Showing 150001 words to 153000 words out of 153671 words
Chapter 51 - GA IRINTA NAN Hausa Novels By Binta Umar Abbale.txt
nayi ina bacci sai bayan la'asar na tashi nai wanka da salolina doguwar riga mai hula nasa kai tsaye kicin na nufa domin samawa cikina abinci, daidai cikina nayi tunda bani ke da girki ba a kicin din na zauna naci na rage wanda zanci da daddare, falon na fito na zauna ina duba waya ta text messages dinshi na gani yana tambayata gida wai ya kasa aikata komai sai tunani na. 'Karamin tsaki naja ina mamakinsa tunda mukayi aure bai ta'ba fad'a min kalmar so ba sai yau da alama akwai abinda yake bukata aikuwa yau da rigima kenan domin ba zan lamunci shiga hakkin wani ba......Kafin magariba ya dawo gidan a maimakon ya wuce gurin mai girki sai ganinsa nayi ya shigo ido jawur sai kace wani bugagge. babu fuska nayi masa sannu ya zauna kusa dani yana ya mutse fuskarsa, Jin zuciyata tana tashi yasa na mike da sauri na bar gurin. dakin ya biyo ni rai a bace yace."Wai meya sa kike min hakane." ? Ba tare dana kalleshi ba nace."Bana son warin turaranka." Babu sukuni yace." Wannan ba hujja bace me yasa tunda nake amfani da turarena baki ta'ba gudu na ba sai yanzu." Shuru nayi masa Ya matso jikina da fadin ." Tunda na fita nake tunaninki gabadaya na kasa aikata komai kinzo kin tsaya min a raina." Kallonsa nayi da fad'in." Ina fatan baka mance cewa ba girki na bane.'' Yace." Ina sane auntyna ke kadai nake bukata Wallahi manège kawai nake da Jamila bata gamsar da ni." Nace."Hakanan za kayi hakuri kaje gurinta." hannuna ya rike murya na rawa yace."Ba zata iya ba wallahi kece zaki iya ki taimaka min." Nace." To jeka tambayeta idan ta amince sai kazo." Shuru yayi yana kallona nace." Ko tsoronta kake.'' Murmushin takaici yayi yace." Ni nafi karfin naji tsoron macan dake karkashina kema ba karfi na kikafi ba kawai ina lallaba'ki ne.'' Nace."Okey to kaje kawai." Mikewa yayi ya fita minti biyar da fitarsa naje na kulle kofar palon na shige daki nai kwanciyata.............Jamila tana zauna a falon ta ya shigo dauke kanta tayi tana kumbura fuska shima bai kula ta ba ya bude dakinsa ya shiga ya watsa ruwa ya shirya jikinsa ya fito massalaci ya nufa sai bayan isha'i ya dawo gidan. Gurin cin abinci ya nufa yaga babu komai akai falon ya sameta tana kallo yace."Ke baki abinci bane."? A kumbure tace." Nayi daidai cikina na cinye." Yace."Saboda me."? Cikin tsiwa tace." Saboda bana bukatar kaci kaje gurin matar so ta baka." Ransa a bace yace."Ke zanci ubanki wallahi ni kike d'agawa murya." Sai ta fashe da kuka tana nuna kirjinta take fadin." Yaya Khalid ni kake zagi."? Yace." Ko zaki rama ne."? Tana share hawaye tace."Duk dai wanda ya zagi uban wani nasa ya zaga." Wani bahagon mari ya kwad'a mata yana huci! yace." Tuntuni na gaji da zama dake domin Baki da wani amfani a gurina saboda haka ki tashi ki fitar min a gida bana bukatarki tunda baki da mutunci." Gabanta na faduwa tana kuka take bashi hakuri rufe idonsa yayi yaki sauraranta yace maza ta tashi ta fitar masa daga gida sai ya neme ta. Jamila na kuka wurjajan ta hada kayanta cikin akwati ta yafa mayafi ta nufi gidansu cikin tsananin tashin hankali.......Ajiyar zuciya ya sauke bayan fitar ta ya kulle sashen kai tsaye gurin auntyn nasa ya nufa.
Ya jima a tsaye a kofar falon yana bugu da dai yaga bata da niyyar bude masa kofar sai ya yanke shawarar kiran wayarta nan yaji wayar a kashe takaici kamar ya kashe shi ransa a masifar bace yaje ya lalobo spire key yazo yana kokarin bude kofar falon yafi awa guda kafin ya samu wanda ya bude kofar shiga yayi ya mayar da kofar ya rufe.........Kai tsaye bedroom dinta ya nufa ya tura kofar ya shiga tana kwance tana bacci sadidan, gadon ya haye ya janyota jikinsa ya fara abinda yake muradi....Cikin wani irin yanayi na tureshi daga jikina zaune na mi'ke na kunna bedlamp dakin yayi haske, tsira masa ido nayi ina kallonsa zuciyata na wani irin tashi, jikinsa na kyarma yasa hannu zai janyo ni na janye ina watsa masa harara. a sarqe yace." Kince na tambayi Jamila idan ta amince to na tambaye ta ta amince min da biyan bukatata." Nace." Ban yarda ba." Zaune ya mike da fadin."Kada fa ki sanya na gwada miki karfina ba zakiji dadi ba." Mikewa nayi na shiga toilet nai uziri na na fito na kwanta kan Sofa na barshi zaune a gadon yana bina da kallo! Cikin kunar zuciya ya sauko daga gadon ya isa inda take. "Kina so na mutu ko? ki duba kiga yanda hallitata ta fito." kallon inda yake nuna min nayi na d'auke kaina da fadin." Bari na kira yarinyar a waya naji daga bakinta." da sauri yace."Baki isa ba." Nace." Ai dama nasan karya kake kana satar kwana kana kawo min saboda rashin tsoron Allah.'' " Kada ki sake k'aryata ni." yafadi maganar a kufule. Nace." To idan kana da gaskiya ka bari a kira ta a tambaye ta mana." Tsugunawa yayi a gabana a sanyaye yace." Ko kin kirata ba zata saurareki ba saboda tana cikin fushi." Nace."Khalid wallahi kaji tsoron Allah kana azabtar da iyalinka kana kuma dorawa kanka nauyin zunubi." Ya jima yana kallona kafin yace."Wace irin azaba nake muku? kuna so na kwanta a kasa ku takani kenan.''? Girgiza kaina kawai nayi Yace."To mu bar wannan maganar muyi wacce zata taimaka mana." Nace "Kasan Allah yau kome za kayi ba zaka samu abinda kake so ba bani ma da lafiya ta kaina nake." A marairaice yace."Don Allah ki bari nayi ko Allah zai sanya ki samu ciki wallahi haihuwa nake so." Kallonsa nayi ya wani langwab'e kai sai lumshe idanuwansa yake. " Kayi hakuri ka bari sai girki yazo hannu tukkuna." Wani irin kallo yake min fuskarsa ta rikid'e da bacin rai yace."Saboda kinga ina sonki kike wulakanta ni." ? Kokarin bar masa gurin nake ya rike min hannu "Ba zan kara tunkarar ki da wata bukata ba." cikin zuciyata nace." Dama haka nake so." Hannuna ya saki yaje ya kwanta kan bed komawa nayi kan Kujarar na kwanta ina sauke ajiyar zuciya sosai naji dadin yanda yayi zuciya dama haka nake so ya kyaleni na huta.......Washe gari da safe babu yabo babu fallasa muka gaisa cikin rashin kuzari ya zauna yayi breakfast, yana shiga wanka kira wayarsa dake samar mirror, Ina dubawa naga sunan Ummatu. ajiye wayar nayi yana fitowa na fad'a masa, daukar wayar yayi ya zauna kusa dani..............."Rai a b'ace naji maganarta "Khalid ni zaka tozarta ko? me Jamila tayi maka kace ta fice maka daga gida."? Yace." Ummatu ki kwantar da hankali yanzu zan shigo na sheda miki dukkanin abinda yake faruwa." Tana kuka tace."Aa ai zuwanka bashi da amfani tunda ban isa na baka umarni ka dauka ba kana so ka tozarta ni ko to shikkenan kaje duniya ce." Kafin yace wani abu ta kashe wayarta. Shuru yayi da wayar a hannunsa nace."Me tayi maka da zaka kore ta a gidanka." ? Hannu ya daga min da fadin." Ba abinda ya shafe ki bane." Nace."Ya shafe ni tunda ya shafe ka." Tsaki yaja ya mike ya nufi wardrobe kayansa ya dauko yasa yana d'acin rai Nace."Don Allah duk abinda tayi maka kayi hakuri ka dawo da ita dakinta ina amfanin hakan idan laifi tayi maka bata wannan sigar zaka hukuntata ba tunda kaga 'yar uwarka ce.'' Uffan bece min ba ya kwashi wayoyinsa da key na mota ya bude kofa ya fita ya barni da mamaki...........Baito har kofar Gwaggo ta shiga ta dinga zazzaga masifa Gwaggo tace."Baito ni dik abinda yake faruwa bani da labari amma kuyi hakuri dukkaninmu mu jira zuwansa domin muji laifin da tayi masa. Baito tace."Bayan daukar kwanan da yake yana kaiwa Jikarki duk hakan be isheshi ba sai da ya koreta to wallahi daku da malamin dake muku aiki sai munyi maganinku." Gwaggo tace."Baito kece kika yarda da shirka da surkulle ni Allah kadai na gazgata saboda haka dik abinda zakuyi kuje kuyi." Baito na numfarfashi ta fita daga gurin...Ita kuwa Gwaggo hawaye kawai take sharewa tana jin bakin ciki da takaicin abinda yaron yayi.........Kwata-kwata Ummatu kin sauraran uzirinsa tayi ta rufe shi da fad'a Baito tana taya ta Jamila tazo ta fada musu karya da Gaskiya sun yarda da maganarta sosai al'amarin yayi masa ciwo ya kuma kudiri aniyar sakin yarinyar tunda ta zame masa annoba....Koda ya shiga gurin Gwaggo ma rufe shi tayi da fada tace."Wannan ai shashanci ne saboda kawai kun samu sa'bani da yarinya sai ka koreta wannan ba hukunci bane." Yace."Gwaggo yarinyar nan fa rashin kunya take min sam bata ganin girmana Sa'ida da take da shekaru sama da nawa tana bani girma tana mutuntani amma Jamila ban isa ta durk'usa min ba kullum cikin tsiwa da izgilanci har da zagi ni ba sakaran namiji bane wallahi matakin da zan dauka a kanta dukkaninku ba zai muku dadi ba." Gwaggo jikinta yayi sanyi tace."Kai amma yarinyar nan bata da mutunci ashe haka kake fama." Yace."Eh hakuri kawai nake da ita a gurin Sa'ida kawai nake samun sasaauci " Tace." To ni na zare hannuna a maganar duk hukuncin da zaka yanke kaje ka yanke hausawa suna cewa(Mai daki shi yasan inda yake masa yoyo.")
Sati guda da faruwar al'amarin Jamila taji shuru babu wani labari tana zaune a gida bata san makomarta ba kullum idan sukayi waya da Ummatu babu wata cikakkiyar magana sai kawai ta shirya ita da kanwarta sukaje har gida suka ci mutuncin Ummatu tas. Al'amarin yayi masifar bata tsoro cikin damuwa ta kira wayar Baito ta sheda mata irin cin mutuncin da jamila tazo tayi mata budar bakin Baito sai tace." Ai hakan da sukayi shine daidai tunda ke kin zama shashasha kin kasa tan'kawara d'anki sai abinda yake so zaiyi saboda haka ni banga laifin Jamila ba Ke da d'anki kun riga kun 'bata mana Zumunci dan haka kada ki sake kira na a waya mutukar ba abin arziki zaki fada min ba." Ummatu a ranar yini tayi cikin tsananin damuwa da tashin hankali, ashe da sauran rina a kaba dan a daran ranar Kawu ya sheda mata da maganar daurin auransa ranar Jumaa mai zuwa, ihu! ta dinga kurmawa kamar zautacciya ta nufi kofar Gwaggo tana kuka na fitar hankali....A lalace Gwaggo ta kalleta tace." Yanzu ke Rabi wannan ba abun kunya bane a gurin ki saboda kawai za'ayi miki kishiya kike kuka sai kace wata k'aramar yarinya." Tace."Gwaggo me nayi miki kika tsaneni yanzu ace Mijina zai kara aure amma a munafurce ni ba za'a fada min ba." Tace."Ashe nice munafuka tunda ni nasa shi yayi auran." Tace." To Gwaggo me yasa zaki sashi yayi aure bayan kema baki ta'ba zama da kishiya ba sai shi." Tace." Allah ne bai nufi mijina da ya kawo min abokiyar zama ba saboda haka idan zakiyi misali ki daina had'ashi dani Ibrahim zaiyi aure babu mahalukin daya isa ya hana abinda Allah ya hukunta." Ummatu tasa bakin hijabinta ta share hawaye ta bar kofar dakin cikin tsananin damuwa da tashin hankali.................Tun daga ranar daya nemi ni naki bashi hadin kai bai sake ba tsakanina dashi ido ne idan magana ta kama muyi ya shige ya tafi harkokinsa...........Ana ya gobe daurin Auran Kawu Hauwwa tazo take sheda min cewa sun tsayar da ranar daurin auransu ita da Yaya Aminu sosai nayi farin ciki da jin hakan, da zata tafi ta dinga tsokana ta da uwar biyu nace." Wai ke waye yace miki ciki ne dani." Hararata tayi da fadin." Kada ki rainawa kanki hankali mana gashinan duk kin sanja kammani kinyi haske da ki'ba goshinki sai kyalli yake." Murmushi nayi nace "Wallahi Hauwwa kunya nake ji wai yau nice dauke da cikin yaron nan Har bana so na fita jama'a su gane gashi gobe Kawu zai daura aure ina jin nauyin zuwa gidan sabida surutun mutane." Tana dariya tace."To menene abin kunya Yaro da babban duk aiki d'aya suke dan Khalid yayi miki ciki ba' abun kunya bane abun alfahari ne." Nace."Hakane." Sallama mukayi da juna na koma cikin gidan da tunanin halin da Gwaggo zata shiga idan ta fahimci cikin da nake dashi..........Washe Da sassafe muka shirya ni dashi muka nufi gidan.Gwaggo taci kwalliya da atampa super tayi lalle a kafafu da hannaye idonta rambad'e da kwalli dauri kuwa har gaban goshi Uwale na kusa da ita suna hira.....Khalid daga bakin kofa ya tsaya suka gaisa ya nufi massalacin da za'a daura auran........Tun kafin na zauna Uwale take rangwada bud'a tana kallona Gwaggo kuwa sai murmushi take tana gyara min gurin zama na zauna da kyar tace."Sannu ashe haka kikayi nauyi babu labari." Cike da mamaki nake kallonta tace."Ga ciki nan har ya huda zani kai alhamdulillhi Allah nagode maka." Nace."Gwaggo waye yace miki ciki ne dani.'' Tace."Idona ne ya gane min munafuka dake da mijin naki." 'Yar dariya nayi nace."Shima Khalid din be sani ba." Tace."Karya kike kina kareshi ne.'' Nace."To shikkenan idan ya shigo sai ki tambayeshi.'' Tace."Ai ba sai kin fada ba yanzu cikin watanshi nawa."? Shuru nayi ina tunanin watannin cikin.Uwale tace."Ai kin san cikin fari ba kowane yake iya gane sanda ya sameshi ba amma dai daka gani yayi kwari." Tace."Aikuwa dai cikin fari tunda ya huda zani ya fito to da alama daf yake da zuwa duniya." Uwale tace."To Allah dai ya raba lafiya." Cikin zuciyata na amsa da ameen ameen....Nace."Gwaggo a ina amaryar Kawu zata tare."? Tace."Can unguwar gadon kaya ne Khalid ya siya mata gida mai kyau shine uwarsa take bakin ciki yanzu maganar da nake miki ma tayi yaji tana gidansu sannan har gida Jamila tazo ta zageta taci mata mutunci tas." Nace."Kai amma banji dadin wannan labarin ba wallahi.'' Uwale tace."Ai duk wanda yace tukunyar wani ba zata tafasa ba to tasa ma ko d'umi ba za tayi ba.".................Khalid tun bayan kammaluwar daurin auran ya tafi harkokinsa bai dawo ba sai yamma likis sai da yaci abinci ya samu damar gabatar da sallar magariba.........Gwaggo ta kalleshi bayan dawowarsa daga massalaci tace."Sannu munafiki to abinda kuke 'boyewa yau Allah ya nuna min." Ya dinga kallonta yana mamakin maganarta. Ta kalleni da fadin." Kince shima bai sani ba ko."? Nace."Eh mana Khalid ko kasan ina dauke da juna biyu."? Kamar wani shashasha ya girgiza kansa." Mafici ta kwada masa da fadin " Ni zaku mayar shashasha ko."? Hankalinsa ya shiga yana kallona babu wasa a tare dashi yace."Yaushe kika samu cikin bani da labari."? murmushi nayi da fadin." Tsayin wata biyar kenan." Ya dinga kallona yana so ya gazgata magana. Nace."Kada kayi kokwanto domin kai ka kasance mara kula shiyasa baka fahimta ba amma lokatan da nake gudunka da kamshin turaranka yaci ace ka gane abinda yake da akwai."
Inda nake ya dawo ya fara kokarin daga rigata. na rike hannunsa da fadin." Me za kayi."? Kai tsaye yace." Gani zanyi." Gwaggo tace" Bude masa ya gani ya tabbatar.'' Kin bude masa nayi ya janyo ni jikinsa ko kunyar Gwaggo ya daga rigar cikina suka tsirawa ido ita dashi Gwaggo ta share hawayen farin ciki a fili tace.''Allah kasa ina da rabon ganin abinda ke cikin nan." Shi kam hannu yasa ya dauke 'yar 'kwallar dake kokarin fitowa daga idonsa yasa hannu kan cikin yana shafawa a hankali a hankali yace."Gwaggo kinga yaro na a cikin Aunty ko."? Gwaggo tace."Eh na gani Jarumi ikon Allah ai yafi gaban wasa ashe da kai zata fara haihuwa duk aure-auren da tayi kaddara ce rabon yana tare da kai." Yace."Gwaggo babu abinda zance da Ubangijina da yayi min wannan kyautar.'' Tace."Kwarai kuwa baka da bakin magana amma abinda za kayi ka kara kusanci dashi shine salatin ANNABI MUHAMMAD (SAW) Yace."Allah ya karawa Annabi daraja da wasila filjannati." Gabad'aya muka amsa da "Ameeen ya Allah.'' Zaune na mike ina gyara rigata yana min wani irin kallo ya janyo ni jikinsa rungumeni yayi tsam-tsam a jikinsa yace." Gwaggo ina rokon Allah ya dawwamar mana da zaman lafiya a zamantakewar auranmu sannan ina rokon Allah ya azurta mu da zuria masu albarka." Tana murmushi ta amsa da "ameeen ya Allah Jarumi Amma meye makomar Jamila ne."? Ajiyar zuciya ya sauke yace " Gwaggo nasha fad'a muku cewa babu wata mace da zan bari ta wulakanta min iyayena tun ranar dana samu labarin irin cin mutuncin da yarinyar tayi wa Ummatu na datse igiyar aura na da ita taje tayi aure ni na gama zama da ita har abadah." Gwaggo tace."Subahanallahi amma gaskiya banji dadin wannan al'amarin ba Jarumi me yasa ka yanke irin wannan hukuncin kana so duniya ta zage mu ko."? Yace "Gwaggo rabuwa ta da Jamila ita tafi alkairi saboda haka kiyi addua akan Allah yasa hakan shi yafi alkairi." Tace."To shikkenan Allah ya kyauta amma yana da kyau kaje kayi bikon mahaifiyarka a gidansu." Yace."Babu inda zanje mijinta shine zaije yayi bikon ta idan yana bukatar zama da ita saboda haka kada ki sake sanya ni cikin al'amarin tunda lokacin da sukayi auransu
17, October 2025
Fatima
Wow