Showing 18001 words to 21000 words out of 153671 words

Chapter 7 - GA IRINTA NAN Hausa Novels By Binta Umar Abbale.txt

27 Sep 2025

9595

Gwaggo na fad'a miki ki daina yarda da surutan mutane akan yarinyar nan shi aure lokaci ne dashi idan lokacinta yayi za tayi aure amma dan Allah ki daina d'ora mata lalura yanzu ina amfanin abinda kikayi Gwaggo da sassafe kin bunka a haya'ki a gida kin firgita yarinya tunda tace bata so ba sai ki k'yaleta ba."


"Kai Ibrahim ba fa zanyi asarar kudina ba dole sai nayi haya'kin nan tunda d'akina ne kuma idan ba aljanun ne da ita ba me yasa take guduwa mu da muke shak'ar haya'kin me yayi mana saboda haka ba zan fasa abinda nayi niyya ba idan tana da inda za taje ta tafi."


Khalid ya fito daga dakin fuska a murtuke yace."Gwaggo ina haya'kin naga irinsa." Kallonsa tayi lokaci guda ta fahimci abinda yake da akwai tace." Babu sauransa kenan nasa a wuta."

Kawu Iro yace."Gwaggo jiya ma fa haka kika ce sai gashi kuma yau da safe kin kuma kunnawa." Kuka ta fashe dashi tace."Yanzu dai kunyi min taron dangi kenan kuna kokarin 'karyata ni ko."?

Kawu Iro hankalinsa ya tashi ya dinga rarrashinta tace."Oh!oh! Ibrahim ai 'yar d'an uwanka ta fini a gurinka tunda gashinan a kanta kana nema ka 'kure ni."

Yace."Aa Gwaggo wallahi ba haka bane ina ni ina 'kure ki nayi laifi ki yafe mun." Ba tare da tace komai ba ta shiga dakinta ta bar mu a tsaye.

Kallonsa nayi naga duk hankalinsa ya tashi nace."Kawu ka kwantar da hankalin ka insha Allahu zan cigaba da hakuri da halinta." Yace."Yawwa Sa'ida dama abinda nake so kenan naji daga gurinki kiyi ta addua kinji ko komai mai wuce wa ne." Cikin dauriya nace."To Kawu nagode." Gurinsu ya nufa ya barmu nida Khalid a tsaye.....Yace."Aunty Sa'ida kada ki damu duk inda ta 'boye haya'kin zan bincika a dakin."

Nace."Khalid kyaleta dakinta ne fa tayi duk abinda take so da abunta." "Eh d'akina ne Sa'ida idan kinyi zuciya kada ki sake shigowa." Tana daga cikin dakin take magana.

Yace."Gwaggo wace irin magana ce wannan."?

"Haba Jarumi ai dole raina ya 'baci akan al'amarin nan ranar da naje 'karbo maganin nan sai da na yini banci ba bansha ba salloli na ma sai had'asu nayi amma saboda wukalancin Sa'ida ta dinga kokarin watsa min 'kasa a ido.


Yace." To wai waye ya saki ne? sai fa da nace dake kada kije okey to zanje har gidan ita Uwalen da take janki yawon gurin masu magani na gargad'eta akan hakan ni idan kinyi min baki ba zai kamani ba tunda dai ni ba Baba Iro ba ne."

Kuka tasa daga cikin dakin take fad'in "Khalid kada kaje kaci mutuncin Uwale bata cancanci hakaba." Ya d'aga labulan d'akin da fad'in."To idan bakya so naje gidan Uwale dauko min haya'kin."

Tace."Shigo ka kar'ba." da sauri ya shiga dakin nima naji wani sanyi a cikin raina.......Wani tsohon magani ta d'auko masa a 'karkashin gadonta a daure a wata tsuhowar leda ta mika masa da fad'in"Gashinan wannan jaraba ta isheni haka."
Kar'ba yayi ba tare da ya tanka mata ba ya fito daga dakin.

Yana fitowa yace." Ki kwantar da hankalinki ga maganin nan a hannuna zan fita dashi na zubar."

Hannunsa na kalla a take na gane ba maganin bane domin wancan a k'ulle yake b'akar leda wannan kuwa ledarsa yaluwa ce.....girgiza kaina kawai nayi na wuce na barshi a gurin, dakin na shiga na sameta tana murd'a redion ta ta dago kanta ta kalleni ta dauke kai tana cigaba da abinda take......gurin dana kwanta na nufa na dauki wayata na nemi gefan gado na zauna wayar na kunna na fara dube dube a ciki.......Ummatu ce ta shigo da jug d'in kunu da mai daidaiciyar silba da 'kosai a ciki.

Abin mamaki cikin mutuncin Gwaggo ta kar'ba "Sannu 'yar albarka ai Ibrahim yayi sa'ar mata Rabi wallahi ina jin dadin zama dake sabida kina mutunta ni Allah yayi miki albarka."


Ita kanta Ummatu sai da tayi mamaki da yake tasan halin Gwaggo sai tayi dariya kawai ta girgiza kanta ta fita daga dakin....Nima dana san dani take ban tanka mata ba na cigaba da duba text d'in da Alhaji Nura ya turo ina mamakin al'amarin.....Kiran wayarsa ne ya katseni da sauri na d'aga nasa a kunnena.

Yanda ya amsa gaisuwata yasa naji jikina yayi sanyi nace."Alhaji naga text dinka amma kuma ban fahimci abinda kake nufi ba."

A d'an fusace! yace."Sa'ida kada ki mayar dani 'karamin yaro mana, jiya kin turo min text din daya hanani bacci amma yanzu kina wata magana."

A nutse nace."Alhaji kayi hakuri kayi min bayanin da zan fahimta na dai ga text d'inka amma ban mayar maka da replay ba."

Ajiyar zuciya ya sauke yace."Haba Sa'ida kada kiyi wasa da hankalina mana, nifa ba yaro bane ballanatana kizo min da wasa da gaske nake auranki zanyi amma me yasa kin san akwai al'kawarin aure a tsakaninki da yaron nan Khalid kikayi wasa da hankalina."


Jikina yayi sanyi nace."Wace irin magana ce wannan waye kuma Khalid."? Lokacin da nayi maganar tayi daidai da lokacin daya shigo dakin shida Gwaggon suka zuba min ido....na cigaba da cewa."Alhaji ina tambayarka kayi shuru waye Khalid da har kake wata magana akansa yanzu a duniya na rasa mijin aure sai Khalid dan Allah ka daina wannan maganar sannan kuma text d'in daka gani mybe shine ya dauki wayata a bayan idona ya turo maka amma ni da hannuna wallahi ban tura maka wani text ba."


Ajiyar zuciya ya sauke yace."Okey to har naji dadi a cikin zuciyata yanzu a'ina maganarmu ta kwana."? nace."Insha Allahu yau ko gobe zan yanke shawara.'' Yace."Haba Sa'ida wace irin shawara ce wannan da har yanzu ba'ai yanke ba."?
Nace."Alhaji ka 'kara hakuri dan Allah." Yace."Shikkenan tom ina sauraranki." Sallama mukayi na kashe wayata rai a 'bace na kalleshi yana tsaye idonsa ya kad'a yayi jajazur!! sai wani irin kallo yake min.

"Khalid waye ya baka izinin d'aukar min waya."? Kai tsaye yace." Ni ne na bawa kaina izini ko kina da abinda zakiyi ne."? Cike da mamaki! nake kallonsa.

Ya zare min manyan idonsa da suka rine da 'bacin rai da 'bakin kishi yace."Ni kike ciwa fuska ko."? Nace."Meye abin cin fuska sarkin tsaurin ido ina kai ina Alhaji Nura da har zaka dauki wayata ka rubuta masa text kasan dai ya kusa haifarka ko."?

Yana 'kokarin magana Gwaggo tace."To daya kusa haifarsa mai zai nuna masa? namiji yake shima namiji yake sannan duk abinda yake dashi shima yana dashi sai me kuma."?

Kallonta nayi tace."Mara mutunci wacce bata san mai sonta ba, dame Alhaji Nuran yafi Khalid da har zaki dinga ci masa fuska."


Nace."Kinga Gwaggo ki cire kanki daga cikin wannan maganarki babu ruwanki ni babu wanda ya isa yayi min dole a gidan nan wanda nake so zan aura bana auran 'karamin yaro a kyaleni."


Gwaggo ta fashe da kuka had'e da fad'in "Zagi na Zakiyi ne naga kina zaburowa ko kuma dukana zakiyi butulu kawai."

Hawaye suka shararo min nace."Me nayi na butulci kuma? ina zaune a gado na mahaifina ina ciyar da kaina sai me? me nayi na butulci da har kike kirana da kalmar."

Jikinta ne kuma yayi sanyi ganin ina kuka.....Girgiza kansa yayi ya fita daga d'akin zuciyarsa kamar ta babbake saboda 'bacin rai.

Bayan fitarsa na share hawaye mi'kewa nayi na fara had'a kayan wanki, sai naga tana satar kallona cigaba nayi da abinda nake tace."Sa'ida kinga yau 'kosan yayi kyau gashi da zafinsa ki zuba kunun kisha sai kiyi wanki."

Nace."Aa Gwaggo ba zan sha kunu ba kisha kawai.'' Shuru tai tana kallona tsaf na gama had'a wankin na fita dashi can bakin rijiya na zubesu komawa dakin nayi na dauko indomee biyu 'karamin gas d'ina na kunna na d'ora tukunya da ruwa akai na zuba indomee a ciki.....ina zaune a gurin ta dahu na juye a plate kana na kashe gas d'in. Nan tsakar gidan na zauna a nutse naci na fara ci ina Nazarin rayuwa wai ni Gwaggo take kira da Butulu hummm! rayuwa kenan.



*Masoya a taimaka da sharing👏🏼*



*IDAN KINA BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN GA YANDA ABIN YAKE.....VIP GRUOP#600 NORMAL GROUP #300 ACCOUNT... 0542382124.....BINTA UMAR GTBANK....IDAN KATI ZAKI TURO #400 NE SAI KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER*
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/6, 2:04 PM] Umm Muhammad: *GA IRINTA NAN!!!🙆🏼‍♀️*
_(LOVE STORY🌺)_
*NA*
_BINTU UMAR ABBALE🍒_
*MANAZARTA WRITES ASSO🖊️📚*


*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA GUDA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*

_*Ina kaunar ku iyayena ina kuma alfahari da irin kaunar da kuke nuna min💜🥰*_


*13*
A daran ranar Gwaggo kasa rintsawa tayi asubar fari ta tashi tai alwala tayi sallah da carbi a hannunta ta fito kai tsaye gurin baba iro ta nufa ta shiga bubbuga musu kofa. Lokacin shi yana massalaci bai shigo ba, bugun kofar da take ya tashi khalid a firgice ya mike zaune dama shima sai dab da asubah baccin ya daukeshi agogon da yake kafe a bangon dakin ya kalla shida da rabi da sauri ya dauki brush dinsa ya fito.....kallo ta bishi dashi da fadin."Kada dai kace sai yanzu ka tashi."? kansa ya daga mata ya ratseta ya wuce bayansa tabi da kallo kafin tace."Khalid me yasa kake wasa da sallah ne."? ba tare da ya tanka mata ba ya dauki buta ya shiga bandaki, sai itama ta bar gurin ta nufi dakinta ta zauna cikin alhini da damuwa.

Baba Iro ne ya shigo dakin da carbi a hannunsa suka gaisa yace."Gwaggo ya kike ganin za'ayi ne."? Tace."Ibrahim ni da kaina zani gidan Alhaji Shamsun dan bana tantama can ta nufa kome suke ji dashi na rantse ni nafi karfinsu Sa'ida ikona ce dan haka tilas ta dawo gabana ta cigaba da zama."

Yace."Gwaggo kada ki fusata komai cikin nutsuwa za'ayi Alhaji Shamsu babban mutum ne mai mutunci bai kamata kije har gidansa gaban iyalinsa kici masa mutunci ba."


"Ibrahim bafa zan zauna nayi lako-lako ba wato ka manta irin d'auki ba dad'in da mukayi dasu a wacan karon ko wane irin abune baiyi ba akan lallai Sai Sa'ida ta zauna a hannunsa to wannan karon ma ko yafi 'kuda naci ba zata zauna a gidansa ba domin bamu gaza dayi mata komai ba."

Baba Iro yayi shuru yana mamakin halin mahaifiyarsa yasan halinta da rashin tsinkaye da hangen nesa zata iya zuwa gidan mutum gaban iyalinsa ta tsinka shi wannan dalilin yasa yayi wani tunani....."Gwaggo ki nutsu ki kwantar da hankalin ki insha Allahu Sa'ida zata dawo gida da kaina nake so naje gidan mu tattauna da Alhajin yana ganin mutuncina sosai itama Sa'idar haka da yardar Allah tare da ita zan dawo gida."

"Aa Iro gwara mu tafi tare ayi komai a gabana wallahi nake fada maka jiya kewarta hana ni rintsawa tayi.'' Yace." Ai bake kad'ai ba Gwaggo ni kaina banyi bacci ba amma insha Allah komai zai zo da sauki kiyi hakuri naje ni kad'ai din."

Shuru tayi alamar bata gamsu da maganarsa ba...Khalid ya shigo dakin suka gaisa da mahaifin nasa tace."Khalid kaje ka aro adaidaita sahun abokin ka kazo ka dauke ni ka kai ni gidan Alhaji Shamsu."


Babu walwala a fuskarsa yace."Me zakije kiyi."? da sauri tace."Zanje na dauko Sa'ida ne." Yace."Gwaggo babu inda zakije aunty Sa'ida zata dawo da kafafunta bayan haka kuma shi wanda zai bani aron adaidaita sahun nasa ya fita aiki da ita saboda haka ki zauna a gida zamuje nida Baba."

Da sauri tace."Zakuwa ku gan ni a gidan domin kuwa Allah ya hore min kudin mota.''

Baba Iro cikin rarrashi yace."Gwaggo abinda nutsuwa bata bayar ba to tashin hankali ma ba zai bayar dashi ba dan Allah ki nutsu kada kizo ki aikata abu daga baya kizo kina jin kunya Alhaji Shamsu bai cancanci tozarci a gurin mu ba yana kuma da ikon ri'ke Sa'ida a hannunsa tunda yana matsayin mijin mahaifiyarta.

Tace."Ai kaji abinda nake gudu dama nasan ko kaje ba wani mataki zaka dauka ba karshe ma ka dawo gida kai kadai ba tare da ita ba to sai naje na fada maka."


Khalid yace."To kije d'in kina shiga gate din zan sa masu gadi su saki karnuka kin san zan iya ko." shuru tayi tana kallonsa, Yace."An fada miki cewa komai a hankali da nutsuwa ake binsa amma kin kasa ganewa." tasa kuka da fad'in "Khalid bana son Sa'ida tayi nesa dani shiyasa kaga duk hankalina ya tashi bana so wannan karon Alhaji Shamsu ya samu galaba akan mu."

Yace."Ba zai samu ba insha Allahu." hawaye ta share tace."Khalid shiyasa nake so ka aureta na dinga ganinku a gabana inaso ku haifa min zuria mai yawa."

Tausayi ta bashi yace."To Allah ya amsa adduarki ina fata dai yanzu kin janye maganarki ta zuwa gidan." Tace."Tunda kunfi karfina na hakura ina zuba ido kuje ku dauko min ita."


Baba Iro yace."To Alhamdulillahi bari na kimtsa na fito, yana kokarin fita ta kira sunansa, juyowa yayi yana kallonta tace."Maganar Rabi baka ce min komai ba."

Yace."Tun jiya tana gidansu ai." girgiza kanta tayi tace."To wannan hukuncin daka yanke ni yayi min daidai na kuma ji dadi gobe ma sai ta sake aikatawa amma inaso yau idan Sa'ida ta dawo gida kaje kayo bikon matarka."

Yace."To Gwaggo yanda kika ce hakan za'ayi.'' ya juya da niyar fita sai ya tsaya da fad'in ."Me zaki karya dashi na aika a siyo miki." Tace."Ibrahim ba sai kayi asarar kudin ka ba ina da d'umame gashi can a jibge yanzu zan d'umama kafin ku tafi sai kuci."

Yace."To shikkenan Gwaggo." Bayan fitarsa daga dakin sai ta fara janyo kwanukan abincin tana dubawa doyar babu abinda tayi sannan itama farar shinkafar da Ummatu ta dafa a daran ranar ba tayi komai ba ta mike ta fita da kwanukan abincin a hannunta tana fad'in "Ruwan zafi kawai zan sa na turara shinkafar tunda da abincin ai ba sai anyi hidimar siyan wani abu ba."

Tsaf ta gyara abincin ya dawo tamkar sabo ta dauko ta kawo daki....cikin plate ta zuba masa ta zuba masa miyar nama da yawa.....yace." Gwaggo a'ina kuka samu nama haka."?

Tace."Kasan duk sati Alhaji Nura yakan kawo mana cefane to jiya da ya kawo sai Sa'ida tayi mana miya harda kayan shayi ma watakila ta tafi da abunta."


'Bata fuska yayi yace."Gwaggo nayi sha'awar abinci amma ba zanci ba." tace."Sabida me Khalid."? Hankalinsa nakan wayarsa yace."Saboda ina kishin mutumin na tsaneshi wallahi."

Tace."Khalid ka kwantar da hankalinka kai zaka auri Sa'ida Alhaji Nura kuwa shi yaga zai iya wahalar da kansa mu dai duk abinda ya kawo hannu biyu zamu sa mu 'karba.


Yace."Gwaggo idan kina bukatar farin ciki na to ki daina cin abinda mutumin zai kawo wa aunty Sa'ida wannan shine abinda nake bukata dake."

Shuru tayi tana girgiza kanta bata tsammanin zata daina cin kayan dad'in da Alhaji Nura zai kawo musu amma saboda ta kwantar masa da hankali tace."To shikkenan tunda baka so na daina."

Mikewa yayi zai fita tace."Yanzu Khalid kana kallon abinci da kyau amma kace ba zaka ci ba." Girgiza kansa yayi yana ta'be bakinsa yasa takalmansa ya fita..........Baba Iro ya shiga dakin cikin shiri yace."Ina Khalid din." tana tsotse 'kashin hannunta tace." Wata'kila ya tafi gurin mai shayi.'' da mamaki a tare dashi yace."Wannan abincin fa."?

Tace."Ibrahim kasan Khalid da zuciya da kishin kansa wai ba zai ci ba saboda yana kishi da wanda ya kawo cefanan."

Baba Iro ya zauna kusa da ita yana girgiza kansa mamaki yake sosai akan irin tarangahumar d'an nasa in banda abinsa inashi ina Sa'ida ko da yake Namiji komai 'kan'kantarsa mutukar ya balaga to mace duk girma da shekarunta bata gagararsa.....Gwaggo ta zuba masa abincin tasa masa miya da uban nama akai." Yace."Gwaggo ki rage naman." Tace."Ibrahim kaci ka 'koshi ka barshi.''

Bisimillah yayi ya fara cin abincin. dakin yayi shuru na tsayin minti biyar yace."Gwaggo ya kamata mu samu zama da mutumin nan idan da gaske yake akan yarinyar nan ya fito ayi abinda za'ayi."

Da sauri tace."Ko da gaske yake ba zamu bashi Sa'ida ba tunda Khalid ya nuna yana so hausawa na cewa gida bai koshi ba ba za'a kai dawa ba."

Yace."Gwaggo duk da Sa'ida budurwa ce to bai cancanci ayi mata dole ba shin da bakinta kinji ta furta tana san auran Khalid."?


Girgiza kanta tayi tace."Aa bata furta ba asali ma kullum cikin fad'a da juna suke sam basa jituwa dalilin ma kenan da yasa naje na kar'bo taimaiko gurin mai magani Ibrahim yarinyar nan Sa'ida na tare da iskokai kaga kuwa idan ba na gida ne ya aureta ba to babu shakka akwai matsala shiyasa kaga sam! bana sha'awar wani na waje ya aure ta."


Baba Iro shuru kawai yayi ya cigaba da cin abincinsa, shi kam ba zai iya da rigimar mahaifiyarsa ba mutukar shine madaurin auran Sa'ida to ba zai daura mata aure da wanda bata so ba.


To Cikin nutsuwar zuciya na wayi gari a gidan mahaifiyata, sai da nayi wanka tsaf na shirya jikina sannan ta shigo dakin fuska a sake tace."Sa'ida kinji shuru ko." Murmushi kawai nayi nace."Umma ai nasan inda kike ina fata kin tashi lafiya."?

Tace."Lafiya kalau alhamdulillahi Jiya duk na shedawa Alhaji abinda yake faruwa shima al'amarin bai masa dadi ba ko kad'an dan haka ya yanke hukuncin kan cewa ko zaki koma can gidan sai kin kwana biyu anan kin samu nutsuwa tukkuna."

Ajiyar zuciya na sauke cikin zuciyata ina jin dadin hukuncin da ya

17, October 2025
Fatima

Wow

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login