Showing 33001 words to 36000 words out of 58385 words

Chapter 12 - BA JININA BACE Book Complete by Hassana Abdul'aziz Yakasai .txt

ta d'an kafe shi da ido yadda taga yayi mugun yin kalar tausayi idanunsa da ta kalla kuwa sai da gabanta yai masifar fad'uwa da sauri ta mai da kanta k'asa.












Abinda ya k'ara bata tsoro yadda ya zame ya durk'usa agabanta yana kallon cikin idonta yace "dan Allah princess in rok'i wani alfarma a wajen ki?"




Yadda yayi matan ne yasaka batasan sanda ta d'aga masa kai ba alaman shi take sauraro " dan Allah princess ina so na zama amininki na k'ut da k'ut yanda komai zakiyi sai kin sanar dani nima duk abinda zanyi sai na sanar dake sannan dan Allah yaron jiya kar ki k'ara d'aga kiran shi namayi blocked d'insa dan Allah kimin wannan"










"Aini bazan iya abota dakai ba kai mugune baka da tausayi daman ai su sojoji basu da imani shi yasa na tsan"..........bai bari ta k'arasa ba yayi saurin rufe mata baki da hannunsa cikin sanyin murya yace "zokiji Allah na daina daga yau bazan kara b'ata miki rai ba"










Idan na tabbatar da hakan sai na zama friend d'in naka amma ni yanzun banyin abota dakai yasin dan zaka iya kashe ni wata rana ai dama Mama tace komai dad'in ka da 'yan " ke"






Ya buga mata wani shegen tsawa "wallahi kika Kuma min zancen d'an ubannan sai na sab'a miki kammani yanzun nan haba kin ishe ni da wani'yan uba'yan uba'yan uban............ya dank'aro k'aton asher ya dank'ara kafin yaci gaba da fad'in duk wanda yasa miki wannan tunanin jakine shi dabba ne mai kwakwalwan kifi Kuma daga yau ina so kisa aranki cewa baki da wani d'an uba duk uwa d'aya uba d'aya muke agidannan tashi ki fita" ya fad'a cikin daka mata tsawa yana nuna mata k'ofa ai da gudu ta fella cikin rawan jiki dan yanayin sa ba k'aramin firgita ta yayiba.










Komawa yayi saman kujeran da ta tashi ya zauna tare da kwantar da bayansa yana fitar da wani mugun huci me azabar zafi aduniya bai tab'a ganin matar daya tsana kamar Sailuba ba ya tsane ta ya tsane ta ya tsane ta har baisan yadda zaiyi ba
















MAMAN ISLAM CE
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*




☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀


FCWA


*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*


https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥BA JININA BACE🔥


2021


NA


HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI


MAMAN ISLAM








. page 28






Tana shiga d'akinta ta mai da k'ofar ta rufe kamar ance ya biyota ne, k'arasawa tayi bakin gado ta zaune tareda dafe k'irjinta da har lokacin bai bar bugawa ba ta "jarababbe kawai mutum babu abinda ya aje sai masifa ta fad'a tana kwanciya akan gadon bata jimaba kuwa bacci yayi awon gaba da ita.












Tunda ya zauna ya lumshe idanunsa zuciyar sa na masa zafi, so yake kota wane hali sai ya raba Maryam da haj. Sailuba domin wannan matar bata da maraba da matar shed'an muguwar hatsabibiya ce tasan takan mugunta shi kansa yana tsoron shirin da take kan 'yar mutane domin yafi kowa sanin cewa ba rainon banza haj. Sailuba tayi wa Maryam ba dan bata aikin banza shi yasa yake son ko ta wane hali ya yakice Maryam daga jikinta kafin ta kai ga halaka ta.














Ganin zaman sai k'ara bijiro masa da wasu irin tunaninka yake yasa yai wanka ya bar gidan.










A falon Baffa kuwa bayan sun gama d'an tab'a hiransu kamar yadda suka saba Baffa ya d'an dubi matan nasa yace "yau ina so naje k'auye ba kuma zan dawo yau d'in ba sai Allah ya kaimu gobe"








A matuk'ar firgice haj. Sailuba ta d'ago tana duban Baffa cikin tashin hankali yaushe tayi wannan saken ca take ta riga da tagama da babin wannan tsohuwar me shegen taurin kan tsiya ai kuwa zata gyara mata zama yanzu dai ba ta ita take ba ta wannan 'yar matsafin mutumin da aiki baya cinta take.












A fuska ma nunawa tayi tafi kowa murnan zuwansa a bad'ini kuwa ji take kamar tayi ta ihu domin har ga Allah tun lokacin da Inna ta bada shawarar ayi mata kishiya ta sha alwashin sai ta d'an d'ana mata guba fiye da wacce ta d'an d'ana mata.














Sai da ya fara zuwa wajen malam Babba kamar yadda ya saba yauma saida ya bashi rubutu yasha ya shafe jikinsa sannan yake bashi a duk lokacin dayake gari, kafin ya sanar dashi zaije ganin gida ba k'aramin dad'i malam yajiba domin hasashen shi yazama gaskiya cewa Baffa rabashi ake son yi da mahaifiyarsa shi yasa yaji sam baya son zuwa, amma duk wanda yake wannan abun sam bai kyautawa kansa ba.














Bayan fitar Baffa babu jimawa itama ta shirya ta fice bata zame ko ina ba sai wajen bokanta kasancewar haj. Zakiyya sunbar k'asar da mijinta yasa batama tsaya b'ata lokacin tab'a ta wuce abin ta.












Bayan tagama korawa bokan ta bayanin aikin da take son yayi mata ya jima sosai yana zane cikin k'asa kafin ya d'ago ya dubeta yace. "akwai abubuwa da yawa wanda kika jima kina k'ullawa duk tunaninki basa yiyuwa?"
Ya fad'a yana kallonta, shiru tayi domin batayi tunanin aikin da take yana ciba dan bata ganin nasara a ciki.












Aikin ki yana ci kuma abubuwan da kike sunyi yawa kuma duk ta sigar da kika d'auko hanyar wargaza komai tanan zai wargaje zaki sha mamakin rana da lokaci da waje amma kuma akwai cin amana da bayyanuwar asirinki daga baya daga wajen mutum mafi kusa dake wannan shine ki tashi kije da baya banda waiwaye daga yau bazai k'ara zuwa wajen uwarsaba sai dai ita tazo shi da garin nan sai dai yaje gaisuwar ta bayan ta rasu.
















Tunda takwanta take waau irin mafarkai marasa kan gado sosai take jujjuya kai tana gumi babu abinda yafi rud'a ta sai tsintar kanta da tayi a wani a hali mara dad'i tana cikin jujjuya kai kamar wacce aka tasa ta bud'e ido a firgice, sai da tayi addu'ar tashi a bacci kafin ta mik'e cikin tashin hankali ta hau karanto hasbinnallahu wani imal wakil sosai abin ya tsaye Mata arai.










D boy ne a office d'in babanshi suna hira yake sako masa maganar Maryam Abba AL HASSAN yace " 'yar waye?"
" 'yar Baffa Abubakar ce"
" Kai k'arya ne wallahi badani ba ka rasa wa zaka d'auko min a matsayin suruka sai k'anwar wannan bom d'in wallahi ba isa ba baka isa ba nace dan ubanka"










"Ni wallahi Dad ita nake so dan haka banga wanda ya isa hanani aurenta ba waima Dad meke tsakaninka da yayannata ne naga ko sunan su kaji saika firgita?"












"Ban sani ba dan uwarka kuma muddun nine ubanka ban yafe maka auren wannan irin masifar ba"
" Muddun kaga ban aure taba ka tabbatar mutuwa nayi amma kai baka isa hanani auren taba wallahi" ya fad'a cikin dukan teburin tsakiyar su cikin murgud'a baki kamar wani sa 'ansa,


Wannan ba komai bane a wajenshi dan al amarin gidan Abba AL HASSAN babu tarbiyya ko kad'an da gaba d'aya sun gama sangarta d'an nasu kasancewar shi kadaine d'an da suke da.










"Tunda haka kace to wallahi babu ruwana duk abinda ya biyo bayan ka kar kasawa ranka cewa na san ka dan wallahi ko kallon inda kake bazanyiba.








"Ba damuwa" Kamal ya fad'a yana ficewa daga office din










Plss manage








Daga taku MAMAN ISLAM CE


بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*




☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀


FCWA


*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*


https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥 BA JININA BACE🔥

2021
NA


HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI


MAMAN ISLAM








Page 29


Wanka tayi ta tayi alwala dake lokacin an fara kiran Azhar dan haka tana gabatar da sallar ta shirya tareda daukar bag d'in ta ta fito babu kowa a falon sai Ammey.








"Ina zaki haka?" Ammey ta tambaya tana kallon fuskar ta dayake cike da damuwa' kamar bazata tanka mataba sai kuma tace "shopping" kamar maijin tsoro tayi maganar"
"Zonan" Ammey ta kirata kallon Ammeyn tayi kamar tayi mata gardama sai kuma ta karasa kusa da Ammeyn ta zauna ta d'an jingina jikinta dana Ammeyn,abinda bata tab'a yiba iya tsawon shekarun datayi a hannun haj. Sailuba batama samu anbar ta taje inda take ba bare ta rab'etan.










Wata irin ajiyar zuciya Maryam ta sauke mai k'arfin gaske lokacin da ta kwantar da kanta jikin mahaifiyar ta ita kanta Ammeyn sai dataji wani iri aranta bata san sanda wasu irin hawaye suka zubo mata ba tayi saurin gogewa dan kar tagani.






Duk inda uwa take ko a ina ne ko a wane hali take ta fita daban hakanne ya kasancewa Maryam jitai wani irin nutsuwa na shigarta tareda wani d'an Karen sanyi da ya dirar mata lokaci guda alamun zazzab'i keson kamata.








Haka nan batasan dalil ba kawai taji ta kama hawayen da batasan ko na menene ba tun iya hawayen ne har tafara shashshek'a, a rud'e Ammey ta d'ago fuskar ta tana kallon yadda take shashshek'a kallon lips d'inta tayi yadda suke rawa sosai batasan sanda ta k'ara k'ank'ame ta ba tana d'an buga bayanta kad'an kad'an batare da tace komai ba domin tasan tabbas itama idan tayi magana nata kukanne zai fasu.












Sai da suka shafe ak'alla mintuna uku kafin Ammey ta d'ago ta ta fara share mata hawayen "me yake damunki?"
Ta tambaye ta ahankali kamar tana jin tsoron wani yajita tace "Ammey jikin yafi na Mama dad'in kwanciya kuma ga d'umi,dan Allah Ammey nima ki rik'a rungumeni kamar yadda kike wa Nassar"










"Naji amma sai kin fad'a min abinda yake damun ki kwanakin nan, na lura kina da damuwa keep ki fad'a min koda ahawaran da zan baki" kallon Ammeyn ta dingayi babu k'ak'k'autawa yayin data ta dinga jin wani abu mai sanyin gaske yana ratsa ta, tunda take da maman ta bata tab'a tambayar ta damuwanta ba sai dai idan taganta a damuwan ta d'ebi manyan kud'ad'e ta bata tace taje ta kore damuwan ta.










" Ina jinki'yar albarka maza ki fad'amin ki d'auka cewar kina fad'awa mahaifiyar ki ne kima sa aranki cewa ni mahaifiyar kine zan miki maganin duk wani damuwaki a duniya,wanda kuma yafi k'arfi na zan fad'a wa ubangiji na"










Ammey ta fad'a tana saurin goge hawayen daya zubo mata dan kar ta gani Muhammad dayake tsaye bakin k'ofar tun sanda Ammey ta kira Maryam ya saki wani boyayyar ajiyar zuciya aransa yana fatan Allah ya karya ak'adarin haj. Sailuba.














"Ba komai" ta fad'a a hankali "kwai baby command fad'a min kinsan babu kyau d'a ya rik'a wa mamansa k'arya" batasan sanda ta rushe da kukaba tace "Ammey k'udi sune maganin ko wane matsala?"
Ta tambaye ta abinda yafi komai damunta a rayuwarta
" Injiwa?
Duk wanda ya fad'a miki wannan k'arya yake ko waye yana yaudarar kine kawai, amma akwai abinda k'udi bai isa yayi maka shi ba da yawa ma a duniya dan haka duk wanda ya fad'a miki hakan yayi karya ya fad'i son ransa ne kawai"




Ta fad'a tana shafa kanta nan "Mama ce koya ta ganni a cikin damuwa sai ta d'ebi manyan kud'ad'e ta bani tace zasuyi min maganin ko wace irin matsala a duniya" duk da cewa tasan zata iya jin abinda yafi haka daga d'iyar tata ma amma hakan sai yayi masifar d'aga mata hankali tace










"Tana iya miki kyautar nawa lokaci guda?" Ta tambaye ta cikin tsantsar tashin hankali "har dubu d'ari biyar cash tana bani tace muje mu kama waje muyi d'an kwarya kwaryan walima wai na jikina ma su mori arzik'in ubana"




"Kina yi?"
Ammey ta k'ara jefo mata wani tambayan "da inayi amma yanzun tara k'udin nakeyi da sukayi yawa na sai gida kuma da wasu kusan 7 million a d'akina har sani fa take na d'ebo mata k'udin Baffa kinsan baya k'irga wa yake ajiyewa"






"Innalillahi wainnailahi raji un" shine abinda Ammeyn ta fad'a cikin tashin hankali "Allah sarki Nanne da Anty shamsiyya yau ga abinda kuke fad'a min yana shirin faruwa tayi maganar cikin zubowar wasu zafafan hawaye.










Da sauri ta share hawayen tace"kin yarda dani zaki iya bani ajiyar duk abinda kika mallaka?" Ta tambaye ta cikin rawan murya
" Eh Ammey me zai hana ta bata amsa yayin da wani irin sanyi yake kwaranya aranta
"Yayanku fa?" ta k'ara tambayar ta
"Tab'ni bazan bashi ba mugu ne gashi masifaffen tsiya ta fad'a tana hararan gefe.




Murmushi Ammey tayi shi kanshi Muhammad dake bakin k'ofar maganar ta ya bashi dariya dan haka ya d'an murmusa yana shafar k'irjinshi a hankali kamar wanda wajen yake masa ciwo






"Kece baki gane halinsa ba amma yana da kirki sosai kuma zai kula daku sosai koda ace yau babu Baffa baku da sama dashi SHINE GATANKU"










Tab'e baki tayi ta mik'e tana cewa "anjima zan kawo miki A T M d'ina Mama bata san dashi ba saboda shegen kashe k'udin ta idan ta sani duk saita rance kuma ba biyana take ba, tunda kince kin yarda dashi sai ki bashi zan had'a shi kuma da na siyi gida ta hanyar sa wallahi ya cinye kwandala ta bazai yi ciwon kai ba biyana zaki"










Duk yadda yaso dauerwa saida ya fashe da dariyan maganta domin ta bashi dariya sosai wallahi, ita kanta Ammeyn murmushi take kafin tace "yanzun to ina zaki naga ko abinci baki ciba"


Eh banjin yunwa zanje shopping, ina Nassar ya rakani?"
"Za daiki siyan kayan zakin da kika saba maza muje yau nima na fanshi hajiyan tunda bata nan muje na baki da kaina tunda ta gama shagwab'a ki"
Sai taji ta kasa yi mata musu tana zuba mata abincin kafin ta fara bata MD ya shigo wajen da sallama Ammey ta d'ago ta dubeshi ganinsa da kayan gida tace "yau kuma ina uniform d'in?"






"Banje office ba yau?" Ya fad'a yana zama facing d'in Maryam datai wani kicin kicin da rai, murmushi ya saki lokacin da ya juyo da hannun Ammey santar bakin sa ya amshe abincin da ta d'ebo zata kaima Maryam baki, bata san sanda ta b'alla masa wata shegiyar harara ba ta juya ta kalli Ammey a marairaice tace Ammey"








"K'yale shi baby in yasa tsiya yanzun zan korashi amshi maza kici ki k'oshi kinji yarinyar kirki ta fad'a tana bata, sosai taci abincin, tunda take zata iya runtsawa cewar bata tab'a samun farin ciki irin na yau a rayuwarta ba sai taji Ammey ta bala in kwanta mata arai.
















tana gamawa tasa tusio ta goge bakinta ta zari mukullin motar ta"sai na dawo Ammey"
"Baki ba Ammeyn ta fad'a tana mik'ewa ta k'arasa kusa da ita kanta ta dafa tayi mata addu'a sosai kafin tace "Allah ya tsaremin ke ki kula da kanki ki kare mutuncin ki domin shine Martaba ki"








Wani irin sanyi Maryam taji aranta ta rungumeta ta tace "na gode sosai Ammey dan Allah ki rik'a min haka please"
"Kullum nake miki haka amma ba kusa da kusa ba amma ko yaushe kece farkon wacce nake fara yiwa addu'a kafin nida kaninki da sauran makusanta na"
"Allah Ammey?" Maryam ta tambaya ciki farin ciki tare dajin yadda matar tak e k'ara bin dukan jikinta, dama haka halin Ammeyn yake amma mama tace muguwa ce.
























MAMAN ISLAM CE
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*




☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀


FCWA


*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*


https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥 BA JININA BACE🔥


2021


NA




HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI






MAMAN ISLAM










Page 30






Rungumeta ta k'ara yi tace "na tafi Ammey na"
"Sai kin dawo'yar albarka"
"Nima zan rakaki zaki siyamin chocolate?"
Yayi mata yadda Nassar yake mata, batasan sanda ta saki murmushi ba ta fice a daga wajen cin abincin, binta yayi shima domin yi mata rakiya.












Tayi zaton shi zai jasu, sai kawai taga ya bud'e wajen mai zaman banza ya k'ame abinsa, tura baki tayi tana d'an hararansa ta gefen ido, sarai ya ganta sai ya mai da kansa gefe yana d'an murmushi hakanan yanzu komai tayi burge shi take.












Sai da ta zauna ta sakarwa mai gadi k'aton hon wannan ba sabon abu ba ne awajenea sam indai zatayi tuk'i batayin na nutsuwa tun lokacin data ke a matsayin Maryam ba yanzun da ta zama mero ba lol🤣🤣🤣














Shi kanshi Muhammad sai da yai mamakin ganin yadda ta wani figi motar da masifar gudu bai san sanda ya juyo yana kallonta ba "ke baki da hankali ne?"
Ya fad'a lokacin dayaga ta kusa fad'awa wani d'an rami dake tsakiyar titin data hau tayi wani irin kaucewa ramin
"Princess tsaya" ya da sauri yana dafe kan sa da duka hannayensa.






Babu musu ta nemi waje ta faka dama da biyu ta keyi dan ya amsa banda son banza tana tare dashi d'in zata zauna ta jashi🤣🤣🤣








Canjin wajen zama sukayi ya amshi tuk'in yana fad'in"naga alamun ke kin shirya mutuwa ni kam gaskiya bana so na mutu banyi aure ba"
Ya fad'a cikin barkwanci.








Murmushi kawai tayi bata tanka masa ba, sai ma wayar ta data d'auko ta bud'e data tana chat da friend d'inta tana duba no d boy babu shi kwata kwata a jerin contact d'in ta da gaske yake ya goge.








D'an kallonsa tayi sai akayi sa a shiama ya wago yana kallonta ta gira ya dage mata alamun ya dai?
D'auke kai tayi tana tuna hargagin sa na d'azu akan mama wani lokacin bata cika ganin lafim su ba domin halin mama sai mai hak'uri.












Kusan sau uku tana kamashi yana kallonta kuma duk sanda zasu had'a ido sai yamata alaman yadai?
Sai kawai ta hak'ura bata k'ara kallonsa ba har suka isa sper market d'in da yawanci anan suke siyayya duka 'yan gidansu.












Bayan ya samu waje ya faka ya bud'e ya fito sannan ya zagayo ya bud'e mata bayan tagama gyara mayafinta ta fito a hankali ya Mai da motar ya rufe ya kama hannunta suka fara jerawa cikin wajen.










Duk inda suka gifta sai idanu sun bisu saboda masifar kyawunsu da kuma yadda sukayi macin d'in da mutane sukayi da juna.










Sunzo shiga shi Kuma d boy sun zo fita shi da abokansa ya gansu sai da gabansa ya fad'i ganin ta tare da wannan gwaskan yayan nata ya wani kafesu da ido har suka k'araso inda suke, sai lokacin ma Maryam ta kula da d boy ta d'an saci kallon MD wanda gaba d'aya hankalin sa yake kan wayar sa.










Sai da tagawa d boy hannu ne shi kuma kamar wanda akace ya d'ago sai kawai yabi hannunta da kallo lokacin shima d

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login