Showing 57001 words to 60000 words out of 153671 words
Chapter 20 - GA IRINTA NAN Hausa Novels By Binta Umar Abbale.txt
so taje inda take...Khalid yayi gaggawar daukarta yana rarrashin ta hawayen tausayi na nema ya kufce masa..
Da yake sun shiga cikin gari yasa basu sha wata wahala ba mazauna gurin suka kawo musu dauki 'yan agaji suka shiga cikin ramin suka fito da mutumin a mace duk ya karkarye, da yawa daga cikin mutanan gurin sai da suka tsorata da wannan tashin hankali masu rauni a ciki suka dinga faduwa suna suma wasu kuwa gefe suke nema su zauna suyi ta share hawaye suna kad'aita Allah shi d'aya.
Khalid wata irin nadama mai tsanani ta rufe shi ya dinga jin kamar ya juya ya koma gida ya nemi gafarar iyayensa da wacce ya zalin ta yanzu idan da 'karar kwana da tuni shima ya zama tarihi ya mutu da fushin iyaye a tare dashi.
Jakar mutumin aka duba akayi sa'ar samun wallet dinsa nan Suka shiga binkicen in da yake a jikin IDcard d'insa aka samu cikakken address dinsa da inda yake aiki. Mutumin dai dan kano ne kuma yana aiki asibitin Koroda dake karkashin gomnati. ba tare da 'bata lokaci ba jami'an tsaron dake gurin suka shiga aikinsu Gawarwakin aka d'aure suka sa a mota suka dauki hanya Khalid ya dinga jin kamar ya tsayar dasu ya bisu ya koma gida suna tsaye a gurin har motar Police din ta 'bacewa ganinsu kafin su koma cikin motar ko wanne da mataccan jiki motar tayi tsit! shima direban duk da ya saba ganin tashin hankali irin wannan amma gaskiya wannan karon ya firgita mutuka jiki a mace ya shiga ya zauna ya kunna motar suka bar gurin...
*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA GUDA BIYU*
*FATIMA MUSA (MOMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
_*Ina kaunar ku iyayena ina kuma alfahari da irin kaunar da kuke nuna minππ₯°*_
*37&38*
Khalid da Salmanu sun sha matukar wahala kafin wani bayerabe ya tausaya musu ya basu gurin kwana a jikin gidansa, tunda suka sauka a garin suke buge-buge a kasuwanni domin su samu abinda zasu ci idan dare yayi su shiga 'kar'kashin gada su kwanta asuba nayi suke futowa daga karkashin gadar suyi sallah su shiga buge-buge kamar yanda suka saba Akande beyerabe ne kullum yana ganinsu a kasuwa suna bulayi da daukar dako sai ya tausaya musu ya dinga jansu a jikinsa yana nuna musu gurin da zasu shiga su samu aiki cikin ikon Allah kuwa suka kutsa cikin kasuwar su shiga cikin kanikawa masu gyaran abubuwan hawa suka fara taimaka musu da yake duk yawanci masu aiki a gurin 'yan jahar kano ne shiyasa suka saki jikinsu dasu suka basu gurin zama suna nuna musu yanda zasuyi sati hudu sun zama 'yan gari domin gyaran mota kona babur babu wanda basu iya ba.
Idan sun tashi daga aiki sai su nufi shagon da suke kwana wanda yake jikin gidan Akande, watansu biyu a legos suka siyi waya Khalid yasa Sim card dinsa a wayar shi kuwa Salmanu sai da ya siyi wani akai masa rigistar Allah yasa yana da number wayar mahaifiyarsa saboda haka kai tsaye ita ya fara kira.
Khalid kuwa babu wanda yayi tunanin kira sai aunty shi domin kullum da ita yake kwana a cikin ransa zuciyarsa na fada masa cewa ta riga tayi auranta fa sai dai ka hakura duk sanda zuciyarsa tayi masa wannan tunin yini yake cikin damuwa da bakin kishi.
Muna tare da Hauwwa a gidanta mai lalle nayi min na biki kiran wayar tashi ya shigo waya ta a lokacin da naga sunansa yana yawo a fuskar waya ta sai da na zabura! mai lallen tayi saurin rike kafata nace."Dan saurara na amsa waya.
Kafata ta saki na kalli Hauwwa a sanyaye nace."Khalid ne."? Baki ta bude da sauri tace."Ikon Allah dama yana raye a duniya.?
Hannu na daga mata nasa wayar a kunnena.
sanyayyar ajiyar zuciyarsa naji a kunnena kafin naji sautin muryarsa yana kiran sunana.
Na amsa a nutse da fad'in "Khalid tsayin wattanin hudu kana ina ne? shin kasan halin damuwar ka jefe iyayen ka a ciki kuwa? Uwa uba Gwaggo na nan ta'ki lafiya kullum sai tayi kuka kafin ta kwanta bacci tana ganin kamar baka raye a duniya dan Allah ka dawo gida ni idan saboda ni ka tafi to ka dawo na yafe maka.''
A sanyaye yace." Aunty Sa'ida idan na dawo gida zaki aure ni."? Gabana ya fad'i nace."Khalid ashe har yau baka daina wannan tatsuniyar ba."?
Ransa ya 'baci yace."Ki daina kiran soyayyata da ta tsuniya insha Allahu sai ta zama gaske."
Nace."Okey to naji yanzu dai yaushe zaka dawo gida."? Yace."Kina so na dawo ne."? Nace."Eh ka dawo ka nemi afuwar iyayenka ni kuma na yafe maka."
Yace."Aunt Sa'ida idan na dawo gida zan takura miki fa." Nace."Khalid na amince zan aureka ka dawo gida."
Da sauri yace."Da gaske kike.''? Ajiyar zuciya na sauke cikin yaudara nace "Eh da gaske nake kana dawowa za'a daura aure."
Yana dariyar farin ciki yace."Okey ki bani Gwaggo mu gaisa insha Allahu zan dawo gida a satin nan.
Nace."To yanzu dai bana gida ina gidan 'kawata Hauwwa insha Allahu idan na koma gida zan kira ka sai ku gaisa."
Yace."Nagode auntyna insha Allahu zakiyi alfaharin aurena zan jiyar dake dadin duniya auntyna zan kula dake zan zama bawanki zan kwanta ki taka ni zan zama d'an aiken ki zan......Katse shi nayi nace."To duk naji na kuma gamsu da maganarka Ka bari idan ka dawo sai ka 'karasa.
Yar dariya yayi yace."Okey to shikkenan zan kira anjima idan kin koma gida." Ina kokarin kashe wayar nace"babu damuwa.
Hauwwa ta zuba min ido tana kallona tace."Sa'ida babu kyau yaudara fa ban so kikayi masa haka ba ya za'ayi kice zaki aureshi bayan kin san gobe daurin auranki."?
A sanyaye nace."Hauwwa ni nasan halin Khalid idan ba haka nai masa ba wallahi ba zai dawo ba ga Gwaggo taki kwantar da hankalinta dan har fargaba nake na tafi na barta cikin halin damuwa kullum da daddare sai na lalla'bata take bacci.'
Hauwwa tace."To yanzu idan yazo ya tarar kinyi aure fa wane hali kike so ya shiga."?
Kai tsaye nace."Sai yayi hakuri ya kaddara cewa ni d'in ba matarsa bace."
Hauwwa tace." A gaskiya da kamar wuya ya iya wannan hakurin dan yaron yana miki mahaukacin so." Nace."To hauwwa idan ba zai yi hakuri ba sai yayi abinda zaiyi." ta bini da kallon mamaki! na Kalli mai kunshin nace."Baiwar Allah ki cigaba." Ta kama kafata da sauri ta cigaba da akinta.
Khalid cike da farin ciki yake shedawa abokinsa Salmanu abinda ke faruwa. Salmanu na washe baki yace."Kai amma naji dadi wallahi to yanzu ya za'ayi naji kace a cikin wannan satin zaka tafi kuma gashi zamu fara buga wasa a Club kasan kana da mutukar mahimmanci a 'kungiyar nan ko zaka bari mu gama wasan in yaso wani satin sai ka tafi."
Girgixa kansa yayi yace."Salmanu hankalina gabadaya yayi gida wallahi kafin na tafi zan nemi shugaban kungiyar na fada masa uziri na idan za'a d'aga wasan nan da sati uku sai ayi min uziri idan kuma yana ganin da akwai wanda zai kawo a madadi na sai ya kawo dan gaskiya babu abinda zai hana ni tafiya gida.
Salmanu jikinsa yayi sanyi sam baya so abokin nasa ya tafi yana ganin kamar damar da suka samu zata iya kufcewa gashi ogan nasu kullum sukaje training yakan fad'a musu cewa yana so su mayar da hankali sosai domin a wannan karon ne yake so ya za'bi za'kwa'kurai a cikinsu da zasuje america su buga wasa to
wannan dalilin yasa gabad'aya Salmanu baya so a bokin nasa ya tafi domin jikinsa na bashi kamar zasu samu nasara.
Khalid yace."Tashi ma muje chamber d'in Allah yasa mu sameshi." Salmanu ya mike yana kokarin cire kayan jikinsa ya sanja wasu.
Sun ci sa'a sun sameshi yana horar da wasu suka samu kujeru suka zauna bayan sun gaisa....Oga Labaran yace."Khalid me yasa yau baku shigo da wuri ba."?
Yace."Wallahi oga mun je gurin aiki ne kasan dama sai da mukayi maka bayani cewa asabar da lahadi ba zamu dinga zuwa da wuri ba saboda muna zuwa gurin aiki da wuri.
Oga Labaran yace."Eh hakane na manta da wannan bayanin dama inaso kuzo mu tattauna ina fata dai kuna cigaba da shirye-shirye kamar dai yanda na fada muku cewa Mr William zai zo a ranar da zamu buga wasa na k'arshe kuma a ranar za'a za'bi muzakkarai a cikinku domin kuje ku fatata da 'yan wasan dake can america.
Khalid yace."Oga sai da ni ayi min uziri wallahi cikin satin nan nake so naje ganin gida."
Oga Labaran da sauri ya kalleshi cikin yanayi na damuwa yace."Khalid me yasa zakayi mana haka? kana fa d'aya daga cikin 'yan wasan da nake alfahari dasu, ka iya buga 'kwallo sosai shiyasa nake so kai ka zama zakaran gwajin dafi nasan ko munje america ba zaka bani kunya ba sai kuma kazo min da wannan maganar.""
Yace."Oga wallahi uziri babba ne zai kai ni gida ayi min alfarma." Oga Labaran ya girgixa kansa da fad'in "Khalid dole fa kayi hakuri domin ba zaka sa nayi asara ba ka bari muyi wasan nan mu gama lafiya a za'bi wanda suka dace ayi dasu in yaso sai ka tafi kafin lokacin tafiya american ya tashi."
Khalid yayi shuru tare da sunkuyar da kansa tunani yake akan lamarin.....Yana son aunty Sa'ida baya so ta kufce masa gefe guda kuma ga wata babbar dama ta same shi wacce yake saka ran samun nasara wai shin ya zaiyi ne?
Oga Labaran ya kalleshi da fad'in "Khalid kayi shuru kada fa ka bani kunya khalid."
Ya dago kansa da fad'in "Oga zanyi nazari akan al'amarin insha Allahu kafin lokacin zan yanke shawara." Yace."To shikkenan Allah yasa naji alkairi."
Har sun miqe da niyyar tafiya ya hana su yace su sanya kaya suyi wasa. ba tare da 'bata lokaci ba suka bi umarninsa suka shiga d'akin da suke shiryawa suka sako kayan kwallo suka fito kai tsaye filin wasa suka nufa su shiga shiga cikin 'yan uwansu Oga Labaran ya mike yana zagaye gurin tare da addua akan Allah ya daukaka 'kungiyarsa ta Kano pillas.
****
Ina komawa gida na fad'awa Gwaggo cewa Khalid ya kira waya sai ta kwantar da hankalinta yana raye bai mutu ba, ba tare da tace min komai ba naga ta mike ta dauki buta ta fita, alwala ta dauro ta dawo dakin ta gyara dadduma ta tayar da sallah, ina zaune ina kallonta tayi raka biyu ta jima a sujjadar karshe tana addua kafin ta dago....ko bayan da tayi sallama ma sai da ta daga hannu sama ta dinga godewa Allah tana share hawaye.....na cika da d'umbin mamakin irin kaunar da takewa yaron
Mi'kewa tayi ta fita daga dakin minti uku suka dawo tare da Ummatu tana washe min baki tace."Sa'ida ashe Khalid ya kira ki a waya ko."? Nace."Eh wallahi d'azu da rana mun jima muna waya har yace yana so yayi magana daku nace ya bari na koma gida.
Gwaggo tace"Dan Allah ki kirasa 'yar albarka so nake naji miryarsa.
Nace."Gwaggo babu kudi a waya ta bari a samu yaro ya siyo kati.'' Da sauri Ummatu tace"Ga dari biyu a siyo katin." kokarin kwance bakin zaninta take nace"Haba dai bari ba sai kin bada kudi ba bari na duba yaro." Gwaggo tace."Sa'ida na dauka gurin siyar da katin babu nisa inace gurin Auwala ne." Nace."Eh tace."To bani na siyo da kaina." kallonta nayi naga duk ta tashi hankalinta na koma na zauna bakin gado ina gwada siyan kati ta banki babu network ko kad'an na mika mata kudin ta yafa mayafi da sauri ta fita.
Ummatu kuwa tsayawa tayi tana jana da hira na dinga mamakin matar ta saki jikinta dani a yanzu ta daina jin haushina kullum kuma na gaisheta da sauri take amsawa komeye dalili oho.
Gwaggo ta dawo gidan da katin mtn a hannunta da sauri na kar'ba nasa a wayar.......Muryar wani mutum naji a kunne na. nace."Dan Allah Khalid fa."? Yace."A yanzu dai suna filin wasa sai dai idan sun fito." ko kafin nace komai ya kashe wayar.
Gwaggo a sanyaye tace."Ya akayi."? Nace."Wani mutum ne ya dauki wayar yake cewa wai khalid din yana filin wasa.
Gwaggo da Ummatu suka had'a baki gurin fad'in "Ina ne kuma filin wasa."? Nace"Watakila gurin ball yake nufi kun san dama Khalid akwai naci ball a lokacin da yake gida.
Gwaggo tace."Eh hakane kuwa to an jima sai a sake kiran wayar. shuru nayi ina duba waya ta Ummatu tace." To bari naje na karasa ayyukana."Gwaggo tace."To shikkenan daga zarar wayar ta shiga zan fito na fada miki." Ummatu tace to shikkenan a yayin da take kokarin barin gurin.
Kallonta nayi a nutse nace."Gwaggo a yau da daddare nake so naje gidan Ummana nayi sallama da ita." Gwaggo tace."Ba zaki bari ba gobe idan za'a kai ki dakin ki sai na raka ki." Nace."Aa Gwaggo gwara naje yau din." Tace."To shikkenan Sa'ida ai ni ban ta'ba ganin biki irin naki ba sam baiyi farin jini ba.
Nace"Saboda me kike ce haka."? Tace."Ai gani nayi gidan nan yaki cika da mutane makota ne kawai suke shigowa a tsaitsaye suyi Allah ya sanya alkairi su fita."
Nace."Gwaggo wannan kuma kanki zaki tuhuma ina dangin suke."? Tace." Sa'ida kenan ai ni dangina duk sun mutu saura qalilan dama bamu da yawan zuria ko baki gani bane."?
Nace."Hakane amma ai Ummana tana taro a gidanta ita da 'yan uwanta'' Tace."Aikuwa mu dai sai gobe idan an daura aure zamuyi namu taron."
Shuru nayi tace."Dan Allah ki zauna a dakin mijinki lafiya tunda dai Allah ya had'aki da kishiya mai mutunci to ki 'ki ji ki 'ki gani babu ruwanki da 'yan bani na iya kada 'kawar data zugaki ki dauka.
Nace."Insha Allahu Gwaggo zan bawa mara d'a kunya." Tace."Allah ya sanya alkairi Ya bada zuria dayyu'ba." a zuciya na amsa da ameeen.
Dakin yayi shuru na minti biyu kafin tace."Sa'ida Alhaji Shamsu mutumin kirki ne kwarai duk hidimar kayan daki ya dauke ya hana Ibrahim siyan komai duk abinda kika gani a dakin ki to Alhaji Shamsu ne ya siya miki saboda haka ki rike shi da kyau kinji ko."
Nace."To Gwaggo insha Allahu.....Ta dauki goro ta gutsira tana taunawa tace."Oh! yau dai zanji muryar Khalid a kunnena wallahi ni kadai nasan halin damuwar da nake ciki akansa, gashi lokaci guda Allah ya amsa addua ta.
Nace."Gwaggo kin san wani abu."? Girgiza kanta tayi tana kallona, nace."Khalid nayi masa dubara kancewa ya idan ya dawo gida zan aureshi koda zaiyi miki maganar to ki nuna masa hakane.
Shuru tayi tana kallona kafin tace."Sa'ida me yasa kike yaudareshi gobe fa za'a daura miki aure."
Nace."Gwaggo Khalid fa idan ba haka akayi masa ba ba zai dawo gida ba zai bar zuciyoyinku cikin damuwa shiyasa nayi masa haka.
Shuru tayi na minti biyu kafin tace."To Allah ya sanyaya masa zuciyarsa idan ya dawo ya iske abinda ba shikkenan ba.
Nace."Ameeen ya rabbi sai ki zaunar dashi ki rarrashe shi ki nuna masa cewa samu da rashi duk na Allah ne idan yayi hakuri sai Allah ya bashi wacce ta fini.
Tace."Zanyi iyakacin bakin kokarina Sa'ida Allah ya sanya masa dangana." na amsa da ameeen ina kokarin fita daga dakin.
*Littafin na kudi ne....Kada ki siya ki fita dashi...idan kika ganshi a gruops kada kiyi sharing......Idan kika karanta baki biya ba na biki bashi.....Idan kina so ki biya kudin littafin ga yanda abin yake... Vip gruop#600 normal gruop#300...account.. 0542382124...Binta umar gtbank....Idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan numbers*
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*
*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*
*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*
*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.π₯°π€π»π_*
*39&40*
Sai daf da magariba Khalid suka fito daga filin wasa, hannunsa rike da karamin towel yana goge zufar dake jikinsa ya nemi guri ya zauna yana mayar da numfashi, Salmanu ya zauna kusa dashi shima da k'aramin towel din a hannunsa yana goge fuskarsa, Oga Labaran ya karaso gurin fuskarsa yawalce da fara'a yace."Khalid a gaskiya kana burgeni da kwazon ka babu shakka nan gaba kad'an za kayi fice a duniya zata san da zamanka."
Khalid murmushi kawai yayi ya kar'bi goran ruwan faro dake hannunsa ya bude ya sha ya mikawa Salmanu sauran. Oga Labaran ya mika masa wayarsa da fad'in "Kana filin wasa aka kira wayar ka ka duba ka gani.''
Da sauri ya kar'bi wayar yana dubawa ganin sunan auntynsa yasa shi sakin murmushi ya mike da sauri ya bar gurin, Salmanu ya bishi da kallo yana girgiza kansa.
Number ta ya shiga kira cikin zumud'i da bukatar son yaji muryarta.
Lokacin da ya kira wayar tana sallah Gwaggo kuma ta idar da tana jan carbi, da sauri ta dauko wayar tana dawurwura domin bata san inda zata ta'ba ba.
Sai kawai tasa wayar a kunnanta ta dinga zabga sallama tana fad'in " Halo Khalid kana jina ko? Halo Khalid nice Gwaggon ka nake magana." Da karfi take maganar gashi wayar sai 'kara take yi kafin kiran ya katse! ta shiga duba fuskar wayar tana surutai da fad'in "To ko dai babu nethook ne." Saura kad'an dariya ta su'bcewa Sa'ida da sauri ta kori shed'an ta cigaba da sallarta.
Gwaggo ta cigaba da surutai da fad'in "Babu shakka yaron nan ne ya kira waya amma saboda abin nasara bashi da tabbas yayi mana rashin mutunci.
Tana rufe bakinta wani kiran ya sake shigowa, da sauri tasa wayar a kunnanta ba tare da ta ta'ba wani guri ba Fad'i take."Halo Khalid kayi min magana mana nice Gwaggonka."
Ummatu dake gurin ta
17, October 2025
Fatima
Wow