Showing 9001 words to 12000 words out of 110071 words
azo ayi yunkurin kashesu har gida. Don har ranta ta yarda Hajiyan zata iya. Ko a garinsu da aka taba yiwa wata irin haka kowa tsanarta yayi bata mantawa ga kyama ita da iyaye. Karshe ma dai barin garin sukayi cikin dare.
Haj Mara ta karance ta tsaf tasan ta dana mata dafi zata rufa musu asiri. Kawarta daya ta fadawa wadda ta bata shawarar ta tattara ta kaita gida kafin mijinta ya dawo don ba karamin aikinsa bane yace sai Babawo ya aureta.
Haka ta tashi suka fita tana ta kukan rashin sanin abinyi. Waye zai kwatar mata 'yanci? Yaya rayuwarta zata kasance? Shin laifi ne don mutum yazo neman halak da guminsa saboda talauci???
A hanya ma haka ta sakata ta rufe fuska da habar hijabin wai kada a gane me ya sameta. Idan an matsa mata da tambaya tace faduwa tayi. Bata ma iya tankawa ba saboda azabar ciwon kai da fargabar haduwa da iyayenta.
*******
Kauyen Tariwa-Bebeji LG
Zaune yake a karkashin katuwar bishiyar kukar da take kusan a tsakiyar gonar mahaifinsa yana shan farau-farau ya hango kaninsa Danlami a guje har yana tuntube da fatanya garin sauri.
"Assha Danlami meye haka kake gudu kamar kaga kura?" Cewar Dahiru bayan ya dangwarar da tasar hannunsa ya taimaka masa ya mike tsaye.
Sai da ya gama kade farar jamfarsa da ta rine zuwa ruwan kasa saboda wahala da gumi sannan ya dubi yayansa yana murmushi.
"Albishirinka, amma dai muyita da wajewa zaka bani aron wannan yadin naka ruwan kasa da ka dinka da sallah karama idan zamu je Kano dasu Samaila kallon hawa"
Dahiru ya girgiza
"Sannu shugaban 'yan son banza, cha nake tare akayi mana dinkin"
"Amma dai kala daban ne ka sani. Nawa dashi naje kallon da karamar sallah yanzu ma sai na sake zuwa dashi saboda nemawa kai raini"
Dahiru yasan halin kaninsa sosai. Tunda ya fara wannan rokon tabbas labari mai dadi ya kawo masa. Murmushi ne ya subuce masa da zuciyarsa ta harbo jirgin inda ya kwasa a guje har yana kifar da sauran farau-farau dinsa. Danlami a tsorace ya bishi shima don yayi zaton ko macizan da suka addabi gonar ne wani ya fito.
Sai da suka isa wurin mutane Dahiru ya dan nutsu sai farinciki bayyane a fuskarsa.
"Su Danlami sai a dau na damo wannan sallar ma da naka kayan zaka je kallo. Mawadda ce tazo ko ko ba haka ba?"
Danlami ya danyi sakato yana kallonsa kafin ya buga tsaki "yanzu fa sai ka nemi raina min wayo kace jikinka ne ya baka ko? Soyayya manya, to munji labarin Lela Majanu ma ehee. Kuma Qur'anin Allah sai ka bani ko yau na raka ka tadi muga tsiya"
Ko kula shi Dahiru bai sake yi ba ya kara sauri yana dokin ganin sahibarsa Mawadda. Sai dai kuma dole ya bada kayan idan ba haka ba baya jin akwai wanda ya isa ya hana Danlami rakashi tadi. Zuwa zaiyi yayi ta zuba karshe ko gaisuwar kirki bazasu sami damar yi ba. Gashi daga shi har ita ba masu magana bane sosai bare su kore shi. Ba karamin raina shi Danlami yayi ba duk da akwai mace tsakaninsu sai dai akwain shakuwa mai karfi tsakaninsu.
Suna isa gida Innarsu tace ko yunwa ce ta dawo dashi saboda bai karya ba ya fita gona sakamakon ruwan da aka kwana ana yi. Abincinsa tasa kanwarsa mai bin Danlami ta kawo masa ya daga hannu alamun ta barshi.
"Wanka zanyi na fita Inna idan na dawo sai naci"
"Da rana tsaka gagal Dahiru ina zuwa haka ka bari yamma tayi mana"
"Sahibar kokon zuciyarsa ce ta dawo" cewar Danlami yana buga masa harara har lokacin fushin kayan da baya tunanin samu yake ga sallah babba saura kwana goma sha biyar.
Inna ta hau fara'a yau tasan Dahiru zai kwana farinciki. Shi kuwa kunya tasa bai iya cewa komai ba ya shige ya watsa ruwa. Shirt da wando ya zaro a kasan akwati ya saka ya fito fes rike da kanbas din da babban wansu mai aikin kanikanci a cikin Kano ya kawo masa da zai zo.
Yana sakawa ya fito Inna ta washe baki jajayen hakoranta suka bayyana "ka gaishe min da 'yar tawa kaji ko"
"To Inna, ko zan dan sami turaren nan na Baffa ko feshi daya ne kiyi min dan Allah"
"Ai ba sai ka roka ba Danlami miko masa kuma idan ka fesa sai na hadaka da Baffan"
Yana kunkuni ya kawo masa sai dai shima yayan nasa ya burgeshi sosai don yayi kyau. Tare suka fito sai da yayi alkawarin bashi kayan sannan ya barshi ya tafi shi kadai.
Sai da ya kusa zuwa gidan don har yana hangoshi sai kuma kunya ta kamashi. Me zaice mata idan ta fito? Garin yaya ma baiyi tunanin bari ta dan huta ba. Yana tsaye yana ta tunanin har aka soma kiraye kirayen la'asar. Dayake da alwalarsa can gefen bishiyar da aka zagaye da duwatsu yaje sukayi sallah harda babanta wanda yace ya karaso mana zai tura a kirawota. Shi dai Dahiru kunya tasa yayi ta lankwasa kai yana murmushi.
Mal Fatihu yayi murmushi shima "kai da ita kowa kunya zanga wannan zama naku Dahiru. Yanzu dai idan ka koma gida ka sanar da Malam yazo muyi maganar bikin nan don bana jin zan bari ta koma birnin nan gaba daya. Gidan aikin nata sunce tafiya zasuyi na wata uku babu kowa a gidan, dama kuma lokacin ai ya matso duka duka bana jin zai kai wata ukun ma a gaba"
[03/12 23:02] Meela Adeel: *GUMIN HALAK...*馃挵4
*Batul Mamman*馃挅
Kunya irin wadda basa jin sun taba ji a rayuwarsu ce ta saukarwa Baba da Yaya. Ade kuwa ko juyawa batayi ba ta yunkura zata kamo hannun Mawadda ta yanke jiki saura kadan ta fadi Baba yayi saurin tareta. A daddafe ta matsa jikin gadon duba marasa lafiyan sai kuka ya kwace mata. Kuka take bilhakki na tausayin Mawadda, na bakincikin yadda rayuwa take gara talaka sannan uwa uba ganin tamkar laifinsu ne ita da Baba da suka bar 'yarsu ta tafi aiki.
Shi dai Baffan Dahiru kunya yaji da suka biyo bayansu gashi sun samesu a wani yanayi da babu mai son a ritsa shi a cikinsa.
Likita ganin yadda jikkunansu suka yi sanyi yasa shi sake cewa suna bukatar dan sanda a gaggauta zuwa kiransu domin su sami damar bawa Mawadda kulawa.
Dahiru kallo daya ya yiwa Mawadda daga inda take rakube akan gadon ta rirrike karfen kamar ta shige cikin bango ya dauke kansa. Zuciyarsa ke wani irin harbawa saboda yadda ya ga fuskarta. Wani daci ya soma ji a wuyansa yayi saurin juyawa zai bar wurin.
Inna duk ta rikice itama ta dakatar da shi "ina kuma zaka tafi?"
Bai kalleta ba sai kallon Baba da yayi "zan je kiran 'yan sandan ne"
Baba yayi saurin fitowa "muje dama tafiya zanyi yanzu"
Fita suka yi tare aka bar sauran da kallon kallo a gefe kuma uwa da 'ya suna kuka mai ban tausayi.
Tafiyar kurame ce tsakanin Baba da Dahiru har suka sami mashin biyu suka hau. Ofishin 'yan sanda mafi kusa suka sauka kowa tunani ya baibaye zuciyarsa.
Da suka shiga 'yan sanda biyu ne a wurin karbar korafi. Daya yana ta sakace hakora ya gama cin tsire dayan kuma gyangyadi yake yi akan wani benci. Sallamarsu ma basa su ji an amsa ba.
Baba ya matsa jikin kantar ya tsaya yana duban mai sakace "yallabai barka da yamma"
Suturar jikinsu kadai ta tabbatarwa jami'in tsaron cewa da wuya wani korafin kirki ya kawosu da ya wuce na satar su akuya ko rikicin iyakar gona. Duk su zo suyi ta damun mutane da yamman nan talauci yayi yawa kowa zuciya a sama. Bai amsa shi ba sai kai da ya gyada alamun yana sauraron shi.
Dan rissina kai yayi duk kuwa da cewa mutumin ko baiyi da dashi ba to lallai kaninsa ne na can baya ya dan rage sautin murya a kunyace ya soma magana
"daga asibiti muke mun kai yarinya ance sai mun zo da dan sanda za'a duba ta"
Tsinken ya ajiye sannan ya gyara zaman hularsa duk cikin nawa da nuna halin ko in kula da damuwar da ba tasu ba "to kai dattijo da baka san lalurar da sai anje damu da wadda ba sai munje ba?"
Dahiru zuciyarsa ta fara tafasa dama ya lafiyar kura ransa a bace yake tun dazu ga wannan mutumin yana musu magana a wulakance. Kafin yayi magana Baba ya cigaba
"Yarinyata ce aka yiwa fyade.." ya karashe kalmar a hankali saboda kunya.
"Babbar magana kai Nalado tashi wannan aikinka ne. Ka bisu asibitin bayan na gama daukar bayanansu."
Lalube ya soma yi a aljihu wai yana neman biro. Can dai ya tambayi wanda ya kira Nalado shima yace babu. Suna ta dibi-dibi duk su biyun wayar Dahiru ta soma kara. Ganin sunan mahaifinsa yasa shi tsorata ya kara a kunnensa da sauri.
"Dahiru kuyi sauri jikinta yayi mugun zafi har tana sambatu. Likitan ya taimaka zai saka mata ruwa"
Da yake waya ce techno mai dan karen kara Baba ya gama ji. Hankalinsa gabadaya ya tashi Dahiru ya tambayi dan sandan biro kadai ne babu yace eh babu ko kunya. Fita yayi yana gudu ya rasa wace hanya zai bi ya sami kantin da zai sayi biro. Daga can tsallake ya hango wani shago da ledojin ruwa, daga kafar da zaiyi takalminsa ya tsinke ya fadi fuska a kasa saboda da hanzari ya motsa. Ko kulawa baiyi ba ya tashi yana kade jikinsa zaiyi gaba wata mota fara kirar marsandi tazo tayi pakin a gefensa tare da buga hon. Abin mamaki sai ga 'yan sanda kusan bakwai sun fito daga cikin ofishin wanda tun dazu yake tsit sai mutum biyun da suka gani.
Duk wurin motar suka nufo DPO dinsu ya fito daga ciki. Yana kallon Dahiru yace wannan fa sai ga Bala wanda yace babu biro ya yo gaba da sauri.
"Yallabai yanzu zan dauki bayanansu. Case din fyade ne zamu je asibitin. Bawan Allah koma ciki muyi sauri"
Baba da Dahiru suka saki baki wato wulakancin da gangan aka yi musu ko don an ga basuyi kama da masu arziki ba.
Kamar yadda ta basu labari haka Baba ya labartawa Bala suka dunguma har Nalado suka bisu asibitin saboda ganin idon DPO da baya wasa da aiki.
Da isarsu ba bata lokaci aka gama abinda za'ayi suka shige da Mawadda wani dakin daban. Iyayen maza sunyi jigum matan na kuka. Inna kuwa hakuri kawai take basu lokaci-lokaci sai ta kallo Dahiru. Sam ta kasa gane a wane hali yake ciki. Shi kadai yasan yadda yake ji a ransa sakamakon wannan tashin hankali.
Su sergent Bala suna jira a fito da ita idan zata iya magana tayi musu bayani sosai idan bazata iya ba su dawo washegari.
Kusan minti arba'in suka dauka kafin likitan da nos suka fito.
"Ina mahaifiyarta" cewar likitan yana binsu daya bayan daya.
Ade tayi saurin nuna Yaya duk da har kasan ranta a matse take taji me yasa ake neman mahaifiya.
Ajiyar zuciya likitan yayi "ki shiga wurinta ko zamu samu ta dena kukan nan don mutum daya nake bukata a dakin. Sannan gaskiya kunyi sakaci wannan abu ya wuce kwana uku ga dukkan alamu ciwo yana neman zame mata wani abu daban. Sauran bayani Baba muje nayi maka"
Yaya da Ade suna kallon juna kowacce na son tafiya wurin Mawadda. Inna tana kula dasu duk suka bata tausayi. Wannan bakar ranar kada Allah Ya nuna min ta fada a zuci.
Yaya da sanin ya kamata ta nemi wuri akan bencin da yake jingine da bango ta zauna "Sa'ade jeki ki rarrasar min ita tun jiya nake fama taki shiru"
Allah sarki dama a dofane take da sauri tayi gaba tana share hawaye.
Mawadda tana kwance tana hawaye taji an turo kofar dakin tana kara keyyyy ba karamin tsoro hakan ya bata ba. Tuna mata yayi da lokacin da BB ya shigar da ita dakinta na gidansu ya kulle. A firgice take gabadaya har Ade ta karasa gaban gadon.
"Ade..."
"Shhhh kukan ya isa haka."
"Gwara in mutu da wannan ..."
"Kada na sake jin kina zancen mutuwa. Shikenan kuma saboda Allah Ya dora miki jarabawa sai ki karaya lokaci guda? Tunda kukan bazai amfana mana komai ba ki daure babu abinda muke bukata yanzu sai samun lafiyarki"
Shiru tayi tana wata irin ajiyar zuciya mai karfi. Cikin dan kankanin lokaci bacci ya soma fizgarta kanta na cinyar Ade. Dama likitan ya sa anyi mata allurar bacci.
Ko minti goma bata cika ba ta tashi a gigice harda ture Ade don ta manta waye a gurin tayi waje. Allurar jikinta ta karin ruwa ta cizge harta ji mata ciwo ga jini yana diga. Mafarkin BB take yi yana kokarin danneta. Jikinta har tsuma yake yi lokacin da taci karo da Dahiru ya dawo daga siyo musu ruwan alwala saboda gabatowar magariba. Su Yaya duk sunyi kanta ana kokarin hanata fita.
A can ofishin likita ya yiwa yan sanda bayanin su dawo washegari saboda bata cikin hayyacinta sosai. Bayan fitarsu ya soma yiwa Baba fadan kai yara aikatau da suke yi.
Baba yayi murmushi mai ciwo yana da bayanai da yake son yiwa likitan akan matsalarsu amma yanzu ba muhallin hakan bane. Likita ya cigaba da yi masa bayanin cewa ciwukan jikinta sun basu dukkan wani taimako da ya dace. Babbar matsalar shine tabon da aka yiwa zuciyarta sai sunyi hakuri kuma sai an daure. Yanzu bazasu gane girman abin ba sai taji saukin ciwukan jikinta.
Suna wannan tattaunawar ne suka jiyo ihunta. Tare suka fito da sauri tana neman fita Dahiru ya saki ledojin hannunsa ya kamota. Jin namiji ya tabata ta sandare cikin murya mai ban tausayi tace
"ka rufa min asiri BB ni ba 'yar iska bace aure za'ayi min. Kayi hakuri don Allah"
Dahiru bai san lokacin da hawaye suka zubo masa ba a yayin da Ade da Yaya suka rikota suna ta koke koke. Baffa da Inna ma abin yayi matukar shigarsu suna kallo aka mayar da ita dakin.
Ba su suka sami kanta ba sai bayan isha da aka kara mata wata allurar da magunguna bacci mai mugun nauyi yayi awon gaba da ita. Sai a lokacin suka fara batun tafiya.
Baba yace Ade tazo su tafi don yasan zuwa yanzu Iya ta sami labarin zuwanta gari gashi bata je gida ba. Shima nasa iyayen dole zasu ji daga wurinta da kuma yara da suka tura musu daga makarantar allo su zo su tada hankalin rashin sanin me yake faruwa.
Ba don taso ba sai don kara da kawaici ta bisu suka tafi.
Su Inna gida suka wuce da Dahiru yayin da Baba da Baffa suka tsaya yana yi masa bayanin yadda abin ya faru. Ade har tayi hanyar gidansu wanda iyayen Mal Fatihu da Iyarta suke ciki tare sai ta fasa. Gidan Mal Isiyaku ta wuce kai tsaye.
Ummiyo ce ta amsa mata sallama Inna ta zaga bayi. Tana fitowa tayi arba da Ade a tsakar gida tace ta shigo cikin rumfa. Dahiru yana bayansu duhu yasa basu ganshi ba. Zai shiga kawai ya ga Ade ta durkusa a kasa gaban Inna tana kuka sosai.
"Don darajar Al'Qur'ani da iyaye Innar Dahiru ki rufawa yarinyar nan asiri. Na sani maganar aure da Dahiru ko ba'a fada ba ta tashi kamar yadda nasan da wuya wani ya taba aurenta. Amma ki taimakeni ko don kada zaman garin nan ya gagaremu don Allah ki rufa mana asiri"
"Haba Sa'ade sai kace wata bare? Wannan magana nayi miki rantsuwar duk ranar da kika ji ta a waje to daga bakin wani ta fito ba ni ba. Bazan taba fadawa kowa an yiwa Mawadda fyade ba. Kinga ai bamu ma san takamaimai me ya faru ba"
Dahiru ja da baya yayi har wani jiri yake ji. Tausayi sosai Ade ta bashi. Motsin da yaji a bayansa yasa shi juyawa ko ma waye ya gudu kafin ya waigo.
Har Ade ta fito tana ta yi mata godiya. Ita dai Inna bata da niyar tozartasu amma taji dadin da kafin magana tayi nisa Ade ta gane cewa batun auren nan a barshi kawai.
****
Kusan tare Ade da Baba suka shiga gidan iyayen nasu. Iya tana daga dakin farko idan an shiga wani soro sai 'yan tumakinta. Daga soro na biyu kuma tsakar gidan iyayen Mal Fatihu ne wato wa ga Iya. Rashin jituwa da dangin miji bayan rasuwarsa yasa ta dawo gidan.
Suna sallama Innar Fatihu da Malam babansa da Iya suka taso suna tararsu da tambayoyi.
Malam yace "kun daga mana hankali yara tun dazu sun zo sun ce Mawadda ba lafiya. Tana ina yanzu? Yaushe ta dawo garin ma duka bamu da labari?"
Iya kuwa harara ta dokawa Ade "wani sabon salon kinibibin ne kika shigo garin nan sai a bakin jama'a naji wai kin fara biyawa gidan tsohon mijinki."
Baba na gaisheta kamar yadda ta saba tun rabuwarsa da Ade ta juya masa keya harda tura dankwali gaba.
Innar Fatihu ta tabe baki "ke kam zan ga lokacin da zaki girma, yaro na gaisheki kina juya keya abu duk a gwaguye"
Sanin cewa yanzu zasu fara rigima Malam ya tsawatar "bana son shirme, ance yarinya ba lafiya baku tambayi halin da take ciki ba sai rigimarku da bata karewa. Sa'ade ina kuka barota?"
Daga ita har Baba duka jikinsu a sabule ga idanunta a kumbure saboda kukan da bata san adadinsa ba a yau.
Baba ne yace duka su zauna magana mai mahimmanci zasu yi. Jin haka Iya ta kwala ihu harda zaman 'yan bori ta soma kuka haikan tana fyatar majina.
"Ni Tarasulu me zan gani, wayyo Allah mun shiga uku mun lalace."
Ade ta bata rai ganin wannan abu da mahaifiyarta take yi "Iya meye haka kuma don Allah?"
Sake fyace hanci tayi sannan ta dago "cha nake ta cika ne, na ga ke da Fatihun kamar kwai ya fashe muku a ciki gashi yace magana ce mai mahimmanci"
Malam ya girgiza kai cike da takaici.
"Fatihu ina jin ka kaji"
Kai a kasa Baba ya soma labarta musu abinda ya sami Mawadda. Kafin ya kai karshe Iya ta mike tana kumfar baka zani na neman faduwa tana kamo shi
"Qur'anin Allah Fatihu baku isa ba...tabdi yo ni na taba jin danyen aiki irin wannan ma. 'Ya'yan Haule sunje sunyi aikatau dinnan kowacce ta kai mutumci gidan miji sai tawa jikar saboda ka tsani uwarta. Idan ma wata manakisa kuka shirya ku kwance don billahillazi bazan yarda