Showing 9001 words to 12000 words out of 58385 words
Chapter 4 - BA JININA BACE Book Complete by Hassana Abdul'aziz Yakasai .txt
JININA BACE🔥
2021
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 9
Haka dai ta daure tayi musu karb'a ta musamman har zuwa lokacin da suka wuce, cikin k'awayenta babu wanda yasan da maganar auren sai haj. Zakiyya dan haka da itakad'ai suka zauna har zuwa bayan sallahr magriba sanda 'yan kawo amarya suka fara shigowa.
Haj. Zakiyya ce ta rik'a tausarta da k'yar tasamu ta hak'ura dan da cewa tayi wallahi saitayi musu hauka sai sun ganecewa mijin mahaukaciya 'yarsu ta aura haj. Zakiyya tace "haba k'awata waishin duk abinda na fad'a miki tun muna gidana baki d'aukaba? na sani da ciwo amma idan kika daure zakiyi dariya harda shewa kinga yanzu idan kikayi wani abu to duk abinda yasamu 'yarsu to kaitsaye zasuce kece dan zaki aikata amma idan kika bi yadda na fad'a miki zakiga yadda zasuga kima da darajanki"
Da k'yar haj. Zakiyya tasamu ta lallab'a haj. Sailuba a wannan gab'ar har ta hak'ura ta karb'i bakin amarya yadda ya kamata har suka tafi suna yabon kirkinta ganin yadda ta karb'i amarya cikin farin ciki da walwala, tare da ita aka raka amarya har d'akinta suka tafi suna godiya
Bayan ta tafiyar sune haj. Zakiyya ta dubeta tasaki shu'umin murmushi tace ba'a faraba k'awata sharar fage ake kafin wasan ya fara"
"Allah ko k'awata?"
"Ai ke d'ince bakya ganewa baki da aiki sai fushi Kuma babu inda wannan zai kaiki sai na dama"
"Abinne ya masifar d'amin hankali k'awata amma yanzun ya zanyi?"
"Shi nake son ai ki nutsu ki fahimta domin abune da zakiji dad'insa kuma zai amfaneki batare da kowa ya fahimtaba, Kinga yanzu angon yana hanya abinda nakeso dake goben ya kasance kin gama musu duk wani aiki har abin kari kafin ki fito, kidai fito da wuri kinsan wajan yana da nisa sosai"
"Angama amine zanyi yadda kikeso insha Allah"
_________________________
Ranar dai ango ya gwangwaje agwancinsa shi da amaryar sa Amina yayin da Sailuba ya yadda taga rana haka taga dare batako runtsaba tsabar masifaffen kishin dayake cin ranta.
Koda gari ya waye tun bayan da ta idar da sallar asuba bata komaba ta zauna ta had'a musu had'ad'd'an break wanda rabon data girka irinsa har ta manta tsab ta gyare gidan tsab aranta take cewa duk wani abu da zanyi agidannan na bankwana ne domin nima lokacin hutawana yazo.
Sanda Baffa suka fito daga d'akinsa shida Amina tuni Sailuba sunyi nisa a hanyarsu ta zuwa wajen shahararren malamain da yai k'aurin suna aciki da wajen garin wanda ake kira da kowa naka.
Sosai yaji dad'in yadda ta gyare ko ina tayi musu girki duk da cewa yaji babu dad'in fitar ta arana irin tayau daya kamata ace ta tsaya ta Kula da komai na gidan kodan bak'in dayasan cewa bazasu rasayi ba aranar irin ta yau d'in.
Bayan gama cin abincinsu babu dad'ewa kuwa saiga yayar Amina wacce takasance ita kad'aice 'yar uwarta mace dan duka yaran malam Babba mata biyune kawai sai maza guda goma Sha uku yayin da ad'akin su Amina ita kad'aice mace sai kuma d'aya d'akin nanma guda d'ayar ce shamsiyya.
Matan malam suna da matuk'ar had'in Kai yadda zai wahala a yaransu ma kaban bance na wannan da na wannan.
Yini su anty shamsiyya sukayi kamar yadda Amina take kiranta tare da bata shawarwari da buga mata misali akan gidansu da kuma nuna mata yadda umman ta take bin nanne mahaifiyar shamsiyya sau da k'afa duk da kasancewar Nanne wacce ainihin sunanta Zahra u irin matan nanne masu fad'an tsiya, hakan bai hanata jin dad'in zama da Mariya ba (Umma) domin ita mutunce mai mugun hak'uri dan zan iya cewa duk wani hali na Amina da shiru shirunta a wajenta ta gadosu, tun bayan da aka kawota gidan malam Babba ta kama yaran nanne ta runguma tamkar nata dake tana da matuk'ar ilimi haka take dad'a fahimtar dasu duk wani abu daya gagaresu a makaranta hakan ba k'aramin dad'i yayiwa malam da Nanne ba gaba d'aya tasakarwa Mariya ragamar yaran hatta kayansu d'akinta suka koma sannan itace ta aurar da Shamsiyya yayin da tunda aka haifi Amina Allah ya jarabce ta da masifar k'aunar yarinyar wacce tun tana k'aramar ta take da wannan hak'urin abin har tsoro yake bawa Nanne takan cewa malam kodai yarinyar bata da lafiyane.murmushi yakeyi mata a duk lokacin datayi masa irin wannan tambayar yace "Zahra'u kenan ai kowane bawa da kikegani yana da kalarsa ita wannan kalar ta kenan hak'urinta har ya zarta na uwar ta"
Baki Nanne takan tab'e tace "sam ni wallahi hakan bamin dad'iba wani hak'urin idan yayi yawa a cutane" shima dariyar yake mata baya k'ara tankawa.
Sosai shamsiyya ta d'an bata kad'an daga tarihin gidansu da irin ribar da Umman take ci na irin tsantsar hak'urin da Allah ya hore mata
Basu bar gidanba sai bayan sallar la'asar kuma har lokacin haj. Sailuba bata dawoba.
_________________________
Tunda haj. Zakiyya tafara jan sailuba wajen malami bata tab'a kaita waje mai wahala da ban tsoron wajen ba dan haka ta matuk'ar wahala tun kafin ma su kai wajen domin tafiyar k'afa ce wacce koda tayi rayuwar k'auye bata tab'a, sai dai abinda ya matuk'ar k'ayatar da ita shine yadda suna zuwa malamain ya hau zayyano mata dukan abinda ya kawosu, sannan shi da kanshi yafara dace"kinyi babban kuskure da har kika k'i yarda ki haihu da mijinki Kuma d'an uwanki Baffa domin dakin haihu dashi shine samun nasarar rayuwarki ni bana fad'awa mutum abinda zai kasance karya dan haka nake tabbatar miki da cewa ita wannan mata zata haihu itace uwar 'ya'yansa sai dai kuma ke kin riga kingama da rayuwarki domin keda haihuwa har abada kin gama lalata mahaifarki da k'wayoyin hana d'aukar ciki shekara goma shabiyar ba kwana goma sha biyar bane babu ke babu haihu amma zaki mulki mijinki da kishiyarki yadda ranki yake so.
Duk inda wani abu mai suna tashin hankali yake sailuba ta shige shi dan tun kafin malam ya k'arasa mata jawabi ta fashe da wani fitinannen kuka domin wani iko da k'udura na ubangiji a lokacin sai taji babu abinda take buk'ata sai haihuwar sai dai ta riga ta gama da rayuwarta tun farko a tunaninta Baffa da yake d'an boko me zaiyi da tarkacen yara su hanashi sakat.
Ranar dai bata tsaya amsar sak'on komai a wajen malaminba saboda tsantsar tashin hankalin data ke ciki wujiga wujiga ta dawo ba ita ta shigo gidan ba sai bayan sallar Isha dan lokacin Baffa yana massalaci Amina tana d'akinta tana sallah, dan haka duk basu san da dawowar taba.
Tayi kuka kuka dana sani da nadama mara amfani domin bakin alk'alami yariga ya bushe Saida tayi jinya saboda tsabar bak'in ciki tareda cin alwashi iri daban daban duk akan abinda ita tajawa kanta
Muje zuwa daga taku
Maman Islam ce
بسم الله الرØÙ…Ù† الر ØÙŠÙ…
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥BA JINANA BACE🔥
2021
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 10
Sai bayan kwana shida suka koma wajen malamin wanda Sailuba tace so take daga mijin har amaryar tasa su zamo a k'ark'ashin ikonsa sai abinda tace zasu Kuma su kasance suna matuk'ar jin tsoronta duk abinda ta basu umarni suyi mata shi jiki na rawa.
Sosai malam ya had'a mata mugun asirin da ta dawo gida ta aiwatar dashi cikin ruwan sanyi ta soma azabtar da Amina batare da wata tsangwama amma bauta iri iri hatta wankinsu sailuba sallamar maiwankin tayi Amina ce wankinsu da guga girki shara wanke wanke da duk wani aiki na wahala tana daga zaune zata bawa Amina umarni ita kuma babu musu zata aiwatar.
Cima mai kyau sutura mai kyau da tsada want bacci mai kyau babu abinda ta nema tarasa agidan Baffa ga kulawar dayake da ita amma uban aikin da ake jibga mata asiyasan ce yasa tafara wata irin rama wadda 'yan uwanta suke tunanin ciki ta had'u dashi mai laulayi tunda basu tab'a katarin zuwa sun tarar da ita cikin wannan uban aikin kamar jaka ba dan boka yace mata ta kiyaye sannan kuma ya tabbatar mata da cewa duk sanda Amina tasamu ciki to aiki ya lalace sai an sabunta.
Haka Amina taci gaba da bautuwa a hannun haj. Sailuba a siyasance batareda ita kanta ta lura da hakan ba domin hatta abinci tare suke ci kuma zasu yi hira suyi wasa da dariyansu koda wasa bata tab'a nunawa Amina wani abuba duk da kasancewar bata k'aunar koda bud'ar idanunta taganta a gidan.
Bayan wasu'yan watanni saiga Amina tana zuba laulayi mai masifar wahala hankalin sailuba kuwa idan yayi dubu to atashe yake domin tunda Amina tafara zazzabi Baffa yakaita asbiti aka tabbatar masa da cikine da ita ya tsinci kansa cikin tsantsar farin ciki ga wata kula ta musamman dayake Bata duk da yana iya bakin k'ok'arinsa wajen danne farin cikinsa dan gudun kada Sailuba taji babu dad'i.
Tunda taji labarin cikin hankalinta yai masifar kad'awa lallai tasan cewa aiki ya lalace kamar yadda boka ya fad'a mata gaahi haj. Zakiyya basa k'asar ita da mijinta ya rakata ganin likita zafine ya had'ar mata dan dole ta danne damuwar ta tacigaba da bawa Amina kulawa ta musamman wanda ya d'auke hankalin Baffa akansu ganin ko baya nan ai sailuba tana nan.
Da k'yar ta samu lambar haj. Zakiyya cikin taahin hankali ta sanar mata da abinda yake faruwa itama ba k'aramin kad'uwa tayi ba dajin wannan labarin sai dai ganin irin halin da k'awar tata ta shiga yasa ta kwantar mata da hankali ta tabbatar mata da nan da k'arahen wata zasu dawo.
Haka dai haj. Sailuba ta daure tacigaba da bawa Amina kulawa na musamman yayin da aranata take kiyasta iya kwanakin da cikin ya rage ajikin Amina Baffa kuwa ba k'aramin Jin dad'in yadda sailuba take kula da Amina yakeba sai ta k'ara wani martaba da kima a idanunsa.
Saboda tsabar iya kissa ko aikin da take azabtar da ita dasu ta daina dan acewar ta lokacin guda zata kwabar da d'anbanzan cikin kowa ya huta, yanzun dai bari ta tayasu raino yadda ko wani abun yafaru babu wanda zai zargi dasa hannunta.
_________________________
Haka sukaci gaba da tattalinta har zuwa sanda haj. Zakiyya ta dawo a lokacin har ya shiga wata na uku yayin da Baffa kullum cikin take tsantsan da tsantseni yake shima dama can shi mutum ne Mai yawan kyauta samun cikin Amina yasa ya k'ara sosai akan yadda yakeyi.
Kwana biyu da dawowar ta suka d'aga wajen boka sosai suka sha mamakin ganin yadda suna zuwa bai saurara da daga garesuba yabasu wani kullin magani yace "Susan yadda zata Shashi ashayi ba Madara ko gama Sha bazata yiba cikin zai soma murd'a maya ina tabbatar miki wannan cikin bazaya kwana dashiba ajikinta"
Tace "ranka yadad'e inaso ayi mata abinda bazata k'ara d'aukar cikinsaba"
"Bazai yiyuba domin tun farko na fad'a miki akwai yara atsakaninsu Kuma dole zata haifesu sai dai zaki iya yin yadda kikaga dama dasu shine kawai abinda nasani"
Bayan sun baro wajen boka suka dawo gida nan ta ninka kulawar datake bata har zuwa kusan sati tana tunanin yadda zata aiwatar da shirinta batare da wani abu mai kama da zargi ya ahiga tsakaninsuba wannan kenan.
Yau kam Amina tashi tayi sam batajin dad'i sai dai dauriya data rigayi dan kar ta d'aga hankalin mutanen gidan ganin yadda suke dai dai bakin gwargwadonsu akanta.
Tana zaune afalo saman dugowar kujera hah. Sailuba ta rako k'awarta Zakiyya har inda take haj. Zakiyya ta k'araso suka gaisa tayi mata sannu da jiki, da ido tayima sailuba alamar kawai ta aiwatar yau.
_________________________
Koda ta rakata ta d'an Jima suna tattaunawa da k'awar tata kafin suyi sallama inda ta barta nan ta dawo tasame ta sai dai sab'anin d'azu yanzun idanunta alumshe suke alamun barci yafara fisgarta wani kayataccen murmushi ta saki ta wuce kicin dake ranata d'anyi dan d'aya ya wuce abincin mutum biyu ta dafa mai rai da lafiya daga ita sai Baffanta dan tasawa ranta yau abincin nan bazai ciyu awajen Amina ba.
Hakan cewa kuwa yafaru bayan ta gama dai dai lokacin ana kiran sallah ta fito da nufin tashinta sai k'eyar ta ta hango tana shigewa d'akinta, tabita da wani shegen harara aranta tana fad'in zanyi maganinki ne, daga haka itama ta wuce nata d'akin danyin tata sallar bayan sun idar kusan atare suka fito da Amina wacce takejin wata mahaukaciyar yumwa har hautsina cikinta yake saboda tsabar yunwar dake d'awainiya da ita ganin haka yasa Sailuba shigewa kicin da sauri ta had'o mata ruwan lipton ta kawo mata tace
"Kinga k'anwata fara da wannan naga yau du bakici komai ba bazai yiyu ki farada abinci Kai tsayeba" sosai hakan yayi mata dad'i dan tana da buk'atar hakan, batare da wani tunaniba ta kafa kai tashanyen tas tun kafin ta dire kofin cikinta yai wani irin masifaffen murd'awa wanda tun jiya takejin hakan, da mugun k'arfi ta dafe cikin gami da fad'in washhh, wani b'oyayyen murmushi tasaki ama azahiri k'arasowa tayi da sauri ta kamata "lafiya kuwa k'anwata?"
Ta bud'a baki kenan zatayi mata magana kenan cikinta yayi way irin fitinannen murd'awa sai cewa tayi"babu" cikin pretanding tace "babu me?"
Kasa magana tayi saboda azaba Saida ta Jima kafin ya lafa mata ta dubi Sailuba tace "dan Allah anty ki taima kamin ki Kira Baffa yazo yakaini asbiti mutuwa zanyi"
Da sauri ta nufi hanyar d'akinta tana fad'in "to bari na kirashi gwanda yazo kar wani abun yazo yafaru mushiga uku"
Tana shiga d'akin tasaki wani uban tsalle tana d'ebo shoki farin ciki fal ranta yau burinta zai cika zatayi kwanan farin ciki wannan alak'ak'an cikin zai bar gidansu ta huta daganin tashin hankali.
Muje zuwa
بسم الله الرØÙ…Ù† الر ØÙŠÙ…
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥BA JININA BACE🔥
2021
NA
HASSANA ABDU AZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 11
Anan ta k'yaleta tana ta faman murk'ususu yayin da tai kwanciyar ta saman gado tana waya da haj. Zakiyya a maimakon Baffa sosai suke shewa, Jin kamar motsi yasa tayi saurin katse Kiran tana laluben wayan Baffa.
Anty shamsiyya ce ta shigo arud'e domin sanda ta shigo har Amina ta sume ga uban jinin dayake malala ta k'asan ta tana ganin haka tayi d'akin haj. Sailuba arud'e, sai dai tashin hankalin data gani akan fuskar sailuba yaci uwar nata dan hawaye tagani shab'e shab'e a fuskar ta tanama Baffa bayani halin da Amina take ciki.
Cikin tsantsar tashin hankali yabaro kamfaninsa wanda yake ziryata a irin ranan dan ganawa da manya da k'ananun ma aikatansa.
_________________________
Wuya ita wuya Amina tacishi kafin tasan inda kanta yake sai da tayi kusan sati guda acikin asbitin kafin tasan inda kanta yake ciki dai Kam babu shi domin ya riga da ya zube tun aranar.
Sosai haj. Sailuba ta rik'a bawa Amina wata irin kulawa dan hatta Nanne wacce Sam bata yarda da Sailuba kuma tana nusar da Amina ta kula da takun matar dan dai sunk'i d'aukan abinda mahimmanci ne saida tazuba ido wannan karon ta k'yale sailuba da Amina amma duk wani takunta tana ankare gane hakan yasa Sailuba matuk'ar taka tsantsan.
Babu wanda yakai Inna takaicin rashin cikin sai dai tayi musu addu'ar Allah yabada na aike tareda yiwa Baffa nasiha mai kamar jirwaye cewa ya kula da matansa ya sanya ido akansu da takunsu, duk da cewa bai gane me take nufiba yayi mata godiya ya maidata har gida dan bai tab'a yarda Innarsa tahau motar haya.
_________________________
Kusan sau hud'u hakan yana faruwa wanda hakan yasa Baffa ya rufe ido yanama Amina bala'i da tambayarta nufinta akanshi ya lura haihuwane batasonyi dashi daga baya har k'asa ya durk'usa mata yana rok'on data taimaka ta haifa masa koda d'a d'aya ne yamata alk'awarin duk abinda takeso zaiyi matashi amma dan Allah kada ta k'ara yimasa asaran gudan jininsa.
Hawaye hawaye fa take gani a idanunsa Baffa ne yake mata kuka da rok'on ta haifa masa 'ya'ya yana nufin ita ke zubar masa da yara idan tasamu ciki.
Itama fashewa tayi da kuka mai k'arfin gaske zuciyar ta yana wani irin suya take kalaman anty shamsiyya suka shiga dawo mata akaro na hud'u data sake rasa cikin dayakai kimanin watanni biyar wanda har sunfara saka rai da shi tunda yafi sauran ukun jimawa.
"Amina nifa nafara zargin kishiyarki akan wannan b'arin dakike yi ajere ajere duk dana san cewa komi dayake faruwa daga Allah ne kuma dama can Allah ya hukunta wannan cikin da suka lalace bamasu taka k'asa bane amma akwai sula kuma Koda ba haka bama idan kin zauna kinyi tunani taya ita bata haihuba zata bar wata tazo da daga baya ta cika gidan aikinsan dole zatayi wani abun akai duk wannan soyayyar da kulawar datake baki duk na banzane ga uban bautar dake da take a siyansace tunda kikazo gidannan baki gaba baki baya kullum ak'are ya kud'in guzuri inzaki farka ki gane ki farka sannan maganar gaskiya Amina ta inda zaki gane cewa magana na gaskiya ne idan kin sake samun wani cikin ko Baffan kada ki sake ki fad'awa sai dai su ganshi tunda na lura ke ba mai girman ciki bane irin girman cikin bane irin cikin Umma ne dake wanda inda anganshi to bazai k'ara sati guda ba zai fito duniya dan haka duk irin wahalar da zakici ki daure ki cije ki raini abinki dan tun mahaifarki tana iya d'aukan ciki zata zo ta gaza kema azo ana samun wata matsalar kinga kunyi duro kenan burinta ya ciki ke babu ita kinga anyi one one kenan daman abinda take so kenan.
Ganin tayi tsaye ga hawaye na tafaman shatatowa daga idanunta yasa ya kamo hannayenta ya zaunar da ita asaman cinyar ta yana cigaba da hawayen tare da rok'on ta daure ta daina Yi Masa ganganci idan tasamu ciki, ganin cewa ko me zata ce ba fahimta zaiba yasa ta tsuke bakinta amma ranta banda suya babu abinda yake mata.
_________________________
Wannan karon Saida tayi wajen wata hud'u kafin Allah yabata wani cikin mai d'an Karen laulayi dan haka kamar yadda 'yar uwarta ta bata shawara ta rik'a daurewa tana shanyewa dan tanaso ta tabbatar da abinda ta fad'a mata akan wannan kareemar matar ma kula da ita da