Showing 3001 words to 6000 words out of 58385 words
Chapter 2 - BA JININA BACE Book Complete by Hassana Abdul'aziz Yakasai .txt
da zubowar hawaye.
"Subhanallahi wake neman kassara min rayuwar uwa ina raye a duniya da lafiyana?"
Had"e rai ta k'arayi tana hararan MD k'asa k'asa sarai ya ganta ya basar yayin da malam ya d'an kalleshi yace "kodai kaine muhammadi kake takurawa uwata?"
Murmushi kawai yayi yana shafa kansa yayin da malam yace "ashe kuwa kaine gaskiya muhammadu karka k'ara dukar min uwata shifa duka baya shirya mutum sai daima ya dad'a kangara shi dan haka naaiha itace kawai zatasa mutum ya rusuna ba wai dukana kaji ko muhammadu"
"Shikenan malam yafad'a cikin sanyin sa" yayin da maryam ta tsagal tace "tab waye zaimin nasihar ai wallahi sai dai yaiwa kansa mutanen da suke zama cikin bariki suna k'arewa matan abokan aikinsu kallo har su kyasa ne zaimin wata nasiha" ta k'arasa tana manna masa wata shegiyar harara dan har ga Allah ta tsanesa saboda gana mata azabar da yake.
Murmushi malam yayi yace "haba uwata shid'infa yayanki ne bai kamata ace kina masa raahin kunyaba"
"Tab' ai wallahi sai dai ya nemi k'anwar sa ni babu abinda na had'a dashi'
Malam yace "gidanku nace gidanku ai ko ke kika had'a hanya da shi kuma alak'arku ba mai yankewa bace har k'arshen rayuwar ku"
"Ai kuwa ni zan Malku wannan bak'ar alak'ar kuma zakace na fad'a maka malam babu ni babu shi wallahi yadda baya sona baya k'auna ta nima haka"
Ta k'arasa maganar yayin da idonta yake nuna gaskiyar abinda yake kenan har k'asan ranta, malam yace "uwata idan zakiyi so kiyi so dan Allah haka idan zakiyi k'i kiyi domin Allah domin bakisan me gobe zai haifarba dan haka nake so ki cire duk abinda kika sanya aranki game da d'an uwanki"
"Malam alkhairi goben zai haifar ta fad'a idanunta yana cikowa da kwalla taci gaba da cewa malam dukanfa dayaimin ne yasa kayi kwanaki baka ganni ba ina can ina jinyar jikina, ni bama dukan ne ya fi b'atamin rai ba irin yadda ya disgani a gaban saurayina da k'awaye na dan haka wallahi ni babu ruwana da shi"
Malam yace "saurayi kuma maryamu shi Baffan naki bai sanar dake yayi miki miji bane?"
Da mamaki Maryam tace miji kuma malam? Ni bai fad'amin ba yadai ce na kasance mai kula da kaine kuma bai amince na saurari kowa ba har sai ya bani izini iya abinda na sani kenan"
"Yanzun bai isaba kenan shiyasa har kika fara kula wani batare da izinin saba"malam ya tambaya babu alamar wasa atare dashi, tace" bafa haka bane malam shid'in fa yayan k'awata ne wallahi yana da nutsuwa"
"Ke zaki fad'a mana hakan ko kuma mu zamu gano da kanmu?"
"Kune malam ta fad'a asanyaye ganin babu alamar wasa atare daahi.
Ranan dai hiran da malam batayi armashi ba ta sallame shi ta wuce, tana barin wajen malam ya dubi MD yace "akwai matsalafa muhammadu MD ya kafe malam da manyan idanunsa batareda ya furta komai ba, gane me yake nufi ne yasa malam cigaba da cewa kamata yaifa ace kaja maryam ajiki ba wai kadasa mata tsanarka a zuciyar taba kasanfa meke faruwa tsakanin ku dan haka nake neman alfarmar ka rik'a janta a jiki ba wai ka rik'a tsan gwamar taba hakan zai iya haifar da Marsala"
"Insha Allahu zanyi yadda kace malam cewar MD cikin sanyin jiki dana murya sannan ya d'ora da cewa " yarinyar ce batajin magana ko kad'an malam"
"Tunda haka Allah yayi ta dolene mu rik'a hak'uri da ita my bita da addu a.
Ita ko maryam bayan tabar wajen malam gida ta dawo ranta babu dad'i domin ko a hanya tak'i jinin su had'u bare su had'a inuwa guda da shi, abakin get tayi kicib'us da Nassar ya rugo da gudu yace "Adda maryam albushir" tace "sweet" hannu ya mik'a mata yace to bani?"
Tace "ai kasan tunda nace zan baka ko" yace Baffa yayo waya aje a d'aukoshi inaji Ammey tana Kiran bros tace yaje ya d'aukoshi" manyan idanun ta ta wara akanshi tace na fara wasa da kaine ABDUL Nassar?"
"Allah da gaske nake kuma idan nayi k'arya kimin duka" hannu ta bashi suka tafa sannan ta kama hannunshi tace "muje nabaka sweet kai yau har wannan ball d'in da ka nunamin jiya kace na sai maka to yau insha Allahu yanzuma zanje na siyo maka wani tsalle ya doka ya rungumeta yace na" gode Adda maryam wallahi wata ran kina da kirki, dan Allah ki daina zagin Ammey na kinga nima bana zagar miki mama" kallonsa ta d'an yi sannan ta shafa kansa har ga Allah ta na son d'an uwanta mama ce bata son mu amalarta dashi wanda duk iya nacinta ta kasa gano dalilin.
Maman islam ce
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥BA JININA BACE🔥
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 4
Tana rik'e da hannunsa suka shiga cikin gidan lokacin mama tayi shirin fita ganinsu tare da Nassar mama tayi kicin kicin da ranta tace"bana hanaki hurd'a da wad'annan annobar ba?"
Itama had'e ran tayi tace ni wallahi k'anina ba annoba bane haka kawai arik'a batamin sunan d'an uwa ubanmu fa d'aya sannan bani da wani k'ani bayan shi ni har ga Allah daga yau na daina hanayarar shi dan bazan masa abinda bros yake mana ba"
Murmushin dole mama tayi tace "haba shalele ba fa haka nake nufiba kawai dai ina gudar miki raini ne amma tunda kina son mu amalantar su ai bazan tab'a hanaki kome kike soba shalelena"
Ita kam maryam kama hannun d'an uwa ta tayi suka shige tana fad'in ina zuwa ne haka da yamma mama?"
"Gidan haj. Fauziyya zani zan amso wasu sak'o" tab'e baki maryam tayi tace "wato duk randa Baffa zai dawo sai anje amsar wannan sak'on da baya k'arewa tun ina yarinya nake ganin wannan sak'on daya k'i ci yak'i cinyewa" ta fad'a suna shigewa d'akinta da Nassar yayin da mama ta fice cikin sanyi jiki.
Suna shiga d'akin Nassar yace "wow Adda dama haka d'akin ki ya had'u gaskiya yafi nawa kyau sosai" yafad'a yana sufa agadonta, murmushi tayi tace "to ai kaine baka tab'a ahigowa d'akin nawaba" aikece Adda kullum cikin hantara ta kike kuma ni ina sonki tunda Ammey tace duk duniya bani da kamar ki dan ke kad'aice 'yar uwata JININA" jikinta ne yai sanyi ta k'arasa bakin gadon ta jashi jikinta ta rungume tace "kayi hak'uri kaji d'an uwa na nima daga yau na daina biyewa mama ina cin zalin tilon k'anina a duniya kaji ko"
"To Adda dan Allah Ammey nama ki daina zaginta kinga wallahi tana sonki sosai ko sallah nayi saita ce nayi miki addu a itama tanayi miki" yanzu kam jikin maryam yagama sanyi tajashi jikinta ta rungume tace "na daina insha Allahu k'anina kaji ko?"
"To Adda naji yanzu dai bani sweet d'in dan bazaki min wayoba sauri nake zanje muci gaba da ball d'inmu da su boy" murmushi ta saki ta d'ebo sweet d'in mai d'an dama ta bashi domin itama gwana ce wajen shan kayan zak'i
6:15 pm
Dai dai lokacin motar bros ta shigo gidan ya dawo daga airport d'aukar Baffa Nassar daya dawo yanzun daga sallah magrib yasan cewa andawo kenan daga d'aukar mahaifin nasu ne ai kuwa wani ihun murna ya saki ya taho da mugun gudu.
Yayin da MD yai saurin fitowa ya bud'e masa k'ofar nan naga wani farin dattijo kal kal ya fito daga motar fuskarsa k'awace da kyakyawan murmushin daya k'arawa fuskarsa kyau, farine sosai d'an siriri kyakyawan bafulatani nasha mamakin ganinsa na kuma fara hasaso haj. Sailuba dan ita bak'ace irin k'irin d'innnan koda wasa maryam batayo kamar Sailuba uwar taba saima kamar da sukeyi da haj. Amina matuk'a kamar itace ta haife ta.
Da sauri Nassar ya rungume Baffa yana murnan ganin sa wanda ihunsa ne yasa maryam fitowa a miliyan har tana bangaje MD ta afka jikin Baffa tana "oyoyo Baffana gaskiya Baffa munyi kewar ka da yawa ko Nassar?" Ta k'are maganar da tambayar sa, yayin da Baffa da MD suka bita da kallon mamaki dan sunfi kowa sanin cewa kwata kwata Maryam da Nassa basa zama inuwa guda, basu k'ara mamaki ba saida sukaji Nassar yace "eh Adda kuma gaskiya inya tashi komawa saidai yaje damu tunda ku kunyi candy ni kuma zan tafi secondry kinga sai musha hutunmu kusa da Baffan mu ko?"
Hannu ta bashi suka tafa sannan sukaja Baffan nasu zuwa cikin gidan yayin da MD wanda ya daskare da mamakin had'in kan daya gani tsakanin maryam da Nassar ya bi bayanau, aransa yana ayyana ina ma zasu d'ore a haka da sai yafi kowa jin dad'i sannan wahalarsa na son ganin had'in kan su zai k'are lallai zaici gaba dayi musu addu a kamar yadda ammeyn nasu ta buk'ata ya tabbata wata rana maryam zata bar abinda takeyi wanda kowa yasan cewa zugar uwar tane yake tasiri aranta.
K'yale Baffansu sukayi ya shiga fat d'insa yai wanka yai sallar magrib yana idarwa ana shiga isha dan haka ya fito suka wuce masallaci da MD da Nassar,
Yayin da maryam da mama suka gabatar da tasu hakama Ammey tayi tata anata d'akin sannan suka fito dirning domin cin abincin dare basu tab'a zaman cin abinci mai dad'in wannan ba tunda suka zauna ba babu fad'a da hayaniya tsakanin maryam da Nassar shi kanshi MD satar kallon ta yake tare da mamakin abinda ya sauyata cikin sauk'i haka.
Aban garen iyayen kuwa Ammey hakan ba k'aramin dad'i yayimata ba domin bata da burin daya wuce ganin had'in kan 'ya'yan nasu
Yayin da mama kuwa hakan yai masifar k'untata mata tayi wani kicin kicin da rai tana hararan maryam wacce ma batasan tanayiba domin sha aninsu kawai suke sha ita da d'an uwanata, yayin da zuciyar ta yake fad'a mata cewa lallai idan bata d'auki matamin gaggawa ba to shirinta na shekaru zai lalace dake ita ba mutum ce mai iya b'iye damuwa ba hakan yasa ta tashi a fusace tabar wajen tana dad'a d'aure fuska duk suka bita da kallo yayin da Baffa yatam bayi maryam ko anwa maman ta wani abunne"
Kagad'a ta motsa kafin tace "itafa mama bak'in cikinta dan taga mun shirya da Nassar ne mun daina fad'a ita kuma bataso shine kawai" dake maryam 'yar gatsal gatsal ce kuma duk inda gaskiya take fad'a take kai tsaye batare da shakka ko tsoron wani abuba.
"Ungo nan" cewar Ammey tana ma maryam irin zagin nan nabaza yatsu tace "yanzun dan gidan ku mamar takice 'yar bak'in ciki?"
"Eh mana Ammey muguwar 'yar bak'in ciki ma kuwa itafa koda wasa bataso taga na rab'i k'anina tafiso na zauna bani da kowa bani da abokin ahawara ni kuma daga yanzun na daina lamunta randa babu wani acikin ku kenan bazanyi huld'a da d'an uwana ba ina bazai yiyuba"
Baffa yace "ga wannan indai kina neman abokin shawara kika same shi ai kin gama dan haka ki daukeshi d'an uwa amini zai baki ki d'aukeshi yaya aboki kuma aminin ki zakiji dad'in hakan wata rana"
"Tab ina wallahi bazan iya ba wannan mai kama da maka ikan d'aukar ran kullum fuska babu annuri ni wallahi ina masifar tausayawa matar sa domin ta shiga uku da bak'in rai wallahi" duka Ammey ta kawo mata ta goce yayin da Baffa tace
"Kika san inda rana zata fad'i?"
"Nassar taso muje muci gaba da buga was an nan idan har kabari nayi winning d'inka saina zazzage bankinka ka yarda?"
Tak'are da tambayarsa
"Eh na yarda amma fa idan nina cinyeki zaki sa Baffa nima ya sai min computer irin naki" ita ma tace ta yarda suka bar wajen tana hararan MD k'asa k'asa, wani b'oyayyen murmushi MD ya saki Binta da kallo k'asa k'asa ta yadda zai wuya ka gane ita yake kallo.
Baffa ya d'an dube shi da damuwa yace 'Muhammad kafasan alak'ar dake tsakanin ka da ita dan haka ina so ka kawo k'arahen wannan bak'ar kiyayyar dan Allah na rok'eka" Baffa ya k'arasa yana had'e hannayen sa alamun rok'o iaka ya fesar batare dayace komai ba ya ture kujerar yabar wajen ba tare da yace komai ba, duk suka bishi da kallo, yayin da Ammey taji wani irin abu yana taso mata saiga idanun ta sun cika da kwallah Baffa ya dafe hannunta yana girgiza mata kai.
Sunan Baffa yasamo asaline tunda ga sunan kakan sa da yaci iyayen sa suka mak'ala masa Baffa shike nan Baffa ya bishi har zuwa yanzun da yaransa ma duk da hakan suke kiransa Baffa d'an gatane sosai awaken iyayen sa kasancewar sa shi d'aya rak hakan yasa yasami gado mai d'umbin yawa daga mahaifinsa bayan ya rasu gata da kulawa babu irin wanda bai samu daga iyayen saba yayi karatu tundaga matakin pir har zuwa dgreen sa na biyu duk afannin likitanci duk da kasan cewar su 'yan k'auye hakan baisa Inna da baba hana d'ansu karatun boko dana zamaniba yanzun haka yana da ilimi mai train yawa daga na zamanin har na wajibin.
Maman Islam ce
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥BA JININA BACE🔥
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 5
Tun bayan raauwar mahaifin sa ya samu aiki acikin gari ya baro k'auyen su babu yadda baiyi Innar sa ta dawo kusa dashi ba mursisi tace ita tafijin dad'in zaman can tunda da nan tasaba saidai ta had'ashi aure da d'iyar k'anwarta SAILUBA wacce ta rika tun bayan rasuwa k'anwar tata wacce ta rasu awajen haihuwar ta ta biyu lokacin Baffa yana matakin secondary dake bording school ce hakan yasa sai lokacin daya dawo suke had'uwa da ita.
Allah ya jarabci Sailuba da matuk'ar son Baffa saidai bata nunaba kasancewar ansa 'ya mace da kunya dan haka ta barwa ranta amma ta dage da addu ar neman zab'in Allah, itama tana danata ilimin daidai gwargwado domin ta kammala aji uku na wato k'aramar secondary sannan afannin addinin ma ta d'anyi nisa,
Koda wasa Baffa bai tab'a nunawa Sailuba cewa aurensu auren had'ine ba domin tun mahaifinsa sa na darai baya iya k'etare duk wani umarni da zasu bashi haka ma yanzu da ya kasance baya raye duk abinda mahaifiyar shi tasaka shi komai wahalar sa baya k'inyi mata
Dan haka yake shan albarka da addu o I kala kala daga mahaifiyar sa wanda yake ganin ci gaba arayuwar sa.
Tunda akayi auren su da Sailuba basu tab'a jin kansuba domin suna matuk'a zaman lafiya komai tare suke yi su kashe su binne tare yayin da Sailuba ta ganta a birni idanunta ya bud'e tafara k'awaye matan abokansa wanda daga baya takejin kanta ta wuce da ajinsu bazata iya alak'a dasu ba saboda d'aukakar da Allah yaiwa mijinta lokaci guda ta hanyar kasuwancin daya somo wannan kenan.
Matsalar farko da suka fara fuskanta shine rashin haihuwa lokacin da Inna taga an kwashe kimanin shekara biyar babu amo babu labari sai abin yafara damunta kullum bata da magana sai na son ganin 'yan jikokinta, tun Baffa baya damuwa shima har abin yasoma damunsa, magani kuwa suyi na gida suyi na asbiti,
Wata rana Sailuba ta kaima babbar aminiyar ta ziyara wacce tun zuwanta garin bata da aminiya sama da ita bayan sun gaisa tasa ankawo mata kayan motsa baki mai aiki ta gabatar mata dashi ta d'an dubi aminiyar tata Zakiyya tace "ni kuwa ina DEEDAH" babbar 'yar haj. Zakiyyan kenan murmushi tayi tace "humm Deeda rikici zakice min tana can d'akin ta tana faman kumbure kumburen banza wai sai nasa Abban ta yacanja mata mota, ni kuma banga abinda motar ta yayi ba shiyasa nayi banza da ita ta cika fitina yarinyar nan wallahi"
'Yar dariya Sailuba tayi tace haba Zakiyya tilon 'yar taki kikasayi mata wani abu gaskiya baki kyautaba tana ina ni tazo ta fad'amin duk kalar data ke so kiga aiki da cikawa" suka yi dariya yayin da haj. Zakiyya tace "kina shagwab'a yarinyar nan da yawa Sailuba ya kamatafa ace tasan cewa ba komai ne mutum yake so arayuwarsa yake samuba"
"Yauwa Sailuba ni kuwa ya batun maganin andace kuwa?"
"Wanne kenan cewar haj. Sailuba tana duban haj. Zakiyya na haihuwa mana" ta bata amsa cikin gaakiya da gaskiya wata 'yar banzar dariya ta saki tace "wai ke anfad'a miki duk wahalar da su Inna suke amfani nake da maganin?"
Kallon rashin fahimta haj. Zakiyya tayi mata sannan tace "ban fahimce kiba k'awata kina so kicemin duk wahalar banza mukeyi bakya amfani da maganin?"
"To mai zai dameni dan ban haihuba kuma ni gaskiya koda zan haihun ma ban shirya yanzun ba saboda haka kuma daina wahalar da kanku da kud'ad'en ku wajen nema min magani domin ba na amfani daahi"
"Ke kuwa mai yakaiki aikata wannan d'anyen acikin k'awata kuma naga ko ba komai ai 'ya'ya rahama ne bakisan wanda zaki moraba sai Allah"
"Nifa kin fara takuramin da wani wai haihuwa haihuwa ki k'yaleni mana dan Allah a a haka kawai nifa babu abinda na nema na rasa mijina bai tauyeni ba haka mahaifiyarsa nima uwata ce bata d'aukeni suruka ba dama can ni 'yar k'anwar tane kuma rainonta dan haka banga abinda zaisani wahal da kaina dole sai na haihu ba"
"Bakya tunanin wata rana idan mijin naki ya gaji yace zai auro wacce zata Haifa masa yara kinsanfa babu wanda bayason ganin kwansa a duniya?"
"Ke dallah saurara taya kike tunanin zan bari hakan yafaru"? Baffa bashi da wata mata a duniya bayan SAILUBA kisawa ranki haka sannan kisa aranki cewa duk yadda yakai ga son yara dole ya hak'ura tunda mahad'in rayuwar sa bata buk'ata kin gane?
Haka rayuwa tayi ta tafiya Sailuba da mai gidanta Baffa ana cin uwar soyayya yayin da inna taci gaba da damun kanta akan rashin jikoki shi kuwa Baffa ko ajikinsa acewar sa haihuwar ma lokacine.
Ana haka ya kammala k'asai taccen gidansa an an wata unguwa tsaka tsaki yabar jerin gidajen ma aikata ya koma nasa, hakan kuma yasa yasamu cigaba sosai dan yakan d'auki wasu daga matasan unguwar irin maau zaman ban zan nan ya bud'e musu wani kasuwancin hakan ba k'aramin kima da daraja yajawa Baffa a idanun iyayen yara ba suna matuk'ar ganin