Showing 78001 words to 81000 words out of 153671 words
Chapter 27 - GA IRINTA NAN Hausa Novels By Binta Umar Abbale.txt
mugun hali irin naki." da saurin gaske ta bude kofa ta fita ba tare da tace wani abu ba.
K
*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.🥰🤝🏻💜_*
*54&55*
A ranar yini nayi da fargaba mai tsananin gaske. koda auntyn Murjan ta dawo sama-sama mukayi magana da juna na bar mata falon na koma daki na zauna ina tunanin rayuwa, Yusura ce ta shigo da fad'in "Auntynmu wai kizo muci abinci." Kallonta nayi da fad'in."Babanku ya dawo ne."? kanta ta daga min alamar Eh. to sanin da nayi bani nake da girki ba yasa ban damu ba, nace."Kije kice gani nan fitowa." Yarinyar ta juya da sauri ta fita.
A maimakon na tashi naje gurin cin abincin sai na nemi guri na kwanta daidai da 'kwayar zarrah bana so na had'a numfashi da ita wani irin tsanarta nake ji a cikin zuciyata.
Motsin shigowarsa dakin yasa ni saurin kallon kofa....jikinsa sanye da jallabiya ruwan toka ya karaso kusa dani.
Zaune na mike ina gyara daurin dankwali na nace."Barka da dare ina fatan ka dawo lafiya."?
Babu sukuni a tare dashi ya amsa da "yawwa zaman me ki keyi ne tun dazu na aiko kizo muci abinci baki fito ba idan kuma ba'a kira ki ba kice anyi miki laifi."
Ajiyar zuciya na sauke nace."Bana d'an jin dadin jikina ne shiyasa ban fito bs babu damuwa kuna iya cin abincin ku."
Idonsa akaina yace."Me yake damun ki domin Murja ta sheda min cewa tunda ta dawo daga gidan biki kika kulle kan ki a daki Sa'ida bana son neman fitina a gidana.
Nace."Yanzu shikkenan bani da damar da zan zauna a daki nayi tunanin rayuwa sai a zargi wani abu har kullum idan na kira Aunty Murja munafuka kana jin haushina to wallahi kayi takatsantsan da ita domin abunda take aikatawa ya sa'bawa addinin Musulunci"
"Kinga ni ba wata magana na nema ba shin rashin lafiyar gaske kike ko kuma ta 'karya kika 'kir'kira domin ki tayar mana da husuma a gida."
Cikin takaici nace."Ni lafiyata lau husuma kuma da kake magana a kai Allah ya tsare mu da ita dalilin da yasa na zauna a daki mai k'arfi ne wanda nake tunanin koda na fada maka bai zama lallai ka yarda ba.
Yace.''Ai fad'ar shi yafi alkairi domin ni a rayuwata na tsani 'kumbiya-'kumbiya." Na bude baki kenan zanyi magana Yusura ta shigo, duk sai muka bita da kallo tace."Abbah kazo inji mommy." Da sauri yace."gani nan zuwa." Yarinyar na fita yabi bayanta kallo na bishi dashi ina mamakin halayyarsa.
Sai da nayi wanka tsaf na shirya jikina na daidaici cewar sun bar daining din sannan na fita falon kai tsaye gurin cin abincin na nufa ba tare dana tanka musu ba.
Ina kokarin zama naji tana fad'in "Sa'ida yau Hajia Aziza tazo ko.''? Nace."Eh tazo." Tace."Wallahi sai da na fita na tuna ashe ban fada mata zani unguwa ba kuma nayi ta kiran wayarta domin na sheda mata wayar ta'ki shiga."
Nace."Eh itama haka tace har nace ta biki gidan biki tace Aa ba zataje ba."
D'an murmushi tayi da fad'in "Hajiya Aziza kenan." cikin zuciyata nace "Gafalallu insha Allahu sai Allah ya tona muku asiri.
Mintina goma sha biyar na kammala cin abincina na mike a nutse na bar gurin. dakina na nufa Yusura tace." Aunty yanzu zasu saka *TARKO KAUNA* Naga zaki shiga daki yau ba zaki kalla ba.'' Ba tare dana juyo ba nace."Yusura yau bacci nake ji na kalli maimaici ranar lahadi.'' Tace."To shikkenan aunty Sai da safe." na amsa da Allah ya tashemu lafiya.
Ina kokarin shiga bargo ya shigo dakin ya tsaya a kaina zaune na mike ina kallonsa yace."Wulakancin naki har akan 'ya'yana zaki gwada.
Nace."Ban fahimci maganarka ba." A hasale yace."Yarinyar nan Yusura tana miki magana sabida kina ji da isa da iko ki gagara kallon inda take shin dame kike takama ne."?
Murmushin takaici nayi nace."Bana takama da kowa sai Allah da ma'aiki'' Da sauri yace."Ki kiyaye b'ata ran d'aya daga cikin iyalina kinji ko baki ji ba."
Nace."Naji yanzu Ita Yusuran ce ta turo ka kazo ka sauke min ashafa ko kuma uwarta ce."? Kallona yayi da fad'in "Zakiyi min rashin kunyar da kika saba ne."
Nace."Ai gaskiya ce sabida nasan wannan hayaniyar da kazo kana yi min ba tunaninka bane turo ka akayi."
Hannu ya daga zai kwada min mari na kauce da sauri ya mari iska.
Yana huci yace."Wai me yasa kika raina ni Sa'ida me kika mayar dani a cikin gidana."
Cike da takaici nace."Alhaji kaine kasa kima da mutuncinka duk suka zube a idona kasan Allah a yanzu dai sai dai kawai na kalleka domin kayi min bazata ban ta'ba zaton zan shigo gidanka nayi irin wannan rayuwar ba."
Yace." Wannan rayuwar kuma ki rubuta ki ajiye yanzu kika fara ni haka tsarina yake a gidana babu wata macan data isa tace min ga yanda zanyi 'karya take.
Dariya ya bani na kalleshi yana tsaye a kaina sai daga murya sama yake nace."Yanzu dai magana ta wuce akan na 'ki zaman falo aka zuga ka kazo kaci min mutunci to naji na dauka nayi laifi kayi hakuri."
Shuru yayi yana sauke ajiyar zuciya, Nace."Ka zauna inaso muyi magana. a watse ya kalleni da fadin"Kin san ba girkin bane ko."? Nace."Eh na sani ai ba wata doguwar magana zamuyi ba.
Zama yayi kusa dani yana kallona. Nace."Kasan me? a ya mutse yace."Sai kin fada." Nace."Ka hana wannan matar zuwa gidan ka ina nufin hajiya Aziza 'kawar aunty Murja."
"A kan wane dalili zan hanata zuwa."? Yayi maganar tare da tsareni da idonsa.
Nace." Ba alkairi ne yake kawo ta gidan ba tana zuwa ta hana mala'ikun rahama shigowa gidanka sabida haka ka hanata zuwa shi yafi alkairi.
"Ba zan hana ta shigowa gidana ba sai naji dalilin ki." ajiyar zuciya na saukw idona akansa nace." *'YAR MADIGO (LESBIAN)* ce."
Wani irin kallo yake min kafin yace."Shine me? dan Aziza tana Lesbian sai kike zargin Matata Murja.''?
Cike da karsashi da kwarin gwiwa nace."Kwarai kuwa dole nayi zarginta saboda tayi abinda zai janyo hakan Hajiya Aziza a sati sai tazo sau uku ko sau hudu sannan idan suka hau sama suka rufe kofa sai yamma suke saukowa."
Shuru yayi kansa a 'kasa na cigaba da cewa''Yau tazo gidan lokacin Aunt Murja ta tafi gidan biki ni kuma ina daki ina bacci ta shigo ta same ni ...........Duk abinda ya faru ta kwashe kaf ta fad'a masa.
Wani irin gumi! ne yake karyo masa ya dinga kallona bakinsa na rawa da alama magana yake so yayi amma tsabar rud'u ya hana shi cewa komai.
Nace."Dan Allah ka fahimci maganata kuma ka yanke hukuncin daya dace wallahi tallahi banyi musu sharri ba.
Da 'kyar ya iya fadin"Sa'ida a gidan nawa ake aikata wannan kafurcin tsayin shekaru ban sani ba.
Ajiyar zuciya na sauke nace."Yau ne Allah yaso kasan abinda yake faruwa saboda haka sai kayi namijin kokari gurin ganin ka kori wannan masifar da ta kunno maka a gida.
Mi'kewa yayi ya kama hanyar fita yana tafiya yana had'a hanya babu shakka al'amarin yayi masifar saka shi cikin rud'u da tashin hankali mai tsanani.
Tana kwance a gado cikin kayan bacci masu fitar da tsaraici ya shiga dakin sama-sama ta amsa sallamarsa domin taji masifar haushin zaman da yayi a dakin Sa'ida.
Ya nemi gefan gado ya zauna yana kallonta a burkice!
Zaune ta mi'ke had'e da ajiye wayar hannunta tace."Lafiya na ganka ka shigo a burkice wani abun ne ya faru."?
Ya kalleta da jajayan idanunsa yace."Murja ashe dama ha'intata kikeyi."? da sauri tace."Wace irin magana ce wannan."? Hannu ya daga mata a kaushashe! yace." Menene tsakanin ki da wannan matar dake zuwa gurunki.?
Gabanta ne ya fad'i baki na rawa tace."Wace mata kake magana."?
Yace."Hajiya Aziza matar da kuka had'u da ita a fece book." Ajiyar zuciya ta sauke tace."Alhaji babu abunda yake tsakanina da Aziza sai mutumci da zumunci."
Yace."Ban yarda da maganarki ba Murja kina gayyato min 'yar iska gida kuna iskanci yaushe kika zama lalatacciya."?
Cikin firgici tace."Wai ya kake magana a baibai ne ka fito fili ka fada min abinda kake nufi dani."
Yace."Sa'ida ta tabbatar min da cewa" Aziza *'YAR MADIGO (LESBIAN)* ce domin a dazu da tazo bakya nan sai ta nemi Sa'idan akan suyi harkar ita kuma ta'ki amince mata."
Wani irin kuka ta fashe dashi tana salati da tafa hannaye tace."Yanzu irin sharrin da yarinyar nan za tayi min kenan."? Yace." Ki fada min gaskiyar magana ba kuka nace kiyi min ba shin kema kina aikatawa ko kuwa.?
Hanci ta shaqa a fusace! ta miqe tsaye da fad'in "Wallahi tunda yarinyar nan ta kai ni karshe sai na hukuntata har ni za tayi wa sharri na lesbian lallai sai na nuna mata kuskuranta.
Kafin yayi wani yunkuri har ta bude kofar dakin ta fita ya mike da saurin gaske ya bi bayanta yana kiran sunanta, da gudu ta sauka k'asa kai tsaye dakin Sa'ida ta durfafa.
Shaf na manta bayan fitarsa ban rufe kofa ta ba na kwanta bacci ya daukeni kawai sai jin shaqa nayi a makogwarona tari ya sarqe ni na bude ido ina kakari! kafin na ankara naji mari mai zafi a kumatuna.
" Ni zakiyi wa k'azafi Sa'ida ashe baki da mutunci da 'ya'yana da mutuncina amma ki zaunar da mijina marufar asirina uban 'ya'yana kice masa ni 'Yar Lesbian ce."
A mutukar galabaice nace."Ki sakar min wuyana." tana kumfar baki tace."Ba zan saki ba sai kin fada min a inda kika gan ni ina lesbian. "
Nace."A cikin gidanki na kama ki a dakin ki kina lesbian sai me."? Ta sake kawo min mari! na rike hannunta da karfin gaske na ture ta na sauko daga gadon ina haki nace."Idan bakya lesbian din meye naki na tayar da hankali."
Tayo kaina tana ihu! nace."Wallahi kika kuskura kika doke ni sai na zubar miki da hakora."Kuka tasa a daidai lokacin daya shigo dakin take fad'in "Amma wannan yarinya kin cuce ni wallahi sai Allah ya sake min gida kuma zan fita na barshi tunda kinfi bukatar haka.
Nace." Idan kin tafi kin bar gidanki da 'ya'yanki kanki kika cuta ba wani ba.
Ta kalleshi tana kuka da fad'in "Alhaji kaga irin abunda nake nuna maka ko? dama nasan sai haka ta faru tunda nasan duk wata mace da zaka aura burinta ta shigo ta rabani da kai shikkenan tunda abin ya kasance a haka ni zan tafi gida domin ba zan zauna ba."
Tana gama maganarta ta bude kofa ta fita, zuwa yayi ya zauna kusa dani yana goge gumi nace."Alhaji kada ka bari ta tafi gidansu kaje ka hanata"
Yace."Sa'ida ki 'kyaleta taje jikina na bani maganarki akwai alamun gaskiya a ciki taje kawai sai nayi binkice."
Jikina yayi sanyi da jin abinda ya fada hakika da nasan haka zata faru da ban fada masa ba domin bana so ta sanadiyar al'amarin auransu ya samu matsala nafi bukatar ta shiryu su cigaba da zama mai tsafta a tsakaninsu.
Aunty Murja kwananta biyu a gidansu mahaifinta ya nemeshi da su tattauna...............Kima da darajar dattijon tasa shi janye kudirinsa akanta domin da yayi niyyar datse igiyar auranta sai kuma dattijon ya bashi tausayi ya hakura amma kafin ta dawo gidan sai da yayi mata gargadi akan cewa babu ita babu hajiya Aziza duk sanda ya sake ganin matar a gidansa to ta tabbatar kwanan auranta dashi ya 'kare."
Tunda ta dawo gidan ta tsiri gaba dani ko na gaisheta bata amsawa ni kuwa da yake ban iya gaba ba ko na fara ajiyewa nake nai mata magana tsakanina da yaran ta babu wata matsala hakanan tsakanina da mijina ma sai godiyar Allah dan yanzu na fahimci halinsa 'bangaran auratayya ma yana kokari yanzu dan bana ta'ba bari ya sauka daga kaina sai na biya bukatata yanzu ya saba da jarabata yana kuma kokari akan hakan.
Ranar Lahadi Khalid yazo min gida wai yazo yayi min sallama zai koma Lego's ni dai tunda ya shigo gidan gabana yake fad'uwa! na kalleshi da fadin."A maimakon ka kira ni a waya kayi min sallama sai kuma kazo min gida kasan dai bani kadai bace ko."?
Yana min wani irin kallo yace."Me kika d'auke ni ne ? bake kadai bace to ina ruwana da kishiyarki ni gurunki nazo muyi sallama ba zuwa nayi na kalli kishiyarki ba.
Nace."To nagode sai ka tashi ka tafi Allah ya kiyaye hanya." Murmushi yayi tare da miqewa tsaye.....Sosai naji dadin hakan dan na dauka zaiyi min gardama. Nace"Tsaya anan ina zuwa." D'akina na bude na shiga na bude drowar domin dauko masa sabulai da turare.....ina d'agowa na hangoshi ta mirror ya shigo dakin....gabana yayi wani irin fad'uwa! sanin da nayi cewa Alhaji Bai fita yana sama dakin Aunty Murja ga Khalid ya shigo masa gida ba tare da sanin sa ba.........jikina na rawa na juyo cikin tsawa! nace......
*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*
*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*
*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.🥰🤝🏻💜_*
*56&57*
"Khalid me yasa zaka shigo min daki bayan cewa nayi ka tsaya a falo na fito me yasa kake so ka janyo min matsala a gidan aurena." ? Ba tare da yace uffan ba ya mayar da kofar ya rufe ya durfafo inda nake tsaye, gabana ya tsananta faduwa cikin rawar baki nace."Ka juya ka fita falo gani nan kaga maigidan yana nan bai fita ba kada ya shigo ya gan ka wata matsalar ta afku." Cikin zuciyarsa yace."Dama ai ni so nake matsalar ta afku. daf dani ya tsaya hucin numfashinsa na sauka a fuskata, kauda kaina nayi tare da matsawa daga kusa dashi. cikin wani irin voice yace." A yanzu Babu wani abu da yake tsakani na dake sai alkairi ni banzo gidanki da niyyar na kashe miki aure ba." Na kalleshi da fadin."Amma dai kasan babu dadi mutumin nan ya shigo ya ganka har gadon baccinsa." Murmushi yayi yana shafa sajensa yace."To menene? ai da sauki ma idan ba wani abu ya shigo ya tarar muna aikatawa ba." Nace."Kasan yanzu yana da ikon d'aukar mataki akanka ko tunda ka shigo masa gida ba tare da izininsa ba." 'Yar dariya yayi idonsa a kaina yace."A'ina zai gan ni da zai dauki mataki a kaina an jima kadan na bar garin." Tsaki! naja cikin jin takaicin abinda yake na ratse shi domin fita na bar masa dakin....Kawai naji ya riko hannuna. cikin wani irin shocking na juyo da saurin gaske na fuzge hannuna da fad'in "Kada ka sake idan kuma ka'ki sai ka fuskanci 'bacin rai."
Daf dani ya matso yana kokarin magana. Ya shigo dakin. naji gabana yayi wani irin rugugi! da mugun sauri na janye jikina gwiwata a bala'in sanyaye na nemi bakin gado na zauna ina zare ido!
Cikin basarwa yace."Alhaji barka da wannan lokaci." Alhaji Nura bai amsa masa ba ya karaso cikin d'akin fuskarsa tamkar hadarin dake daf da zubar da ruwan sama.
"Kai me ya kawo ka gidana? waye kuma ya baka damar shigowa har dakin bacci na."? A nutse yace."Afuwa Alhaji nima nasan ban kyauta ba kuma a yanzu ma maganar da mukeyi kenan da ita tana nuna min rashin dacewar abunda na aikata kayi hakuri dama nazo nayi mata sallama ne zan koma gurun sana'ata Lego's. "
Yace."Kada ka kuskura ka kara shigo min cikin gida domin ni ban yarda da kai ba babu ruwana da 'yan uwantakar dake tsakaninku."
Cikin mamaki yake kallonsa kafin yace."Kana nufin zaka iya raba hanta da jini kenan."? Alhaji Nura yaji tamkar ya soka masa wuka a ma'koshi yace."Kai ashe baka da kunya ? ka taka sharia ka shigo gidana babu izini na amma kake kalubalanta ta."
Killer smile yayi yace."Aa Alhaji naji kana wata magana ne mara ma'ana shiyasa nayi wannan maganar shigowa gidanka kuma babu izini ai na nemi afuwarka.
Mikewa tsaye nayi rai a 'bace! nace."Khalid kama hanya ka fita bana bukatar ganinka a gidan aurena."
Wani irin kallo yayi mata zuciyarsa na wani irin zafi ya lura duk da ya kar'be budurcinta mutumin na sonta yana kuma kishinta bai ta'ba tsammanin cewar za tayi watanni a gidansa ba tare da ya sake ta ba.
Murmushi yayi ya kalleta ya kalli mijin nata yace."Kuyi hakuri da aikin 'kuruciya kada kuma ku fassara abinda nayi da wata manufa mara kyau saboda haka ni na barku lafiya."
Hanyar futa ya kama gabad'ayan mu muka bishi da kallo har ya bude kofar dakin ya fita......Kaina ya juyo yana wani irin numfarfashi da huci! yace."Ashe dama baki da mutunci da kamun kai Sa'ida."?
Shuru nayi masa domin nasan nike da laifi. ya cigaba da cewa''Sabida rashin kamun kai da rashin sanin darajar aure ki gayyato tsohon saurayin ki dakin auranki shin me hakan yake nufi.''?
Cikin 'kokarin kare kaina nace."Wallahi bani na gayyatoshi ba shigowa yayi." a fusace! yace."Rufe min baki munafuka idan baki bashi fuska ba ta yaya zai shigo min gida har dakin bacci na''
Kaina na sunkuyar 'kasa ina addua a cikin zuciyata.....Cikin sigar cin mutunci da wulakanci ya cigaba da zazzaga min bala'i yana fad'ar duk maganar da tazo bakinsa.
Cikin kuka nace."Ni dai dan Allah kayi hakuri an san ba'a kyauta maka ba amma ka daina zargi na da yaron nan wallahi babu abinda mukayi wanda ya sa'bawa sharia.
"Babu abinda kukayi na shigo na sameku daf da juna kamar zaku rungume junanku." shuru nayi ban tanka masa ba, ya cigaba da cewa''To wallahi wannan shine na farko kuma shine na karshe duk ranar da
17, October 2025
Fatima
Wow