Showing 81001 words to 84000 words out of 153671 words
Chapter 28 - GA IRINTA NAN Hausa Novels By Binta Umar Abbale.txt
yaron nan ya sake shigo min gida a bakin auranki."
Da sauri na daga kaina ina kallonsa da mamakin maganarsa.....Yace.'' Kwarai kuwa ki kalleni da kyau ni ba yaro karami bane da zaku dinga wasa da tunani na na lura har yanzu da akwai soyayyar yaron nan a zuciyarki sabida haka wallahi kuka ci amanata sai na baku mamaki.
Hannu nasa na goge hawayen fuskata nace."Amma dai kasan ba zaka hana ni zumunci dashi ba ko."?
"Babu ruwana da wani zumuncin ku idan kun had'u can kuje kuyi amma ban lamunce a shigo min gida ba." Yana gama maganarsa ya bude dakin a fusace ya fita.
Kwanciya nayi naci kukana na koshi a gaskiya Alhaji Nura bashi da sauki mugun masifaffen mutum ne mara fahimta.........Gabadaya dauke min wuta yayi a gidan ya daina shiga sabgata ko nice da girki bama mu'amular arziki fuska a murtuke yake 'kare kwanakin sa ya bar min dakina babu kyakykyawar mu'amula. sosai na shiga damuwa mai tsanani domin a cikin 'yan watannin da muke shiri dashi na saba sosai dashi da soyayyarsa tunda duk ranar girkina sai munyi auratayya duk da baya bani had'in kai sosai amma ina gamsuwa dashi......Gabadaya sai na shiga cikin wani irin yanayi na tashin hankali da fargaba gefe guda kuma ga masifaffiyar sha'awar dake nema ta zautar dani.
Yau dai girki na ne kuma nayi alkawarin neman sa a kan hakki na domin ba zan zauna kullum marata na ciwo ba. Koda ya shigo dakin kai tsaye toilet ya nufa yayi uzirinsa ya fito ba tare da ya kalli inda nake zaune ba ya haye gadon yaja bargo ya rufe jikinsa.
Murya na rawa nace."Ina da magana da kai." shuru yayi min be tanka ba. Nace."Ni gaskiya na gaji da irin wannan zaman da mukeyi ina cikin matsatsi da takura ya kamata kayi hakuri da abinda ya faru ka daina fushi mu cigaba da mu'amula kamar yanda muka saba.''
Nan ma uffan bece ba. na matsa jikinsa ina kokarin shiga bargon ya mike a fusace! yace."Kada ki kuskura ki hana ni bacci Sa'ida idan kuma kin 'kiji to ranki ne zai 'baci."A sanyaye nace."Bangane ba Alhaji dan na matso kusa da kai sai na hana ka bacci."
Yace."Eh bana bukatar wata fitina a yanzu ni bacci zanyi na huta gajiya.'' Kai tsaye nace."Ni kuma gashi ina bukatarka ya za'ayi kenan."?
Tsaki yaja ya juya min baya. na dauki hannu na dora a bayanshi a harzuke ya ture ni dan har sai da na kusa faduwa a kasan gadon.....Na bishi da kallon mamaki! rufe jikinsa yayi ya gyara kwanciyarsa kawai sai naji wasu zafafan hawaye masu ciwo sun kwace min.
Sauka nayi daga gadon na kwanta kasan kafet tare da takure jikina wata irin gawurtacciya sha'awa ce take taso min na dinga mutsu-mutsu ina takure jikina hawayen bakin ciki da dana sani suna ta ambaliya a fuskata.
Yanda naga rana haka naga dare da asuba ina jin motsinsa ya tashi ya shiga toilet yayi wanka ya fito yayi shirye-shiryensa ba tare daya ko kalli inda nake kwance ba ya kama hanya ya fita daga dakin.
A daddafe na mike na shiga toilet nayi wanka na dauro alwala na fito riga da zani na atamfa nasa a jikina ko mai ban shafa ba nasa hijabi na tayar da sallah......Koda na idar da sallar kasa fita falo nayi sai nayi kwance a kan daddumar ina matse hawaye marata har yanzu ciwo take mun.
Muryar Yusura naji a kaina tana fad'in "Aunty Sa'ida kizo muyi breakfast inji babanmu."
Bude idona nayi ina kallonta dishi-dishi a idona nace."Kije gani nan." Yarinyar ta bude kofa ta fita ba.
Sun dan zauna zaman jiran fitowarta da suka ga bata fito ba sai kawai ya umarcesu da suyi breakfast d'insu..............Ba tare da damuwar komai ba ya shige ya tafi kasuwa bai ko duba halin da take ciki ba.
Sai kusan sha d'aya da rabi na samu sassaucin abinda yake damuna na mike da mataccan jiki na fita falon......Shuru yaran duk sun tafi makaranta ita kuma tana sama kamar tsuntsuwa, gurin cin abincin na nufa naja kujera na zauna a nutse na had'e tea domin shi kadai nake jin zan iya sawa a cikina ba tare dana sa madara ba na dauki cup din ina kur'ba tare da had'awa da soyayyan dankali da kwai.
Koda na gama karyawa banyi tunanin shiga kicin ba kai tsaye daki na koma na kwanta kan bed wayata na dauka na nemi number Hauwwa ita kadai nake jin zan iya fadawa matsalata.
"Kinga Sa'ida ki rabu da mutumin nan tun kafin ya jefa rayuwarki a matsala wannan ce shawarar da zan baki." Hauwwa ce ke wannan maganar bayan ta gama sauraran duk jawabin da nayi mata.
Shuru nayi ina nazarin maganarta Tace."Ni wallahi a rayuwata na tsani maza marasa adalci irinsu Alhaji Nura Sa'ida wallahi bana shakka wannan halayyar tasa itace ta janyo matarsa take lesbian saboda baya tsayawa ya biya mata bukatarta kawai kansa ya sani bukatarsa na biya shikkenan bai damu da halin da zaku shiga ba.
Nace."Hauwwa nima na fara zargin haka wallahi dan gaskiya idan ya kasance Aunty Murja tana da karfin sha'awa kuma tana da rauni to zata iya jefa kanta cikin matsala amma ni bana fatan nayi wannan harkar Hauwwa zan duba shawarar ki dan gaskiya ina masifar 'kwaruwa a zamantakewa ta da mutumin nan."
Tace."To shikkenan Allah ya za'ba miki abinda yafi alkairi." na amsa da ameen ya Allah 'kawata nagode kwarai da gaske."
Haka rayuwar ta cigaba da tafiya yau da dad'i goge babu ta 'bangaran maigidan babu dad'i bangaran Aunty Murjar ma haka domin kwata kwata yanxu ni da ita bama shiri tun ranar da ta fahimci cewa na gane abinda takeyi ta sanja taku a gidan bata shiga sabgata sai da ni sa'i da lokaci inayi mata magana idan tayi ra'ayi ta amsa idan ba tayi ba ta share ni...........
Ranar Wata laraba tayi bakuwa da yake a falo suka zauna ina jin hayaniyarsu a dakina a nutse na bude kofa na fito. ganin matar dake zaune a kusa da ita yasa gabana ya yanke ya fadi da sauri nayi niyyar komawa daki sai kuma na fasa domin nasan sun riga sun gan ni! A dake na k'arasa falon na nemu kujera na zauna da fadin."Aunty Murja bakuwa kikayi ne."? Yau da mutuminci ta amsa min da "Eh wallahi dama yanzu take cewa zata tafi kuma baku gaisa ba.
Nace." Allah sarki ina kallonta nace."Ina wuni ya gida ya yara."? Ta amsa tana min wani irin kallo kaina na sunkuyar kasa gabana na faduwa ina addua a zuciyata akan Allah yasa bata gane ni ba.
Tace."Ni kam kamar na san wannan fuskar taki." na kalleta tare da kokarin kauda fargabata nace."Allah ko."? Tace."Kwarai kuwa kamar kece watanni takwas da suka wuce kikaje asibiti keda wata tsohuwa domun a duba miki virginal d'inki."
Nace."Anya kuwa bani bace." 'Yar dariya tayi tace."Kece mana ko ba sunanki Sa'ida ba."? Nace."Sunana Sa'ida mana." Tace."Sannan kuma kice min bake bace." shuru nayi mata domin idan nace zanyi magana zan iya fashewa da kuka shikkenan asirina ya tonu.
Aunty Murja tace." Maryam naji kina maganar wata takwas da suka wuce kuma yanzu auransu da Abban Yusura wata biyar kenan.
Tace."Nima dai abinda ya bani mamaki kenan lokacin taje akan a dubata ko ta qaru a d'inke ta lokacin dana duba sai na fahimci cewar kamar tayi gardama ne a lokacin da za'a kar'bi budurcinta sai na rubuta mata magunguna. har nake tambayarta ina mijinta a lokacin take cewa dani yayi tafiya shine yace tazo asibiti a dubata duk ina da sheda a rubuce."
Aunty Murja ta dinga yi min wani irin kallo ni kuma sai wani irin gumi nake zabgawa tamkar wacce tayi gudun famfalaki.!
Mi'kewa nayi jikina a bala'in mace na bude dakina na shiga na fada a saman gado kuka na dinga rafsawa ina kiran sunan Allah.
Aunty Murja wayarta ta dauka da fad'in "Dama neman hanyar da zan hukunta yarinyar nan nake domin nima data rufa min asiri zan rufa mata dan haka yanzu zan kira Abban Yusura a waya yazo kiyi masa bayani da bakin ki."
Dr Maryam tace."Aa Murja kada kiyi haka dan Allah wallahi ni ban fadi wannan maganar da wata manufa ba ki rufa mata asiri ta zauna dakinta."
Murmushin takaici tayi tace."Maryam wallahi ba zan kyale yarinyar nan ba domin itace tayi sanadiyar da Alhaji ya hana Aziza zuwa gidan nan sannan kuma tayi sanadin zuwana gidanmu nayi kwanaki tsayin shekarun aurena da mijina hakan bata ta'ba faruwa ba sai da ta shigo gidan sannan kuma kice na kyaleta ni dai kawai idan yazo kiyi masa cikakken bayanin da zai gamsu nayi miki alkawarin kyauta ta mussaman."
Dr Maryam tace."Ai shikkenan tunda ta kasa rufa miki asiri kema sai ki bankad'a nata." tace."Ashe kin fahimce ni.
Aunty Murja ta dauki waya ta kira mijinta tace dashi maza maza yazo gida akwai abinda yake faruwa. jin haka Alhaji Nura ya shigo motarsa ya kamo hanyar gida.
Wani irin tashin hankali ya shiga a lokacin da Dr Maryam ta gama warware masa 'boyayyan sirrin Sa'ida dake lullu'be! ya cire hularsa ya ajiye a hannun kujera yasa hannu ya sharce gumin goshinsa ido jajawur ya kallesu yace."A ranar dana kusanci yarinyar nan sai da na gane ba budurwa bace amma sabida ta iya tsari da 'karya ta kawo min wasu hojjojinta na banza to sabida haka tunda yanzu na gane gaskiya lamari zan dauki mataki a kanta domin ni ba zan lamunci zama da macen da zata ha'ince ni ba."
Yana gama maganarsa ya mike da saurin gaske ya kama hanyar dakinta, ido suka bishi dashi har ya bude dakin ya shiga.
Maganarsa naji a saman a kaina, a furgice na mike zaune ina kallonsa tunda na ganshi a burkice nasan ya samu labarin abinda yake da akwai.
Yana huci! yace." Sa'ida an yanka ta tashi yau Allah ya tona asirinki Dr Maryam ta bud'a min dukkanin sirrukan ki saboda haka tunda ke kin kasance ma ha'inciya macuciya kije na sake ki saki uku! sai kiji ki auri yaron da yake bibiyarki har gidan auranki wanda dama shi nake zargin ya lalataki kafin aure na dake."!
Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! kawai nake nanatawa a cikin raina yayin da nake jin wani irin mugun ciwon kai da mugun jiri d'akin sai juyawa yake dani a takaice dai ban san sanda ya gama cin mutuncinsa ya fita daga dakin ba.
*708 465 3262: *SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*
*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*
*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.🥰🤝🏻💜_*
*58&59*
Na jima ina nanata kalmar innalillahi wa'ina ilahiri raji'un a fili da zucci kafin naji wani k'arfin gwiwa gami da danga a tare dani......mikewa nayi jiki a mace na bude wardrobe na had'a kayana cikin akwati tsaf sai da na kwashe kayan sanyawata da duk abinda nasan ina bukata nasa a akwatin kana na rufe ta da kyar ina tunanin wanda zai dau'kar min.
Hijabi na nasa na d'aga akwatin tare da janyo hannunta da yake mai tayoyi ce sai kawai naja ta na bude dakin na fito kaina a kasa dan ko kadan bana kaunar na hada idona dasu....maganarsa naji a kunnena yana fad'in "Tsaya ki tafi da sakamonki cutar da kikayi min kuma na barki da Allah."
Tsayawa nayi ba tare dana juya ba zuciyata in banda tafarfasa babu abinda take
Daf dani ya tsaya hannunsa rike da takardar sakin nawa...."Kar'bi ki fice min daga gida bana bukatar sake ganinki shiyasa nayi miki saki uku domin hukuncin daya cancanta dake kenan "
Hawayen dake kokarin kwace min na danne hannuna na rawa na kar'bi takardar da fad'in "Nagode ina rokon Allah yasa haka shi yafi alkairi.''
"Shine ma alkairi kije ki auri daidai dake amma ni ban kasance mazinaciya ba nasan Allah ba zai jarrabe ni da auran mazin.....Hannu na daga masa da fadin" Kaga ka daina kira na da wannan sunan tunda dai ka datse igiyoyin auranka shikkenan.
Aunty Murja dake zaune akan kujera tace."Ai gaskiya Abban Yusura kayi kuskure banji dadin sakin wulakancin da kayi mata ba haba ina laifi kayi daya ko biyu.A harzuke yace."Murja saki uku ne ya dace da wannan macuciyar saboda haka ki daina nadama dan na sake ta.
Juyowa yayi kaina yana magana ban tsaya sauraransa ba da sauri na bude kofar falon na fita ina jan akwatin kaya na.
Duk da babu wata tazara mai tsayi sai da na nemi adaidaita sahu ya sauke ni har kofar gida, dari biyu na bashi naja akwatin kayana na shiga gidan gabana har yanzu bai daina faduwa ba.
Yau Gwaggo towon alkama take sha'awa dan haka sau ta tuka abin ta da miyar bushashshiyar ku'bewa ta idar da sallar isha'i ta janyo kwanukan abincin domun taci nayi sallama a gidan.
Labule ta d'aga da fadin."Kamar muryar Sa'ida nake ji da daddaran nan." Nace."Itace Gwaggo.
Tana kallona tace."To maraba lale shigo daga ciki nima danshi (ra'ba) ne ya hana ni zaman tsakar gidan kin san kwana biyu an tafka ruwan sama.
Ina kokarin shiga dakin nace."Eh Kwarai hakane kwana biyu ana ruwa sosai."
"Amma dai lafiya dai domin na gan ki da akwati Allah dai yasa ba yaji kikayi ba.
A sanyaye na zauna gefan tabarmarta nace." Ya sake ni Gwaggo."
Wani irin shocking taji a jikinta da sauri tace."Sa'ida me kike fad'a"?
hawaye na zuba nace."Gwaggo ina nufin Alhaji Nura ya sake ni kinga ma shedar nan." Takardar hannuna na mika mata.
A sanyaye tace."Yo ni ina nayi karantawa Sa'ida me ya faru mutumin nan yayi miki wulakanci kuma saki nawa yayi miki."
"Saki uku ne."? Na fada muryata na rawa, Gwaggo innalillahi wa'ina ilaihi raji'un kawai take nanata wa cikin furgici tace."Sa'ida anya mutumin nan kuwa yana da hankali saki uku a lokaci guda ke kuwa wane irin laifi kikayi masa."?
Cikin kokarin danne damuwata nace." Asiri ne ya tono Alhaji Nura ya gane 'boyayyan sirrin dake lullu'be shine ya yanke min wannan hukuncin."
"Sa'ida ta ina zai gane ke ba budurwa bace bayan da farko kinyi masa bayani kuma ya amince.
hawaye na share nace." Nifa Gwaggo bana zargin kowa da mutuwar aurena sai Khalid." Da sauri tace."Tofa! bakya zargin kowa sai Khalid to me yayi miki yaron da tuntuni ya tafi gurin sana'arsa.
Hannu nasa na share fuskata nace."Gwaggo Khalid yaje gidana kuma har cikin 'kuryar dakina sai da ya shiga kuma Alhaji ya shigo ya sameshi.
Gwaggo rike baki tayi da fad'in "Ashe dai duk jan kunnan da nayi wa yaron nan be ji ba sai da yaje to me yaje yayi miki."?
Nace."Gwaggo ya kike tambayata me yaje yayi min gashinan abu a zahiri Khalid yaje gidana dan ya lalata min aure to bukatarsa ta biya sai ya zuba ruwa a kasa yasha.
Gwaggo ta dinga girgiza kai tana fadin."Kai amma wannan al'amari beyi dadi ba Khalid kuma bai kyauta duk da khalid ya kasance dan uwanki amma ai bai cancanta yana baligi irin wannan ba ya shiga gidan matan aure ba tare da neman izina ba dik abinda Alhaji Nura yayi masa na hukunci daidai ne tunda shi ya taka sharia.
Nace."Gwaggo to me yasa kin san gaskiya kike takewa me yasa bakya ganin Laifin Khalid kuma me yasa kike fifitashi akaina."
Cikin nutsuwa tace."Sa'ida kada ki fassarani da wata manufa mara kyau ni dake da Khalid dik daya kuke a gurina babu wanda yafi wani hakika kuma naji bakin ciki da takaicin abinda yayi saboda haka an jima idan ya kira ni a wayar daya siya min zan nuna masa 'bacin raina."
Shuru nayi ina sha'kar bakin ciki! ta girgiza kanta tana jimanta al'amarin tace."Wai saki uku a gaskiya wannan mutumin bashi da hankali ko kad'an wallahi naji ciwon abinda yayi."
Nace."Gwaggo kiyi min addua kawai Allah yasa haka shi yafi alkairi Allah ya za'ba min miji nagari."
A sanyaye ta amsa da ameeen ya rabbi. dakin ya sake daukar shuru na 'yan mintina kafin nace."Gwaggo kin tuna asibitin da kika rakani a washe garin ranar da Khalid yayi min fyad'e."?
Kallonta tayi a sanyaye tace."Sa'ida bana so naji kina wannan maganar wallahi babu dadin ji.'' Cike da takaici nace."Gwaggo har duniya ta nad'e ba zan daina maganar nan ba kuma ba zan fasa neman sakayya gurin Ubangiji ba."
Babu walwala a tare da ita tace."To naji ya isa haka magana dai tuntuni ta wuce tayar da ita bashi da amfani yanzu sai ki fuskanci abinda yake gabanki.
Nace."Magana ai tuntuni na barwa Allah yanzu ma dalili tayi shiyasa na fada miki abinda yake zuciyata.
Shuru tayi ba tai magana ba, nace."Wannan likitar data duba ni ashe kawar aunty Murja ce."
Kallona tayi da mamaki a tare da ita, na cigaba da cewa "Itace duk ta warware masa komai shi kuma ya fusata ya yanke min wannan hukuncin kafin na fito daga gidan ba kiji irin zagi da cin mutuncin da Yayi min ba."
Hawaye ta goge tace."Ki rabu dashi daga shi har ita likitan Allah zai saka miki kuma duk wanda ya tona asirin wani shima sai Allah ya tona nasa yanzu ni tsorana Allah da Annabi kada maganar ta fita jama'ar gari su dinga yi mana wani irin kallo." Tana kuka take maganar.
Gabadaya naji zuciyata ta karye zafafan hawaye suka fara zubo min nace."Gwaggo insha Allahu hakan ba zata kasance ba idan kuwa maganar ta fita to zan tattara kayana na gudu gurin mahaifiyata."
Kuka takeyi sosai tana kallona had'e
17, October 2025
Fatima
Wow