Showing 24001 words to 27000 words out of 110071 words

Chapter 9 - GUMIN HALAK Complete Book by Maman Batul.txt

22 Sep 2025

182

wadda ta zame masa tamkar horror. Ta matsa masa sosai duk wani motsinsa abin tsokana ne a wurinta. Ta kai ta kawo idan yaji muryarta gabansa har faduwa yake saboda bai san me zata ce masa ba.

Yau ta kama litinin dama tun jiya ya sanar cewa yana da uzurin da zai sa bazai sami damar zuwa da wuri ba. Asibitin makaranta suka je inda akayi masa gwaje-gwaje na sanin yanayin lafiyarsa kamar yadda makarantu suke bukata. Yana gamawa ya wuce wurin aikinsa ko gidan Bilya bai koma ba. Ga rana ga yunwa don bai ci komai ba ya fita.

Sanye yake da koriyar t-shirt da dogon wandonsa ruwan dorawa mai duhu sai farin canbas din da yake ji dashi. Yayi kyau abinsa daidai da kwalliyarsa.

Tunda ya fara aikin maigadi ya bashi shawarar ya ware kaya daya da zai rinka amfani dasu kada ya kashe suturunsa a bawa filawa ruwa da su shara. Kafin ya tafi jiya ya wanke su ya shanya a bayan gidan inda igiyoyin shanyar suke. Yana isowa hanyar bayan yayi domin dauko su.

Ta cikin falo Qareeba ta hango shi yana tafiya da sauri ta dawo bakin taga inda zata ganshi sosai.

Dariya yaji an saka ya dan cije lebe. Yau ya shiga uku kuma ko da me tazo.

Kayansa ne suka bata dariya yaji ta ce

"Ahirin irin wannan gayu haka. Gaskiya ka burge maza enyee."

Ta zuge labulen tana kallonsa sosai bayan ta bude tagar. Shi kuwa kamar ya kwadeta. Cigaba yayi da tafiya kawai sai ta fara masa waka harda tafi.

" Gayu, gayu Ahirin on top, gayu, gayu Dashiru on top"

Abin ya sosa masa rai fiye da zato saboda dariya akwai cin rai ga yunwa. Karasawa yayi ya kwaso kayansa tana ta shirmen wakarta. Sai da yazo daidai tagar zai wuce ya daga hannu ya yi mata dakuwa.

Zaro idanu tayi ta nuna kanta "Ni?"

Ya gyada kai tare da harararta ya wuce. Bai ko karasa gaban gidan ba yaji Dr. Tani tana kiransa. Hankali kwance ya nufi bakin kofar shiga gidan don a tunaninsa aiki zata saka shi. Yana tsaye a gefe ta fito. Ko gaisuwar da yake mata bata amsa ba ta soma fada.

"Dahiru har wuyanka yayi kaurin da za ka zagar min 'ya?".

Qareeba ya gani tana goge hawaye a gefenta ya dago kai fuskarsa na nuna mamaki.

"Hajiya ni din? Yanzu fa na shigo gidan."

A shagwabe Qareeba tana wani tale baki tace "Mummy ta window ya harareni yayi min haka..." ta yiwa Dr. Tani dakuwa yadda yayi.

Mummy tayi saurin rike mata hannun ganin ya bisu da kallon mamakin gaske yanzu.

Sai kuma ya koma kallon Qareeba "Assha Anti Qareeba kila dai baki kula bane sosai. Na hangoki ne ta taga shine na dago miki hannu"

"Mummy kinji wani wulakamcin wai Anti kamar wata babba"

"Abokiyar wasanka ce to da za ka daga mata hannu?" Dr. Tani ta fada a fusace.

Girgiza kai ya shiga yi "A'a Hajiya kiyi hakuri in sha Allahu zan kiyaye"

Tsaki tayi ta juya tana jan hannun Qareeba mai dagewa da gaske zaginta yayi. Bayan sun wuce ya kada kai yayi gaba yana mamakin jama'ar wannan gida. A haka fa ance masa Qareeban bautar kasa zata soma. Yayyenta sun gama don Najib har ya fara masters. Amma dukkansu wasu iri yake ganinsu saboda dabi'unsu.

A dakin Qareeba tana zaune a kan gado Dr. Tani tace "bana son wannan shisshigewa yaron nan da kike yi kinji ko. Kinsan sarai Sani da sauran dangin Daddynku basa kaunarku. Kila ma turo shi akayi sa ido shine ke kuma da abin dariya baya yi miki wuya kin saka shi a gaba"
******

Karfe biyar a kofar bangaren da aka kwantar da Mawadda tayi masa. Tunda ya fara aikin sai yau ya sami damar komawa.

Kusan duka 'yan uwan Mawadda suna dakin idan ka cire Baba. Kanta ta kifa akan cinya tana kuka Innar Fatihu tana mata fada.

"Haba Mawadda ace mutum baya jin rarrashi ko kadan. Idan zaki karar da hawayenki fa babu wani abu da zai iya goge wannan abin. Ki rungumi kaddara kin kasa kullum sai koke-koke ki tayarwa kanki hankali muma ki tada mana"

"To, to, taji sai a barta haka." Cewar Iya tana rungume Mawadda a jikinta "kuma dole tayi kuka. Sati guda tana bakin kokarinta amma fitsarin nan yaki daukewa."

"Cuta dai aka sani da shiga farat daya amma sauki sai anyi hakuri. Wannan abin da kike yi mata Ta Rasulu ba soyayya bace"

Cacar baki suka yi ta yi 'ya'yansu da jikoki suna basu baki.

Dahiru ya matso a hankali yana kallon yadda mutanen da suke sauran gadajen suka kafesu da ido suna neman cika dakin da hayaniya.

Ai kuwa sai ga security tace gabadayansu su fita. Yaya ce ta lura da Dahiru tayi masa murmushi ya duka ya gaishesu.

"Zauna ku gaisa bari muje waje"

Ade ma murmushi tayi ta fita. Ita dai tana son yaron nan amma tana jiye musu lokacin da Baba zaiyi magana da Baffa. Abin da kamar wuya dai.

Sai da kowa ya fita ya matso tare da dafa bayan kujerar dake gafen gadon.

"Bazaki dago mu gaisa ba Mawaddan wa Rahma."

Wani sanyi taji a ranta sai kuma kunya ta sake jan mayafi tana kuma tura kanta cikin cinyoyinta.

"Yangar da kike yi min yanzu ko da bana jin kinyi irinta. Yanzu dai kin yini lafiya?"

A hankali ta dago "kai Yayanmu nice zan fara gaisheka fa"

"Kina wannan kukan me hada tsofaffi rigimar ne zan jira ki gaisheni?"

Shiru tayi tana son gyara zamanta amma tana kunyar ko yaya ta matsa kamar zai ga yadda wurin ya jike.

Shiru suka yi na dan lokaci can yace "kukan me kike yi ne?"

"Ba komai"

Yace "Ban isa a fada min ba kenan"

Da sauri ta dago "a'a"

Ya dan ja kujerar ya zauna "to ina jin ki"

Bagarar da zancen tayi tace "Ashe zaka fara karatu na tayaka murna"

"Murnar ba tamu bace mu biyu?" Ya tsareta da ido.

"Tamu ce mana harda duka 'yan Tariwa. Kowa yaji nasan zaiyi murna"

Tambayarta yayi yaushe za'a sallameta tace saura kwana biyu. Yayi alkawarin zuwa ranar suyi sallama.

"Kinsan yanzu na fara aiki babu damar kalula da na rakaki har gida. Zan cigaba da kokarin samar mana gida in Allah Yaso."

Jinsa kawai take don tasan ko me zata fada masa yanzu bazai fahimceta ba. Da zai tafi ya kawo dari biyar ya dora mata akan pillow. Tayi ta magiyar ya dauka yace idan tana rokonsa zasuyi rigima ne. Ba don yasa ba haka ya tafi ya barta.
******

Kwana biyu a tsakani aka sallameta. Dr. Tani ta bata magunguna sannan tayi gargadi sosai akan ta kula da wadannan abubuwa da ta sanar da ita ta kiyaye idan tana jin fitsarin.

Kalandar wayarta ta kalla sannan tace "nan da kwana shabakwai ku dawo. Zai kama sallah da sati biyu kenan. Akwai wani matakin da zamu dauka amma sai naga yadda wadannan suka karbeki"

Tasha godiya sosai sannan suka hada kayansu suka wuce. An bar Mawadda a gidan Malam saboda zata fi kusa da Ade don indai ta koma gidansu Ade da wuya taje.
*****

Anyi sallah babba lafiya. A bangaren Dahiru ya zage yana aiki sosai musamman ranar sallah da aka yanka katon sa da raguna uku. Sun aikatu sosai shi da maigadi wurin gyaran naman. Sai mata biyu da aka samo tare da ainihin kukun gidan suka hadu suka soya.

Ranar sai dare ya tafi. Yana bude gate Dr. Auwal yana shigowa. Suka gaisa ya wuce da ledar naman da aka bashi yana ta sauri ma kada yaje Furaira tayi bacci naman ya lalace tunda idan ba iyalin yayansa ba bashi da wanda zai bawa.

Dr. Auwal suna hira da matarsa yake ce mata "na kula yaron nan Dahiru yana da kwazo kuma babu kyuya"

"Kai kuwa yaji kudi in maka ta Qareeba tace ahirin" tayi dariya.

Ido ya zaro "Dubu ashirin? Dubu ashirin za'a bashi?"

Dan turus tayi tana kallonsa "a'a fa Daddy maganar nan kai ka fadeta ranar da safe kace idan yazo ga abinda zan ce masa ni har inata mamaki ma"

Goshinsa ya shafa "gaskiya akwai matsala don wallahi subutar baki nayi. Ke a lokacin ai kya gyara min. Idan na bayar da yawa ya wuce dubu goma tunda nasan karatu zaiyi. Amma ke kin taba jin ana biyan dubu har ashirin a aikin shara banda abinki"

Cikin nuna rashin damuwa tace "ba wani damuwa bane. Idan wata ya kare sai a bashi abinda ya samu. Ga ci ga sha ko dubu biyar ka bashi ai ya gode"

Dr. Auwal ya dan fi matarsa sassauci duk da harka indai ta hada da fitar kudi sam baya kaunarta.
"Zan bashi takwas dai nasan ya riga yasa rai. Amma sai anyi min hakuri zuwa next month saboda harkar sallah duk nayi kaf. Daga shi har sauran kowa yayi hakuri wani watan sai na hada musu duka. Ai kin basu sadakar nama ko"

Ta amsa da cewar ta bayar kowa ya sami mai yawa ba laifi.

Hirarsu suka cigaba suna tsara yadda zata kasance nan da 'yan kwanaki da BB zai zo ganin Qareeba. A yadda abin yayi musu dadi saboda matsuwar da sukayi tayi aure basa so a dauki wani dogon lokaci.
*****

Can kuma Gambo mai kai masu aiki birni ta shige gaba tare dasu Baba akan kai karar BB. Fadi take dole ne su mutunta kawunansu idan suna so wani ya mutunta su. Aikin da suke yi kansa su wuni aikin ruwa, girki, wanke kashi da fitsarin yara da sauran ayyukan wahala da karfi amma abin da ake basu baya taka kara ya karya kuma a haka ma gani ake anyi musu gagarumar alfarma. Duk ranar da ta kuskure ta bangarensu masu gida basa musu da sauki. Kwandala aka nema aka rasa su ake fara zargi. Amma idan reshen ya juya aka cutar dasu sai dai ace suyi hakuri saboda su talakawa ne.

Ofishin 'yan sanda na Bebeji suka fara zuwa daga nan aka turasu Kano. Bayan daukar bayanan korafi daga bakin Baba suka tattara komai aka mika kotu don yanzu ana kokarin ganin an kawo karshen wannan mummunar al'ada ta fyade.

Cikin sati guda komai ya kammala aka aikawa BB da shammaci har gida da taimakon adireshinsu da Gambo ta bayar.

A tsakar gidan Malam an taru ana shawarar neman lauya da yadda za'a tara kudin.

Malam ya ce da Mawadda "amaryata sai kin daure sosai kamar yadda kika faro a baya. Duk wata tsangwama da surutun da ake yi miki na fada miki bazai fito miki a jiki ba. Da farko na dauki kai karar nan kamar daukar wuka mu dabawa cikinmu ne. To amma yanzu ina ganin lokaci yayi da zamu tashi tsaye mu dena rufawa masu laifi irin wannan asiri saboda gudun surutu"

Iya tayi shewa "dama can saboda shawarata ce shiyasa kuka yi ta runtse ido ana nuna muku hanya. Zance ya riga ya baza duniya tunda 'yan garin nan suka sani. To me kuma ya rage sama da a bi mata hakkinta. Shegen yaro bakin mugu babu abinda yafi kona min rai kamar uban dukan da yayi mata banda karfin da ya sa mata"

Kowa yana ta tofa albarkacin bakinsa banda Ade. Ita dai wannan tone-tone a bainar jama'a ranta baya so ko kadan.

*****
Abu kamar wasa Haj Mara tana shan fruit salad maigadi yayi sallama. Aikin gidan da tayi ta cika bakin zata iya ya gagara ta nemo wata tsohuwa tana mata.

Kwada mata kira tayi ta leka taji me yake bukata. Jim kadan ta dawo da takarda ta mika mata.

Tana kashingide hankali a kwance ta bude. Taken takardar kawai ta karanta hannunta ya soma rawa ta tashi a gigice tayi sama inda ta baro wayarta tana chaji.

Alh Sule ta kira yana China kwanansa uku da tafiya. A can dare ne tuni yayi bacci tayi ta kira shiru. Kuka take bilhakki ta karance takardar tsaf.
Ga gumi ga hawaye ta sake saukowa tayi bangaren BB tana kwala masa kira tun kafin ta isa. Wani mahaukacin bugu take yiwa kofar.

"Babawo bude min kofar nan mun shiga uku"


Tsaki yaja ya taso ya bude. Abubuwan da suke damunsa da yawa Hajiya kuma zata kara masa da damuwarta.

Bai lura da yanayin da take ba yace "Hajiya akwai matsala fa"

Ta daure fuska a zatonta yasan da sammancin.
"Kasan da matsalar ka ki gaya min da wuri sai da na gani yanzu"

"Ni dai kawai kiyi hakuri tunda kin sani yanzu a aura min ita. Wallahi kwanakin nam tunaninta baya barina ko baccin kirki nayi"

Haushi ya bata "kaga idan ba kashe wannan gobarar akayi ba babu abinda zaisa Dr. Tani ta baka auren 'yarta."

Ya wani hade gira "wai kin zata da wannan doluwar nake Qarira take ko wa. Nifa gaskiya bata yi min ba ko kadan. Shekaranjiyan ma da na zauna a gidan kawai don kada ranki ya baci ne. Maganar Mawadda nake miki, Hajiya sonta nake da aure"

Yadda maganarsa ta kona mata rai bata san lokacin da ta kwashe shi da mari ba. Yana rike da kumatun ta harzuka ta soma fada tare da jifansa da takardar.

"Idan ma kaje kayi shaye-shayenka ne ai baka manta yadda ake karatu ba ko. Shashashan banza"

Ko a jikinsa da ya karanta. Sai ma cewa yayi ta taimaka masa a kashe case din tun kafin aje kotu ta hanyar aura masa Mawadda.

Magana take son yi amma ta rasa abin cewa. Ta ga alama Babawo so yake ya kasheta da ranta. Fita tayi tana kuka ta koma dakinta tana sake gwada kiran Alh Sule amma shiru. Sai daga baya ta tuna lokacin ta tura masa sakon text.

Da safe haka ta tashi sukuku. Da wa zatayi shawara kuma meye mafita? Sauran yaranta ta nema amma duka tayi musu karyar sharri Mawadda ta yiwa BB kamar yadda ta fadawa 'yan uwanta da na mijinta sai dai kadan cikinsu ne suka yarda saboda sun san waye BB. Dole ta yiwa tufkar hanci kafin mutumcinsu ya zube.

*****

Yau kwana biyar kenan Dahiru da sauran ma'aikatan gidan suna jiran albashi. Inna da kanta tazo gidan Bilya ta sanar dashi su Mawadda zasu shiga kotu. Ta kuma dage akan cewa indai suka shiga kotun nan to wajibi ya manta da wata maganar aure. Ita a ganinta ba gara ma surutun Ummiyo iyakarsa kauyensu ba. Amma yanzu kila har a In Da Ranka sai an fada.

Shima dai hankalinsa ya tashi baya maraba da wannan terere. Gashi bata da waya ko magana da sunyi. Albashinsa yake jira ya tafi gida ko kwana biyu ne yayi. Ya gama daidaitawa da wani mai shagon waya a kusa da garejin su Bilya ya sami 'yar karama second hand da zai kaiwa Mawadda. Ga gwanjo da zai saya saboda sun kusa fara lacca. Sannan ma dai nauyinsa dake wuyan Bilya da gorin da Furaira take yi masa yasa ya kuma matsuwa da kudin. A kalla ko cefane zai rage masa ya bashi wani abin.

Yana ta hamma Kuku ta fito da abincinsa da na maigadi. Sun dan taba barkwanci sannan Maigadin yace

"Ni kuwa baki ji komai game da albashinmu ba? Yarona aka koro daga makaranta kayansa sun lalace. Kinsan halin maza gwiwar duk ta fashe. Bana son bashi tunda wata ya riga ya kare nace ya zauna ayi albashi tukunna."

Mikawa Dahiru kwanukan tayi shima hankalinsa yana kan zancen.

"Shekaranjiya bayan bakon nan na Qareeba ya tafi naje na tambayi Hajiya saboda nima ina da bukatarsu. Shine tace wai muyi hakuri maigidan bashi da halin biyanmu yanzu saboda shidimar sallah da akayi, sai mu jira wani watan a hada mana duka"

Hankalin maigadi ya tashi tsaye na Dahiru ya tashi sama. Abincin fice masa yayi daga rai ya rasa inda zaisa ransa yaji dadi. Ya dogara da kudin nan sosai. Bai gama fita daga wannan tashin hankalin ba Safwan ya leko yace masa ya shigo falo Mummy na kira.

A sanyaye ya tashi yabi bayansa. Hadadden falo ne da bai taba shiga irinsa ba.

"Daddy yace zaka je ganin gida karshen wata kunyi magana ko"

"Eh"

"Naji shiru baka tafi bane wani abin kake jira ko ka fasa?"

Ji yayi tambayar ma kamar wani rainin hankali.
"Dama albashi..."

Tayi dan murmshi "au ashe fa ban sanar daku ba. Albashi dai sai wani watan yanzu babu kudi. Sannan dubu takwas za'a baka"

Da sauri ya dago kai suka hada ido sai kuma ya sunkuyar da nasa. Dubu takwas din ma kudi ce kuma bai raina ba amma me zaisa su saka masa rai haka. Da dubu takwas anya zai iya rike Mawadda ga karatu? Ko dai ya sake neman wani aikin ne ya hada biyu?

Kallonsa tayi tsaf "kudin yayi kadan ne zaka fasa aikin?"

"A'a Allah Ya amfana. Gobe zan tafi in Allah Ya yarda." Tashi yayi kamar an zare masa laka ya fita ta bishi da dogon tsaki. Kasancewar kanin mijinta ne ya kawo shi yasa bata son shi ko kadan.
*****
Gari na wayewa ya gama shirinsa sai Tariwa. Abin takaici kudin mota ma Bilya ne ya bashi. Ganin Dahirun ya damu ya rinka bashi baki akan yayi hakuri neman halak da wuya. Haka nan ya kama hanya babu ko sisi sai kudin mota.

Iyayensa duk hakuri suka bashi akan rashin albashin. Allah Yaso shi ma baiyi gaggawar fada musu za'a bashi dubu ashirin ba da yaji kunya.

Rana na sanyi ya tafi gidan Mal Fatihu sai dai yayi rashin sa'a ba anan Mawadda take ba yanzu. Kaninta ne ya sanar dashi sannan yace ya jira Baba nason ganin shi.

"Mal Dahiru saukar yaushe? Ya ya Kano ya wurin aikin naka" Baba yace yana fitowa.

Kamar kullum a kunyace ya duka suka gaisa.

Baba ya soma magana "Mal Dahiru kaji maganar zuwa kotu ko?"

"Eh Baba Allah Ya bamu sa'a"

"To amin, amma na dakatar da kai ne saboda munyi magana jiya da Baffanku. Alal hakika idan na baka Mawadda na cuceka. Sannan mutane da dama basu goyi bayan karar da muka shigar ba. To amma bani da niyar janyewa. Yarinya an rabata da farinciki ya kamata ko yaya a kwatar mata hakkinta ta hanyar ganin an hukunta yaron nan"

"Amma Baba zamu iya daukar lauya ne?"

Bayani yayi masa cewa kotu ta basu lauyan gwamnati da zai waklicesu saboda haka kudaden da zasu biya babu yawa sosai. Yanzu haka nan da kwana biyu za'a fara shari'a. Amma gobe zasu koma Kanon saboda likita da Mawadda za ta gani.

"Sauran magana nasan zakuyi da su Mal Isiyaku. Nagode sosai Allah Ya shi maka albarka. Mawadda tana tare da Sa'ade amma ba sai kaje ba. Ku fara magana a gida"

Gidan ya koma ya sami Inna ta tabbatar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login