Showing 6001 words to 9000 words out of 153671 words
Chapter 3 - GA IRINTA NAN Hausa Novels By Binta Umar Abbale.txt
na dauki wannan matakin." shuru tayi tana kallona, nasan mamakina take, dan na 'kara tsoratata nace" Yanzu ma bari na kira wani abokin aikina wanda d'an uwansa yake aiki a kotun musulunci ta kasuwa na fad'a masa dukkanin abinda yake faruwa." Da sauri ta rike hannuna tana kokarin kar'be wayar tace."Sa'ida ashe baki da hankali kina so ki tona mana asirin gida."
Nace." Wane irin zan tona asiri ai gaskiya ce idan munje gaban alkali sai kuyi bayani dake dashi wanda kike daurewa gindin."
Hannunta na rawa tace"Yi hakuri dan Allah abar kaza cikin gashinta domin hakan yafi mutunci zan samu Khalid din naja masa kunne ya daina ta'baki tunda dai ba'a d'aura aure ba."
Nace."Shin yanzu kin yarda da maganata akan Khalid din ko kuwa baki yarda ba."? Da sauri tace."Haba na yarda mana dama sabida kada maganar tayi tsayi ne yasa kikaji nace ban yarda ba amma nasan Khalid zai aikata kuma zanja masa kunne kiyi hakuri kinji ko."
Ajiyar zuciya na sauke nace"To wannan karon dai na hakura idan ya 'kara kwatantawa to zaiga abinda zai biyo baya." Tace."Bama zai 'kara ba insha Allahu.''
Mi'kewa nayi na fita daga dakin ina jin tana fad'in"Kizo ka abincin naki ai tuntuni na shigo miki dashi daki." Nace."Wanka zanyi tukkuna." Da sauri tace."To shikkenan sai kin fito." Bakin rijiya na nufa na cika bokiti da ruwa na dauka na kai bandakin, dakin na koma domin cire kayan jikina.
Bayan sallahr isha'i kasancewar ana zafi a gari gashi babu wuta sai mukayi shimfid'a a tsakar gida muna hira, Ya shigo gidan cikin rashin 'kwarin jiki ya zauna kusa da ita da fad'in "Wash Allah Gwaggo na gaji wallahi nayi mutukar galabaita."
Zaune ta mi'ke tana gyara daurin dankwalinta tace."Yaron kirki ina kaje ne kuma me kayi ka gaji kana yawo cikin ka babu komai ina fata dai ka samu wani abu kaci."?
Ajiyar zuciya ya sauke 'kasa-'kasa ya d'an kalli mutuniyar tasa kafin yace." Wallahi Gwaggo har yanzu banci abinci ba Yau Salim ne ya jani yawo cikin adaidaita sahunsa." Tace."Allah sarki to ina fata ka samo d'an kwabo da d'ari.'' Goshinsa ya murza yace." Na samu me kike bukata."?
Baki ta washe tace."Ina bukatar Gashashshiyar kazar Malo mai nama." Dariya yasa yana kallonta yace."Gwaggo kina san dad'i a rayuwarki duba dan Allah kin iya fad'ar Malo mai nama." itama dariya tasa harda tafa hannu tace."To yaron kirki waye baya san dad'i ai mutukar ban takura maka ba to ka siyo min kazar malo mai nama." Khalid ya dinga dariya yana kallonta.
Takaicin abinda suke ya isheni sai kawai na dauki wayata ina dubawa, naji yace."Gwaggo ko kudin kenan yau sai kinci kazar Malo." Yun'kurawa yayi ya mi'ke tsaye yana kokarin sa takalmansa yace."Auntyna ke me kike so."? Banza nai masa, Tace."Sa'ida kina ji ya nayi miki magana ko babu dai kyau gaba."
Ba tare dana kallesu ba nace."Bana bukatar komai." Tayi sauri tace."Kaji wai bata bukata." Yace."Okey to babu damuwa ai " hanyar fita ya nufa tace"To ina jira dan Allah kada ka fita abokai su ri'ke ka har nayi bacci." Yace."Yanzu zan dawo nima yunwa nakeji ai." tace."To kafin ka dawo bari na fito maka da abincinka." Ba tare da yace wani abuba ya fita daga gidan
Mi'kewa tayi ta shiga daki ta dauko masa fulas din abincinsa kana ta dauko kofin silba ta ciko masa da ruwan randarta tazo ta ajiye a kusa da ita.
Kallonta nayi rai a 'bace nace"Gwaggo keda zaki sanja masa fuska saboda laifin da yayi shine harda dauko masa abinci ko da yake ai nasan kin manta tunda kinga ya samo kudin siya miki kaza idonki ya rufe to har yanzu ina nan akan bakana."
"Aa Sa'ida ban manta ba ina sane inaso yaci abinci ya huta sai nai masa maganar." "Umm! nace naja bakina nai shuru! jin maganarsa shida abokansa a soro yasa na mi'ke na shiga daki, yana shigowa kai tsaye 'kofar Ummatu ya nufa da fad'in " Gwaggo ina zuwa."
Da sauri tace."Aa zo ka bani leda ta kafin ka shiga bana so ta za'be abinda ka shigo dashi.''! Dariya nasa ina mamakin 'karfin halin Gwaggo mata ta haifi d'anta amma ta fita iko dashi.....Dawowa yayi da baya ya mi'ka mata leda guda tace."To yawwa yanzu naji magana ka fito ga abincin naka." Yana 'yar dariya yace."To Gwaggo." Gurin mahaifiyar tasa ya nufa domin itama ya bata tata ledar.
kwance a d'an tsakar gidanta ya sameta da Mafici a hannu tana firfita shigowarsa yasa ta mike zauna tana kallon ladar hannunsa.....Zama yayi gefan tabarmar da take zaune yace."Ummatu me zai sanya ki takura kanki bakya fita babban tsakar gida kisha iska sosai."
Girgixa kanta tayi tace."Khalid 'kyaleni anan yafi min kwanciyar hankali akan na fita Gwaggo ta fad'a min ba'kar magana."
Yace."Ummatu idan da sabo yaci ace ki saba da halin Gwaggo wata irin macace mai wani irin hali bayan haka kuma akwai rikicin tsufa a tare da ita." Girgiza kanta tayi tace."Khalid dama ai kai baka ganin laifin Gwaggo duk abinda tayi daidai ne a gurinka."
Girgiza kansa yayi yace."Ba haka bane wallahi Ummatu yanzu a matsayin na shekarun Gwaggo dole ayi mata uziri shiyasa kikaga duk abinda tayi nake biye mata saboda samun nutsuwarta ba wai bana san laifinta bane."
Tsaki taja tace."Duk da da akwai tsufa to da akwai iskanci wannan tsohuwar guda ce Khalid ni kad'ai nasan irin takaicin da take kuntuka min a gidan nan."
Yace."To kiyi hakuri dan Allah komai mai wuce wa ne gashi kema na siyo miki nama." Kar'ba tayi tana duba ledar tace."Sai da ka kai musu suka za'ba tukkuna ni aka kawo min saura ko."
Girgiza kansa yayi yace."Aa Ummatu duk d'aya ne wallahi dake da Gwaggon." Tace."Ai kamata yayi ka daina daidaita ni da ita tunda ni na haifeka idan kana neman albarka sai kayi min biyayya."
Yace."Ummatu dan Allah ki daina irin wannan maganar wallahi dake da Gwaggo duk daya kuke a gurina ke kika haifeni dole kina da martaba ta mussaman a gurina Gwaggo kuma itace ta raine ni har na girma Gwaggo bata san 'bacin raina komai ta samu nawa ne abinci wannan Gwaggo bata ci sai tare dani sai dana na tafi makaranta tukkuna muka raba kwano da ita Gwaggo takan iya hana cikinta abu ta ajiye min Ummatu kada ki manta Gwaggo itace tayi rabin dawainiyar Karatuna idan tayi sana'arta haka zata tattara kudin ta bani nayi hidimar makaranta dasu duk lokacin da nazo hutu sai ta bani kudi wata bukatar zata taso Gwaggo tayi Baba yayi a haka fa akayi ta tafiya har Allah ya kawo ni wannan lokacin da nake daf da kammala makaranta kinga kuwa dole na kyautata mata domin ta taka muhimiyyar rawa a rayuwata."
"Khalid wato ka sani a gaba kanayi min gori ko? to ko banyi maka hidima ba ai ba zaka iya biyana irin dawainiyar cikin ka da haihuwar ka ba, saboda haka kada ka sake sani a gabana kana kawo min wata banzar magana."
Shuru yayi yana jinta sai fad'a take masa yace."To Ummatu kiyi hakuri dan Allah insha Allahu ba zan kara ba." Shuru tayi masa ta mike ta nufi kicin plate ta dauko tazo ta zauna tana kokarin sa naman a ciki.....mikewa yayi ya fita daga gurin, nan ya samu Gwaggo a kashingid'e har taci ta gyatse tana gyangyad'i! zamansa a kusa da ita yasa da sauri ta tashi zaune tana fad."Khalid ka fito."
"Umm." kawai yace ya zauna ya dafe kansa, cikin kulawa tace."Menene yake damunka."? Shuru yayi yana girgiza kansa, 'kasa-'kasa tace."Kada ka damu da barazanar Sa'ida akan abinda kayi mata d'azu nan ta titsiye ni tanayi min jaraba wai sai ta kaimu kotu ni dakai."
Cike da mamaki! yace."Akan wane dalili zata kaimu kotu kuma me nayi mata da har take wannan furucin."? Da sauri tace."Yi magana a hankali Dan bana tsammanin tayi bacci."
Tsaki yaja 'kasa-'kasa yace."Me tazo tace anyi mata."? Gwaggo murya a 'kasa tace."Wai cewa tayi kana tare ta a soro kana lalubeta."
Yanda Gwaggo ta fadi maganar yasa dariya ta 'kwace masa yace."Ni sharri kawai tayi min abinda ma yau ban yini a gida ba." Gwaggo tace."To nima haka nagani ta shigo fuska a murtuke ta dinga jaraba dan har mahaifiyarka taso ta biye mata na shiga tsakaninsu, jin tana maganar kaimu gaban alkali yasa na bata hakuri nace zan ja maka kunne."
Yace."Gwaggo da kin sani ma baki wahalar da kanki gurin bata hakuri ba ni ba d'an iska bane da zatayi min irin wannan sharrin nima zan dauki mataki a kanta dan kafin ta kaini 'kara kotu ni zan kaita tunda tayi min sharri."! Sosai ya fitittuke yake kare kansa Al'amarin ya dinga bani mamaki! dan duk maganar da suke ina jinsu raina kuma ya 'baci sosai da naji Gwaggon na rarrashinsa har tana cewa ai dama tasan Sharrin nai masa ba zai aikata ba, naji tamkar na fita naci masa mutunci sai dai kawai na taushi zuciyata na hakura na kyaleshi ina tunanin irin matakin da zan dauka a duk ranar da ya sake kuskuran ta'ba jikina..
*Masoya a taimaka da sharing a gruops👏🏼*
*IDAN KINA BUKATAR KI BIYA KUDIN LITTAFIN GA YANDA ABIN YAKE.....VIP #600 NORMAL#300 ACCOUNT.... 0542382124.....BINTA UMAR GTBANK....IDAN KATI ZAKI TURO #400 NE SAI KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER.*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/6, 2:04 PM] Umm Muhammad: *GA IRINTA NAN!!!🙆🏼♀️*
_(LOVE STORY🌺)_
*NA*
_BINTU UMAR ABBALE🍒_
*MANAZARTA WRITES ASSO🖊️📚*
*4*
Sa'ida cewa nayi fa ki sawa Rabi doyar nan kada mu wayi gari ta dinga yar mana da habaici kin san dai halinta bata da hakuri." Gwaggo ce ke wannan maganar a lokacin da take kokarin shigowa dakin da buta a hannunta da alama bandaki taje.
Zaune na mi'ke ba tare da nace mata komai ba na fara kokarin bud'e fulas din dake kan tabarmar ta. ido ta tsira min a lokacin da nake zuba doyar tace." Bafa cewa nayi ki kwashe mata ba guda biyu kika sa mata ta isa tunda itama idan tayi soye-soyen ta ba bamu take ba."
Nace."Gwaggo dan Allah abin duniya ya daina rufe miki ido mecece doya da 'kwai tun d'azu duk kin damu kanki."
"Sa'ida kada ki fad'a min magana akan Rabi na lura kema asirin nata ya fara tasiri a kanki ai sai kije ki 'karata ke da ita." shuru kawai nayi mata na fita daga dakin.
Ummatu na zaune a gurinta tana saurarar redio na shiga da sallama a bakina, kallon mamaki ta shiga bina dashi, nace."Ummatu doya ce na kawo miki." Babu yabo babu fallasa tace"To nagode." Kar'ba tayi ta ajiye kusa da ita nace"To sai da safe." kamar bata so tace."Allah ya tashe mu lafiya."
Koda na koma dakin gwaggo samunta nayi har ta kwanta bacci kan gadonta redion ta a kusa da kanta tana saurara Gwaggo bata kashe redio kullum a kunne take kwana shiyasa kullum cikin siyan batir take da daddare idan ta isheni da shuuuuu! zan tashi na kashe amma idan ta farka sai ta kunna alhalin ko wace tasha sun rufe, al'amarin Gwaggo nada wuyar sha'ani.
Da wuri na tashi nayi duk abinda na saba karfe bakwai da rabi na shirya tsaf a gurguje na karya kummalo nayi mata sallama domin tafiya gurin aiki.....Shuru tayi min ba tace komai ba nace."Gwaggo kina ji ina magana ko."? kallona tayi da fadin."Me kika ce."? cike da mamaki nake kallonta nasan sarai taji abinda na fada amma wai tambayata take, ajiyar zuciya na sauke nace."Na tafi sai na dawo." a maimakon tayi min irin adduar data saba sai kawai naji tace."Umm!! juyowa nai ina kallonta nace"Gwaggo ba zakiyi min addua ba."'
"Sa'ida kyaleni dan Allah kije kawai ni da wannan aikin naki gwara babu kullum kina yawo a kan titi zagade-zagade babu mijin aure duk wannan kyawun naki da kyawun surar zai tashi a banza a wofi wannan al'amari yana damuna."
Jim! nayi ina kallonta kafin nace."Gwaggo Al'amarina ya daina damunki komai da kika gani yana da lokaci ki cigaba dayi min addua."
"Umm."! ta sake fada tana ta'be bakinta, kaina na girgiza kawai na kama hanyar fita daga dakin, karo mukaci dashi a lokacin da yake 'kokarin shiga, yana sanye da singlet fara kal da 3qutar fuskarsa ta nuna alamun bai jima da tashi a bacci ba.
Cikin kulawa yace." Aunty Sa'ida ki bari yanzu zamu fita cikin a daidaita sahun Salim sai mu kai ki makarantar taku."
Ba tare dana kalleshi ba nace."Bana bukata." da sauri na ratse shi na wuce! Ina jin sautin muryar Gwaggo tana surutai wanda suke nuni da jin haushin abinda nai masa.
Sai da nayi dana sani akan k'in kar'bar tayin da Khalid yayi min domin nafi karfin minti goma sha biyar a tsaye a bakin titi wani abun hawa na haya bai gilma ta gabana ba motocin gida ne kawai suke wuce wa, dama wani sa'in ina fama da irin wannan matsalar ta rashin abin hawa, wani lokacin kuma ina fitowa titi nake samu yau dai al'amarin sai addua dan tamkar anyi musu gori ko kuma wa'inda suka tafi yajin aiki, agogon dake daure a hannuna na duba takwas saura minti biyar gashi karfe takwas da minti goma nake da Period ajiyar zuciya na sauke ganin adaidaita sahun nasu na kokarin fitowa daga layin duk abuna dole nayi hakuri na shiga mutukar baso nake na makara ba, Motar Alhaji Nura na sake hangowa tana bin bayan babur d'in nasu, saurin dauke kaina nayi ina kallon hanya tabbas nasan sai ya tsaya yayi min magana gashi gabad'aya ban yanke hukunci akan maganarsa ba gabad'aya ma na manta munyi magana dashi jiya.
Aikuwa gabana yayi parking ya sauke gilashin motar fuskarsa dauke da k'ayataccen murmushi yace."Ranki ya dad'i an fito kenan."? sakin fuskata nayi nace"Eh wallahi Alhaji barka da asuba ya kwanan iyali." ? cikin kulawa yace."Lafiya kalau sun tafi skull yanzu me zai hana ki shigo na rage miki hanya." Yafada yana kallon kwayar idona, ina kokarin magana adaidaita sahun nasu ta tsaya kusa dani. da sauri nayi 'yar dariya da fad'in"To nagode Alhaji dama na jima a tsaye babu abun hawa." cike da jin dadin kar'bar tayinsa yasa hannu ya bude mota kofar had'e da fad'in ''bisimillah." ba tare da na tsaya na saurari maganar da Khalid yake min ba na shiga motar da murmushi na mussaman a fuskata duk dan na cuzgunawa zuciyar yaron......Motar ya kunna muka bar gurin ko da wasa banyi kuskuran kallonsa ba so nake na 'kuntata masa dan saboda nasan ya tsani ya gan ni tare da mutumin bayan haka kuma inaso na nuna masa bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane ni ba matar 'kananun yara bace.
Khalid iskar dake gurin ya kaiwa naushi! rai a 'bace ya shiga kai kawo a gurin zuciyarsa kamar zata tsaga kirjinsa ta fito saboda tsananin kishi! Salim yace."Khalid dan Allah shigo mu tafi ka rabu da ita." Yana huci! ya shiga motar, Salim ya mika masa pure water da fadin"Kar'bi kasa zuciyarsa tai sanyi kar'ba yayi kamar gaske sai kawai yayi wurgi dashi kan titi lips d'insa ya ciza da fad'in "Allah Salim wannan Alhajin idan baiyi wasa ba sai nayi masa rashin mutunci babu ruwana da wani kud'insa da shekarunsa wallahi mutukar bai fita daga harkarta ba sai na bashi mamaki."!
Salim girgiza kansa yayi yace." Khalid idan da zan baka shawara ka d'auka sai nace maka ka rabu da Aunty Sa'ida saboda nasan kai kanka kasan ba tsaranka bace aunty Sa'ida matar manya ce ganin idonka babu wani gajarabul d'in mutum da yake tunkararta duk masu nemanta manyan mutane ne kana dai kallo da idonka duk kudi da muqami irin na Alhaji Nura idan ya ganta rawar jiki yake mata."
Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke yana kallon abokin nasa yace."Salim duk abinda ka fad'a akan auntyna gaskiya ne wallahi ni kaina ina mamakin tsaurin idona a kanta Salim na rasa yanda zanyi wallahi aunty Sa'ida ta shiga zuciyata tayi kakagida! a cikinta, Salim bari na fad'a maka wani sirrina da ba kowane yasan dashi ba, tun inada shekara goma sha takwas a duniya na fara mafarki da ita haka zan wayi gari jikina a 'bace! to tun daga sannan na gane cewa na balaga na zama cikakken namiji wallahi Salim babu ranar da zan kwanta bacci banyi mafarkinta ba kuma kai idan kaga irin rayuwar da muke da ita a mafarkin sai kayi mamaki wallahi sosai nake sex da ita ina jiyar da ita dadi tana jiyar dani! na rasa yanda zanyi da wannan masifar Salim ko a skull haka nake fama da wannan jarabar dan dai kawai adduar iyaye na tasiri a kaina amma da badan haka ba da tuni na nemi hanyar da zan biyawa kaina bukata.''
Girgiza kai Salim yayi yace."Gaskiya Abokina na tausaya maka domin ni tuntuni na gane son maso wani kake yi domin jikina na bani aunty Sa'ida bata sonka duba da irin halin ko'in kulan da take nuna maka me zai hana kayi ya'ki da zuciyarka akan abinda kasan ba zaka samu ba."
Ranshi a 'bace! yace."Salim idan kaga na daina bibiyar Aunty Sa'ida to aure tayi kai wallahi ko aure tayi ba zan hakura da ita ba saboda bata da wani miji sai ni wannan dalilin ne ma yasa na samu gwaggo na fad'a mata maganar ina ganin ko kowa ya'ki amincewa ita zata goya min baya."
Salim yace." Khalid ina jiye
17, October 2025
Fatima
Wow