wuta za'a tayar da inji. Idan aikin yayi maka albashinka dubu ashirin"
Tsabar murna Dahiru bai san lokacin da yace "ahirin???" ba.
Wata irin dariya suka ji an kwashe da ita daga bayansu. Yarinya ce budurwa ta fito daga cikin motar da take a kunne tun zuwansu taci ado sosai.
Dariya take har tana rankwafawa ta kalli Dahiru "yaya sunanka?"
"Dahiru" ya bata amsa a takaice.
Tana dariya tace "Sannu Dashiru"
"Dahiru ne sunan" ya gyara mata a zatonsa bata ji bane sosai.
"To Malam Dashiru mai ahirin" ta sake kyalkyalewa da dariya.
Ransa in yayi dubu to ya gama baci. Hatta Bilya shima fuskarsa ta sauya.
"Kawu Sani ina ka samo mana 'yan ahirin?"
Hade fuska yayi sosai "bana son wannan shirmen naki Qariba"
Mamanta ta bata rai itama jin anyi mata tsawa "kai fa Sani idan kazo gidan nan to yaran nan basu da sauran sukuni"
"Yara ko magidanta? Kin ajiye dika-dikan yara saboda boko kunyi yi musu aure. Kuma kina kallo nazo da bako tana yi masa dariya don rainin hankali"
"Bakon naka ba me aikin gidansu zai zama ba? Kai kudin yayi maka zaka iya?"
A sanyaye Dahiru yace eh. Ya ma isa yace bazai iya ba tashi daya dubu ashirin a wata me ya manta.
Sunyi sallama da matar bayan an daidaita zai fara zuwa ranar litinin nan da kwana hudu kenan. Batun karatunsa wanda Oga Sani ya fada mata tace zasu daidaita idan an fara karatun a tsara yadda zai rinka aikin.
Sun juya zasu tafi Qariba ta daga murya tace "Malam Dahiru me ahirin sai monday" dariya ta rinka yi har ta shige cikin gidan.
Oga Sani yace masa sai yayi hakuri sosai da yaran dan uwansa. Shi maigidan Dr. Auwal rikakken dan boko ne wanda yake taba kasuwancin sayar da motoci yayin da matarsa Dr. Tani likita ce tana da asibitinta mai zaman kansa. Yaransu hudu maza uku sai Qariba mace kuma ita ce ta uku. Sangarta ta wuce tunani da gata yaran sun tashi dashi shiyasa zama dasu sai an kai zuciya nesa.
[08/01 : *GUMIN HALAK...*💰6
*Batul Mamman*💖
"Baffa anya ba zanje gidansu Mawadda ba da kaina?" Cewar Inna tana kallonsa ya zurfafa a tunani.
Dan guntun tsaki yayi "kije kice kinzo bada hakuri saboda 'yarki bakinta bashi da linzami ko"
"To naga ka kasa komawa kuma ance sun dawo. Danlami yace tun daga bakin titi ake binsu da kallo nasan surutun ma sai anyi"
Takaici ne kawai yake cinsa a rai. Idan ya fita an rinka zundensa kenan ko shine Mal Fatihu sai haka. Wasu har cewa suke Dahiru ne ma yayi mata fyaden. Wasu kuma suna ganin bai kyauta ba sun tonawa surukansu asiri saboda tsautsayi ya fadawa yarinyar. Yanzu ta yaya zai dawo da mutumcinsa a gari? Tashi yayi ya zura takalmansa yayi waje Inna na kiransa bai ko saurareta ba ya fita.
Gidansu Mawadda yaje abin mamaki tun kafin yayi sallama gabansa ke faduwa saboda kunyar ganin Baba. Lallai baki shi ke yanka wuya. A da shine abin girmamawa ko ba komai ya girmi Baba a shekaru haka zalika ya fishi rufin asiri. Amma yanzu da yake ganin kansa mai laifi gareshi duk sai yaji ya muzanta.
Yayi sa'a Mal Fatihu ya dawo daga kasuwa inda ya sayar da dabbobin Iya tun magariba domin kuwa lokacin tara saura na dare ne.
Da Baba ya fito suka kalli juna sai wani nauyi ya sake lullube shi.
Da kyar ya iya bude baki yace "Mal Fatihu do Allah do Annabi kayi hakuri. Kuruciya da tsabagen surutu yasa Ummiyo wannan barambarama"
"Babu komai kada ka damu"
Yadda Baba ya amsa Baffa yasan ko kadan bai kai zuci ba to amma baya son jan zancen.
"Ga wannan ka rike saboda kulawa da ita." Kudi ya mikawa Mal.Fatihu har naira dubu biyar.
Shi kuwa ya noke hannu "idan domin abinda ya faru ne Mal Isiyaku ka dena damun kanka dama ko ba dade ko ba jima ai gaskiya zata fito"
Duk yadda Baffa yaso Baba yaki karbar kudin har sai da yace ko dai ya rike shi a rai ne. Jin haka yasa ya karba suka yi sallama.
Washegari Baba ne ya jagoranci tafiyarsu Kano tare da Mawadda da Yaya. Iya ba yadda batayi ba akan Ade ta bisu tace kada a ga rashin kawaicinta tunda Yayan ta tsaya tsayin daka akan lamarin. Idan sun je Baba zai kira ya sanar dasu halin da ake ciki. Idan da bukatar su tafi sai su bi bayansu.
Dubu talatin yasa a aljihu banda kudin mota. Kanwar Yaya da take aure a sallari wata unguwa cikin Kano ita ce zata shige musu gaba zuwa asibitin Malam Aminu Kano. Da isarsu gidanta suka fara wucewa. Mawadda tana ta dararewa a baya saboda ko yaya aka kalleta sai ta tsargu.
Gani take kamar ana ganinta ake gane abinda BB yayi mata. Uwa uba ta kara shiga takura saboda fitsarin nan. Duk wani motsi a sannu take yinsa sannan tana bakin kokarinta wurin ganin ta rike fitsarin. Da aka kawo musu abinci baifi loma biyar tayi ba shima don an matsa mata ne. Suna gamawa kuwa suka wuce asibitin kai tsaye.
Ita Barira a iya saninta layi ake bi idan anje asibiti a karbi kati. Saboda haka wurin ta kaisu gashi shadaya saura. Sun jima a kan layin da basu tantance na menene ba sai daga baya wani ya sanar dasu na karbar sakamakon gwaji ne ba na karbar ko bude fayil ba. Haka suka sake komawa su ka bi layin da aka nuna musu. Sun sha matukar wahala kafin suyi sa'ar bude kati amma saboda makara da suka yi aka ce bazasu ga likita ba a ranar sai washegari su tabbatar sunyi sammako.
Baba yaso su ga likita a yau saboda baya son takurawa Barira da maigidanta. Ita ce autar su Yaya bata fi shekarun Bilki ba. Bisa lalura suka kwana a gidan inda aka bawa Baba wani daki a soro.
Duk yadda suka yi ya sanar da Ade ita kuma ta fadawa su Malam. Da safe kuwa waahegari bakwai akan layi tayi musu. Suna nan har rana ta gama budewa suka karbi kati aka ce su bi layin ganin likita. Har wata ajiyar zuciya Baba yayi don murnar suna gab da samun abinda ya kawosu. Da yake ko karyawa basuyi ba suka fito yace su jira shi ya samo musu wani abin da zasu ci.
Ya dan sha wahala kafin ya sami wurin masu abinci don shi gabadaya kansa ma juyewa yayi ya kasa gane hanyar komawa inda ya baro su.
Zaman awa kusan biyu suka yi kafin a kirasu. Baba yace su shiga da Yaya zai jira su a waje. Takardun wancan asibitin da na 'yan sanda duka ya bata suka shiga.
Mawadda ta yiwa likitan bayani daidai gwargwado tana kuka. Shi tunda yake bai taba jin abu irin wannan ace daga fyade sai kasa rikon fitsari ba. Ya kira nos tazo ta duba masa jikinta har sai da tayi kwalla ganin yadda karamar yarinya irin wannan ta tsinci kanta a wannan yanayi. Ta yarda mutanen kauye akwai dauriya ba raki irin na 'yan matan birni.
Suna jiran su ji me zai ce ya daga waya ya kira. Da gani dai da na gaba dashi yake magana saboda yadda yake ta kwantar da kai tare da yin bayanin lalurar patient dinsa.
Dan dakatawa yayi yace "daga ina kuke?"
Yaya ta amsa masa "kauyen Tariwa"
Da ya gama yace suje daga waje zai kirasu akwai wadda zata zo ta duba ta.
*****
Dr Tani ta ajiye wayar ta gyara kwanciyarta tana tsaki. Maigidanta Dr Auwal yayi murmushi
"Ke da wa wannan tsakin haka?"
"Dr Yunus mana. Wai ya kasa gane kan wani case ne shine yake neman alfarmar nazo. Ni kuma yau bani ma da ra'ayin fita. Raina daya naje AKTH naje nawa asibitin."
"Idan bazai yiwu ba ko ajiye aikin AKTH din mana ki mayarda hankalinki ga naki."
"Ina jin haka za'ayi don na gaji. Yace mutanen daga kauye suke so nasan zasu iya jira ba tare da damuwa ba"
Gyara kwanciya tayi abinta duk da tasan dama ita zata karbi Dr Yunus din karfe daya. Bata jima ba ta koma bacci sai shabiyu da rabi ta farka. Shima zafi ne ya tasheta saboda an dauke wuta.
A tsanake take komai hankali kwance. Marasa lafiya indai sun damu da lafiyarsu ai dole su jira. Ba ita ta gama shiryawa ba sai wuraren biyu.
Cikin shigar da ta saba yi idan zata je asibiti ta sauko. Doguwar riga ce mai dogon hannu ta atamfa sai hijab dan madaidaici saboda dora labcoat.
Qareeba ce kadai a falon tana kallo.
""Mummy kin sauko" shine kalmar da ta fara fada mata a madadin gaisuwa.
"Eh, ina su Najib?"
"Basu tashi ba"
"Jeki ki taso min su bana son suna kaiwa rana basu yi breakfast ba" ta fada tana ajiye jakarta a gefen kujera.
Baki Qareeba ta soma turowa ta tashi ba don taso ba.
Dakunan yayyenta ta je Najib, Faisal da kuma kaninta Safwan. Da gunaguni suka iso falon Mummynsu tana cewa su ci abinci bata son suna zama da yunwa.
Abin da zai bada mamaki shine dukkaninsu sun bawa shekara ashirin baya. Safwan shekarunsa ashirin da uku. Shi da sauran duka shekaru bibbiyu ne a tsakaninsu. Dr. Tani ba karamin so take yi musu ba shiyasa tsabar gata yasa suka tashi su ba dolaye ba su ba shagwabbabu ba. Har gara Qareeba mace ce amma mazan idan suka yi wani abin tamkar a bugesu don takaici.
Zamanta tayi suna ta tabara da sokonci har suka gama cin abinci sannan ta tashi ta fita dreba ya kaita asibitin.
******
Yunwa, gajiya, kishi da bacci duka babu wanda su Mawadda basa ji. Gashi suna tattalin 'yan kudadensu saboda basu san yadda zata kaya musu ba.
Dan abin kunzugun da Ade tace ta rinka sakawa saboda danshin fitsari tuni ya gama jikewa ita kanta tasan idan ta mike za'a gani.
Yaya tana sallah a gefensu akan dankwalinta Mawadda ta dan matsa kusa da Baba. Duk yawan marasa lafiyan gurin duk sun kare sai su kadai.
"Baba ko zamu tafi gobe mu dawo" tayi maganar a hankali.
Cike da tausayawa ya kalleta "kiyi hakuri Mawadda tunda likitan yace akwai me zuwa dubaki. Nasan basu manta ba. Kinsan fa aiki yawa yake musu shiyasa kika ji shiru har yanzu"
So take ta fada masa ta soma jikewa amma kunya ta hana.
Wata mata ce ta shigo ganin Yaya tana sallah a wurin ta tabe baki.
"Babu wanda ya kai dan kauye kazanta. Ji wannan matar ta rasa wurin da zata shimfida dankwali tayi sallah sai nan da kowa yake wucewa."
Ba wasu manya bane masu maganar amma sunyi shiga ta alfarma da zata nuna ba kananun mutane bane.
Mawadda da Baba sunji ta amma duka sukayi shiru. Wadda aka nunawa yaya harda yin tsaki. Kamar hadin baki sai ga nurses da wasu likitoci uku sun fito suna gaisawa dasu. Ashe 'yar wani minista ce.
Sannan Dr Yunus ya hango su Mawadda wanda ya ma manta dasu gabadaya.
"Har yanzu kuna nan dama? Nayi zaton kun gama kun tafi tun dazu"
Baba ya danne bacin ransa. Su da babu wanda ya kulasu tun fitowarsu me zasu gama?
"Likitan da zata dubata bata iso bane?"
Dr Yunus ya dauko waya yana son sake kiran Dr. Tani amma kuma yana tsoron fadanta. Sai gashi yayi sa'a ta shigo lokacin uku da rabi tuni ta wuce ana neman hudu.
A mutumce suka gaisa da kowa musamman 'yar minista ana ta tambayarta yaya jiki sannan tace ina mara lafiyar da zata duba.
Fayil din Mawadda aka kai mata office sannan aka kirata.
Tana tashi kusan kowa a wurin ya ga yadda kujerar da ta zauna tayi naso alamun danshi. Ganin ana musu kallon wulakanci Yaya ta dauki dankwalinta ta tsiyaya pure water a wurin ta hau gogewa. Daga wannan ya yamutsa fuska sai masu kananun maganganu don me tasan tana da lalura zata zauna akan kujerar. Maganganun sun yiwa Yaya zafi ta dai gyara wurin ta bi bayan Mawadda da Baba zuwa ofishin likitar.
A nutse take gabatar da komai Baba duk haushi ya ishe shi. Sai da ta gama karanta duka bayanan wancan asibitin sannan ta dan kalli Baba.
"Yallabai a bamu wuri muyi aikinmu ko. Ko a gabanka zan dubata?"
Har dan rissinawa yayi mata saboda kawai ta kyautata duba masa Mawadda "yi hakuri ranki ya dade bari na dakata daga waje. Mawadda kiyi bayani sosai kinji ko"
Kai ta