Showing 54001 words to 57000 words out of 58385 words
Chapter 19 - BA JININA BACE Book Complete by Hassana Abdul'aziz Yakasai .txt
CLASS WRITERS ASSOCIATION ☀️*
FCWA
*Home of qualities and trusted writers of the nation*
https://free.facebook.com/111719967001810/photos/a.111720050335135/116072649899875/?type=3&source=45&refid=17
______________________________________
🔥 *BA JININA BACE* 🔥
*2021*
NA
*HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI*
*MAMAN ISLAM*
PAGE 44
Da sauri Maryam ta nufeta, yay saurin tareta yana kallon cikin idonta da kallon kar ki soma.
"Mama nace fa" ta fada a raunane "maman naki ban lamunta ba kibar ta zata tashi ga Ammeyn ki cen ciwon zuciyar ta ya tashi" da sauri ta kafe shi da ido gabanta yana wani irin dokawa tace "ba yanzun muka dawo daga unguwa ba?"
"Eh kinsan al'amarin ubangiji babu yadda baya juyawa bawa kuna shigowa bayan shigewar ki ciki ta yanke jiki ta fad'i, yanzun ma magani zan amso mata na gama dubata.
A hankali ta juya ta kafe mama da wani irin kallon tuhuma da tsoro tace "kece ko?"
Mama da tun da ta fad'i take wani irin kukan zuci mai azabar radadi tayi saurin girgiza kai, alamun babu ruwanta.
Wata irin ajiyar zuciya ta sauke tare da kwafa ganin yaja hannunta sun fice,.
"Sai naga bayanka wallahi Muhammad tunda kayi sanadin rusamin shirina saikayi nadamar yin hakan dan haka nice ajalinka wallahi saikayi nadamar shiga rayuwana da kayi" ta mik'e tashige d'aki tana sakin kukan bak'in ciki.
Yanayin da taga Ammey yasa ta k'arasa da sauri ta rungumeta tareda fashewa da kuka tace "Ammeyna me ya sameki daga dawowar mu?
Kodai akanki ne naji mama na waya?"
Kafeta da ido Ammey tayi batare da tace mata komai ba yayin da zuciyar ta yake mata wani irin fitinannen suka, batasan lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba mai mugun cin rai.
Ita ma maryam fashewa tayi da kuka tare da k'ara k'ank'ame Ammey tana fad'in "sannu Ammey yana miki zafi ko zai daina kinji dan Allah ki bar kukan nan haka yana Kona min rai.
Wani mugun kukanne ya kuma taho mata tayi saurin toshe bakinta da hannun ta tana jin wani mugun tausayin Maryam yana kamata, ta sani rayuwar Maryam yana cikin gagarumin matsala, tasan Sailuba tasan wacece ita muguwa ce azzalumar matar da batasan Allah ba babu d'igon tsoron Allah a tareda ita makira ce ta ajin k'arshe bata da imani ko k'ank'ani.
"Maryam kiyi hak'uri da rayuwa ki gyara d'abi'unki duk da kasancewar naga sauyi mai yawan gaske atare da ke, amma ina so kisani rayuwa bashi da tabbas, idan yau mune gobe ba mu bane, dan Allah zan rok'eki duk halin da kika tsinci kanki, ki kasance mai yawan godewa Allah, ki kare Martaba da kimar ki na d'iya mace k""""'''''''''ya isa dan Allah ya isa Ammey ki daina min irin wannan zantukan masu kama da wasiyya, daga kinyi d'an zazzab'i sai ki kama wasiyya kamar mai shirin barin duniya yanzu yanzu, insha Allah sai kinga jikoki na" ta fad'a cikin matsanan cin rawan jiki ga kukan da take ya kasa tsayawa tsabar tashin hankalin da kalaman Ammey suka saka ta a ciki.
Wani irin murmushi tayi mai ciwo sannan hawayen ta basu bar zuba ba, sannan bata fasa yiwa Maryam nasiha ba akan rayuwa da zaman takwar mutane tare da fad'a mata yau da gobe kai ranan dai babu wani jin dad'i a wannan gida.
Acan k'auye kuwa bayan Baffa ya isa ba k'aramin farin ciki Inna tayi da ganin tilon d'an nata ba, sai dai shi kad'an sa ta ganshi babu maryam kamar yadda yadda ta buk'ata, hakan bai wani bata mamaki ba tunda tafi kowa sanin halin Sailuba "kai wannan yarinya Allah dai ya shirya, Allah kanaji kuma kana gani na fita hakkinta na bata tarbiyya gwargwadon iyawa ta Allah karka kamani da laifin gurbacewar halinta dan alfarmar fiyayyen haltta (S A W).
Nan falon ta tayi masa shimfida ya zauna takawo masa ruwan randa mai sanyi da fura wacce taji lafiyayyan nonon shanu zuryan, kasan cewar tasan da zuwan sa.
Sai da suka gama gaisawa sannan ya soma furar kasancewar yana sonta sosai yana sha suna d'an tab'a hirar duniya da Inna wanda duk rabin sa nasiha ne da shawarwari cikin hikima.
Bayan ya kammala ne ta dubeshi tace "kaje kasamu kawun Muhammadu dan a tsaida daidai lokacin da za a d'aura auren Maryama da shi Muhammadun dan insha Allahu jibinnan za'ayi babu jinkir tawa"
Da sauri Baffa ya dubeta yace "jibi kuma Inna?"
K
"Ko ban isa zartar da hukunci akan jika ta bane?"
"A haba Inna kin isa har kinyi yawa"
"To katashi kaje ka dawo kazo ka amshi naka iv da zaka rabawa 'yan uwa da abokan arzik'i, saboda nasan shiriri tarka shiyasa nasa aka buga har kai, sannan magana tagaba Baffa koda wasa Sailuba kar tasan jibi daurin auren Maryama domin na fahimci ita d'in fitina ce arayuwar Maryama, kai wannan yarinya Allah dai ya ganar da ita"
Daga Baffa ya fita zuwa gurin yan uwan marigayi aminin shi Hassan
MAMAN ISLAM CE
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION ☀️*

Masha Allah kungiyata kungiyar albarka ce kungiyar da babu irin ta d'aya tamkar da dubu ina matuk'ar alfahari da first class tare da dukkan 'yan uwa masoya na cikin ta Allah ya k'ara had'e kanmu
Allah sarki islamiyya ta Allah ya k'ara shiryamin ke ya sanya miki nutsuwa da jin tsoron sa Allah ya tsarkake min zuciyar ki tareda kullum yayan musulmi baki d'aya
D'an auta na Al'mustapha d'an rikici na yanzun an girma ya kamata a daina rigimar banza da wofi.
PAGE 45
Bai wani jima ba ya dawo haka ma Inna yana dawowa tace ya koma gida yaci gaba da shiryen sa ita tagama nata haka nan gobe zata iso da tawagar ta, sannan ta kawo wani rubutu ta bashi tace yana shiga get d'in gidan sa kafin yakai ciki yayi Bismillah ya sha daga tsaye, ta jaddada masa hakan sau ba adadi har ya daga yana mamakin wannan wane irin rubutu ne me muhimmanci haka.
Sanda ya isa sai da yafara zuwa gidan malam lokacin yana tare da bak'i ganin Baffa yasa ya sallami bakin yace "k'araso mana Baffa kamar wani bak'o zaka tsaya daga nesa".
K'arasa wa yay yana d'an murmushi yace "barka da yamma malam"
Yauwa Baffa, ya kuma na ganka fasa zuwa wajen Innan kayi?"
"Naje malam sai dai bata barni na kwana ba saboda tace auren Maryam jibi ne, gama iv ta bayar wai araba tun yau tunda abin ya kure".
Cikin madaukakin farin ciki malam yace " a a to Abu yayi kyau gaskiya naji dad'in hakan sosai Allah ya tabbatar mana da alkhairi" amen amen sun dan jima da malam suna tattaunawa kafin ya sallame shi ya taho gida.
Kafin ya shiga gid saida ya kira Halima dake yar abokansa ce Kuma makocin sa na amana yabata iv na daurin auren masu dan dama yace ta kaiwa Abban ta sannan ya bata na 'yan mata yace dan Allah yau ta fara rabawa k'awayen saboda Maryam bata nan su sosai tayi mamakin auren na Maryam yadda yazo musu babu shiri yadda sukaci burin wannan ranar, take ta kira Maryam k'awar Maryam ta jami'a suka sha mamakin su kafin su sannan suka fara rabo tunda lokaci ya riga da ya k'ure.
Wannan tsaye tsaye da Baffa yayi shi yasa ya manta da rubutun da Inna tace lallai lallai yasha kafin ya shiga gida
Dake yau Ammey ce da girki kuma yasan yadda suka rabu akan sai anbata 'yarta dan haka d'akin ta ya fara nufa sai dai yadda ya tadda ita ba k'aramin d'aga masa hankali yayi ba ya k'arasa kusa da ita yana tambayar Maryam abinda ya faru shida ya fita basa nan.
Cikin kuka tace itama bata sani ba bayan sun dawo MD ya kirata yace tazo ta kula da ita kafin ya kawo magani, daga haka ta fice ganin yadda Ammey take kalloan Baffa tasan akwai abinda take son fad'a masa.
Tana fita sukayi kicibus da MD wanda da k'yar ya samu maganin da Ammey take sha yace "ya kika fito?"
"Baffa ya dawo yana ciki"
Da mamaki yake kallon ta yace "bai kwana ba?"
"Inaga ya fasa ne"
Ta bashi amsa tana wucewa ciki saboda jin ana kiran sallar isaha, dan haka shima ya nufi part d'insa dan yayi tasa alwalar dan kar ya rasa jam i.
A b'angaren Mama kuwa tunda ta shiga d'aki ta kasa nutsuwa sai zarya take daga k'arshe ma kai tsaye bokanta ta kira ba aminiyar tata ba ta sanar masa duk halin da ake ciki,
Yace "kin lalata komai Sailuba dole ne abinda kike gudu zai faru, sannan bazaki samu komai da kike buk'ata ba, idan kina son cikar burinki dole ne kizo nan mu kadaice dake na kwana biyu dole nayi kwana biyu ina saduwa dake da wannan maniyin da zai fita a jikin ki zan miki aikin da zai baki mamaki bayan haka banida wata hanya ta samun nasarar ki".
Idanunta ya rufe,
Zuciyar ta ya toshe
Tunanin ta ya b'ace
Imanin ta ya barta
Bata da wani buri ko fata illah tarwatsa rayuwar yarinyar da babu abinda tayi mata wanda ya wuce yi mata biyayya da gwada mata k'auna irin na uwa mahaifiya da 'ya mai mutukar biyayya agareta.
Hakkan ne yasa Baffa yana shigowa ta fice dan boka yace kar ta bari su had'u dama dakon dawowar sa take wannan kenan.
Bayan Maryam ta idar da sallar tana shirin komawa b'angaren Ammey kiran name sake d'in ta ya shigo wayar ta ta d'aga tana fad'in 'yar halak wallahi jikin Ammey ne ya hanani kiranki"
"Eh kyace haka mana saboda rainin hankalin da kika saba, yanzu sahiba ace jibi jubi daurin auren ki amma sai yau muke sani kin kyauta ai"
Dakatar da ita Maryam tayi ta hanyar cewa " dake yar tsana ce ni shiyasa aurena zai kasance jibi har na kasa sani, ko shirin film ko kuma a littafi wanda suke shirya abu nan take"
"Idan kina musu ki bud'e data ki duba status dina mana ko muna da wata MARYAM BAFFA ABUBAKAR ne bayan ke?"
Ai bata tsaya jin k'arshen labarin ba ta katse kiran tana katsewa kiran Halima yana shigowa ta daga asanyaye saboda bazata iya katse kiran Halima ba amma bataso Kiran ba sai ta fara duba sak'on Maryam.
"Ba zaiyiyu mu zaga duka k'awayen mu yau ba dan haka waso duk ta whatsoapp muka tura musu katin gayyatar, idan Kuma kina da wani wanda zaki bawa idan kun dawo daga unguwar saina kawo miki sauran"
Da mamaki Maryam tace "ke nifa bangane inda wannan dogon sharhin naki ya nufa ba katin gayyatar me?"
Yadda tayi maganar ya tabbatar wa da Halima cewa Maryam bata san da maganar aurenta jibi ba dan haka tace mata "kun dawo ne?"
"Eh "kawai tace mata tana dafe kanta da ya soma k'ullewa da maganganun Halima da maryam
"Bari nazo yanzu" ta fad'a tare da katse kiran.
Ba a rufa cikakken minti uku ba Halima ta shigo d'akin ta karasa kusa da Maryam ta dafata tunda tayi sallama bata jitaba ta fad'a duniyar tunani.
Ba tare da ta ce mata komaiba ta mik'a mata iv mai d'auke da sunanta baro baro da sunan MD tareda tabbatar da d'aurin auren su ranan 2/3/2021
Sosai mamakin ganin katin ya kamata yaushe nema har tace tana son MD da za ayanke mata d'anyen hukunci haka?
Dafatan da Halima tayi ne ya maidota hankalin ta a hakanli tace "nayi matuk'ar farin cikin kasancewar wannan abun kuma nasan cewa kema baki san da maganar ba Maryam nasan wannan shirin Baffa ne dan Allah karki bujere"
"To" shine kawai abinda Maryam ta iya fad'a tana tunanin yadda MD zai d'auki abin yadda yake nacin soyayyar ta d'in nan bai samu gamshashshen amsa ba gashi yanzun ya sameta a arha, arha mana tunda tasan cewa wannan ba shirin Baffa bane na Inna ne dan Baffa duk abinda zaiyi sai yai shawara da ita da MD daga haka sukayi sallama da Halima bayan tayi mata nasiha ta bata ahawarwari sannan tace yanzun maman Niger zatazo tunda abin yazo a kurace ta d'an yi mata gyara sama sama Umma ne tasa a kirata.
Tana fita MD yana shigowa d'akin cikin wani irin sauri ya k'araso kusa da ita ya tsaya yace "my happiness kinga abinda nagani kuwa?"
"Eh na gani" ta fad'a a sanyaye haka nan maganar take sa mata wani irin fitinannen bugun zuciya "me kika ce akai to?"
A dan sanyaye ta kalleshi kafin lumshe idanunta ta bud'e akanshi zuciyar ta na wani irin fitinannen bugu har tana dafewa tace "me kake so nace to?
So kake naje nacewa Baffana ban amince da zab'in saba?"
Sam bai kula da yanayin ta ba ya duka ya d'an tsotsi tattausan lab'b'an duk kuwa da irin yadda take nuna masa bata son hakan ya dafa kanta yace "miki alk'awarin insha Allahu bazaki tab'a nadamar kasancewa na mijinki ba ya kuma manna mata wani kiss d'in a goshinta kafin ya fita da d'an gudun sa dan kar tayi masa magana, gane hakanne yasa ta saki murmushin da bata shiryawa zuwansa ba.
Bayan Baffa ya dawo daga massalaci ya shigo d'akin Ammey yaji dad'in ganinta akan sallaya itama tayi sallar tana jingine a jikin gado tana jan carbi.
K'arasawa yayi kusa da ita ya zauna dab'as yana dubanta kafin yakai hannun saman fuskar ta ya d'an shafo "ya jikin babyta?"
Ya fad'a da salon tsokana wanda rabon da hakan ya kasance an d'an jima sai abin ya bata dariya sosai, sai ta d'an murmusa tace "da sauk'i kafin takai hannunta saman nashi tace "Baffa"
"Na am"