Showing 153001 words to 153671 words out of 153671 words
Chapter 52 - GA IRINTA NAN Hausa Novels By Binta Umar Abbale.txt
ban sani ba." Yanda ya fadi maganar ya nuna mata cewa ransa a 'bace yake. Tace."Kayi hakuri ba laifin Ibrahim bane tunda shi dai bece mata ta tafi gida ba itace ta tafi." Yace."To idan yana ra'ayin cigaba da zama da ita sai yaje yayi bikon ta." Tace."Sosai kuwa ai dole ma yaje ya daukota ta dawo dakinta ta zauna kishiya kuma ba akanta aka fara ba.".............Kwanciya nayi bacci na nema ya dauke ni yace na tashi mu tafi gida Gwaggo tace." Ka barta ta kwana mana." Girgiza kansa yayi yace." Gwaggo mai rabani da matata sai mutuwa ba zan barta ba" Tace."To ai shikkenan ba sai ka fada min bakar magana ba." Ni dai dariya kawai nake musu tana fada yana fad'a haka muka fito har soro ta rako mu tana mana fatan alkairi...............Bacci nayi a motar sai da muka isa gidan ya tashe ni da kansa ya bude min mota na fito, ya rike hannuna muka nufi cikin gidan sai tarairayata yake har yaso ya bani tausayi. tare mukayi wanka na dinga Jin feelings na taso idona a lumshe nake kallonsa yana cud'a jikinsa nace."Kazo kayi min idan ka gama. Yace."Okey kada ki damu ." Yana gamawa ya daura towel yazo yana min duk sha'awar dake taso masa danneta yayi ya kauda kansa yayi mata wankan kamar yanda ta bukata, yayin da ita kuma nata b'angaran tayi masifar galabaita sai kallonsa take tana lumshe ido da lasar lips hannunta ya rike suka fito daga toilet din gefan bed ya zaunar da ita ya bude wardrobe kayan bacci ya dauko musu yasa nasa ya karaso gadon da nata, da kyar na iya kar'bar kayan nasa a jikina na kwanta ina kallonsa zaune a Sofa yana duba wayarsa a sarqe nace."Kazo ka kwanta mana." Yace."Yanzu zanzo kada ki damu." lumshe idona nayi ina jan ajiyar zuciya.....Jin shigowarsa cikin bargon yasa na sauke ajiyar zuciya dan motsawa nayi na Juyo ina kallonsa idonsa a rufe bakinsa yana motsi da alama adduar bacci yake.....Sunansa na kira ya bude ido yana kallona nace."Babynka yana bukatar ku gaisa." Murmushi yayi yace " Yanzu zamu gaisa" Dad'i ne ya ratsa ni, dan matsowa yayi ya daga rigar jikina sumbatar cikin ya dinga yana surutai Na dinga murmushi ina kallonsa ya gyara min rigar yana kallona fuskarsa na fitar da annuri yace."Mun gaisa yace yana gaishe dake." Dariya nasa nace."Aa ni ba irin wannan gaisuwar nake so kuyi ba." Tsira min ido yayi yace" Wace iri kike so."? Jikinsa na matsa nasa hannuna a kirjinsa da fadin.'' Irin wacce kuka kwana biyu bakuyi ba." Yace." To ai ke kika hana mu shiyasa na kyale ki." Da sauri nace." To yanzu ina bukatar ku gaisa" a kasalance yace."Kin amince kenan."? Nace." Eh na amince ku gaisa sosai da sosai." Murmushin jin dadi yayi yasa hannu ya janyota jikinsa ya rungume ta tsam-tsam! a kirjinsa suka dinga sauke wani irin numfashi........
*ALHAMDULILLAHI*
_Jama'a Nan na kawo 'karshen wannan Littafin mai suna GA IRINTA NAN! Ina rokon Allah ya yafe min kuskurena ladan dake ciki kuma Allah ya had'amu dashi Ina mika godiya ga 'Yan Vip group godiya ta mussaman a gare ku, dubban masoyana ina godiya ta mussaman nagode kwarai da adduarku Allah ya kara kauna ina alfahari daku💜🤝🏻 Sai mun sake saduwa daku a littafina mai zuwa. NAGODE_
*LITTAFAN MARUBUCIYAR*
*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUDI*
*GIMBIYA BALARABA*
*BABBAN YARO*
*MASHAHURI*
*LADADI KWADAGA*
*SADAUKI OMAR*
*NIDA YAYA SADAM*
*TSANTSAR BUTULCI*
*'YAR BANGAR SIYASA*
*DA WATA A KASA*
*MADADI*
*RUWAN DARE*
*KWARYA TABI KWARYA*
*GA IRINTA NAN*
*Ga mai bukatar d'aya da cikin books din sai ya nemi wannan numbers domin karin bayani 08089965176_07084653262* *BINTA UMAR ABBALE*
17, October 2025
Fatima
Wow